Showing 264001 words to 267000 words out of 359620 words

Chapter 89 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1970

Sai dai fa yaki yardawa kansa sonta yake yi, shi dai ya bari a wata alaƙa kawai or tausayi, dan a cewarsa bai ga abin da zai so a wajenta ba, sai dai idan renonta zai yi.

Lokacin da ya dawo gida, ya dawo ne da niyar ya taka mata birki a kan kada ya sake ganinta a in da yake, kada ta bari ya sake ganinta a gidan nan, duk yanda zata yi ta yi kada su haɗu, baya son ganinta, amma da ya shigo cikin bedroom nasa ya sameta, sai ya ji ba zai iya aikata hakan ba, shi ne ya wuce ya yi wanka ya yi shirin barci ya kwanta, yana jin yunwa amma yaki cin abinci saboda yana yaki da zuciyarsa wajen cireta, lokacin da ta yi mishi magana sai ya ji ya mance da komai hakan tasa dole ya ci abincin ba dan ya so ba.

So yanzu ya fahimci dole akwai wata alaƙa mai karfi a tsakaninsu, ya kuma hakura ya dai'na tilastawa zuciyarsa a kan ta dai'na tunaninta, dan ya gano hakan ba zai yiwu ba, ya yi sake face nata ya zauna a cikin zuciyar tasa ta yanda ba zai ciru ba, shi ne ya hakura ya karɓi kaddararsa. Mu koma kan labarinmu.

Miƙewa ya yi ya ɗauketa a kafaɗarsa zuwa cikin toilet ɗin, saman wani kyakkyawan chair ya zaunar da ita kafin ya haɗa mata ruwan wankan da kansa, bayan ya kammala ya sauketa kasa daga saman chair ɗin tare da kwance mata sarin ya cire pil dake jikin wanda ta yafo a kafaɗarta, sannan ya fara warware mata shi, bayan ya cire shi ne ya yi ƙoƙarin cire mata vest ɗin jikinta, daga ta kasa kuma irin short ɗin nan ne masu matse mutun mai jikinsa roba shi ta sanya.

Yana damko vest ɗin da nufin ya cire, bata san lokacin da a sukwane ta sanya hannunta ta rike dan kada ya cire ba, ko a jikinsa ya sake mata ya juya ya fice abinsa, saman bed ya haye bayan ya ɗaura sarin nata a saman sofa, wayarsa ya ɗauko ya yi wa Mark text a kan ya kawo musu abinci, yana gama rubutawa ya kwanta yana tunanin irin nasa kaddarar kenan, wai tunanin wannan halitta a cikin zuciyarsa tab, babban bakin ciki shi ma ɗaya shi ne wai wannan ƴar yarinyar, wannan kam renonta kawai zai yi ne ko ya ya? Ya rasa me ma yake tunani a kanta, shi dai face nata kawai ne yake yi mishi yawo a kwakwalwarsa, idan kuma ya yi ƙoƙarin tilastawa kansa rabuwa da tunaninta to fa ba makawa zai cutar da kansa ne a banza, kuma ba dai'na tunanin zai yi ba............ Eh to lallai Lion har yanzu da sauranka ba kaɗan ba, wato har yanzu baka dai'na ganin mata a halitta ba, to dai ga karamar halitta na neman zautar da kai😌🙃

Da gudu Brady ya shigo ya haye jikinsa, Mark ya bashi abinci ya ci ya ƙoshi abinsa, sai murna yake yi, shafa gashinsa ya fara yi, ita kuma tun da ta shiga toilet ɗin sai ta fahimci ba'a toilet na gida take ba, mamaki ne cike fal ranta, haka ya lallaɓa ta karisa wajen baf ɗin wankar, shiga ciki ta yi tare da fara yin wanka.

After some minutes Mark ya shigo musu da abinci cikin wasu tsadaddun kayan abinci masu tsananin kyan gaske, akwai table na cin abinci ɗan madaidai ci a cikin ɗakin, sai tashin kamshi abincin yake yi tun ma ba'a buɗe shi ba, a saman table ɗin ya ɗaura musu abincin, yana fita ita ma ta fito daga cikin toilet ɗin daure da towel fari kal mai bala'in kyau da tsada, da yake towel nasa ne yana da ɗan girma, sai ya saukan mata har zuwa gwiwa, tsayuwa ta yi tana tunanin wai a ina ma suke ne? Sam bata lura da glass ɗin dake gefe ba, ƴan waige waige ta fara yi can ta hango trolleys guda uku, ɗago kai da zata yi idanunta suka sauka a kan glass ɗin, baki ta saki tana kallon tabkeken ruwan da suke ciki, a hankali ta ɗaga idanu sama tana kallon saman ɗakin nasu, ta rasa gane a ina suke, tunani ta fara yi ta saka kaya ta shirya sai ta fita waje ta duba, da wannan tunani ta nufi kusa da gadon.

Idanunsa a lumshe kamar mai barci, kusa da shi ta zauna cikin natsuwa ta ce "Yaya Saif kayan sakawa". Tana tsoron taɓa mishi trolleys ɗin nasa ne kada ya yi mata faɗa, shiyasa gara ta tambaye shi, dan yanzu ma tasan tabbas ta ɓata mishi rai, taga hakan a face nasa, so tana gudun kara yin wani laifi.

Shiru bai amsa ba kuma bai ɗago kai ba, sai Brady ne sarkin gulma ya ɗago kai yana kallonta, harara ta watsa mishi ta tsani karen nan tun da yake takura mata.

Haushi ya daka mata shi kuma yana ƙoƙarin tashi daga jikin Lion ɗin dan ya yi kanta, rike shi Lion ɗin ya yi ba tare da ya buɗe idanu ba, can kasan maƙoshinsa ya ce "Me kika yi mishi?" Mamaki ne ya kamata, lallai Brady ya cika munafukin, yanzu dan ta harare shi, shi ne dama zai mike ya yi kanta? Wato har Lion ma ya gane anyi mishi wani abin kenan? Wannan kare akwai ɗan iska, ɗan bala'i ne, abu kamar wani mutun, yasan komai.

"Babu abin da nayi mishi fa". Ta faɗa tana kumbura kumatu ita a dole ta ji haushi. Haushi ya kuma dakawa irin kamar karya take yin nan, baki ta saki tana ganin ikon Allah wajen karen nan, shi kuma Lion rungume shi ya yi yana shafa jikinsa alamar lallarashi, harara ta watsa musu dukkansu biyu a cikin zuciyarta tana faɗin "Kasan yanda zaka bi da kare a hankali, kasan yanda zaka rarrashi kare da yake dabba, amma saboda mugunta da zalinci baka san ta yanda zaka yi magana da mutane cikin girmamawa da tausasawa ba, ba abin na sami bulala wlh na zaneka ba, iskancin kawai".

A fili kuma shagwaɓe murya ta yi tamkar zata yi kuka ta fara magana "Yaya Saif wlh garin akwai sanyi sosai, kayan sakawa, Allah sanyi nake ji ba kaɗan ba". Mikewa zaune ya yi tare da Bradyn nasa a jikinsa, waro idanuwansa ya yi a kanta, kasa ta yi da kallonta, shi kuma zubawa dogon wuyarta idanu ya yi yana mata wani irin kallo, murza yatsun hannunta ta shiga yi tana wasu ƴan kame kame kamar mara gaskiya, duk kunya ta isheta, bata yi tunanin zai tashi ba, da yake tasan halinsa sai dai ya yi magana daga kwance idanu a rufe, so bata yi tunanin zai tashi ba, shi kuma ya tashi ne ma dan ya sauka kasa ya ci abinci bayan ya gaya mata ga in da kayanta suke kenan, yunwa shi ma yake ji.

Ganin bai yi magana bane yasa ta ɗan ɗago kallonta dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, wani irin azababben kunya ta ji, da sauri ta miƙe dan ta bar wajen ta koma cikin toilet ɗin kawai, hannu yasa ya riƙota a kugu, kasa ta yi da kallonta tana jin kirjinta na bugawa da sauri da sauri, kasa jurewa ya yi har sai da ya jawota jikinsa, kusa da Brady ta kwanta a gefen kirjin nasa kenan, haushi Brady ya fara yi alamar ta tashi mishi a jikinsa, ai jikin Lion nasa ne shi kaɗai, cikin faɗa ya tashi yana daka haushi tare da yin kanta da nufi zai cijeta da gaske, ihu ta kurma tare da rike Lion ɗin kam, zubawa Bradyn idanu ya yi yana kallon haukan da yake yi.

Sai da ya ga da gaske zai kai mata cizo ne ya hana shi ta hanyar yi mishi magana, da sauri ya dawo kusa da face nasa yana wani buɗe baki shi ala dole cizo zai yi. Magana Lion ɗin ya yi mishi a cikin kunne ta yadda Rimsha ba zata ji me suka ce ba, wani girgiza ya yi tare da daka tsalle ya diro kasa ya koma saman sofa ya kwanta kamar mai jin barci.

Ita kuma ta kankame shi sosai tana kuka kasa kasa, shiru ya yi yana jin kukan nata, har ga Allah bashi da yawan magana, bai ma iya dogon magana ba, so ba zai wani iya magana da ita da baki ba wajen rarrashi, sai kawai ya ɗagota da kyau ya gyara mata kwanciya a kirjin nasa yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, rike shi ta yi a gefen kafaɗarsa tana sauke ajiyar zuciya, hannu ya kai yana goge mata hawaye.

Ganin taki dai'na kukan ne yasa ya ce "Ya isa haka to sarkin rigima". Ya yi maganar kasa kasa, ɗago idanunta ta yi tare da kan nata gabaɗaya daga saman kirjin nasa, ƴan waige waige ta fara yi tana neman Bradyn, zuba mata idanu kawai ya yi tamkar kurma haka ya yi yana kallonta.

Ganin Bradyn baya saman bed ɗin ne yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗan ɗagowa dan ta saci kallonsa, 4 eyes suka yi da blue eyes nasa, tana ƙoƙarin kawar da kallonta daga kansa ya sanya hannu ya tallaɓo haɓarta yana mai karewa face nata kallo, runtse idanu ta yi gam. "Meesha". Ya furta kasa kasa, na'am ta amsa mishi amma taki buɗe idanu, shi kuma sleeping eyes ɗin yake son kallah ta kama ta rufe mishi kayansa.

Shiru ya yi yana tunanin me zai yi mata ta buɗe idanun nan ya yi ta kallonsu, ranƙwafowa kanta ya yi tare da haɗe gashinsa da nata, wani irin tsorata ta yi, nan take jikinta ya fara kerma, tunani take yi wai me kuma zai yi mata?. Zazzakar muryarsa ne ya katse mata tunani da cewa "Open your eyes".

Turo ɗan bakin nan ta yi har sai da ya taɓa nasa lips ɗin da yake fuskokinsu a haɗe, a tsananin shagwaɓe ta ce "Allah yaya Saif ni ba zan iya ganin cikin idanunka ba, sai dai ka rufe ido ni kuma na buɗe". Jikinta na kerma take maganar, kamar yanda jikinta yake kerma kuma haka laɓɓanta suke kerma, ba ƙaramin tsuma shi suka yi ba yanda suke kerman nan, ga shi yanayin yanda take motsasu tana magana, ya ilahi ya lillahi har wani irin shock yake ji a jikinsa, uwa uba ga shagwaɓar da take zuba mishi wajen yin magana, ta gama kwance mishi lissafin ƙwaƙwalwa.

Sam bai san time da ya ɗaura lallausan lips nasa a saman..........


E 67-68




Sam bai san time da ya ɗaura lallausan lips nasa a saman tata ba, wani irin azababben daɗi laushin lips nata suka yi mishi, ita kuwa a sukwane ta waro idanunta waje sosai, kai tsaye sai cikin nasa idanu, da yake shi bai san menene kunya ba, tsareta da idanu ya yi tare da capko lips nata na kasa ya fara sha, ita kam babu shiri ta mayar da idamunta ta datse gam tamkar zata fashesu, wani irin harbawa kirjinta yake tamkar zuciyarta zai fasa kirjinta ya fito waje, baiwar Allah sam bata taɓa jin makamancin abin da take ji yau ba, ruɗu da shiga firgici yasa sam bata jin abin da yake yi mata, da alama ma ta fita a hayyacinta bata tare da ya sani ba.

Shi kuwa kissing nata yake yi cikin kwanciyar hankali da natsuwa, hannu ɗaya yasa ya tallaɓo wuyarta da kyau, har wani irin azababben shock yake ji daga kansa har tafin ƙafarsa, nan take duk wasu kofofi na feeling a jikinsa da suka shafe shakaru talati a rufe, nan take suka fara buɗewa a yau, gabaɗaya tsikar jikinsa miƙewa ya yi, wani sabon bakon yanayi yake karɓa a jikinsa, shekara talatin bai san da hakan ba sai yau da ko'ina ya buɗe a jikinsa, ba ita kaɗai ce ta fita a hayyacinta ba, har da shi bawan Allah, 30 years yana cutar da rayuwarsa ba tare da ya sani ba, ba wani abin da ya sani fa ce hukunci, kisa da ɗaure fuska sai bada umarni, bacin haka bashi da wani feeling a rayuwarsa, a yau ne ya fahimci waye ne ma shi bakiɗaya.

A hankali ya mayar da hannun nasa ta bayan wutarta a in da ya yi sama da shi zuwa cikin gashin kanta ta bayan, cikin natsuwa ya kwanta da ita a jikinsa yana cigaba da shan lips ɗin nata cikin salo da natsuwa, ko motsi ta kasa yi, da alama bata a duniyar nan bakiɗaya, ɗaga ɗayan hannunsa ya yi tare da ɗaura shi a saman mazaunanta zuwa kugunta yana ɗan shafawa a hankali, nan take numfashinsa ya sauya, har lokacin kuma yana kallon face nata sosai, ganin tana hawaye ne yasa cikin natsuwa ya zame bakin nasa daga tata, tare da juyawa da ita ta koma saman gadon ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa.

Can kasan maƙoshinsa da kyar ya iya furta "Meesha". Bata amsa ba, kuma bata buɗe idanun nata ba, hawaye ne kawai ke gangaro mata daga idanun nata, sai Allah kaɗai yasan me take tunani Baiwar Allah, hannu ya kai sama face nata yana ɗan taɓa kumatunta, yana ambatar Meesha, sam kamar ba ta a wajen ko motsi ta ki yi.

"Why are you crying Meesha?" Ya tambaya yana goge mata hawayen nata, wayarsa ce ta fara ruri alamar shigowar kira, kai kallonsa kan wayar ya yi, Areef ne yake kiransa, kuma video call ne, komawa ya yi ɗan gefe saman pillownsa ya kwanta tare da ɗauko wayar, idanunsa sun yi jawur kamar jini, sai sauke nauyayyar ajiyar zuciya yake yi.

Picking call ɗin ya yi dan yasan idan bai ɗauka ba Areef ba zai taɓa barinsa ya yi numfashin da kyau ba, dan ya rinƙa kira kenan ba kakkautawa, ya kiransu ne kuma dan ya ji sun isa Lagos ɗin lafiya dai ko?.

Yana ɗauka cool murmushi Areef ɗin ya sakar mishi yana zaune a bedroom ɗin su Rimsha, da alama ya je tsokanar Jehan ne.

Assalamu alaikum ya yi wa Lion ɗin yana ɗan daga hannu sama zuwa saitin face nasa a yanda suke gaisuwa kenan, shi ma Lion ɗin amsa mishi sallamar da hakan ya yi.

"Ya hanya ya kuma our Queen?". Cewar Areef ɗin, ya yi maganar yana murmushi, sai yanzu Lion ya fara fahimtar dalilin da yasa su Areef suke cewa Rimsha Queen or Gimbiyar TRIPLETS, tabbas idan hasashensa gaskiya ne dalilin shi suke ce mata hakan.

"Lion meyake faruwa ne? Me ya sami idanunka? Ina sister take? Baka yi mata hukunci ba ko? Ina fatan ka yi mata afuwa?". Areef ya jera mishi tambayoyi.

Ɗan dawo da blue eyes nasa kanta ya yi ta miƙe ta sauko kasan gadon ba tare da ta kalli in da yake ba, tun da ta ji ya yi picking call ta dai'na kukan nata, shi ne ma ta mike ta sauko, toilet ta nufa har lokacin tana hawaye sai dai ba sautin kuka, da kyar take iya ɗaga kafarta saboda gabaɗaya ilahirin jikinta a mace, gaɓoɓin jikinta tamkar an yanke su an rabasu da jijiyar jininta.

"Lion lafiya kuwa?" Areef ɗin ya sake katse mishi kallonta da yake yi. Dawo da kallonsa kan wayar ya yi yana faɗin "Kai ba jami'e bane? To sai ka canka ni ka dai'na tambayata yakake? Ina my pleasure?". Kara faɗaɗa murmushin fuskarsa Areef ɗin ya yi kafin ya ce "Kasan dai zan iya ganewan ai, yanzu dai kun isa lafiya? Ina sister?". Jinjina mishi kai ya yi alamar lafiya ba tare da ya yi magana ba.

"Ina sister ina kewarta sosai?". Ɗan ɗaure fuska ya yi yana faɗin "Idan kana kewarta ai sai ka nemeta ko? Ai bani zaka tambaya ba tun da baka bani ajiyarta ba". "Sarkin faɗa mai da wukar ni ka nuna mini ita mu gaisa dan Allah, ko dai nima kishi kake yi da ni ne a kanta?".

Shiru ya yi bai sake tanka mishi ba, sai magana Areef ɗin yake ta yi mishi ya yi banza da shi, almost 10 mins suka a haka kafin ya ce "Am coming Areef ba sai ka katse kiran ba". Ya kai karshen maganar tare da ajiye wayar a saman bedside drawer ba tare da ya jira amsar Areef ɗin ba ya miƙe zaune tare da zuro kafafunsa kasa ya miƙe tsaye.

Toilet ɗin ya nufa dan ya dubata, zaune ya iskota saman chair tana kuka ta kifa kai da gwigwarta, cikin natsuwa ya karisa wajen nata, hannu yasa ya ɗauketa cancak ya nufi waje da ita, sam taki ɗago kanta bare ta buɗe idanunta, ta san cewa shi ne, so sai bata wani damu ba.

Saman sofa kusa da Brady ya sauƙeta tare da juyawa ya nufi wajen trolleyns ɗin, jin numfashin Brady yasa ta buɗe idanu, ganinta kusa da shi yasa ta miƙe da gudu ta nufi Lion ɗin, jin gudunta yasa ya juyo, yana juyowa ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa tana kuka mai ɗan sauti, shi sam ya manta ma tana tsoron Bradyn, da yake ya saba da sweetheart ɗin nasa, sai yana ganin kamar kowa ma ya saba da shi kuma baya tsoronsa.

Kankame shi sosai ta yi har sai da ta saukar mishi da kasala a jiki, dan yanzu fa duk wasu ƙofofin feeling a jikinsa sun buɗe, abu kaɗan zai iya sanya shi ya ji feeling, dan fa ba'a magana ta wannan fannin oga ne, dama dan bai sani bane bai kuma taɓa kwatantawa ba, shi ne abin baya damunsa, ga kuma yanayin training da aikin da yake yi, shiyasa bashi da feeling ɗin sai yanzu da ita ta zama sanadiyar buɗewa kofofin nasa, yanzu da zarar ta taɓa shi gabaɗaya jikinsa zai amsa ta taɓa shi saɓanin da da zai iya kwana da ita a jikinsa normal ne babu wani abin da zai ji.

Shafa kanta ya yi yana kallon kyakkyawan wuyarta, yana son dogon wuyar nan nata, hannu yasa ya ɗan raba jikinsu ba tare da ya yi magana ba, hannunta ya riko zuwa wajen trolleys ɗin, da hannu ya nuna mata nata tare da wucewa zuwa saman bed ɗin.

Tsugunnawa ta yi a gaban trolleys ɗin ta kwantar da wanda ya ce shi ne nata, zuge zip ɗin ta yi tare da fara duba kayan sakawa, shi kuma wayar nasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login