Showing 69001 words to 72000 words out of 359620 words
a baki to, kila idan na baki, zaki iya yi mini magana" . Har wayau cikin harshen turanci ya yi maganar.
Kara rikicewa ta yi, wlh haka yake ce mata a waya, sai ya ce ta zo ya bata coffee a baki, amma yanzu ya nuna kamar bai gane ta ba, lallai ma mutumin nan ya kware a iya basaja, shi ɗin number ɗaya ne.
Shi kuma ya kasa hakuri ya shareta, yana son ta saki jiki su yi hira, dan haka sai ya miƙe ya dawo kusa da ita, a saman sofar ya zauna yana faɗin "To buɗe baki na zuba maki". Yana magana yana kawo mata cup ɗin saitin ɗan bakinta.
"Na ƙoshi ni kam!" Shi ne abin da ta faɗa, kuma cikin harshen Hausa ta yi maganar, ga mamakinta sai ta ji ya ce "No open your mouth". Shi kuma dai da turanci yake magana, kwata kwata yaki furta ko word ɗaya da Hausa, amma kuma ga dukkan alamu dai yana jin yaren, tun da ga shi idan ta yi magana yana ji har yana amsa mata da English.
A wannan hali Imran ya shigo ya same su, har cikin ransa bai ji daɗin dressing dake a jikinta ba, ya ji haushi sosai, yana ƙoƙarin hana Rimsha yin irin wannan shiga, ita kuma ta zo ta yi, sai dai bai damu ba dan ya ganta kusa da Areef, yasan halin Areef sarai da wasa da dariya, kuma Areef ya yi mata farin sani, ita ce bata san shi ba, tun suna makaranta Imran ɗin yake yawan basu labarin Heartbeat ɗin sa, idan sun je yin shopping na school, in ya ga wani color irin wadda take so, yana ce masu ga irin color da my Heartbeat take so, a takaice dai Areef ya santa sosai, ita ce bata san shi ba, bata taɓa ganinsu face to face ba, yanzu haka akwai hotunan ita Akilar ita da Imran da Akil duk akwai hotunansu a wayar Areef ɗin, yana ma da hotonta tun bata kai haka ba, lokacin tana karama, lokacin suna school da Imran, idan ta turo ma Imran ɗin hoton, sai Areef ɗin ya ce ya tura mashi zai ajiye hoton kanwarsa, duk lokacin da ya je Nigeria in ya ganta a hanya ya ganeta, wasa wasa Areef ya tara hotunanta dayawa a email nasa, idan baku manta ba shi dai Areef na kowa ne, ya iya zama da mutane sosai da sosai.
Ganin Imran yasa ta miƙe da sauri zata rungume shi, sai ta tuna idan ta rungume shi yau sai sunyi faɗa da masoyin nata, domin kuwa ko hannunta wani ya taɓa sai sunyi faɗa da shi, sai ya yi fushi, kuma bata son fushinsa ko kaɗan, dan haka sai ta fasa rungumar yayan nata, ta tsaya a gefensa tana karewa Areef kallo.
Mamaki sosai Imran ya yi akan meyasa bata rungume shi ba, bayan kuma ta saba yin hakan?. Hannunta ya riƙe suka zauna yana mai yi mata faɗa akan irin wannan shiga da ta yi, sai binsu da ash eyes nasan nan yake yi, yana ta murmushi.
"Prof where is my Rimsha?" Ya tambaya yana ƙoƙarin kunna hasken screen ɗin wayarsa. "Ta je kaiwa Saif abinci". Cool murmushi ya saki kafin ya ce "Saif!! Saif!! Hmmm wlh Saif idan Allah ya tashi kama shi ba zai yi mashi da kyau ba, ya yi laifi dayawa wlh, Allah dai ya yafe mashi, ni bana da wani damuwa, dan na san our Queen tana da kirki, shiyasa ma fa na zaɓa mashi ita, tana da hakurin jure halinsa, zata jure, yana da saurin hawa, shi ma wannan zata jure, zuciyar bala'i, zata jure, nuna tsantsar isa akan abin da ba mallakinsa ba, ya dage sai ya juya kowa da kowa ya zama kamar uban kowa, shima zata jure, sai dai kuma kasan me nake tunani Prof?".
Girgiza kai ya yi alamar A'a. "Yana da matukar wuyar gaske uncle Hosain ya bawa ɗan uwana Rimsha". "Meyasa ka ce haka Areef?". "Hmmmm kai baka san faɗar dake tsakanin uncle da Lion bane, ni ranar da uncle ya zo aka ce sister ƴarsa ce, ba abin da ya faɗo mani a raina face wannan rikici dake a tsakaninsu, Lion fa ya mayar da uncle kamar wani yaron shi ne, fata na dai Allah ya daidai ta su kafin nan".
Amin suka amsa da shi, daga nan suka yi shiru kowa da abin da yake tunani, shi Areef yana tunanin da ace idan Lion ya gama warware case ɗin Musharraf ya ɗauki mataki a kai, to da zai gayawa Musharraf ɗin, wata kila ya yafe mashi, mari da kuma abubuwa da ya yi mashi, sai dai shi Lion baya abu ya faɗa, kamar yadda bai tambayesu menene gaskiyar abin da ya faru ba, to haka idan ya binciko gaskiya ba gaya masu zai yi ba, idan ma yaga suna da laifi, sai dai ya sanya a hukuntasu ba tare da sun san waye ya hukunta su ɗin ba, kuma a kan me aka hukuntasu ɗin, mafiya yawancin lokuta haka yake yi akan wadda suke tare, shi wani irin bahagon mutun ne da baka gane mishi, idan kuma haka ne akwai gagarumin matsala, domin shi ma daddyn Rimsha zuciya gare shi kamar me, tun da ga shi har yau ya kasa mance abin da su Abba suka yi mashi, kuma yana sane sun yi nadama, duk da haka ya riƙesu a rai, to fa da alama haka ya riƙe Lion ma a rai.
RIMSHA💋
Kai tsaye kitchen ta nufa, kamar kullum sai da ta wanke hannunta kafin ta ɗauki abincin ta fito, a bakin kofa ta tsaya ta yi mashi sallama, yana ciki, yana zaune a bakin bed nasa yana fuskartar kofar shigowa.
Kutsa kai cikin ɗakin ta yi, ta kasan idanunsa ya kalleta, bai ga fuskarta ba, saboda bai ɗago ba, a yadda ya kalleta ba zai wuce ya kalli daga kafafunta zuwa kugunta ba, sai dai shi ma kugun nata tray ɗin abinci da ta ɗauka ya rufe shi.
A in da ta saba ajiye Mishi ta je ta ajiye tare da zama tana jiran shi. Shiru shiru almost 20 mins yana zaune a haka, har ta fiddaran zai ci abincin, sai kuma ta gan shi ya miƙe ya nufeta, ita ma dai ta kasan idanunta ta saci kallonsa, yau sanye yake da short zuwa cinyoyinsa, daga ta sama kuma polo t-shirt ne, dukka farare ne tas tamkar yanzu ya cirosu daga ledarsu, kyawawan fararen cinyoyinsa masu ɗauke da bakin lallausan kwantaccen gashi a waje.
Tun da ya taso daga saman gadon take kallon kyawawan fararen kafafunsa har ya iso in da take, a in da ya saba zama ya zo ya zauna, saboda tsabar kyan fararen kafafunsa sai ka rantse da Allah bai taɓa taka kasa ba saboda haske da kuma kyan ƙafafuwansu, sai santin su take yi tana yabasu a cikin zuciyarta.
Abinci ta zuba mishi kamar ko yaushe, yau ɗan gefenta da ɗan nisa ya zauna, ta dukar da kanta kasa tana zuba mishi wasu daga cikin cimarsu, shi kuma ya ɗago kai zai kalli abin da take zuba Mishi ɗin, karaf sai saman kyakkyawar dark black curly hairnta dara daran blue eyes nasa suka sauƙa, gashi Akila ta hana ta sanya ɗankwali, ta saki gashin har baya, mai da kallonsa kan plate ɗin ya yi, gently ya ce "Is okey". A nitse ta dagata da zuba mishi, ya ɗan yi mamaki, idan tana aiki tana yin komai a nitse, amma idan ba aiki take yi ba akwai bala'in shegen rawar kai kamar me, to me yasa hakan kenan?.
Spoon ya ɗauka ya fara cin abincinsa kamar yadda ya saba, ita kuwa yatsun kafarsa kawai ta zubawa idanu, har ga Allah sun yi mata mugun kyau ba kaɗan ba, ji take yi kamar ta sanya hannu ta shafosu.
Yana tsaka da cin abincin Aseef ya kira shi video call, da hannu ya yi mata nuni a kan ta miƙo mashi wayar ba tare da ya yi magana ba, cikin natsuwa ta miƙe ta nufi saman bedside drawer, ta ɗauki ta dawo ta miƙa mishi.
Karɓa ya yi tare da yin picking na call ɗin, saman table da Areef ya ajiye wayar ranar, shi ma a nan ya ɗaura tasa yana cigaba da cin abincinsa.
Ganin Rimsha yasa Aseef sakin kayatatcen murmushi. "Our Queen!" Ya ambaci sunanta da ɗan karfi, jin muryarsa yasa ta ɗago kai da sauri, cool murmushi ta sakar mishi, sai kuma ta sake ɗaure fuska tare da ɗan komawa baya kamar taga abin tsoro, da mamaki yake kallonta yadda ta ɗaure fuska lokaci guda.
"Lafiya Rimsha? Kina murmushi kuma kika sake ɗaure fuska, me ya faru?" Ya yi magana yana shafa gashin jikin coper da Lucky dane kusa da shi, ɗan turo makin nan nata ta yi, a shagwaɓe ta ce "Yaya Aseef waƴan nan karnikan kusa da kai ne suka bani tsoro ai, bana son su".
Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Okey to bari na fita daga ɗakin nasu sai mu yi magana ko? Idan na fita zaki yi mini dariya ai ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e zata yi mishi.
Miƙewa ya yi daga shi sai shot da singlet farare tas a jikinsa, waje ya nufa, haushi su Lucky suka fara daga mishi alamar basu son ya fita, da sauri ta toshe kunnuwanta tare da kawar da kallonta daga kan wayar zuwa gefe, shi kuwa Lion tamkar babu shi a cikin ɗakin, abincinsa kawai yake ci cikin kwanciyar hankali.
After some minutes, a hankali ta zame hannayen nata da kunnuwanta da ta toshe tare da mai do da kallonta a kan wayar.
"Sarkin tsoro". Ya ambata yana ɗaga mata gera ɗaya, wow Aseef shi ma fa ba dai kyau ba, bakin nan nasa ɗan ƙaramin.
Cikin zolaya da wata kwaɓaɓiyar Hausarsa da ya koyo wajen Musharraf ya ce "Ina kowa (ina kwana)". Bata san lokacin da dariya ya subce mata ba, wai ina kowa, babu kowa ne to.
Tana tsaka da dariya ta tsingayo zazzakar muryarsa ya daki dodon kunnenta "give me water". Cikin sauri ta daidai ta natsuwarta tare zuba mishi ruwa ta miƙa mishi, karɓa ya yi tare da kaiwa ɗan bakinsa ya fara sha.
Cigaba da janta da hira Aseef ya yi, ba dan ta so ba ta rinƙa biye mishi, tana tsoron kada Lion ya koreta a ɗakin ne idan ta cika surutu, abin da bata sani ba shi ne, matikar pleasure sa (farincikinsa) zai yi farinciki ya yi murmushi, to zai iya jure surutun nata, shi bai damu da kowa ya shiga kunci ba, matikar TRIPLETS nasa suna farinciki to bukatarsa ta gama biya a duniya.
Sun sha hira da Aseef sosai, ta rinƙa cin gyaransa a kwabaɓɓiyar hausar nan tasa, sai dariya yake yi har da kyakyatawa, sai da ya kammala cin abincin zai miƙe ya ɗauki wayarsa ba tare da kalli in da take ba ya wuce saman sofa ya zauna, ita kuma fara haɗa kayan abincin ta yi.
Yana zama Aseef ya sa mishi kuka akan shi bai gaji da magana da Rimsha ba, tamkar bai ji me Aseef ɗin ya ce, ya yi banza da shi, daga karshe ma katse kiran ya yi tare da ajiye wayar a gefensa yana mai kishingiɗa a saman sofar.
Kwashe kayan abincin tas ta yi tare da ficewa daga ɗakin ta nufi waje, kitchen ta fara komawa ta ajiye kayan kafin ta wuce garden wajensu Akila.
Tasha ruwan mamakin ganin Imran da Areef a wajen, duk da cewa tasan wajen zamansu ne, amma bata yi zaton ganinsu yanzu a wajen ba.
Kusa da Akila ta je ta zauna, da fara'a Areef ya ce ya mata "Our Queen gaskiya yau kin yi kyau over". Ba ƙaramin faduwar gaba Akila take ji ba a duk san da ta saurari muryarsa, to me yake nufi da ya nuna bai gane ta ba? Ko dai ya fi son ya kai kansa da kansa gida ne? Sai jerowa kanata da kanta tambayoyi take yi.
Wayarta dake hannunta ne ya ɗan yi kara alamar shigowar saƙo, jikinta duk a mace ta kunna hasken screen ɗin wayar dan ta duba saƙon wanene.
Ganin saƙon ɓoyayyen masoyi ne yasa ta ɗago da sauri ta kalli Areef, kansa na duke a kan wayarsa yana latsawa, da alama dai shi ma wani saƙon yake turawa, ko yake rubutawa, dawo da kallonta a kan wayar tata ta yi, password ɗin wayar ta fara cire wa, kai tsaye saƙon ta buɗe. "My heartbeat sarkin ruɗu da son sanya ƙwaƙwalwarta a cikin tunani, yanzu me na tunanin ni ne ko bani bane? Bayan kin rigada kin san ni, shiyasa fa tun farko naki turo miki hotona, dan bana son ki ganni a wani waje ma ki gane ni har sai na kawo miki kaina gida, amma kika takura mini na turo miki hotona, duk da haka sai kin sake shiga ruɗu a kai na?". Zaro idanu ta yi tana karanta saƙon, da hausa ya rubuta mata kamar yadda ya saba, ita kam gaskiya yanzu ta kara tsorata da lamarinsa, ta sare sosai, anya zata iya jurewa ta cigaba da nuna mishi tamkar bata gane shi ba kuwa? Anya ma zata iya cigaba da soyayya da shi kuwa? Ta tambayi kanta, wani ɓangare na zuciyarta ne ya bata amsa da cewa, to ya zaki yi tun da kina son shi, ko dai akwai wani da kike yi wa rabin son da kike yi mishi ne?. Shiru ta yi ta rasa ina zata sanya rayuwarta ta ji daɗi, har lokacin sai dukan uku uku kirjinta yake yi, su Rimsha sun lula duniyar hira sun barta a duniyar tunani, kwata kwata bata jin me suke faɗe, daga karshe ma miƙewa ta yi ta nufi waje, Imran na kiranta amma ina bata ji ba, bata tare da su.
Binta da ash eyes nasa ya yi yana kare mata kallo har ta fice, dawo da kallonsa a kan wayarsa ya yi tare da cigaba da abin da yake yi na latsa wayar, da sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayanta, su kuma su Imran suka cigaba da hiran da suke yi.
A ɗaki zaune saman tsakiyar gado ta iso ka, kusa da ita ta zo ta zauna tare da taɓata tana faɗin "Aunty Akila lafiya kuwa?". Ƴar firgita ta yi tare da juyowa suna fuskantar juna, idanuwanta cike tap da kwallah, babu ɓoye ɓoye babu komai ta fara bawa Rimsha labarin halin da take ciki, yanzu ta rasa mafita, tana magana tana hawaye.
Dafata Rimsha ta yi ta fara bata hakuri, wani saƙon ne ya sake shigowa wayar Akilar a wannan lokacin, kin buɗewa ta yi, ta ce ita ko mutuwa zata yi sai dai ta mutu, amma ɓoyayyen masoyi ta hakura da shi, karɓar wayar Rimsha ta yi ta buɗe saƙon, rubutu ne kamar haka. "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, na san nayi wasa sosai da ƙwaƙwalwarki, amma ki yi mini afuwa, ba zan sake ba, wlh waya ta yi kaɗan wajen ɗaukar sorry dake cike a bakina, girman laifin da nayi, sorry a waya ya yi kaɗan ya goge shi, ki bani dama gobe kamar yadda na faɗa zanzo har gida, na yi alkawarin zangoge dukkan laifukana, dan Allah kada ki yi fushi dani, kin san cewa kece bugun numfashina ko? Tun ba yau ba ina gaya miki hakan, kin ɗauka wasa nake yi ne ko kuma kawai kalamai ne irin na masoya da suka saba faɗa? To idan haka kike ɗaukar kalamaina ki daina, duk abin da zan gaya miki na kalmar soyayya, wallahil azim da gaske nake yi, da gaske daga karkashin zuciyata take, ni ban taɓa soyayya ba sai a kanki, tun hotonki na farko da Prof ya turo mini na kamu da son ki, ban sanki ba, ban san halinki ba, amma zuciyata ta kamu da masifaffen Kaunarki, mace ta yi mana illar da ba za mu taɓa mancewa da shi bane, Shiyasa dana kamu da sonki na zaɓi na gwadaki ta wannan hanyar, ban taɓa yarda da mace ba sai a kanki ke da Rimsha, dan Allah ki fahimceni, ki gane abin da nake nufi, ki gane abin da ya sanya na saka miki idanu da kuma duk wani motsin da zaki yi ina gani, ki gane dalilin da ya sanya naki gaya miki ni waye, ina son ne ki soni domin Allah ba dan wani abu ba, ina son ne ki soni kamar yadda nake son ki, hakan yasa nayi miki wasa da hankali na kuma ki gaya miki waye ni, amma ai hotona na gaskiya na tura miki dan bana son ganinki cikin damuwa, kin shiga damuwa sosai a kan kina son gani na, hankan yasa na baki hotona tun na 22 years, na tuba My Heartbeat, ki fahimceni bugun zuciyata, wlh ba zan sake ba, yanzu komai zan rinƙa gaya miki gaskiya ne, ba zan sake ɓoye miki komai ba, i really love you more than anything except my TRIPLETS and Prof, idan kika ciresu, kece mutun ta farko a zuciyata, wlh ban taɓa rokan wani abu a wajen wani ba sai soyayyarki, ban taɓa cewa wani sorry ba sai a kanki, ki yi hakuri ki karɓi sorry na dan kinyi breaking record ɗin TRIPLETS, yau na ce miki sorry". A karshen massage ɗin ya sanya mata emojin kuka da kuma tambarin zuciya.
A bayyane Rimsha ta karanta mata komai, shiru ta yi har lokacin tana ruwan hawaye, tabbas tana yi mishi wani irin mahaukacin makauniyar soyayya, wadda ko kanta bata yi wa irin wannan soyayya, amma kuma har cikin ranta tana jin tamkar taraiyarsu ba zata yiwu ba.
To me yasa take jin hakan❓
Sosai Rimsha take rarrashinta tare da bata baki, cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi ta fara magana "Aunty Akila in dai ɗaya daga cikin TRIPLETS ne, in dai yaya Areef ne yake sonki, wlh ina mai baki shawara da iya gaskiyata da basirata, ina mai gaya miki ki yarda da shi, ba wai dan wani abu ba, ba wai dan ina bin bayansu ba, ni nasan waye yaya Areef a ɗan zama na da shi, wlh, wlh mutumin kirki ne da samun na biyunsa zai yi matukar wahala, ko yaya Imran ne ya ji wannan magana shawarar da