Showing 54001 words to 57000 words out of 359620 words

Chapter 19 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1986

tun daga lokacin kuma bai sake zuwa Nigeria ba har sai da suka haifi Mummyn Rimsha tana da shekara biyar a duniya suka zo Nigeria, a lokacin uncle Shitu yana da 15 to 16 years, da suka tashi koma a wannan karon, sun tafi da uncle Shitu ɗin, dan ya je ya ga in da suke ya yi masu hutu ya dawo, ba ƙaramin jin daɗin zaman Niger uncle Shitu ya yi ba, ba dan yaso ba ya dawo NIGERIA, tun daga nan kuma ba su sake jin ya su mummyn Rimsha suke ba, har bayan shakaru 7, lokacin mummyn Rimsha tana da shakaru 12 zuwa 13 a duniya, shi kuma uncle Shitu 22 to 23 years yake da shi kenan, a lokacin ya shirya yaje Niger ɗin bisa umarnin Mahaifinsa akan ya je ya dubo mashi ɗan uwansa ya yake, a lokacin yana 100 level karatu a Ahmadu Bello University, hutu yake zuwa Maiduguri, da yazo hutun ne ya je Niger duba bappan nasa, a nan ya sami mummunar labari na ce wa, bappansa Allah ya yi mashi rasuwa shekara ɗaya da ta wuce, ya sha kuka ba kaɗan ba, ya so su dawo tare da mummyn Rimsha da mahaifiyarta, amma iyayenta wato kakannin mummyn Rimsha sun ki yarda, haka ya hakura ya dawo ya sanar da gida abin da ya faru, sun sha kuka sosai kuma sun ji haushin mahaifiyar mummyn Rimsha da ta kasa turo ɗan aika ko ta nemi waya ta gaya masu rasuwar ɗan uwan nasu, sun ji ba daɗi ainun, hakan yasa suka yi fushi suka ce ba zasu karɓo mummyn Rimsha ɗin ba, sun yi fushi da mahaifiyarta, kun san Shuwa Arab su ma sun iya fushi ba kaɗan ba, daga nan kuma basu sake bibiyar ya Mummy Rimsha take ba, sun watsar da su, basu sake sanin ya suke ba sai yanzu da ta kai kanta da kanta ga dangin mahaifin nata, to shi ne suka sake sanyata a idanunsu..... KUNJI ALAƘAR DAKE TSAKANIN UNCLE SHITU DA MUMMY RIMSHA, YA AKAYI MUMMY RIMSHA TA AURI DADDY RIMSHA? YA AKAYI TA ZO NIGERIA? INA MAHAIFIYARTA? MEYASA BATA TAƁA ZANCEN MAHAIFIYAR TATA BA? MEYASA BATA KOMA NIGER BA BAYAN ƁATAR DADDY RIMSHA? DUK AMSA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN DADDY RIMSHA DA UNCLE SHITU, YANZU DAI NA FAYYACE MAKU ALAƘAR TA DA UNCLE SHITU NE A TAKAICE DAN KU GANE ME MATSAYINSA A WAJEN SU RIMSHA, DAN HAKA MU KOMA KAN LABARIN MU.

STORY💋

"Allah sarki Anaya ni dai ina son ganin Gwaggo Aisha nan naki, wlh ko dan takura mini da zancensu da kike yi ma dole naso ganinsu" . Ta yi maganar tana mai dafe kirjinta, ta rasa dalilin da yasa duk lokacin da Anaya take bata labarin ƴan uwanta sai ta rinƙa jin gabanta yana faɗuwa, kirjinta na bugawa da sauri sauri, wani lokaci har sai ta dafe kirji nata take samun sauƙi.

A ɓangaren ita ma Anaya duk lokacin data kalli Rimsha sai gabanta ya faɗi, da yake dukka dai yara ne sai ba wanda ya kawo komai a ransa, kuma sosai Anaya tana ganin muguwar Kamannin dake tsakanin Rimsha da kuma Gwaggo Maryam wadda ta kasace mummy Rimsha ɗin kenan, amma bata taɓa gayawa Rimsha ba, sau da dama tana zucci zuccin gaya mata tana yi mata kama da Gwaggon ta Maryam matar uncle ɗinta, sai dai idan sun haɗu sai hiran school ko hirar wani abin, Anaya ta na mancewa da zancen kullum.

"Rimsha In Sha Allah zaki kalli su Gwaggo Aisha, kin san me? ". A'a ta bata amsa. "Idan su Gwaggo Aisha suka sake zuwa zan ce daddy ya kawo ni gidanku mu ɗauko ki, kizo ku gaisa, jiya ma munyi waya da Gwaggo Aisha ta ce mini zasu zo azumi, kuma kinga azumi ya kusa, tun da an kusa babban zaɓe, to suna zuwa zan gaya miki, wlh suna da kirki kuma suna son mu sosai, musamman ma ni, gwaggon A'isha ta fi sona fiye da kowa, dan nayi kama da ita, naso su zauna damu a gidan nan, amma suka ce a'a, daddy ma ba yadda bai yi ba, sunki yarda suka ce sun fi son Maiduguri, shi ne kawai daddy ya barsu a can yana saya musu duk wani abin da suke so ya tura musu can, amma zan gaya miki gaskiyar meyasa basu son zama damu, wlh mummymu ce bata son su, tana zaginsu, shi ne suka ce zasu koma Maiduguri, kuma gwaggo A'isha ta ce kada na gayawa daddy mummy ta zagesu, da nace sai na gaya, amma sai na fasa dan kar gwaggo A'isha ta ji na daɗi". Anaya sarki magana, faɗi ba'a tambaye ki ba, sai mamaki Akila take yi na irin shegen surutun nan na Anaya, duk ta gama tune asirin gidan nasu kamar wadda aka tambaya, ta zube komai a faranti abinta.

Ita dai Rimsha da yake ba mai cika son surutu bane, tun tana amsawa Anaya har ta dawo binta da to, a'a, da kuma e, wani lokaci ma girgiza kai kawai take yi tamkar Anaya ɗin na a gabanta. Sai dariya kasa kasa Akila take yi, dan ta tula Rimsha ta gaji da surutun Anaya, ita kuma Anaya tamkar yanzu ma ta fara, babu niyar dakatawa a lamuranta.

Sai da aka kira sallar issha, cikin sauri Rimsha ta sallameta tana sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya tare da godiya ga Allah ta tsira daga takurar Anaya, ita kuwa Anaya cewa ta yi idan ta yi Sallah zata sake kiran ta, da okey kawai Rimsha ta bita da shi, ba dai idan ta kira ɗin sai ta ɗauka ne zata ji surutun ba? To wlh ba zata ɗauka ba, ta faɗa a ranta tana turo ɗan bakin, da haka ta nufi toilet dan yin alwala.

Bayan ta fito Akila ta shiga ita ma. A tare suka yi sallar mangariba suka zauna har lokacin issha ya yi, bayan sun yi issha ne Rimsha ta miƙe dan ta kaiwa Lion abinci, ita kuma Akila ta haye saman gado tare da jawo wayarta dan ta yi hira da masoyinta a WhatsApp, tun da yanzu ya bata damar tana iya yi mishi massage a WhatsApp, amma ko a WhatsApp ɗin numbersa a rufe take.

Kamar kullum, Kitchen ta nufa dan ɗaukar abincin, bayan ta wanke hannayenta ta ɗauka a nutse, ba tare da ta ce da Mark ko sannu ba, shi ma ko sannu bai ce mata ba, kamar kullu ko kallon in da take bai yi ba.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, yanzu ta daina tsayuwar jiran sai an amsa mata sallamar ta, tana zuwa zata yi sallama ta faɗa.

Babu kowa a ɗakin, da alama sun fita, a in da ta saba ajiye abincin, a nan taje ta ajiye tare da zama tana tunanin ina kuma suka shiga.

Bata gama rufe tunanin nata ba ya shigo cikin ɗakin yana mai yin sallama kasa kasa, da mamaki ta amsa sallamar kasa kasa ita ma, kenan dama idan zai shigo ɗakin nasa yana yin sallama? Ta tambayi kanta tana ɗan satar kallon shi, yes idan zai shiga ɗakin nasa yana yin sallama, duk da yasan babu kowa a ciki, amma yana yin Sallama saboda sunnah ce ta annabi yin hakan, idan kayi sallama mala'ikun rahma zasu amsa maka idan ba mutane, yanzu ma bai san da ita a cikin ɗakin ba, ya dai yi sallamarsa ne kamar yadda ya saba.

Ta kasar ido ya kalli inuwarta, hakan ya tabbatar mashi da mutun a cikin ɗakin, kwata kwata ya manta da ya ce zai kalleta idan ta shigo, zai kalli wacece su Areef suke so haka?, Allah sarki sabo tirken wawa, ya saba da ɗabi'arsa na rashin ɗaga idanu ya kalli abu, da wuya ya dai'na.

Da yake yana jin yunwa, sai ya wuce wajen da ya saba zama ya zauna, yana zama gabaɗaya wutar gidan ta ɗauke diff tamkar dama wutar nepa ce, mamaki ne ya kama shi, ta ya akayi engine nan ya mutu? Tun da yazo Naija da aka ɗauke nepa sau ɗaya aka yi wajen 3 hours ba'a dawo da shi ba, daga nan ya yi watsi da nepa ya saho wani tampatsetsen engine wuta, mai matukar gudu da bada wuta mai karfi, baya shiri da zafi, Shiyasa ba zai iya zama babu wuta ba.

Wani irin mugun tsoro ne ya dira mata a ranta ganin duhu ya mayaye ko'ina na cikin ɗakin, kun santa da tsoron bala'i, shi kuma jingina kansa da jikin sofar dake kusa da shi ya yi tare da waro idabunsa sosai yana kallon gabansa, ma'ana yana kallon in da yake fuskanta.

Shiru shiru wutar bata dawo ba, shi kuma bai kunna wutar wayarsa ba, yana jin ta yadda take wani jan numfashin tsoro a hankali hankali, alamar ta tsorata over.

Almost 10 mins shiru babu wuta babu labarinsa, sai raba idanu take yi, shi kuma har jikinsa ta fara haɗa zufa, ya tsani zafi fiye da tunanin mai tunani, Sojoji goma sha huɗu da su Mark a gidan amma wuta ta ɗauke har tsawon minti goma basu duba me matsalar ba?.

Guntun tsaki ya ja tare da ɗago kan nasa da nufin ya miƙe ya nufi wajen, kwatsam sai ga hasken wutar ta dawo, wani mahaukaciyar ihu ta kurma tare da sulalewa kasa sumammiya.

Da mamaki ya kalleta kwance a kasar, ko me ya sumar da ita Oho, yarinya tamkar mai aljanu, tamkar kanta biyu, da yake tana kwance ne sai bai samu damar ganin face nata ba, kuma irin kwanciyar da ta yi, ta ɗaura hannunta ɗaya a saman kumatunta, dan lokacin da take kurma ihun sai da ta dafe kumatun nata da hannayenta dukka biyu, ba komai ne kuma ya sanyata ihu da suma ba fa ce ganin cikin kwanyar idanunsa da ta yi, tana fuskantarsa, ga shi da yake a duhune idanun nasa a buɗe suke sosai, kuma shima yadda ya yunkura zai tashi ita yake fuskanta, hakan yasa ta kalli tsakiyar kwayar idanun nasa, ba ƙaramin razanata suka yi ba, saboda hasken wutar yasa kwayar idanun sun kara kyalli.

Komawa ya yi ya zauna, har ya kai hannu zai ɗauki ruwa ya zazzage mata a kai, nan take zuciyarsa ta tunano mashi da irin farincikin da TRIPLETS nasa suka shiga ɗazun a ta dalilinta, har ga Allah yaji daɗin da bai taɓa ji ba na ganinsu a wannan farincikin, tuna hakan yasa ya fasa zazzaga mata ruwan sanyi, dan kada ta cutu sosai, idan ya zazzaga mata wannan ruwa mai uban sanyi, to fa a haukace zata tashi, idan ba'a yi Sa'a bama, tana iya hayewa kansa, dan fita zata yi a hayyacinta.

A na haka sai ga Areef ya shigo ɗakin shima yanzu ya idar da sallah, daman sun rabu da Lion ne, shi ya wuce bedroom nasa dan yin Sallah a can, Imran, Lion kuma suka wuce masallaci.

Wajensu ya nufo dansu ci abinci, yanzu kusan gabaɗaya ya tare a ɗakin ɗan uwan nasa.

"Kai subhanallah Lion menene ya sami sister kuma?" Tamkar babu shi a ɗakin, bai amsa ba, sai ma yunkurawa da ya yi zai miƙe ya bar wajen, cikin sauri Areef ɗin ya ce "Please zauna bari ni nayi serving naka ko?". Ba musu ya koma ya zauna dan yunwa yake ji, ɗaukarta cak Areef ya fara yi yana ciza laɓɓansa alamar zafi kafaɗarsa ke mashi, dan akwai sauran ciwo sosai, ko sannu Lion bai ce mashi ba, ai shi ba ƙaramin yaro bane, yasan abin da ya dace da shi, da kuma wanda bai dace ba, idan ya yi wa kansa illah ma shi ya jiwo.

Saman sofa dake a cikin ɗakin ya kwantar da ita tare da dawowa wajen ɗan uwan nasa yana cizar lallausan laɓɓansa.

Abinci ya zuba masu suka ci a tare kamar ɗazun, bayan sun kammala ya kwashe kayan abincin ya ɗaura saman table dake cikin ɗakin.

A tare suka miƙe Lion ya nufi toilet shi kuma ya haye saman bed, ita kuma tana sume a samar sofa.

Wanka Lion ya yi tare da fitowa ya shirya cikin kayan barcinsa riga da wando masu shegen kyau ga laushi kamar auduga, ba su da nauyi ko kaɗan, kamar dai kullum launin white color ne, bai ɗaure kyakkyawar gashin kansa ba, ya barshi zube sai kyalli yake yi yana tashin kamshi.

Saman gadon ya dawo ya kwanta yana zuba uban kamshi, yana kwanciya Areef ya miƙe ya nufi toilet ɗin dan shima ya yi wanka, saboda ciwon dake a kirjinsa shi ba wanka yake yi kamar kowa ya yi ta zuba ruwa ba, no a hankali yake yi ta yadda ruwar ba zata taɓa bandejin dake wajen ba, har ta taba ciwon, hakan yasa idan ya shiga wanka sai ya ɗauki almost 1 hour kafin ya kammala, daki daki yake yin komai.

Shiryawa ya yi cikin kayan barcin Lion, a ƴan kwanakin nan ma kayan ɗan uwan nasa yake yawan sawa, dan kusan ya tare a ya dawo ɗakin Lion ɗin, idan ya shigo baya fita har sai idan zai yi wani abin, kayan barcin launin black color ya sanya, bai cika sanya farin abu ba a yanzu, sabida ciwon nan nasa, baya son ganin stain na jini a jikin kayansa, so ya fi sanya Black colar or brawn, wadda ba zasu fitar da shaidar abu ba, duk kaunar da yake yi wa white color ya hakura.

Saman gadon yazo ya kwanta kusa da ɗan uwan nasa, har lokacin Rimsha tana sume kwance saman sofa, da alama shi ma Areef ɗin ya mance da ita a wajen.

A kwanciyar tasu suna fuskantar juna, Lion idanunsa a lumshe, shi kuma Areef ya tsare shi da idanu yana kare mashi kallo tare da godiya ga ubangijin daya yi masu wannan kyakkyawar halittar haka, Lion kyakkyawar gaske ne kamar shi ya yi kansa, har ta ƴan uwan nasa yaba kyansa suke yi, da yake su basu ganin nasu kyau ɗin sai nashi, dama kuma haka ne, baka cika ganin abu ba idan a jikinka yake, kafi ganin kyaunsa a jikin wani, to suma haka ne sunfi ganin kyan juna, ɗaya yaga na ɗaya haka.

Daga karshe Areef ya juya tare da ɗauko wayarsa daya ɗaura saman bedside drawer ya shiga latsawa, dan kwata kwata baya jin barci, shi kuma Lion da alama barci yake ji sosai, Shiyasa ma ya yi barcinsa abinsa.

Ita kuwa Akila tana kwance tana chatting da masoyinta, bata wani damu ba dan Rimsha bata dawo ba, while shi kuma Imran yana ɗakinsa yana shirin barci.

☠️DAULAR MUTUWA☠️

A YAU DAULAR MUTUWA TAKE KARA SHEKARA GUDA A KAN SHEKARUN HASSASATA DA AKA YI.

Sai murna suke yi, an kawata gidan tamkar ba gidan ba, sun yi amfani da tsafinsu wajen sauya gine ginen dake a cikin gidan, sun fito da sabbin gine gine tare da sabon penti, ga wasu baloon da kayan kyalkyali da aka zuba, tamkar wajen party, kai idan ba ance maka nan DAULAR MUTUWA bane ba zaka taɓa ganewa ba, saboda tsantsar kyan da ya yi, su barbushi duk sun zama kyawawan matasa masu jini a jika, ma'ana sun koma aihanin halittar da Allah ya yi masu, kyawawan matasan kabilar Ebo ne, duk wanda ya san Ebo ya sansu da tsawo da kuma ƙiba, mafiya yawancinsu farere ne kuma kyawawa, to suma haka suke, fararene tas kyawawa, ga tsawo da ƙiba, suna da kirar karfi tamkar masu ɗaka karfe, ma'ana masu yin gym, kuma ba wani gym da suke yi, halittace kawai da mafiya yawan mazan Ebo haka suke.

Fadar QUEEN an kawata shi da wani irin mahaukacin kyakkyawar zazzafar kwalliya, komai na cikin fadar Navy blue ne, ga wasu tsala tsalar kujeru da suka yi amfani da tsafinsu wajen kyara su, idan ka kalli fadar QUEEN sai ka yi zaton wani katafaren Daula mai tarin arziki na wani hamshakin basarake ne.

A cikin fadar akwai wani hawa step 3 haka, a saman step ɗin ne a ka kawata wa QUEEN kujeran da zata zauna, sai dai kujerun guda biyu ne a wajen ba ɗaya ba.

Sai shagali ake yi, su baba da yake sun saba gani duk shekara sai basu wani damu ba.... WAI SHIN MENENE MAKASUDIN HASSASA DAULAR MUTUWA NE? kamar yadda na gaya maku a baya, ta kabilar Ebo ce, sun hassasata ne ma dan tsafe tsafensu na samun makudan kuɗaɗe, suna ɗebo yara daga arewa zuwa wajen, da wuya ka samu ɗan gudu a cikin waƴan da ke cikin gidan, ko da gigin wasa ba zaka taɓa gani sun yi kuskuren kamo ƙabilar tasu ba, suna tsafi sosai da jikin mutane, ba iya yara ba, har da manya wanda ya yi sake da addininsa, yanzu matsafa sunyi yawa a duniya fiye da tunanin mai tunani, sai a riƙe ibada dan a tsiranwa gaidinsu, suna shan jini sannan kuma suna cin namar mutane, suna sayarwa wasu gidan matsafar wani sassa na ɗan adam idan suka buƙata dan yin tsafinsu, a caf faɗin kasar nan da wuya a samu gidan matsafa da suka kaisu girma da komai da komai, sun shahara ta wannan ɓangaren ba kaɗan ba, duk wanda ya shiga wannan gida baya fita, an rufe babinsa.... MU KOMA KAN LABARIN MU.

Murna a wajensu ba'a magana, wata kyakkyawar halitta ce ta fito daga wani katafaren kyakkyawar ɗaki, wannan halitta mace ce, a shakaru ba zata wuci 22 years ba, tana da tsawo sosai, amma bata da ƙiba sosai, ga shape kamar ita ta yi kanta, fara ce tas, ga hancin nan ɗan siriri kamar karas, ya zauna sosai da kyau a saman kyakkyawar farin fuskar tata, ɗan bakin nan nata ɗan karami, lips nata launin dark purple, kyau iya kyau wannar matar ta yi, sanye take da doguwar riga launin black color, rigar tata tana ja har kasa, rigar irin weeding gown ɗin nan, kanta babu ɗan kwali, ta zuba gashin nan nata har gadon baya, tamkar ita ta bawa kanta wannan kyakkyawar gashin, ga shi irin gashi mai gazar gazar ɗin nan ne, sai ya kwanto mata har baya. Wannan mata ba kowa bace fa ce QUEEN.

Saman ɗaya daga cikin kujerun da aka tana da mata ta nufa, ga wasu kyawawan fararen samari guda biyu suna take mata baya, sai kasa da kai su barbushi suke yi alamar girmamawa, a gabaɗaya cikin fadar QUEEN ɗin ita ce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login