Showing 171001 words to 174000 words out of 359620 words

Chapter 58 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2015

yasa su Aseef zasu kawo mishi mai laifi gida. To fa kada ku ga laifinsa, a kan dai'dai yake, doka ce dole a matsayinsu na masu doka su girmama dokan kafin na kasa da su subita, ba zai ce kada su kamata ba tun da shi bai san wacece ita ba, bai kuma san gaskiya a kan me ya faru ba, kuma kunga news ɗin da suka baza a gari a kan daɓa wa ABUBAKAR SALAHUDDEEN ɗin wuka ta yi a ciki, kuma ko su Aseef ne zasu yarda da yes ta daɓa mishi ɗin, dan kuwa a kan hanya suka ganta ana binta, basu san daga ina ta fito ba, sai dai idan sun yi bincike mai tsanani ne suna iya gane gaskiya, amma yanzu dai duk yarda zasu yi akan abin da ta yi kenan, babbar magana. WANNAN ABIN DA ƊAURE KAI YAKE AMMA MUKE ZUWA, DAN JIN DALILIN DA YASA AKA JUYA LABARIN YA KOMA KARYA, SUKA BINNE NA GASKIYAR.

Shigowa police biyu suka yi, mace ɗaya namiji ɗaya, in da su Jehan suke tsaye suka nufa, ko motsi Jehan ɗin bata yi ba, babu kuma alamar tsoro ko ɗigo a ranta, ita kuwa Rimsha ta tsorata sosai, sai ambatar sunan ta take yi tana tambayarta ko lafiya, su koma cikin ɗaki, amma ina ko motsawa Jehan ɗin bata yi ba, kamar wadda ta taki wata tsiya.

Kamata macen ta zo ta yi tana faɗin "Wuce mu tafi". Kankameta Rimsha ta yi tana kuka tana faɗin "Dan Allah kada ku tafimin da ita, wlh bata aikata laifin komai ba, dan girman Allah ku sake mini ita, wayyo Allah na, nashiga uku, daddy kazo ka hanasu tafiya da Jehan, zasu tafi da ita". Jehan ɗin kuwa, ko a jikinta tamkar ba ita ba, kamar bata san hukuma ne suka zo kamata ba, tsakaninta da Allah Rimsha take kuka kamar ranta zai fita, haka suka tafi da Jehan ɗin tana ji tana gani, da gudu ta koma cikin gida ta ɗauki wayarta dan ta kira su Areef ko daddynta, har wani jiri take gani, dama ga yunwa.

Number Areef ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a haukace ta kasa natsuwa ta fara gaya mishi abin da yake faruwa, zaro idanuwansa ya yi yana tambayarta dama tana da sister ne? Kenan gaskiyar Aseef da ya ce Sister ta ce?. Muryarta na rawa ta gaya mishi e tana da sister, su biyu daddy ya haifa, cikin kwanciyar hankali ya ce "To ya isa haka kuka, ba dai ƴar uncle bace? To kada ki ji komai dole ma su dawo da ita, bari na dawo muyi magana da Lion, wai laifin me ma tayi musu ne?" Da kyar ta iya furta "Ban sani ba, ban sani ba yaya Areef, kawai sun tafi da ita ne, kuma nima basu gaya mini abin da ta yi musu ba". "To shikenan ya isa ki kwantar da hankalinki, ina nan juyowa yanzu, na ma fasa zuwa wajen Heartbeat ɗin, Aseef zai je shi kaɗai, bari na hau abin hawa na dawo". Okey ta amsa mishi da shi, katse kiran ya yi dan baya son jin kukanta, Allah sarki bawan Allah.

Ɗaura wayar saman bedside drawer ta yi tare da kifa kanta da jikin gado tana mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, duk da ta yarda da Areef, tasan idan ya ce abu to zai aikata, sai dai hankalinta ya kasa kwanciya ne dan tasan idan Lion bai bada goyon baya ba, shi ma Areef ɗin dole ya hakura, abin da bata sani ba shi ne, His excellency dukkansu kakansu ne, suna da damar su ce mushi ga abin da suke so ya yi musu, sai dai wani hanzari ba gudu ba, abin da ya shafi doka, shi kanshi his excellency sai ya nemi jin ta bakin Lion, sai abin da ya yanke zasu yi amfani da shi, babbar magana, akwai kura fa.......

A wannan hali Areef ya shigo ya sameta, ko kaɗan bai ji daɗin ganin tana kuka har haka ba, rarrashinta ya fara yi tare da yi mata alkawarin kada ta damu dole sisterta zata fito da izinin Allah, amma bari ya yi magana da Lion zai je police station ɗin yanzu da kansa dan ya ji laifin da ta aikata da har zasu kamata, idan ma laifin babba ne to ya yi mata alkawarin zai tsaya tsayin daka ya yi bincike a kan case ɗin sai in da karfinsa ya kare, ma'ana sai in da hujjojinsa suka kare, dan yasan Lion ba zai taɓa tallafawa rashin gaskiya ba, duk wuya duk daɗi yana bayan gaskiya.... TOFA GASKIYA A WANNAN LAMARI BINCIKO GASKIYA BA KARAMIN WAHALA BANE A WAJEN AREEF, DAN JEHAN BATA DA SHAIDAR BA'A KAN HANYA TA KASHE ABUBAKAR SALAHUDDEEN BA, KUMA SUN ƊAURETA TA YADDA FITA ZAI YI MATA WAHALA, DOLE TA KAWO SHAIDAR A GIDA TA KASHE SHI GA KUMA DALILINTA, SAI DAI KUNA GANIN JENAN ZATA IYA DA WANNAN SHARI'AR? ZATA IYA KAWO SHAIDAR KUWA?

Da kyar ya lallaɓata ta yi shiru, miƙewa ya yi ya nufi bedroom ɗin Lion,. Zaune saman sofa ya isko shi yana.......

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️





E45-46💋




Da kyar ya lallaɓata ta yi shiru, miƙewa ya yi ya nufi bedroom ɗin Lion,. Zaune saman sofa ya isko shi yana latsa waya, kusa da shi ya zauna, cike da kulawa ya ce "Good morning". Shiru bai amsa mishi ba, dama ya san ba amsawar zai yi ba, dan haka sai ya cigaba da cewa "Zanje police station na dawo". Jinjina mishi kai ya yi alamar okey ya ji, "Idan na dawo zamu yi magana da kai". Nan ma jinjina mishi kai ya yi, ya kuma barshi ya shiga case ɗin ne dan ya gano Jehan ƴar Nawazudden ce, sai dai ko da take ƴarsa idan har bata gaskiya, to shi babu ruwansa, ba zai shiga rigimar ba, yanzu kuma ba zai yi bincike a kan case ɗin nata ba, dan a kan na babanta yake har yanzu tukunnan, da saura bai kammala ba, wani sabon babi ma ya buɗe a kan binciken nasa, idan baku manta ba, baya haɗa abubuwa biyu, ko wanne da lokacin yinsa, idan ya fara sai ya kammala yake capko wani, shiyasa bai damu ba dan Areef ɗin zai shiga, saboda shi ba zai shi ga ba sai ya gama wadda yake kai, ya kuma lura ana son nunawa yarinyar fin karfi ne, shiyasa ya kyasu da Areef ɗin.

"Me yasa ka yin faɗa jiya? Kuma da waye kuka yi faɗar?" Ya yi maganar ba tare da ya ɗago da kallonsa ba, "Waƴan da suka biyo yarinyar ne suka nemi yi mini ba dai'dai ba, shi ne na taka musu birki". Shiru ya yi tamkar ba zai sake yin magana ba, can kuma sai ya ce "Yana da kyau ka dai'na wasa da ciwon nan naka, ka san me zai iya biyowa baya idan har baka bari wajen nan ya warke ba, wajen zai iya ci ya tafi kai tsaye ya huda zuciyarka, yana da kyau ka kula sosai".

Jinjina mishi kai ya yi, dan shi ma ya sani, tabbas idan ya yi wasa da wannan ciwo, to rayuwarsa tana cikin babbar haɗari, sai dai fa ko mutuwa zai yi sai da ya mutu amma babu wanda ya isa ya taɓa Aseef a duniyar nan ya kyale shi, da wani suka daka zai iya kawar da kai, amma Aseef ba zai taɓa yiwuwa ba, sun mari kyakkyawa kuma lallausan fuskar da bata taɓa shan mari ba, da yake shi Areef ɗin bai san da cewa Lion ya taɓa marin Aseef ɗin ba, so yana ganin ai babu wanda ya taɓa kusantar wannan kyakkyawar fuska ko da sunan wasa da sunan zai mara.

Miƙewa ya yi tare da mannawa Lion ɗin sumbata a kumatu yana faɗin "Zamu je da Mark". Jinjina mishi kai ya yi tare da mai do mishi da martanin sumbata shi ma, kai TRIPLETS suna kaunar junansu na wuce misali wlh.
Waje ya nufa, kafin ya fita sai da ya sake komawa ɗakin Rimsha dan ya sake rarrashinta, nan fa ta kafe mishi a kan lallai sai ta bishi sun tafi tare, ba yadda ya iya, in dai yana son farincikinta to dole ne ya tafi tare da ita.

Hannunta ya kama suka nufi palon kasa, a kitchen ya isko Mark, nan ya sanar da shi zai jasu zuwa police station mafi kusa, okey ya amsa cikin girmamawa yana risinar da kansa kasa. Kai tsaye police station na kusa da su suka nufa, ita da Areef a gidan baya suka zauna, sai kwantar mata da hankali yake yi yana karfafa mata gwiwa a kan kada ta damu lallai Jehan ɗinsu zata fito, ɗan kwantar da kanta a kafaɗarsa ta yi tana lumshe idanu tare da shaƙar daddaɗar kamshin perfume nasa, hannu yasa ya ɗan shafa lallausan kumatunta yana faɗin "Sarkin saurin kuka, ya kamata ki zama jaruma, ke da kike da ni, ai bai kamata ki shiga damuwa dan ƴan'sanda su kama sisterki ba, kin san dole zan tsaya mata tun da ƴar uncle ce, ni kuma ki ɗauke ni tamkar Lion, dan in na tsaya dole Lion ya hakura shi ma ya tsaya, dan ba zai iya ganina cikin damuwa ba, ni kuma ba zan iya ganinki a cikin damuwa ba". Da irin waƴan nan daɗaɗan kalamai ya yi ta amfani wajen kwantar mata da hankali har ta saki jikinta sosai da shi.

Ko da suka isa police station ɗin, ƴan'sandan suka sanar da su ba nan a ka kawo ta ba, tana sama da su, tambaya ya yi suka yi mishi kwatance ya kunna goggle map suka ɗauki hanya, sai dai kuma abin mamaki ko da suka je wajen sai aka ce musu bata nan an wuce da ita kai tsaye prison, dan ba ƙaramin laifi ta aikata ba, bai tsaya tambaya me ta aikata ba ya ce da Mark su je prison ɗin, wani ɗan'sandan ne ya sanar da shi ai ba za'a bar kowa ya ganta ba, ko kallon in da suke bai yi ba, dan bai ga uban da ya isa ya hana shi ganinta ba, waya ya yi wa Lion a kan yana son ganinta, ya taimaka ya shirya haɗuwarsu kafin su isa prison ɗin, da farko kamar ba zai yi ba, sai kuma tunanin kyautata musu da irin tsantsar kauna da daddyn Rimsha yake nunawa TRIPLETS nasa ta faɗo masa, ya kuma tuna irin Kaunar da TRIPLETS ɗin suke yi wa daddyn, hakan yasa ya amsa da okey tare da ciro waya kai tsaye ya kira president na Nigeria, dan yanzu Already sun san da yana cikin kasar, sun san shi ne ya zo, so mafiya yawan lokuta baya kiran His excellency a nan kawai yake shirya duk abin da yake so.

Ko da suka isa prison da aka kai ta, wani ganduroba ne ya yi musu jagora zuwa ciki, sai mamaki Rimsha take yi, wai ba da ance ba za su sami damar ganinta ba? To ya aka yi da kansu suke yi musu jagoranci zuwa ciki kuma? Sai tambayar kanta take yi, bata san cewa duk da ba kasarsu bace suna da daman yin abin da ya fi ɗan kasa, saboda sun fito daga babbar kasa, kuma ga His excellency ai dole ma a yi musu abin da ya fi na ɗan kasa, sun fi ƴan kasa samun ƴanci.

Office ɗin ogansu ya wuce suka zauna, idan ba dan su manya bane, yaushe za'ace yarinyar da ta kashe ɗan takarar shugaban kasa ace har wasu zasu iya samin damar ganinta, kai abin da abin mamaki.

Har cikin office ɗin Mark ya bisu, dan hakki ne a wuyarsa da ya kula da Areef kada ya bari wani abin ya taɓa shi, saman doguwar kujerar dake cikin office ɗin Areef da Rimsha suka zauna, shi kuma Mark yana tsaye tamkar wani robot.

Ba'a ɓata musu lokaci wajen fito da ita ba, da gudu Rimsha ta miƙe zata je wajenta, cikin sauri Areef ya riƙeta yana girgiza mata kai, shi tun daga farkon case ɗin ma ya fahimci akwai zalinci a ciki, na farko a kallon da ya yi wa jenan bata kai shakarun da za'ayi mata irin wannan hukuncin ba, na biyu yadda suka zuba mata tsaro kamar wata kungurumiyar ƴar ta'adda, na uku yadda suka wuce da ita prison kai tsaye tamkar dama jira suke yi su kamata, akwai wasu kananan dalili dai, amma waƴan nan sune manya, yadda case ɗin nata ya tafi ma sam ba tsari, dan sun yi abin ne a yunwacen suna son kamata, sai kuma suka fitowa da duniya hakan, mai basira tsab zai iya gane ina suka dosa, sai dai fa Areef bai damu sosai ba, dan yana ganin kamar mu kuma dokokin kasar mu ce a hakan kenan, shiyasa bai damu ba, ya fi son ya ji magana daga bakinta, dan ya yi imanin gabaɗaya jikin Nawazudden ba zasu yi karya ba, ya yarda da su, ya yi wa Uncle nashi kyakkyawar yarda.

Kasan carpet dake wajen ta zauna, hannunta na sanye cikin sarka wadda ya tafi har kafarta, shiru Areef ya ɗan zubawa sarkar idanu yana kallonsu, shi dai ya san gunguma gunguman ƴan ta'addan kasa da kasa suke ɗaurewa da irin wannan sarka, amma an tashi an lafkawa ƴar yarinyar da bata wuce goyo ba a cewarsa.

Wani ganduroba ɗaya daga cikin waƴan da suka fito da ita ne ya ce "Sir kuna da only 10 mins". Bai bi ta kansu ba, dan bai ga uban da ya isa ya saka mishi time a rayuwarsa ba, idan suka yi wasa ma sai ya ce ba zai bar nan ba sai da ita ya ga karshen iskanci, idan ya ce lalllai ba zai tafi ba sai da ita, ai dole Lion ya zo, kuma dole His excellency ya saka baki, dan sufa kasar American tsuntsuwar kasarsu ma ranta na da muguwar daraja bare kuma mutun ɗan cikin kasarsu, mutun ɗin ma jika ga His excellency ai dole ma su tursasa kasar Nigeria a bawa Areef Jehan dan ya bar wajen kada wani abin ya same shi, amma ba zai yi hakan ba, dan yasan doka kuma ba zai taka ba, saboda suke faɗa kullum abi doka, suke kama masu karya doka su hukunta, to idan su basu bi ba, waye zai bi kenan? Ai kowa ma take dokar zai yi, idan ba doka kuma ai ba al'umma.

Cikin sanyin murya ya tambayeta ya sunanta, kin magana ta yi, tamkar bata ji shi ba, sai kallon kasa take yi abinta, kallon Rimsha ya yi yana faɗin "Our Queen bata magana ne?" "Wlh tana magana yaya Areef, bari ka ji na tambayeta". Sauƙowa kasan ta yi kusa da ita, tana hawaye ta fara magana tare da riƙo hannunsu cikin na juna "Jehan dan Allah ki yi mishi magana, ki gaya mishi gaskiyar abin da ya faru, wlh zai taimaka miki, kinga shi ya taimaka mini ya kuma taimakawa daddy, nasan kema ba zai barki ba". Jin ta ambaci daddy yasa Jehan ɗin ɗago dara daran idanunta da suke farare tas babu ko alamar ɗigon hawaye, suna bushe garau kamar bata san me ake tuhumarta da shi ba, har wani haske idanun nata ma suka kara, shi kansa Areef ya sha ruwan mamaki dakiya irin nata, gata yarinya karama, ga ta a prison, sannan jikinta duk ya sha sarkuna a ɗaure kafa da hannu, amma a haka ko a jikinta, bugu da kari gata mace, abin dole a jinjina mata, kuma ayi mamaki, idan da wata mace ce ai ta rinƙa ihu kenan ganinta a hannun hukuma.

Shi ma dai sauƙowa ya yi dan ya kama Rimsha ta dai'na kuka, mamaki ne ya kama Mark yadda Areef yake bala'in kaunar su Rimsha, ko a mafarki bai taɓa tunanin ɗaya daga cikin TRIPLETS zai yi hakan ba, ya sauƙo ya zauna a saman carpet sabida Rimsha, abin dole ga wadda ya sansu a baya ya yi mamaki over.

"Jehan wlh daddy ya yarda da shi sosai, ki yi mishi magana kin ji". Cewar Rimsha, kuma da harshen Hausa ta yi maganar nata, jinjina mata kai Jehan ɗin ta yi alamar to. "My name is Jehan Nawazudden Salman Sultan". Ta bashi amsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan kuwa har voice nata sak na daddynta ne, babu in da ta baro shi, hannun Rimsha ya kama suka koma saman sofa suka zauna, baya son ganinta tana kuka.

"Okey Jehan zaki iya gaya mini a kan wani laifi suke tuhumarki da kuma gaskiyar abin da ya faru". Ba musu ta gaya mishi a kan laifin kisan kai suke tuhumarta da shi, ba ƙaramin tsorata Rimsha ta yi ba, shi dai Mark ya zuba musu idanu ne yana kallon ikon Allah, Jehan na magana kamar wata babbar jarumar soja, babu tsoro ko ɗarɗar a muryarta, kai tsaye ta ce kisan kai lallai.

"Okey to da gaske kece kika yi kisan ne?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e ita ta yi, Rimsha bata san lokacin da ta kurma ihu ba, da karfi ta ce "Wlh karya ne, ni nasan wacece ƴar uwata, tana da faɗa sosai, amma wlh ko kaza ba zata iya kashewa ba, karya ne". Rungumota Areef ya yi yana ƙoƙarin miƙewa dan komai ya lalace tun da Jehan ta amsa da bakinta ita ta yi kisan, shikenan kuma. Har zai miƙe sai kuma ya koma ya zauna yana karewa Jehan ɗin kallo, yarinyar nan ko a jikinta wai an yakushi kakkausa.

Mark ne ya yi gyaran murya cikin girmamawa ya ce "Sir am sorry to say amma wannan yarinyar ba ita ta yi kisan nan ba, ko da ita tayi to akwai dalili mai karfi ko kuma by mistake ne". Jinjina mishi kai ya yi alamar ya gamsu, shi ma ya yi tunanin hakan shiyasa ya fasa tafiya ya dawo ya zauna, cikin sanyin murya ya sake tambayarta ko zata gaya musu ya akayi ta yi kisan, nan ne kuma Rimsha ta yi shiru ta nitsu tana son jin ta ya akayi hakan ta faru.

Ba musu ta gaya musu tsab, sai dai bata gaya musu daga ina ya ɗauko ta ba, ta dai ce musu ya ɗaukota ne da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login