Showing 261001 words to 264000 words out of 359620 words

Chapter 88 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

3096

niyar idan suka tashi taro sai ya kirata sun yi magana, dan duk yanda akayi wannan ƴar Hosain ɗinsa ne, tana kama da mummynta da yake tare da ita a gidansa yanzu, shi daddyn Rimsha ya ga kalli Hassan ɗin nasa, amma kun sani dama can yaki yardan musu da shi ne Hosain, dan haka sai bai kula daddyn Anaya ba, ya yi kamar ma bai ganshi ba, Anayar kawai yake ta kallo, ta girma sosai, hotonta da yake da shi lokacin bata wuce 12 years ba, yanzu kuma 16 years take da shi, har cikin ransa yake jin kaunar Anayar dan kamanninsu ta ɗauko, irin Jehan ce sak, da daddyn Rimsha da daddyn Anaya fa ba karya akwai kamanin, da suke yara ma ba'a banbantasu, sai da suka girma ne kamannin ya ragu, to haka Jehan da Anayar suke kamani, ga su dai ba twins ba, amma kowa ta ɗauko babanta, sai suka zama twins ɗin kawai.

Gabaɗaya malaman makaranta sai da waƴan nan jibga jibgan sojojinsa da zasu tafi da su Russia suka kamasu, dukkansu sai da suka sanyasu suka zube gwiwowinsu a kasa, yau dai anyi yaki a cikin school ɗin, ba wanda hankalinsa bai tashi ba, shi dama uncle Faisal tun washe garin ranar da ya kira Rimsha a waya ya wuce gadon asibiti, dan Mark ne ya yi mishi wani ɗan iskan duka bisa umarnin Lion, yanzu ko in da kansa yake ma bai sani ba, so baya school ɗin.

Tun da TRIPLETS suka ga abin da yake faruwa, tun da suka ga sojojin sun san lallai an yiwa Lion ba daidai ba, shi kam Areef ya san komai dan ya bisu wajen, sai da ya kalli sun nika Mr Emmanuel lilis ne ya dawo cikin hall ɗin ya rasa ma me zai ce da su Aseef.

Tambayarsa Aseef ya yi a kan me akayiwa Lion yasa aka kama malamai gabaɗaya? Ba ɓoye ɓoye Areef ɗin ya sanar musu da abin da yake faruwa, sosai daddy ya shiga tashin hankali, a hanzarce har yana haɗe words ya tambayi Areef ɗin amma babu abin da ya sami Rimsha ko? Basu yi mata wani abu ba ko? Babu abin da suka yi mata Areef ɗin ya bashi amsa, Allah sarki uba mai daɗi, shi dai burinsa ya ji babu abin da akayi mata kawai.

Da mamaki Aseef ya tambayi Areef ɗin to su kuma malaman makarantar me ruwansu da za'a haɗa da su, a kule Areef ɗin ya bashi amsa da cewa "Akwai ruwansu kam azzalumai, ace suna da malami irin wannan mai lalata ɗalibai kuma su ce basu sani ba? Ai yau ni zan yankewa shugaban makarantar nan abin da baby ta yankewa wancan kazamin".

Jinjina kai Aseef ɗin ya yi tare da riko hannun heartbeat nasa suka nufi hanyar fita daga cikin hall ɗin, dan ya je wajen motarsu ya duba ɗan uwansa, cikin girmamawa sojoji biyu da suka tare bakin hall ɗin suka bashi hanya suna sara mishi.

"Uncle muje wajensu Lion, tsayuwa a nan sam bai dace damu ba" . Ya kai karshen maganar tare da riko hannun Jehan dan su nufi waje, bata kwace hannun nata ba, dan kuwa tana bala'in tsoron sojijin da suka tare kofar nan, kada ta je ta kwace hannunta su hanata fita, sai kawai ta bishi suka nufi wajen. Suna fita ta kwace hannunta, shi ma bai wani damu ba, burinsa kawai su isa ga Lion.

Tattare malaman gabaɗaya sojojin suka yi, sauran students da parents nasu kuma suka rufesu a cikin hall ɗin.

Lion yana tsaye yana waya cikin fushi, da alama a kan tafiyar tasu yake magana, zasu bi jirgi sama ne zuwa Lagos, daga nan sai su shiga jirgin ruwan, so an gama shirya komai shi kaɗai ake jira, sai kiransa suke yi a waya, shi ne suka kara ɓata mishi rai yake kwashe musu albarka da kyau da kyau.

Tsayuwa su Aseef duka zo suka yi kusa da shi, Akila ta kankame Aseef sosai saboda tsananin tsoron Lion, bare ma yanda taga face nasa yau, ai rike mijinta kam ta yi abinta, daddyn Rimsha da Areef kuma sun jingina da jikin motarsu Tyrone suna kallon Lion ɗin, yau fa Jehan kusa da Areef sosai ta tsaya saboda tsoron Lion, tasan ko daddynta bai isa ya yi magana ba, so gara mata Areef ɗin dai duk bala'i, ta san dai idan ta kama shi shi ne ta kama dahir...... Wayyo rashin kunya ma ashe waje yake samu.

Ganin yanda Lion yake magana cikin fushi da faɗa faɗa ne yasa Jehan ɗin ta yi mugun tsorata, dama tsoronsa kamar ta mutu, yau kuma ga shi ya kara ɗaure fuska over yana faɗa, sai dai fa duk faɗan da yake yi kasa kasa yake magana, bai iya ɗaga murya a magana ba sai idan ya zama dole.

Bayan ya kammala wayar ne ya juyo garesu, ganin daddy a wajen yasa zuciyarsa ta kara hasala ba kaɗan ba, cikin fushi ya nufo daddyn, a kausashe ya ce da shi dama kenan yana ganin Rimsha ta fita da irin shigar jikintan nan?! Ga sarin ma bai gama rufe mata cikinta ba, wato ya san komai ya zuba mata idanu ko? To tukun nan ma me ta je yi a office ɗin Mr Emmanuel? Dole yau su karɓi hukunci baki ɗayansu.

Cikin sauri Areef ya ari bakin daddy ya ci mishi albasa, dan baya son ta sake kwaɓe musu a karo na huɗu, yana son ya ga suna zaman lafiya da mutunta juna.

"Lion seriously uncle bai san time da ta zo school ba, mu daga baya muka zo, kuma ka dai'na tambayar me ya kaita office na Mr Emmanuel, kasan fa uncle nasu ne, so maybe kiranta ya yi, kadai san sister ba zata je office nasa haka kawai ba, sannan kuma......". Hannu ya ɗaga mishi yana faɗin "Ba da kai nake magana ba!". Dafe kai Areef ɗin ya yi yana mamakin wai meyasa daddyn Rimsha da Lion basu shiri ne? Meyasa Lion ya raina daddy har haka ne? Why yake yi mishi haka? Mutun ya ɗauki yaransa guda biyu da Allah ya bashi su kawai a duniya ya basu aurensu amma Lion baya ɗaga mishi kafa, a gaskiya wannan karon bai ga abin da zai sa ya bari ayiwa daddy wani hukunci ba, dan kuwa bashi da laifi, bai san Rimsha ta fita haka ba, kuma Lion ɗin yasan hakan, yasan cewa daddy ba tarbiya ta banza ya bawa yaransa ba, shi mutun ne mai kula, a gabaɗaya ƴan uwansa ma shi ne ya fi bawa ƴaƴansa ilimin addini da kuma tarbiyarsu mai kyau, so yasan tarihinsu, ya san komai, kawai dai rashin jituwa da basu yi da daddyn ne yasa ya kasa yi mishi adalci, da kuma azababben kishi da ya rufe mishi idanu.

Zai sake yin magana sojojinsa da malaman makarantar suka iso wajen, hakan yasa ya danne maganar tare da bawa Areef umarni a kan zai turo wasu sojojin a wuce mishi da malaman gabaɗaya gida, sojojinsa su fara basu hulunci idan ya hau hanya ma'ana idan sun shiga ruwa zai waiwayesu dan yaga hukuncin da ya dace da su, so Areef ɗin ya kula da komai sauri yake yi yanzu, shi kuma daddy ya jira dawowarsa, dan ba zai kyale shi ba!!.

Umarni ya yi wa su Mark a kan su shiga motocinsu su tafi, okey suka amsa, cikin girmamawa Mark ya ce yana son ya mayar da Anaya gidansu, da yake shi ma Lion ɗin yana son Mark ɗin saboda zaman amana da suka yi, sai ya ce to su shiga mota sai su fara biyawa ta gidan nasu kafin su wuce airport, ya san gidan ne, yasani ya amsa da shi dan jiya ta yi mishi kwatance a waya da ya ce mata zai zo, so sai ya yi amfani da google map ya duba sunan unguwar tasu, ya ji daɗi sosai.

Ko da suka je gidan uncle Shitu da ya dawo daga tafiya yanzu suka samu, mika mishi Anayar Mark ya yi ba tare da ya yi magana ba suka wuce, lokacin Rimsha tana sume bata sami damar ganin uncle Shitu ba, ga shi su mummynta ma sun zo jiya dan azumi ya kawo kai, daddyn Anayar ya ce sai dai su zo nan su yi azumi, shi ne suka zo, da yake tana cikin motar Lion ne, ga kuma bakin glass ne da motar, sai basu sami damar ganinta ba.

Da haka suka wuce airport, suna barin school ɗin sauran sojojinsa shidda take gida suka yi wa makarantar dirar mikiya, dama idan baku manta ba sojoji 12 ya kawo, da Mark 13 sai gateman nasa 14, so gateman da Mark ba'a sanyasu a lissafi, kun ga kenan sojoji 12 ne dai, to dama gateman ba shi da lafiya ɗaya daga cikin sojojin ne ya karɓi aikin nasa wanda shi ne cikon sojoji biyar da ya tafi da su Mark ya cike shidda.

Suna zuwa airport jirginsu ya ɗaga dan dama an gama shirya komai, su kuma malaman makarantar sojijin suka tasasu a gaba suka wuce da su, daddy da su Aseef suka shiga cikin motocinsu suka koma gida.

After some hours suka yi leading a garin Lagos, ba ɓata lokaci suka nufi bakin ruwa, Rimsha bata ɗauki kaya ba, bata ma san da tafiyar ba, shi kuma ya shirya duk wani abin da zai buƙata akwai uku, sai dai akwati ɗayar tata ce, kayan da suka saya jiya ya shirya mata a ciki, sai ya ɗauki kayanta da ya gani a cikin dressing room nasa dukka ya zuba mata a ciki har da uniform nata, kamar zai shiga bedroom nasu ya kwaso mata wasu, sai kuma ya fasa, ya ɗauki iya waɗan nan dake bedroom ɗin nasa kaf. Brady na biye da shi a bayansa ya saɓi Rimshar a kafaɗa suka shiga dankareren jirgin ruwan.

Jirgin ya haɗu haɗuwa ta wuce misali, akwai ɗakuna da dama a ciki, kitchens, toilets da duk wani abin bunata tamkar gida, tsadaddun beds ne a cikin ɗakunan, ko wani ɗaki akwai sofa guda ɗaya a cikinta da table, gadon ma kawai abin kallo ne, nera ta yi kuka a kan jirgin nan, daga Washington DC aka turo mishi ita, ya ce baya son na nan, His excellency ya shirya mishi komai, shi ma fa His excellency baya son tafiyar, kawai ba yanda ya iya da jikan nasa ne dole ya hakura.

Bedroom nasa komai a cikinta fari ne tas, sai sheki komai yake yi, duk abubuwan da suke ciki sababbi ne gal a laidansu, gadon nasa wani irin laushi ne da shi, ga wani dankareren bed sheet fari tas dake shinfiɗe a kai, ga wasu kyawawan pillows masu laushi kamar audiga, kai abin dai ba'a magana, tamkar bedroom nasa na gida haka shi ma wannan yake, har da su pool wajen wasanni, kananan mashunan shiga ruwa koda wata matsala ta taso irin ko jirgin ya fashe da sauransu, akwai kananan jirage da mashunan shiga ruwan dan tsirar da rai, akwai su parachute da sauran kayan shiga cikin ruwa kala kala, akwai wuta da engine jirgin ke bawa cikin jirgin kamar wutar nepa, a takaice dai tamkar gida hakan jirgin take,.

Saman bed nasa ya shinfiɗeta sai tsalle Brady yake yi, yana leƙa ruwa ta glass ɗin dake cikin ɗakin nasu, bango guda a gefen dama dafaffen glass ne mai karfin gaske da kana iya ganin cikin ruwan da komai da komai dake wajen, nan Brady ya je ya tsaya abinsa.

Toilet Lion ya nufa, wanka ya yi tare da fitowa, already sun fara tafiya tun da ya shiga cikin jirgin, sojojinsa kuma sun rarrabune a kowani ɓangare na jirgin, hannunsu na rike da manya manyan jiga jigan makamai masu numfashi, wanda basu saɓa saiti. Bayan ya yi wanka ya fito ne ya shirya cikin pajama tare da fitowa waje ya ce da sojojin nasa su yi wanka su cire kakin jikinsun nan su sanya fararen kaya, okey suka amsa cikin girmamawa.

Komawa ciki ya yi sai tashin kamshi yake yi, Mark kuwa tuni ya yi wanka ya shiga kitchen dan ya yi musu girki. A box Lion ya ɗauko daga cikin akwatin kayansa, ya nufo saman bed in da take kwance, a gefenta ya zauna, wayar dake kankame a hannunta ya fara karɓa ya ajiye a gefe guda, da kyar ya iya zaro wayar daga irin kankame shi da ta yi, allurar da zai iya karya karfin powder da Mr Emmanuel ya shaka mata ya fara haɗawa, tana shimfiɗe kamar gawa a saman bed ɗin, wani abu sai suma, duk bala'i tsoron alkura irin tata yau Lion ya yi mata allura a jijiyar hannu lafiya lou.

Gabaɗaya ma haushinta yake ji, wayarsa ya ɗauka ya kira Areef a kan yasa a buɗe students ɗin nan sannan a jefar da gawar Mr Emmanuel kada ma a binnesa, a bawa karnika shi. Okey Areef ya amsa da shi.

Yana kashe wayar ta fara motsi alamar tana son farkawa, miƙewa ya yi kamar zai bar wajen, sai kuma ya koma ya zauna dan ya san a haukace zata farka, ya zai yi? Ba zai iya barinta ta je ta afka wani waje ba, dole dai ya dawo ya zauna kusa da ita yana jiran ta farka.

Juyi ta fara yi tana sambatu kafin ta waro idanunta da suka yi ja tamkar ƴar shaye shaye, wani irin azababben zufa ne ya fara karyo mata, a tsananin razane ta farka tare da yunkurawa zata sauka, alluran yana sanya ta tana ganin abu da girma, komai da girma yake zuwa mata, hakan zai sa duk kankantar abin da ta gani zata ganshi da girma har ta yi ƙoƙarin kauce mishi dan a tunaninta babba ne, a haka zata iya faɗawa wani wajen.

Tana ƙoƙarin sauka daga gadon ya rikota, wani irin wahalallen kuma ta saka mishi tana sauke numfashi da sauri sauri, tana ƙoƙarin kwace kanta, nan take wasu zufa suka fara tsatsafo mata daga gefe da gefen kunnenta, yanayin yanda take kukan gwanin ban tausayi, ba shiri ya jawota jikinsa dan kwata kwata bata a hayyacinta, rungume sosai ya yi tana kukan kasa kasa mara sauti.

Sun ɗan jima a haka mafin karfin alluran ya fara yin kasa, har lokacin bata dai na wannan wahalallen kukan ba, Brady kuwa tuni ya nufi waje, can wajen Mark ya je dan ya bashi abinci yana jin yunwa.

Lokacin guda ta yi shiru kukan ya ɗauke diff, ta kwanta shiru a saman faffasar kirjin nasa idanunta a buɗe kamar mai tunanin wani abin, can kasan maƙoshinsa ya furta "Meesha". Ɗago idanu ta yi tare da saukesu a kan kyakkyawar face nasa, hawayen da suka cika mata idanu ne suka fara zubowa a saman face ɗin nata, sai lokacin ta sami damar furta "Ina Anaya take? Dan Allah yaya Saif ka taimaketa, kada ka bari Mr Emmanuel ya yi mata komai". Tana magana tana shakewa saboda kuka, voice nata ma sam baya fita.

Hannu ya kai saman face ɗin nata ya ɗago haɓarta da kyau suna fuskantar juna. "Tana gida kuma bai yi mata komai ba". Ya bata amsa a takaice, cak ta tsaya da kukan nata tare da zaro idanu da suke jawur tana kallo wuyarsa, can kuma kome ta tuna sai ta yunkura zata tashi.

Riketa ya yi yana faɗin "Me ya kaiki office nasa?!" Ya yi maganar murya a ɗan kausashe, lafewa ta yi a kirjin nasa tun da ya hanata sauka, murya a dashe ta fara bashi labari tun lokacin da ta dawo school ɗin da abin da ya shiga tsakaninsu da kuma abin da Mark ya yi mishi, daga karshe ta rufe da labarin abin da ya faru yau na ta je office ɗin ne neman Anaya.

Iya ɓacin rai ya ji ɓacin rai, sai yaga kamar ma ai bai yi wa Mr Emmanuel hukuncin da ta dace ba, fin haka ya kamata su yi mishi, ciza lallausan laɓɓansa na kasa ya yi yana ɗan shafa kansa. "Meyasa kika yi irin wannan dressing ɗin kika je school?!". Shiru ta ɗan yi tana wasa da butirin rigan jikinsa. "Bazaki bani amsa ba sai na hukunta ki?!" Cikin natsuwa ta gaya mishi dama sun ce zasu yi irin dressing ɗin ne ita da Anaya, shi ne yasa suka yi, amma ta tuba ba zata sake ba.

Can kasa kasa ya furta "Without head tight!". Shiru ta yi bata bashi amsa ba, ita da kanta ta san tayi kuskure, ta rasa me ya shiga kanta da har ta fito babu ɗankwalin, zame hannunta daga saman botirin nasa ta yi zuwa saman cikinta dake murɗa mata tamkar mai jin yunwa, ɗan dafe cikin ta yi tana jin ciwon kai.

Zuba mata idanu ya yi yana kallonta kamar ya mareta yake ji, dan ya ji haushi ba kaɗan ba, sai dai fa yasan idan ya mareta wlh idan ta sume mishi sai ta fi sati bata tashi ba, hakan yasa ya danne kawai.

Tamkar zata yi kuka cikin shagwaɓa ta ce "Yaya Saif ina jin yunwa sosai har cikina yana murɗa mini". Yanda ta yi maganar har cikin ransa ya ji, hakan yasa ya saketa tare da cewa "Jeki ki yi wanka bari Mark ya kawo abinci". Okey ta amsa mishi da shi tare da miƙewa daga jikin nasa, sai dai kuma tana sauka kasan gadon jiri ya ɗebeta ta faɗo saman bed ɗin, ɗan zuba mata idanu ya yi, shi kansa yanzu ya san cewa har zuciyarsa dole akwai wata alaƙa tsakaninsu, shiyasa ya dai'na yaki da zuciyar tasa ma wajen yin ƙoƙarin cireta da tunaninta, ya hakura kawai ya karɓi kaddararsa, mu koma baya kaɗan, abin da ya sanya daren jiya ya dawo cikin ɓacin rai kenan.

Ya yi tafiya zuwa Abuja, so tun da ya tafi ya kasa samun sukuni, banda tunaninta babu wani abin da yake yi, ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya kawar da tunaninta a cikin ƙwaƙwalwarsa, amma ina abin ya citura, ya wuni bai ganta ba, gabaɗaya ya rasa sukuninsa, hakan ce ta ɓata mishi rai ba kaɗan ba, dan ma Allah yasa yana da hotonta a wayarsa, wannan hoton ne na wayar mutumin can da ya ce a nemo mishi ita, so hoton ce ta rage mishi raɗaɗin kewarta da yake ta fama da shi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login