Showing 285001 words to 288000 words out of 359620 words

Chapter 96 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2030

abu ba tare da sunan Allah a bakinsa ba bawan Allah, komai zai yi sai ya ambaci mahaliccinmu.

Wani irin ajijiya ruwan robar ya yi tare da fallatsuwa sama tamkar an watsa shi, sannan ya koma cikin robar babu ko ɗaya da ya ɗiga a kasa duk irin tashi sama da ya yi, duk cikin ɗakin sun yi matukar tsorata ban da daddyn Rimsha da yake dake yana furta sunan Allah, shi kansa Lion da yake kallonsu sunan Allah ya furta a cikin zuciyarsa, dan kuwa wannan abin sai Allah ne kawai zai iya kare bawansa daga sharrinsu.

Suratul Aaraf Areef ya fara karantawa a cikin ziciyarsa yana mai cigaba da kallon ruwan yanda yake wani irin juyawa da karfi karfi yana fitar da kumfa tamkar mutum ya ci guba, tsit ɗakin ya yi daddy yana ta ƙoƙarin ceto rayuwar Akila, ya ɗan tsaga wutarta kaɗan dan ya samu aikinsa ta yi mishi cikin ƙanƙanin lokaci, idan ba haka ba tana iya mutuwa nan take.

Areef bai matsa daga wajen ba, yana dake yana kiran sunan Allah har sai da ruwan nan ta gama ajijiyarta bakiɗaya ta koma ta natsu tsin, chain ɗin ya kwanta a kasar ruwan, juyowa ya yi yana kallon Lion da ya zuba musu idanu yana kallonsu.

"Waye ya bata wannan chain ɗin?!". Cewar Lion ɗin, ya faɗa a tsawace, ya yi maganar kuma yana mayar da kallonsa a kan Brady da ya shigo yanzu yana ƙoƙarin haukata Rimsha, ya kawo mata wayar Mark ne, ya je ya sami Mark ɗin yana kallon hoton Anaya, shi ne ya kwace wayar ya kawo mata ta gani, dan yasan a wayarta kawai ya taɓa kallon hoton Anaya ɗin, ita kaɗai ya taɓa gani tana kallon hoton, to yau kuma sai ya ga Mark yana kallo, shi ne ya kwace wayar ya kawo mata, ita kuma ta yi muguwar tsorata na hawa jikinta da ya yi yana miƙa mata wayar ta ɗauka cizonta zai yi.

Da gudun gaske ta miƙe daga saman table ɗin ta haye saman bed ɗin wajen Lion tana kuka kasa kasa. Sam bai ji komai ba ko a jikinsa su daddy su Jehan duk suna kallon shi ta cikin camera ya runhumeta yana ɗan bubbuga bayanta, jin kukanta yasa dukka suka ɗago suka zubawa wayar idanu, harta Jehan ɗagowa ta yi cikin sauri dan ta kalli me ya sami ƴar uwar tata take kurma ihu haka, shi ma daddynta ɗagowa ya yi yana kallon wayar da yake Areef ya karɓi wayar dan ya nunawa Lion ɗin yanda chain ɗin ta koma.

Ganin ta haye jikinsa tana kuka ne yasa suka saki baki har su John suna ganin ikon Allah, shi ma daddynta dai mamaki ya yi, har da kara waro idanu yana kallon shin wai da gaske ne Rimsha ce ta haye jikin Lion har haka? To me ya tsoratata da ta hau jikinsa haka? Shi ne abin da daddynta yake tambaya, haurowar Brady saman gadon ne yasa suka fahimci dalilin yin ihun nata da kuma kukan da take yi yanzu.

"Areef i said waye ya bata chain ɗin nan?". Yana magana yana cigaba da bubbuga bayan Meeshar tasa dan ta yi shiru, ya kara ɗaure fuska sosai, sam babu alamar wasa a tattare da shi, nan take kowa dake kallonsa ya sha jinin jikinsa, duk suna tunanin waye ya bata chain ɗin, dan kuwa wannan kara ɗaure fusataccen fuskar nan nasa da Lion ya yi da alama za su ji ne a jikinsu.

"Lion i don't know, ita kaɗai ce zata bamu wannan amsar". Cikin rawar murya John ya amsa da "Ni na bawa Aseef ya bata". Tashin hankali, ya zaɓi ya bada masa ta gaskiya ce, dan kuwa yasan Lion dai ba'a yi mishi karya kuma baka isa ya ɓoye mishi abu ba, idan ma kayi kuskuren yin hakan to ka kwana da shirin tabbas zai gamo koma me ka ɓoye, idan kuma ya gano da kansa to fa zai ninninka maka hukuncin ne a kan wanda ya yi niyar yi maka a baya.

A razane gabaɗaya ɗakin suka mai da kallonsu a kan John ɗin, cikin tsawa tare da ɓacin rai Areef ya ce "Kai ne kenan kake son kashe mini my pleasure? Dan ba matarsa zaka kashe ba, shi zaka kashe, saboda idan ta mutu shi ma ba zai rayu ba!!". Ya kai karshen maganar tare da nufar John ɗin gadan gadan, da karfin gaske ya damko wuyarsa ya shaƙe shi yana faɗin "Before ka kashe shi ni bari na kasheka!!".

Tsawa Lion ya daka mishi yana faɗin ya sake shi, da mamaki ya juyo da ash eyes nasa da suka rikiɗe suka yi jawur Saboda tsantsar ɓacin rai. "Lion cewa fa ka yi na sake shi? Heartbeat namu fa ya yi ƙoƙarin hallakawa, a haka zan kyale shi?".

"Areef i said ka sake shi, calm down mana, ya kamata a ko da yaushe ka yi aiki tamkar jami'i ba mutun kamar kowa ba!". Ciza laɓɓansa ya yi da karfi tare da furzar da iska mai tsananin zafi daga bakinsa, ba haka ya so ba, ya so ne yau ya kashe John da hannunsa, amma tun da Lion ya ce ya sake shi yasan akwai dalili, dan haka sai ya sake shi ɗin yana wani huci tamkar shi ma John ɗin ba ɗan uwansa bane, su dai su ukun nan sune kawai ƴan uwa, a kan junansu zasu iya kisan kai!.

Ita kuma Rimsha jin maganar Areef ne yasa ta ɗago kai daga saman kirjin nasa tana kallon wayar hannunsa, ganin su daddynta bakiɗaya a wajen ne yasa ta yunkura ta gyara kwanciyarta da kyau a saman kirjin nasa tana kallon daddyn nata, shi ma ita yake kallo tamkar ya sa hannu ya jawota ya rungume, tana son ta yi musu magana, amma ba hali domin Lion yana magana da Areef, ba su isa su saka musu baki or su yi wata magana ba har sai sun kammala, ɗagawa daddyn nata hannu kawai ta yi tana sakin kayatatcen murmushi.

Sam daddy bai murmusa ba, dan suna cikin tashin hankali, ta yi mamakin ganin daddyn nata bai yi murmushi ba, Baiwar Allah bata san me yake faruwa ba.

"John who give you this chain?". Cewar Lion, Bawan Allah ya ji shakar manya, tuni ya jiyo kamshin mutuwa, har wani jawur idanunsa suka yi yana fitar da kwallah.

Da kyar ya iya buɗe baki ya ce "Jo....sep....hine ne ta bani su guda uku a kan na bawa matar Michael da kuma wannan da take kusa da kai sai wannan ɗayar." Ya kai karshen maganar tare da nuna Jehan, da kyar ya iya furta sunan Josephine ɗin saboda wani irin azababben shake mishi wuya da aka yi, ji ya yi tamkar ana zare mishi jijiyoyin wuyar nasa, wannan ma dan Allah yasa suna tare da Musulmai ne a cikin ɗakin, da su kaɗai ne kila kashe John ɗin za'ayi. BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI, JOSEPHINE KUMA? TO A INA TA SAN SU AKILA? WAYE YA GAYA MATA ƳAƳAN NATA SUN YI AURE? ME HAKAN YAKE NUFI? WANNAN SHI NE CAKWAKIYA, SHI WAI A TSAKANIN JOSEPHINE DA WILLIAM WAYE MAI GASKIYA NE? MU DAI JE ZUWA.

"Areef ku bashi ruwa ya sha". Cewar Lion, da sauri Jay ya ɗauko ruwan daga cikin fridge ya kawo musu, a cikin zuciya Areef ɗin ya yi bismillahi tare da yin tamkar zai sha ruwan ya tofa ayoyi biyar na farkon suratul baƙara ba tare da sun ankara ba, sannan ya bawa John ɗin dan ya sha, abin da yasa ya yi hakan saboda kowa da yake cikin ɗakin ya lura da irin mawuyacin halin da John ɗin ya shiga na shake shi da aka yi lokaci guda, so shi ne ya taimaka mishi dan su sami abin da suke so.

Kowa da yake wajen ya shiga tashin hankali jin cewa daga wajen Josephine sarkar ta fito, shi kuwa Lion ko a jikinsa, kallon Areef ya yi yana faɗin "Why kake magana da ita a ɓoye ba tare da na sani ba? Kana tunanin na zan gane ba ko?". Ya yi mishi magana ta sigar da ba wanda zai gane nufinsa, dan ya yi maganar ne a matsayinsu na jami'ai wanda ko daddynsu bai gane me ya ce ba, saboda ba baki da baki ya faɗa ba, da laɓɓansa kawai ya motsa suka yi ƴar kurma, da yake Areef ɗin yana kallonsa.

Shi kuwa daddynsu jin John ya ce Josephine ce ta bada chain ɗin ba ƙaramin razana ya yi ba, saukowa kasa daga saman gadon ya yi yana mai kara tambayar John ɗin wace Josephine? Kuma a ina ya ga Josephine ɗin?. Katsesu Lion ya yi da cewa "Its okey dad, komai ya wuce, ni zan yi bincike a kai, dan haka kada ku sake tambayar John, kada wanda ya sake tayar da maganar nan, Areef go out let's talk".

Gabaɗaya ɗakin jikinsu ya yi sanyi, daddyn Rimsha da yake ta ƙoƙarin ya ga sun yafe wa mahaifiyar tasu dan a nashi hangen ba ita ce mai laifi ba daddynsu ne da laifi, amma sai ga shi yau kuma ta yi wani abin da duk mai hankali ya san me hakan yake nufi, kenan da gaske tana tsafi? Kenan ba kungiyar matsafa ɗaya ta shiga ba ne ko ya ya abin yake? Wannan chain da aka cire a wuyar Akila chain ne mai matuƙar haɗari, yana haɗe ne da guba mai karfin da samun maganinsa yana da matuƙar wahala a duniya, sannan an tsafe chain ɗin sosai ta yanda ba wan da zai ga ne cewa na tsafi ne, Aseef ya taɓa chain ɗin har ya ɗaura mata a wuya lokacin da zasu fita zuwa wajen cin abinci, amma lafiya lou ya ci abincin ba tare da wata tangarɗa ba, ita kuma ɗan shafa chain ɗin da ta yi tana ta cewa ya yi kyau ya yi kyau tana yaba kyautar surukar tata tana murmushi, shi ne musabbabin kunnuwar gubar dan dama saboda ita aka yi shi, dalilin kenan da ya sa tana fara cin abincin poison ɗin ya hau kanta ta fara fitar da kumfa, dan ita jinin Hajiya Umaiya ce ma yasa abin bai yi mata kaca kaca lokaci guda ba, da su Rimsha ne izuwa yanzu namar jikinsu ma sai ya zama green color saboda karfi gubar nan haɗe da tsafi, ba sai na gaya muku ba, kun san jinin Hajiya Umaiya baya taɓuwa, yanzu ma dan abin mai bala'in karfi ne yasa ya jijjiga Akilar har haka, amma babu wani ciwo da ya ji mata daga ta ciki, babban nasarar da suka yi kuma lokacin da ta faɗi tana fitar da kumfa a palo, sai ya zamana Aseef ɗin ne kawai ya ɗauketa, daddyn Rimsha ya taɓata lokacin da suka shigo da ita ɗaki, amma shi saboda ya yi askar na safe sai abin bai shafe shi ba, an yi sa'a Jehan bata taɓa ta ba, da wlh sai gawa, su dai jinin William ɗin su suka taɓa ta, shiyasa duk abin bai kama su ba, dan ba dan su aka haɗa ba, dan bakaƙen fata dake kewaye da su aka yi.

Jugum jugum suka zauna a cikin ɗakin, shi kuma daddynsu Lion ya koma wajenta dan ya cigaba da bata kulawa, duk wannan abin da suke yi Aseef yana kwance idanunsa biyu, amma ko motsi baya yi, daddyn Rimsha ya tsorata sosai, tunaninsa kuma damuwarsa ɗaya shi ne Allah yasa kada su ja ƙwaƙwalwar Aseef ta koma kamar ta baya, sai tayarwa da bawan Allah hankali suke yi, suna jefa shi cikin masifa da bala'i, lokacin aurensa da Akila ya sha dakyar bawan Allah nan, yanzu kuma sun sake jefa shi cikin masifar da ta fi ta baya, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, a garin haukarsu na cewa basu son bakaƙen fata ga shi zasu kashe ƴaƴan nasu da kansu, dan kuwa a ƴanda TRIPLETS suke a yanzu, wlh duk wanda aka ce ta mutu daga cikin matansu, to fa sai ta Allah da wuya idan suma basu mutu ba ko wani abin ya same su, dan fa sun kamu da muguwar soyayya mara jin magana, bata sauraron maganar kowa sai na masoyan nasu, fatan mu dai Allah yasa waƴan nan masu jajayen kunnuwa su gane gaskiya su hakura kawai su kyale TRIPLETS da farincikinsu wato matansu. Sai addua'o'i daddyn Rimsha yake tofa Aseef ɗin, amma ko motsi bai yi ba, kuma idanunsa biyu yana kallon kowa a cikin ɗakin, yanzu ma sam ya dai'na hawayen da yake yi tamkar ba shi ba, sai dai jawur ɗin da idanun nasa suka yi kamar wuta ne zai nuna maka yana cikin tsananin tashin hankali.

Areef yana fita waje Lion ya ce mishi "Ka bani amsar tambayar da na yi maka, meyasa kake magana da ita?". "Nothing kawai dai ina so ne naga ko da ba zan je kusa da ita ba, in rinƙa kiranta a waya mu gaisa, in kuma ji idan tana buƙatar wani abin, shi ne kawai yasa nake kiranta". "To meyasa ka gaya mata Aseef ya yi aure?".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Seriously Lion ban gaya mata Aseef ya yi aure ba, ba mu yin irin wannan hirar da ita, gaisawa kawai muke yi sai in tambayeta ko tana bukatar wani abin, amma ana gobe su dad zasu zo Nigeria ta ce mini zata bawa John gift ya kawowa matan da zamu aura a matsayinta na suruka, ni ban tambayeta waye ya gaya mata zamu yi aure ba, dan ban cika jan magana da ita ba, ban kuma ce mata a'a ba, sai na ce mata to kawai zan gayawa John ɗin ya je ya karɓa, bayan mun gama magana da ita na sanar da TGA ya ce da John ya je New York ya karɓo mini saƙon, so ni daga nan na fita harkarsu, ban san ya karɓa ko bai karɓa ba, ban san ya suka yi ba, ban kuma san menene ta ba shi ba, so ban san ya aka yi ya bawa matar Aseef ba".

Nisawa Lion ɗin ya yi kafin ya ce da Rimsha dake kwance a jikinsa "Ina kyautar da John ya baki?" Ɗan ɗago kai ta yi tare da yin shiru tamkar mai tunani dan ita ta manta ma da in da ta ajiye abin. Zuba mata idanu suka yi daga shi har Areef ɗin suna kallonta, wani irin giyar soyayyarta ne take kara fusgar Lion, musamman da ta ɗaga dara daran idanun nan nata sama tana tunanin in da ta ajiye chain ɗin, hakan ba ƙaramin tafiya da imaninsa over ya yi ba.

"Sister kin manta da ni ko?" Cewar Areef, sauko da idanunta a kansa ta yi tana ƙoƙarin yin magana Lion ya rufe mata baki yana faɗin ta bashi amsar abin da ya tambayeta first tukun nan. "Yaya Saif kyautar da John ya bani fa ina ga yana gida cikin drawer kayanmu, dan zan tafi school ne da safe ya bani, sai na kai ɗakinmu na ajiye na tafi, daga school kuma sai nan muka zo ai, so yana cikin drawer". "Da ke da waye ya bamawa?".

Kwantar da kanta a saman kinjin nasa ta yi tana faɗin "Lokacin ni da Jehan ne kawai a palon saman, ya bawa Jehan ɗin ta ce bata buƙata, na ce ta karɓa mana ta ajiye ta ce mini bata yi ra'ayi ba kuma ba zata karɓa ba, shi ne ni na karɓa dukka biyun har da natan a kan idan na dawo daga school zan lallaɓata ta karɓa".

Nauyayyar ajiyar zuciya Areef ya sauke, shi dai masifar Jehan ta yi mishi rana ato, shiyasa yake bala'in son masifar nan tata, dan kuwa tana tsare kanta daga shiga bala'i sosai, da yanzu irin Rimshar ce ita, ai da ta karɓa ta koma ɗaki ta buɗe kwalin ta ciro shi ta saka a wuyarta, ai da tana ciro shi ma zata zube kasa kafin a kawo mata wani taimako ta mutu, amma sai Allah yasa ita ɗin ba komai ne take kulawa ba, wannan abin ya yi mishi daɗi, ya ji ya kara sonta sosai, wlh da Rimsha ba school zata tafi a lokacin ba, da tsab zata je ɗaki ta buɗe kwalin ta cirosu dan ta ga menene a ciki ki, kai Jehan duniya ce, mace mai jan aji da tsare gida da halin ko in kula ga masifa da faɗa ma ta yi a rayuwar nan, musamman irin ita Jehan ɗin da idan ka iya zama da ita zaku zauna lafiya, raini ne bata so, bazata shiga harkar ka ba, kai ma kada ka shiga tata, abin da yasa kenan bata karɓi kyautar John ɗin ba, saboda a cewarta babu wani abin da masu jajayen kunnuwar nan zasu bata da bata da shi, ita tafi karfin wani ma ya yi mata kyauta, bare ma yanda suke dirama da Areef ai ba zata karɓa ba dama.

"Areef sai ka je ka ɗauki chain ɗin dukka biyu ka haɗa dana matar Aseef ɗin ka kai mini bedroom na sai na dawo, na gaji da wannan bala'i na daddy da mummy, amma bari na dawo duk sai na yi maganinsu, ka ajiye komai yanda ya dace sannan ka kwantar da case ɗin sai na dawo, ka da ka sake kiranta a waya kuma daga yau, za mu yi waya anjuma!!". Okey ya amsa mishi da shi, sannan suka yi sallama.

Cikin shagwaɓa ta ce "Yaya Areef wato ma katse kiran ka zaka yi ko? Ina jiran ku gama magana shi ne har da cewa yaya Saif sai anjuma kenan?". Tana magana har da turo baki, "Sorry our Queen, ai naga kamar baki tare da ni ne shiyasa na ce bari na barki sai kin sauko ki ɗauki wayarki". Areef sarkin iya magana a dunkule, nan ma magana ya gaya mata daga ita har Lion ɗin, dan Lion ne ya ce mishi zasu yi waya anjima abin da bai taɓa ce mishi ba, hakan na nufin yanzu lokacin matarsa ce kenan, ita kuma ta wani lafe a saman kirjin mijin nata tana wasa da yatsun hannunsa ta ce wai zata yi magana da shi, lallai sun raina mishi wayo nema, shi ne ya yi musu magana a dunkule,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login