Showing 300001 words to 303000 words out of 359620 words
zalika labarina ko in ce labaraina dan har da na gaba in da rai da lafiya, labaraina salonsu daban ne da kowa, labarina ya wuci nan🤪👊 ku dai jira, anya kun taɓa......... Bari dai na barku sai mun haɗu a next book ɗin kawai, akwai tashin kwakwalwa dan fa shi da dafasa yake tafe ba da zafi ba, tafasa yake yi!!!!!.)
Miƙewa ya yi tare da riko hannunta yana faɗin "Uncle ya bada izini zo mu je ki busar mini ko?". Ɗan kallon daddyn ta yi, jinjina mata kai ya yi a kan ta je ba komai, mamaki take yi yanda daddyn nata yake haɗa ta da wani namijin da ba muharraminta ba, abin ya fara ɗaure mata, ita dai tasan tun suna yara daddy yake tsawatar musu a kan maza, amma how comes zai ce ta rinƙa bin wani yanzu kuma?.
Bedroom nasa ya wuce da ita, a nan ta ga abin mamaki, duniya guda, komai yana nan clear tamkar sabo, sai tashin kamshi komai yake yi ga hasken wuta ta ko'ina a cikin É—akin, saman mirror chair ya zauna tare da zame pil da yake rike mishi da gashin nasa ya sake ta zuba mishi har tsakiyar gadon bayansa, wani irin kyau ya kara sosai, ya tafi da imaninta sosai. Nuna mata in da hand dryer yake ya yi, ba musu ta É—auko ta dawo kusa da shi, jonawa suka yi yana faÉ—in to ta fara busar mishi.
Ai da sauri ta fara dan tana bala'in son taɓa gashin nasa, ya yi matukar burgeta, kamar wata mace har tsakiyar bayansa, ga tsantsi a kwance luf, zuba mata idanu shi kuma ya yi ta cikin mirror yana kallonta yana jin tsantsar daɗin yanda take cakuɗa gashin nasa.
Ya shagala da kallonta bai san lokacin da ta kammala ba, sai dai gani ya yi ta ajiye dryer tana ƙoƙarin nufar hanyar fita, da sauri ya riko hannunta yana faɗin "Saura ni kuma na busar miki da naki". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin ita bata so zata je ɗaki ta yi wa kanta. "Haba baby bafa haka boyfriend and girlfriend suke yi ba, please ni ki zauna na yi miki kin ji ko babyna?". Ba dan ta so ba ya miƙe daga wajen ita kuma ta zauna.
Da hannunsa ya zame mayafin kanta tare da ɗauko dryer ya fara busar mata, har cikin ranta take jin tsantsar daɗin hakan. Tsab ya busar mata kafin ya ajiye dryer tare da kasheta, tana ƙokarin ta miƙe dan ta tafi ya mayar da ita yana faɗin "Wait for me mana, ai ban gama ba, ke ce kika yi mini rowa kika ki gyarawa boyfriend naki gashinsa da kyau, amma ni ki jirani ki gani". Shiru bata ce da shi komai ba.
Mayukan gashinsa ya ɗauko ya fara shafa mata a kan nata tare da turaren gashi, nan take gashin ya fara kyalli yana wani kara tsantsi, bayan ya kammala ya tara a bayan wuyarta ya sanya pil nasa ya kama mata da shi, a hankali ya kwanto da kansa a saman kafaɗarta tare da matso da face nasa kusa da tata sannan ya ɗago idanu yana kallon kansu a mirror, sun yi matuƙar kyau da ɗaukar hankali over, sun dace fiye da tunanin mai tunani, kasa ta yi da nata idanu duk da tana son kallon fuskokin nasu, ita kanta sun burgeta bare kuma shi da ya jima a cikin kogin sonta.
"My baby you are really beauty over wlh, gaskiya na yi dace, please É—ago idanu ki kalle ni mana, kada ki yi mini musu game muke yi". Bata san time da murmushi ya subce mata ba, wato ya san zata yi musu kenan shiyasa ya yi saurin cewa kada ta yi mishi musu game suke yi, kai gaskiya Areef ya gama karantarta tsab ba kari.
Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a gefe da gefen wuyarta tare da ɗan masto da lallausan laɓɓansa kusa da kunnenta ya fara magana can kasa kasa kamar mai raɗa. "A duk lokacin da kika yi murmushi ina ji na tamkar ba'a duniya nake ba, gaskiya murmushinki yana yi mini kyau over my baby". Abin ku da zuciyar mace, duk in da mace take tana son yabo, shiyasa ya yi saurin tafiya da imaninta.
"Yanzu dai ɗago idanu ki kalleni kin ji my beauty?". Ɗan ɗago idanunta ta yi tana faɗin "Ai kai ma kana da kyau sosai". "Da gaske?" Jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatarwa, "Amma ai ban kai ki kyau ba ko?". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Seriously ka fin....." Bai bari ta karisa ba ya rufe mata baki da lallausan hannunsa yana faɗin "Zaki yi saɓofa". Shiru ta yi bata yi magana ba, dan har ga Allah bata son yawan magana, kawai dan ya ce game ne yasa take ƙoƙarin taga ta yi magana, ya ce mata idan bata yi mishi kamar yanda yake yi mata ba, to ta faɗi game ɗin, ita kuma bata son faɗuwa sai dai nasara, shi ne yasa ta dage, amma ba dan haka ba, wlh Jehan bata da yawan magana sam, bata ma iya surutun ba.
"Baby meyasa kika yi shiru?". Babu komai ta bashi amsa, zuba mata idanu ya yi yana jin tamkar kawai ya yi kissing nata, amma ina bayason hakan a tsakaninsu yanzu har sai ta fara son shi sosai. "Yaya Areef in tafi É—aki?". Ya É—an É—auki lokaci kafin ya ce "Babyn baby ne sunana, ki daina ce mini yaya now we are playing a game, ni ba yayanki ba ne a wannan wasa, ni babynki ne, dan haka call me baby direct".
Nisawa ta yi kafin ta ce "Baby zan iya tafiya É—aki?". "Har kin gaji da nine my baby?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a. "To why kike son ki tafi É—aki?". Bata son ce mishi saboda tsare mutuncinta ne, sai ta ce mishi "I want to go and do something, ina jin sanyi over, kuma kaga ka ce zan raka unguwa ko?". Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce "Haka ne my baby, to shikenan I will going to miss you, ki kula mini da kanki, i really love you more than your expectations". Kasa kasa ta bashi amsa tun bai tambaya ba, dan tasan zai tambaya É—in.
"I love you too my baby". Wani irin daɗi ya ji sosai, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa dan tsabar murna. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar fita, tana son ta juyo ta kalle shi, amma kuma bata son ta juyo su haɗa idanu, dan ta san confirm yana kallonta, haka dai ta daure ta fita ba dan ta so bata samu damar sake kallonsa ba. Shi kuwa ya tsareta da idanu ta cikin mirror har ya fita.
Tana fita ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da nufar toilet dan ya yi wanka saboda ruwan saman da ya jiƙasu, ita ma toilet ta nufa lokacin da ta shigo ɗakin nasu kenan dan ta yi wanka.
A ɓangaren Rimsha kuwa, sai misalin karfe 10 na safe ta farka daga barcin farincikin da ya ɗauketa, a hankali ta waro idanunta waje, baya ɗakin ya fita, miƙewa zaune ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon kafin ta miƙe tsaye gabaɗaya, toilet ta nufa, a gurguje ta yi wanka tare da fitowa ta nufi wajen trolleys nasu.
Wasu shegun riga da wando ta É—auko, wandon jeans ne pink color mai rastin fari a jiki, daga ta saman wandon ya kamata sosai a in da ya bayyanar mata da kyakkyawan shape nata, kasan kuma a buÉ—e yake kamar palozo, rigar kuma high neck t-shirt ne wanda jikinsa gabaÉ—aya roba ce ta kamata sosai launin fari tas, ta sanya vest daga ciki kafin ta sanya rigar, kasan cewar babu É—an kwali a cikin akwaitin sai ta gyara gashinta ta hanyar amfani da mayukansa, ta sako shi har bayanta yana wani kyalli, ta yi kyau over, perfume nasa ta É—auka ta sanya a jikinta dan bata ga nata ba, dama guda É—aya ya É—auko mata, so ya shige cikin kaya sai ta saka nasa kawai, bedroom slippers nasa ta sanya dan ita bata da shi.
Bedroom É—in ta gyara musu tsab tare da gyara musu gado kafin ta feshe É—akin da wani shegen daddaÉ—ar air freshener mai tashin kai da kamshi, ta kara gudun Ac sannan ta sake komawa wajen trolleys É—in ta kara gyara jikinta.
Ba karya ta haÉ—u iya haÉ—awa, ta saki gashin nan tamkar ba Indiya, ta so ta É—an yi simple make up, sai dai babu kayan make up É—in a cikin trolleyn. Haka ta nufo waje, ga abinci a saman table a jere, an jera musu komai tun kafin ta tashi, amma sam bata bi ta kan abincin ba ta nufi waje.
Wani ni'imantaccen iska mai matuƙar daɗin gaske ne ya fara kaɗata tun lokacin da ta sako kafarta wajen bedroom ɗin, ɗan waige waige ta fara yi tana wani lumshe idanu saboda daɗin iskan. Can ta hango mijin nata yana tsaye ya goya hannu a saman faffaɗar kirjinsa yana kallon ruwa ya bata baya tamkar mai tunanin wani abin, jikinsa na sanye da pajama launin sky blue mai matuƙar kyau, a ko da yaushe yana nan tsab tamkar a lokacin yake ciro kayan da zai yi amfani da su daga laida saboda bala'in tsabtarsa.
Da sauri ta karisa wajen da yake tana tunano maganar Akila da take cewa idan yana tsaye ki rinƙa hayewa jikinsa babu abin da zai yi miki, haka kuwa aka yi, tana zuwa ta rungume shi ya baya tare da kwantar da kanta a saman bayansa, tamkar abin haɗin baki a tare gabaɗaya sojojin nasa suka juya musu baya, tamkar waƴan da ya bawa umarni, haka suka yi maza suka juya baya dan ma kada su kallesu, abin ya yi mugun burgeta ya kuma bata mamaki yanda ya zamana sun juya a tare tamkar waƴan da aka bawa umarni.
Shi kuwa nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke ta wani kwantar da kanta a saman bayansa, a hankali ya juyo da jikinsa gareta, wani irin sanyi ya ji a cikin zuciyarsa lokacin da ya É—aura idanunsa a kan kyakkyawar fuskarta, fara kallonta ya yi from head to toe, babu karya ta haÉ—u, ta kuma jijjiga daular birnin zuciyarsa, musamman yanda ta saki gashin nan nata tamkar wata Baturiya.
Ganin ya tsareta da idanu ne yasa ta faɗa saman kirjin nasa tana faɗin "Good morning my lovely brother". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai kuma can kasa kasa, ɗaga idanunsa ya yi a in da ya kai kallonsa kan sojojinsa da suka juya musu baya har da runtse idanu bayin Allah, shi Mark dama yana cikin ɗaki ya samu damar magana da Anaya ta wayar mummynta, sai yau ya gane number mummyn nata tun lokacin da Lion ya bashi wayar, abin ka da ba wayarka ba, ba kuma ka san da wani suna aka yi saving number ba, bai kuma isa ya zo ya ce zai tambayi da wani suna aka yi saving ba, shi ne kawai ya yi ta nema bawan Allah sai yau ya gane, so yana ciki suna zuba soyayya da beb nasa.
"Yaya Saif ba zaka amsa gaisuwa ta bane?" Wannan karonma a shagwaɓe ta yi maganar, hannu yasa ya ɗauketa cancak zuwa saman kirjinsa suka nufi cikin bedroom nasa, dan kuwa ita kaɗai ya canzawa, bayan ita babu wanda ya ga alamar canji ko da sunan wasa a tattare da shi, hakan yasa ma ya ɗauketa suka nufi ɗaki dan kada ma ya yi magana sojojin nasa su ji, sai dai fa suma sojojin sun san ogan nasu ya faɗa tarkon son ƙaramar yarinya, dan kuwa babu wata mace a duniya da ta isa ta tinkare shi ma bare kuma har ta kwanta a jikinsa haka ba tare da ya yi wurgi da ita a cikin wannan ruwan tekun ba, amma ita Rimsha lafiya lou ta kwanta, ga shi kuma har da ɗaukarta ya yi suka wuce ciki, ko daga nan sun san oga fa ya shiga tarkon mata.
Bai direta ko'ina ba sai saman bed nasu, in da ya kwanta da ita a jikin nasa, ya ji tsantsar farinciki na yanda ta gyara gadon nan fes ga wani daddaɗar kamshin air freshener da ta fesa musu mai kwantar da hankalin mai shaƙa.
"Kada ki sake fita wajen nan ki na ji na?". Ya yi maganar cikin bada umarni kamar baya, kuma ya yi maganar yana ɗaure fuska sosai. Jinjina mishi kai ta yi tana amsawa da okey, ya bata tsoro yanda ya ɗaure fusataccen fuskar nan nasa yana magana, dama ga fuskar kullum a ɗaure, idan ya kara ɗaurewa har wani fitsari take ji, ta sha jinin jikinta, shi kuwa sam lokacin da ta zo ta rungume shi bai ji daɗi ba, kawai ba zai iya daka mata tsawa ko makamancin hakan ba ne yasa ya kyaleta, amma sam bai so ta rungume shi a gaban sojojinsa ba, saboda shi baya son raini ko kaɗan, ko da yake rungumarta a gaban su daddy, ya san ko giyar wake suka sha basu isa su yi mishi wani magana ba ne, kuma a cikinsu babu mai karfin gwiwar da zai iya ɗaukarsa a hoto ya ɗaura a media duniya ta gani saɓanin idan tana rungumarsa a waje gaban kowa, za'a iya samun wani ya ɗauke shi hoto ta ja mishi raini.............. Tab Lion duniya, amma dai ka yi kokarin da ka iya canza mata ita kaɗai ɗin ma, dama ita kaɗai ya kamata ta ga wasu abubuwa naka, a matsayinka na babba a cikinsu kam dama bai kamata ta ja su rai'naka ba.
Bugu da kari ga bala'in kishin yanda ta fito ta wuce sojojin ta zo in da yake, ya ji kishi sosai, shiyasa ya ce kada ta sake fitowa waje baya so.
Yunkurawa ya yi zai sauka daga gadon zai kuma sauketa daga jikin nasa ya fita waje, cikin sauri ta kara ƙanƙame shi tana faɗin "Yaya Saif to ai baka amsa mishi gaisuwar tawa ba". Komawa ya yi ya kwanta yana kare mata kallo. Shiru ta yi dan taga gudun ruwansa, shin zai amsa ne ko zai cigaba da kallonta ne kawai.
Almost 5 mins suna a haka bai ce ko uppan ba yana ta kallonta, kukan shagwaɓa ta saka mishi tana turo ɗan bakin. Nisawa ya yi a nutse ya fara magana. "A duk lokacin da nake tare dake, wlh Aseef ne kawai yake yi mini yawo a cikin kwakwalwata, ina kewar shi sosai, duk wani abin da yake yi mini na tsiya shi kike yi mini yanzu, that is the reason why nake jin daɗin ganinki a kusa da ni". Ya yi maganar a sanyaye cikin natsuwa da kwanciyar hankali, babu wata hayaniya a voice nasa.
Cool murmushi ta sakar mishi tana faÉ—in "To shikenan ka É—auka ni ce shi, dama kuma ai ni renonsa ne". A yanzu ma yanda ta yi maganar kamar Aseef É—in, tana yi tana turo baki, yatsa É—aya ya tura mata cikin dimple nata yana kara jawota jikinsa, duk sai ya ji yana bala'in kewar TRIPLETS nasa, wani azababben son su ne yake karuwa mishi a cikin zuciyarsa bawan Allah.
Hannu ta kai ta kama É—an guntun gashin nan nasa dake gaban goshinsa tana wasa da shi, shi dai shiru ya zuba mata idanu dan bai san me zai ce ba, bai wani iya dogon magana ba, sai dai idan ta yi ya bata amsa, amma dan kansa kam bai san me zai ce ba.
Wayarsa ce ta yi kara, ɗaukowa ya yi, Video call ne kuma TGA ne yake kiransa, su dai sun fi jin daɗin su yi video call suna kallon juna. Ganin hoton TGA yasa ta ce "Yaya Saif wannan TGA ne ko?". Ɗan zaro idanunsa waje ya yi yana mamakin a ina kuma ta san TGA?. Ba ƙaramin tsoratata ya yi ba yanda ya zaro idanun nan nasa, runtse nata idanun ta yi. Katse kiran ya yi tare da ajiye wayar, yana wani abin ba zai yi wani ba.......... LION DUNIYA WATO YANA WANI ABIN BA ZAI YI WANI BA.🤣🤣 KO DA YAKE DAMA WANNAN DOKARSA CE BAYA HAƊA ABUBUWA BIYU LOKACI GUDA, A TSANAKE YAKE KOMAI.
"A ina kika san TGA?". Ya tambaya yana tsareta da idanu. Labari ta fara bashi cikin shagwaɓa tun kallonsu da take yi a Tv lokacin tana ƴar shekara 9, yanda aka yi ta iya banbanta su da yanda ta yi ƙoƙarin banbantawa ƴan gidansu su kowa ya kasa ganewa sai ita kaɗai, ita kaɗai ta iya rabesu, da yanda aka yi ta fara zanensa, dukka ta bashi labari. Shiru ya yi ya kuma sha jinin jikinsa gaskiya, bai taɓa tunani a duniya bayan TRIPLETS nasa za'a samu mai yi mishi mahaukacin soyayya irinta ba, tub tana 9 years, kai, kai, kai, kuma har ta iya rabe shi da TGA abin da ko mutane a waje basu iya rabesu, idan ba a tare ka gansu ba ba zaka iya rabasu ba, idan suna tare suna da banbanci sosai, amma idan ganin daban daban zaka yi musu ba zaka taɓa ganin banbancin ba, amma ita har ta iya ganewa ba tare da ta taɓa ganinsu a tare ko ta taɓa ganin face nasu babu face mask ba, lallai tabbas ta cancanci a jinjina mata.
Sai dai kuma fa ya ji a jikinsa wannan kaifin kwakwalwa da take da shi tabbas irin nasu ne, irin kwakwalwar TRIPLETS gareta, tamkar wata twins, dama da TWINS da TRIPLETS Allah ya basu baiwa over, mafiya yawan lokuta abin da zasu yi ba kowani É—an adam ne yake iya yin shi ba, ga su da kaifin kwakwalwa kamar ba gobe, sai dai idan basu sami kula bane kwakwalwar da basirar tasu take tafiya a banza, amma wlh baiwa garesu na wuce misali, ga shi wani abin cutarwa baya saurin kamasu, Allah yana tsaresu.
Tunanin cewa daddynta TWINS ne ya faɗo mishi, tuna hakan yasa ya ce kila kwakwalwar daddyn nata ta gado, shafa kanta ya yi ba tare da ya yi magana ba yana tunanin yanda Areef ya rinƙa bashi labarin yanda ta iya rabesu shi da Aseef, ko a cikin duhu suka yi magana tana iya rabesu, abin da ko daddynsu baya iya rabe