Showing 186001 words to 189000 words out of 359620 words

Chapter 63 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2026

bayan ta shiga ɗakin da sallama ɗauke a bakinta, Aseef ne ya amsa mata sallamar tata, kusa da Lion ɗin ta zo ta tsaya tana faɗin "Good morning Yaya Saif and yaya Aseef". Bai amsa ba kuma bai ɗago ba, Aseef dai ya amsa amma bai ɗago ba. Miƙa mishi rigar tasa ta yi tana faɗin "Ga shi nan Nagode". Sai lokacin ya ɗago da kallonsa kai tsaye sai saman idanunta, dan suke yake son kallah, yanzu gabaɗaya ma haushin family'n Nawazudden ɗin ya fara ji, dan suna jefa mishi TRIPLETS nasa cikin haɗari, ya kuma sanya a ransa sai an yanke hannun wannan ɗan'sanda da ya mari Aseef ɗin, dan ba zai barshi ba, bai ga wanda ya isa ya taɓa masa TRIPLETS nasa kuma ya kyale shi ba.

Kallonsu na ƴan sakanni ya yi kafin ya dawo da kallonsa saman rigar da take riƙe da shi ɗin, shiru ya ɗan yi, ya kalli rigar kafin ya mai da kallonsa kan abin da yake yi, bai ce da ita komai ba, kuma ba shi da niyar yin maganar ma baki ɗaya. Shiru ta tsaya tana jiran ta ji me zai ce.

Ganin Lion ɗin bai da niyar yin magana ne yasa Aseef ya karɓi rigar yana faɗin "Sarkin rigima me kuma kika je ki ka taɓo ya shiga miki idanunki? Ko kuka kika yi ne?" Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Barci dai nake ji". "Daren jiya baki yi barci bane?". Ɗan satar kallon Lion ta yi kafin ta ce "Nayi amma dai ina jin wani ne sosai". Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "To jeki kiyi ko?". Okey ta amsa mishi tare da juyawa ta nufi waje da sauri dan ta je wajen Areef su tafi wajen Jehan, duk da tsananin barci da take ji tana son kallon ƴar uwanta, dole ta danne ta je wajenta.

Cikin bedroom nata ta koma ta kwasanwa Jehan ɗin kayan sakawarta wajen kala biyar, ta haɗa mata da hijabin sallah har kasa, guda biyu, ta ɗauka mata daddumarta ta haɗa, duk dai abin da ta san ƴar uwar tata zata buƙata sai da ta ɗauka mata ta zuba a cikin school bag nata ta ɗauka ta fito waje.

A cikin mota ta isko Areef da Mark suna jiranta, tana shiga Mark ya kunna motar suka bar gidan, sai hira suke yi shi da ita har suka isa prison ɗin, kamar dai jiya haka aka rakasu har ciki, in da suka zauna jiya yau ma a nan suka zauna.

Ba'a ɓata musu lokaci ba aka fito musu da Jehan ɗin, gaisawa suka yi da Rimsha kafin ta ɗagawa Areef da Mark gaisuwa, har yau tana cike fal da confidence, babu fa alamar sarewa ko karaya a tattare da ita, cike take da kwarin gwiwa, Areef bai yi mamankin ganin bata yi laushi ba, dan a bincike a kan ta da ya yi daren jiya, ya gano tun ainahinta ma mafaɗaciya ce, ga zafin rai, ga kuma taurin kai, bata magana ta canza, bata da fara'a ko kaɗan, so silent take, bata shiga abin da bai shafeta, sai dai idan taga za'ayi zalinci to fa sai in da karfinta ya kare, hakan nema ya kara karfafa mishi gwiwa a kan lallai tana da gaskiya kuma zai taimaka mata, zai tsaya mata.

"Jehan zaki iya yi mini kwantancen gidan mutumin, wato in da abin ya faru?". Cewar Areef ɗin. Shiru ta yi kamar mai tunani, can kuma sai ta girgiza mishi kai tana faɗin "No daga nan ba zan iya yi maka kwantance ba, sai dai idan naje unguwar zan gane gidan, ni ban taɓa zuwa Kaduna ba sai wannan karon, ban san ya yake ba tare na iya kwatantawa". Shiru ya zuba mata idanu yana kallon yadda take magana, shi dai kome ta yi wlh burge shi take yi, "Okey yanzu abin da ya kawo ni nan, ina son duk wanda zai zo nan ya ce yana son yin magana dake, to kada ki yarda, kada ki kuskura ki bawa kowa damar yin magana da ke, ko da an sanyaki fitowa dole, to idan kin fito ko sun yi miki tambayoyi amsa ɗaya zaki basu shi ne baki san komai ba, daga haka kada ki kara kada ki rage, nasan akwai lauyoyin da zasu buƙaci ganinki or ƴan jarida, da sauran manyan mutane, na san kamar yadda kike da makiya suma makiyan naki suna da makiya masu son ganin bayansu, so wasu zasu samu damar amfani dake dan cimma burinsu a ɓangaren siyasa, dan na ga yanzu faɗar taku ta koma ta siyasa ce, dan haka ki kula, kada ki kuskura ki buɗe baki ga kowa".

Jinjina mishi kai ta yi alamar to ta ji, miƙa mata jakar kayan Rimsha ta yi suka miƙe dan su tafi, ita ma Jehan ɗin miƙewa ta yi dan ta koma ciki. Kamar jiya har ya ɗan yi gaba, sai kuma ya sake dawowa tare da riƙo haɓarta yana faɗin "Shi ne baki tambayi sunana ba ko?" Kallon gefen ido mai kama da harara ta watsa mishi kafin ta ce "To me sunanka zai kara mini?". Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da yi mata signal da gera ɗaya yana faɗin "Wai ke jiya baki yi tunani na bane? Ni fa na kwana tunaninki". Shiru bata tanka mishi ba, dan a cewarta bata da lokacin shirmensa, dama kuma idan baku manta ba, ita haka take, bata san wani abu wai shi shauki or wasa da dariya ba, tsare gida kawai ta iya.

"Au ba zaki yi magana ba?" Nan ma shiru ta yi, tana kokarin buge hannunsa da ya riƙe haɓarta da shi.

"Sarkin faɗa, ai jiya duk naga tarihinki tun kina ƴar shekara 2 a duniya, kika rinƙa takurawa my Rimsha da masifa a baya ko? To zan rama mata ai, mai rama mata ya zo, masifaffa kawai, ni kada ki ce zaki yi mini dan maganinki zan yi, yanzu dai ki ajiye sunana dan zai yi miki amfani, sunan babyn baby kin ji ko?" Zaro idanu Rimsha ta yi tana maimaita sunan babyn baby kuma? Ga shi dai da Hausa ya faɗi babyn baby, to ko a ina ya jiyo sunan oho mishi, shi da ba jin Hausa yake yi ba, ita yanzu ta ma dai'na mamaki a kan TRIPLETS dan sun wuci tunanin mai tunani, idan ka biye musu mamaki ne zai kashe ka, wai babyn baby dan iya shege.

Harara ta watsa mishi kafin ta sa kai ta wuce abinta, juyawa ya yi ya riƙo hannun Rimsha yana faɗin "Wannan ƴar diramace, ta iya juyawa mutun idanunta fararen nan, kuma suna da kyau idanun sosai kamar na uncle na". Ita dai Rimsha ko a jikinta tun da ta zo ta ga Jehan tana nan lafiya lukui ai shikenan.

Suna barin prison ɗin suka nufi gida, shiru suka yi a cikin motar Areef yana tunani a kan Jehan, shi kuma Mark yana tunaninsa na daban, ita kuma Rimsha kamar kullum ne, kun sani tunanin Lion take yi.

A ɓangaren gidan Abbo kuwa waton gidan su Nawid
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️



*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*



E49-50💋



A ɓangaren gidan Abbo kuwa waton gidan su Nawid, har yanzu dai Abbo shiru ba shi ba labarinsa, soyayya babu kama hannun yaro suke zubawa a tsakaninsu, A'afia ta saki jiki sosai da Dr Nawid, ta mance ma da abin da ya taɓa faruwa da ita a rayuwarta ta baya, ta shiga sabuwar yaruwa mai cike da nishaɗi da annashuwa, mijinta na nuna mata so, surukuwarta na nuna mata tsantsar kula, hankalinta ya kwanta over.

Yau ta kama ranar Friday, tun misalin karfe 5 ta kammala komai nata, ta Shiryawa mijin nata duk wani abin da ta san zai buƙata saboda yau da wuri zai dawo daga wajen aiki, ba zai kai mangariba ba, tsara wanka ta yi tsab ta zuba kwalliya sosai da sosai, doguwar riga baka mai kama jiki ta sanya, ta haye saman bed nata ta yi shiru tana tunane tunane yadda zata yi da batun Ommunsu na case nata ita da Umaisha, gaskiya ba zata iya barin Umaisha ta yi sata ba, idan Ommu ta cika matsawa to ita gaskiya zata sanar da Abbi da kuma Irfan sai dai duk abin da zai faru ya faru, ita ta jawa kanta da kanta.

Ta nutsa cikin tunanin kamar a mafarki ta ji ya kwanto a jikinta yana faɗin "Me kike tunani har nayi sallama baki amsa mini ba?". Kayatatcen murmushi ta sakar mishi tana shafa kumatunsa tana faɗin "Kai mana my mijina, kai nake tunani, to barka da dawowa ya aiki? Ya su Bahijja?" Ɗan jan dogon hancinta na gadon turawa ya yi yana faɗin "Sarkin kishi ba, kullum sai an ce yasu Bahijja, ni nasan ba dan kiji ya suke kike wani tambayata ba, kawai dai dan kiji na kallesu ko na kula su ne, to ki sani ni bana kula mata haka yadda kike tunani, ina fa sane da abin da nake yi, dama da kike gani sometimes nake cewa zan kula mace dan na nemi matar aure ce, na gaji da zama a gwauro, to yanzu kuma tun da Allah ya bani mata saliha, kamila, mai kaunata tsakani da Allah tare da bani kulawa, to ina ruwana da wasu matan kuma? Ni tun ainahima su Bahijja a ƴan aikina suke, basu taɓa wuce wannan matsayin ba, idan da ina kulasu ai da na jima da yin aure, to ba ko wace mace nake ɗaga idanu na kalla ba ma, sai a rage kishi". Ya kai karshen maganar tare da bata sumbata a kumatu, kashe murya ta yi a ɗan shagwaɓe ta ce "Ni fa nace maka ba kishi nake yi ba, kawai dai kula da kai nake yi ne".

Matso da face nasa daf da tata sosai ya yi, harshensa ya fitar yana ɗan lasan lips nata cikin salo da kwarewa irin nasu na likitoci, dan sun kware a sanin sirrin mata da iya sarrafasu, a hankali ya zura harshen nasa cikin bakinta yana jujjuyawa, nisawa ta yi tare da fara yin kissing nasa da kyau da kyau, kankameta ya yi cikin dabara ya fara laluɓar breast nata dake ta faman sokinsa a kirji daman, ta saman wuyar rigarta ya zura hannunsa ciki ya capko ɗaya, cikin salo ya fara murzasu yana wani lumshe idanu kamar mai jin barci, zura hannunta ta yi cikin gashin kansa ta shiga shafawa har zuwa wuyarsa, nan take ya birkice mata.

Zame rigar jikin nata ya fara yi, bata damu ba, dan ita ta mance ma da ana wani abu wai sex a rayuwar aure, kullum zasu yi wasa iya wasa da shi, amma bai taɓa kwatanta shigarta ba, shiyasa ko da ya rabata da kayan jikinta bata wani damuwa, wasa da ita ya fara yi sosai yana sauke numfashi, ita ma bata yi kasa a gwiwa ba wajen taya shi tare da ruɗar da shi ya kara fita a hayyacinsa sosai, surutai ya rinƙa zuba mata tare da sambatu, har duhun mangariba ya fara saukowa, miƙewa daga kan nata ya yi tare da kashe wutar ɗakin ya fara cire kayan jikinsa.

Tana kwance shiru yadda ya barta, ya gama rabata da komai na daga jikinta, da yake akwai duhun mangariba sai ya zama da ya kashe wutar ɗakin bata iya ganinsa sosai. Tas ya cire kayan jikinsa bai rage komai ba, dawowa saman gadon ya yi tare da hayewa kanta ya cigaba da abin da yake yi, ta ɗan tsorata lokacin da ta ji saukar jikinsa a nata kuma babu short, idan suna wasa baya cire short nasa gaskiya, iya kayan yake ragewa, wani lokaci ma ko singlet nasa baya cirewa, amma yau gabaɗaya ya cire komai, abin ya bata mamaki.

Tana can tana tunani bata ankaraba sai ji ta yi ya shigeta, zaro idanu waje ta yi kusan a tare suka zaro idanun nasu, shi ya yi hakan ne dan ya ji ta ba'a budurwa ba, ita kuma ta yi hakan ne dan tsorata da shigarta da ya yi, shiru ya ɗan yi kafin kuma ya fasa abin da ya yi niyar yi ɗin ya zare jikinsa daga nata, ita har ga Allah ma ta manta da abin da ya faru da ita a baya, ya mantar da ita komai da soyayyarsa.

Kwanciya ya yi a gefenta yana mayar da numfashi tare da yin ruf da ciki a saman gadon, bata motsa daga in da take ba, shi kuma juyi ya fara yi har aka yi sallar mangariba, sun yi shiru dukkansu, can tamkar a mafarki ta tsinkayo muryarsa cikin dodan kunnenta yana faɗin "Aafia ina kika kai budurcin ki? Waye kika bamawa? Waye kika sadaukarmawa?". TASHIN HANKALI, WANNAN TAMBAYA CE DA DUK WATA MACE A DUNIYA BA ZATA TAƁA SON MIJINTA NA SUNNA YA YI MATA SHI BA, KO WACE MACE ZATA SO NE TA ZAMA MAI DARAJA DA KIMA A WAJEN MIJINTA, IDAN BABU WANNAN ABIN, TO BABU WATA DARAJA DA KIMA A TATTARE DA MACE, KOMAI ABINKI BA ZAKI TAƁA SON KIJI IRIN WANNAN TAMBAYA DAGA BAKIN MIJINKI BA, DAN HAKA MATA MU KULA, IYAYE A KULA SOSAI, KI KULA DA MUTUNCINKI DAN KI GUJEWA IRIN WANNAN TAMBAYA, DA ZARAR KIN SAMI IRIN WANNAN TAMBAYA DAGA FARKO TO SHIKENAN KE KAM KIN GAMA YAWO, KE DA DARAJA I IDONSA KAM SAI DAI KI HANGA A MAKOTA, YANA DA KYAU MU KARA TSANANTA KULA, ITA DAI AAFIA KADDARACE TA FAƊA MATA, TO AMMA SHI BAI SAN DA HAKAN BA, DOLE YA YI MATA TAMBAYAR DAN YA JI MENENE YA FARU? DUK WANI NAMIJI A DUNIYA TAKAMARSA WANNAN ABIN NE, IDAN BAKU SANI BA KU SANI ALFAHIRI YAKE YI DA SHI IDAN YA SAMU, HAR YA MUTU YANA ALFAHARI DA SHI YA KARƁI BUDURCIN MATARSA, ALLAH YA KARA TSAREMU A DUK IN DA MUKE.

Wani dum dum gabanta ya bada bugu, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin kuncinta, ta rasa me zata ce da shi, a nashi ɓangaren kuwa, tunani yake yi a kan su Imran, gabaɗaya sai ya ji kimarsu Imran ɗin ta ragu a idanunsa, bawan Allah bai san cewa shi Imran ma bai san da maganar ba, harta Abbi da ya haifeta bai san da maganar ba, da ya sani zai yi gaggawar sanar da shi, kuma ba zai aura mishi ita ba har sai ya sanar da shi idan ha aminci, iya daddyn Jelly, Irfan da Akil ne kawai suka san da maganar, su ma bayin Allah sun mance da zancen ne baki ɗaya, da basu mance ba, zasu sanar da shi tun da wuri.

"Ba zaki bani amsa ba?" Ya yi maganar tare da miƙewa zaune, ban da hawaye babu abin da take yi, ta kasa magana, yau abin ya dawo mata sabo, ta tuna komai a cikin ƙwaƙwalwarta, ya ilahi ya lillahi. Ganin bata da niyar yin magana yasa ya ce "Amma dai gaskiya baki yi wa su Abbi adalci ba, kin cucesu kin zaluncesu, dama shiyasa kike guduna dan kada rana irin ta yau ta zo? Baki kyauta musu ba, nima kuma kin cuceni baki kyauta mini ba, amma babu komai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi toilet dan ya yi wanka ya yi sallah lokacin sallar isha ta kusa, dan anyi mangariba kam tun ɗazun, sai kuka take yi, ta rasa bakin magana, kada kuga laifin Dr bai san gaskiyan abin da ya faru bane, ya ma yi mata da sauki da bai sameta a yadda yake tunani ba ya hakura, da wani namijin ne sai ya haɗa mata da mari, amma shi ya danne saboda da Mahaifiyarsa da tata ƴa da kanwa ce, ga shi ta kasance kanwa ce ga babban amininsa ɗaya tilo a duniya, hakan yasa ya daure ya danne abin, amma fa ba karya ya yi mishi ciwo ba kaɗan ba.

Tana kwance har ya fito ya shirya tare da yin sallar mangariba sannan ya fice daga ɗakin zuwa masallaci dan ya yi sallar issha, bayan tafiyarsa ne ta miƙe da kyar ta nufi toilet, har lokacin kuka take yi, wanka tayi tare da ɗauro alwala, fitowa ta yi ta shirya cikin doguwar riga, ta zuba hijabi, ta tada sallah, bayan ta idar ne ta kunna wutar ɗakin tare da gyara gadon fes kafin ta sanya air freshener a ɗakin, har lokacin tana cikin tsananin damuwa na wuce misali.

Bayan ta kammala ta hau gadon ta kwanta, ko wajen Ummi yau ta ji bata bukatar fita, gara mata ta yi kwanciyarta a cikin ɗaki kawai, Ummi kuma tana palo tana jiran su zo su yi hira, dama haka suka saba yi, idan sun ci abinci sai su fito su sha hira zuwa karfe tara kowa ya wuce bedroom nasa, to yau dai hayewa saman bed nata ta yi ta kwanta tana tunanin abubuwan da suka faru da ita a rayuwarta ta baya, sai yanzu take jin cewa Rufee ta cuceta, ta gama da rayuwarta, da alama dai asirin da Rufee ta yi mata ya sake ta ne, to anya ba bokan bane ya mutu ko kuma Rufee ne ta fito ta warware asirin da kanta? Mu dai je zuwa zamu ji komai.

A ɓangaren Dr ma, da kyar ya iya yin sallah dan ɓacin rai, shi da tun farko ta gaya mishi ita ba budurwa bace ai da ya fi mishi, matsalar kuma da aka samu shi babban likita ne, duk wasu matsaloli na mata ya sani, dole zai gane ita ba budurwa ba ce, idan kuma da kansa ya gane dama dole a sami irin wannan matsala, farkon abin da zai fara tunani ma to da waye ta kwanta? Wani irin mutun ne? Yana ɗauke da wani ciwo or not? Ita ɗin lafiya take or not? Koma dai akwai karamin ciki a jikinta? Tambayoyi dai kala kala zai yi ta yi wa kansa wanda kuma daga haka babu samun yarda kenan a tsakaninsu, dan zai yi ta tunanin ai bin maza take yi, ya Allah ka tsare mana imaninmu mutincinmu da martabanmu, masu yi wa yaran mutane fyaɗe ku dubi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login