Showing 315001 words to 318000 words out of 359620 words

Chapter 106 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1965

ƙoshi. "Idan mace tana period bata zama da yunwa". Waro idanunta ta yi tana kallon shi, ko a ina ya san wannan karatu kuma? Ta tambayi kanta, bata san cewa shi ma ai ya iya aikin likita da ya koya daga wajen daddynsa, ya san abubuwan da suke yi wa mutun illah ga lafiya, ya san komai kawai dai dan bata shafe shi ba ne yasa baya bi ta kai, kuma kunga shi bai taɓa kula mace ba bare ku san ya sani ko bai sani ba, sai yanzu da suke tare ne yake fito da saninsa a kan abubuwa da yake gigita ƙwaƙwalwarta dan bata taɓa tunanin ya sani ɗin ba...... YO DAMA SHI LION WAYE YAKE GANE IN DA YA DOSA? AI KO YA SANI BA ZAKA TAƁA SANIN YA SANI ƊIN BA HAR SAI IDAN SHI YA FITO YA NUNA MAKA YA SANI, SHI A RAYUWARSA MA BAYA TAƁA BARIN WATA ALAMA DA ZATA NUNAWA MUTUN GA HALIN DA YAKE CIKI KO GA IN DA YA DOSA, DUK SA IDONKA BA ZAKA TAƁA GANE MISHI BA!!.

Ganin ta ɓata sofar da jini ne yasa ya miƙe ya kwantar mata da kanta a saman sofar ta nufi wajen table ɗin cin abincin nasu, ba zai yiwu ta tashi ba saboda jinin da yake jikinta, dole shi zai ɗauko mata abincin dan tun jiya rabonta da abinci, so yanzu kuma a halin da take ciki ga shi sabon fara period ne dole ta ci abu mai ɗumi dan kada ta samu matsala, idan mace tana period sam zama da yunwa ba nata ba ne, idan ta zauna da yunwa mugun lalata mace yake yi ba kaɗan ba, so haɗari ne babba ga ƴa mace ta zauna da yunwa a irin wannan lokaci, ya san da haka shiyasa ya gwammaci gara ya ɗebo mata abincin ya bata.

Zuba abincin a plate ya yi tare da ɗaba mata green tea mai zafi sai tiriri yake yi sosai, jawo ɗan ƙaramin table dake kusa da sofar ya yi zuwa gabanta a in da ya ɗaura mata abincin a sama sannan ya nufi waje yana faɗin ta cinye dukka kafin ya dawo.

Da kyar ta miƙe zaune saboda kullewa da cikinta ya yi na azababben yunwa, tea ɗin ta fara sha, duk da bata son tea ɗin nasu, amma ta sha dan ya ce ta cinye komai.

Shi kuma waje ya nufa wajen sojojin nasa, almost 10 mins ya ɗauka yana magana da su kafin ya koma cikin ɗakin, saman bed ya hau ya kwanta dan har ga Allah baya son ganin yanda ta ɓata jikinta, ga shi basu da zaɓi dan ba pad dai a cikin jirgin, wayarsa ya sake ɗauka ya latsa na tsawon 5mins kafin ya ajiye saman bedside drawer, lumshe idanunsa ya yi yana tunane tunane har barci ya ɗan ɗaukesa.

Ita kuma ta gama cin abincinta tas kafin ta matsar da table ɗin sannan ta koma ta kwanta, sam bata ma lura da ta ɓata saman sofar ba, ita ma tana kwanciya ba jimawa barci ya ɗauke ta.

AFTER SOME HOURS💋

Karar sautin Helicopter ne ya tashe shi daga barcin da yake yi na tsawon awanni, ita kuma da yake tana da ɗan nauyin barci, sam bata motsa ba, a hankali ya waro idanunsa waje ba tare da ya miƙe ba, duk jikinsa a mace, har mamakin irin barci da ya sha yau yake yi, ya jima bai yi barci na tsawon awanni haka ba, ko sallar azahar bai yi ba, kuma barcin nasa ta ɗan yi nauyi yau.

Wani dankareren Helicopter ne ya tsaya a tsakiyar saitin jirgin ruwan nasu ta sama, Helicopter ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali launin army uniform, daga ganin Helicopter kasan na manya ne, dan fa ya kawatu iya kawatuwa.

Sako matakar Helicopter suka yi kasa izuwa cikin jirgin ruwan, wata kyakkyawar Baturiya doguwa jajir da ita ce ta fito daga cikin Helicopter ta biyo matalar, gashin kanta har baya bakinkirin, jikinta na sanye da kayan sojoji, kayan sun yi mata kyau sosai, babbar mace ce da akalla zata kai 35 years haka, Taku uku ta yi a saman matalar Helicopter wata macen soja ta leƙo daga ta ciki ta miƙa mata wani dankareren akwati mai matukar kyau da tsananin tsada, kasa da Helicopter kaɗan driver ya kara yi dan matan tamkar ba zata iya ɗaukar trolleyn ba, trolleyn ya yi mata girma, dan ma soja ce, da hannu ɗaya ta rike trolley ta kuma riƙe matalakar saukowar da hannu ɗaya tana sauka.

Karisowa wajen Mark ya yi da nufin ya karɓa mata trolleyn tun da ta kusa isa kasa, girgiza mishi kai ta yi alamar ya bari kawai, Mark ya santa sojansu ce, sai dai kuma bai taɓa yi mata magana ba sai yau, ta sha mamaki ita ma duk da ta san cewa dan trolleyn ya yi mata magana.

Da kyar dai ta sauko kasa, tana gama saukowa Helicopter ta tashi sama dan ta ɗan yi zagaye kafin ta dawo ta ɗauketa. Cikin harshen Spanish ta tambayi Mark da ina Lion? Kallon bedroom nasu ya yi kafin ya ce ta jira sai time da ya fito, tana ƙoƙarin sake yin magana idanunta suka sauka a kansa yana tsaye a kofar bedroom ɗin nasu, fuskar nan tasa tamkar hadari a ɗaure tamau, dama shi bai san menene murmushi ba a rayuwarsa, gabaɗaya sojojin kara natsuwa suka yi suka sha jinin jikinsu, wasu malaman natsuwa ne suka shiga jikinsu lokaci guda, nan take suka kame waje guda, ɗaga hannu macen sojan nan ta yi cikin girmamawa tare da tsoro sosai a tattare da ita ta sara mishi, shi kuma kallon Mark da ya kame ma yake yi, ya ga wani irin kyalli face ɗin Mark ɗin yake yi, sai aikin ɗan ciza laɓɓansa yake yi tamkar ba lafiya ba, hankakinsa da kallonsa sam baya a kan matar.

Daga jiya zuwa yau ya lura da Mark fa sai a hankali, shi kaɗai sai ya rinƙa wasu abubuwa tamkar mara gaskiya, bai san Mark ya shiga hannun Anaya dumu dumu ba ne, birgita mishi ƙwaƙwalwa take yi da shagwaɓa da kalaman soyayya, shi ne bawan Allah duk ya damu su koma ya je ya ga babyn nasa.

Hannu ya miƙawa macen sojan a kan ta kawo mishi trolleyn ba tare da ya yi magana ba, cikin hanzari tare da taku irin na jaruman sojojin da suka sami tsantsar horo ta kariso gabansa, sai da ta sake kamewa kam ta sara mishi kafin ta miƙa mishi trolleyn, sam bai karɓa ba bai kuma ɗaga ido ya kalleta ba, hankalinsa ya koma a kan wayarsa dake hannunsa, ya barta rike da trolleyn for almost 5 mins, ga trolleyn da bala'in nauyi, ta gaji amma ba damar ta nuna hakan, daurewa ta yi har sai da ya kara tsayuwar 2 mins kafin ya yi mata alama da hannu a kan ta ajiye ta wuce mishi ta bashi waje, sam bai yi magana ba dan nuna tsantsar isa da izza.

A hanzarce ta ajiye mishi ta juya ta koma wajen da ta sauko dan ta jira Helicopter ta dawo ta ɗauke ta, ya ɗauki almost 2 mins ba tare da ya motsa ba yana latsa wayarsa cike da nuna isa, tamkar ba shi ne ya gama cewa Meesha yanzu a cikin ɗaki ba, ko da yake dama Meeshansa kawai ya canzawa, ita kaɗai taga canji a tattare da shi, da ya bar wajen ta, to ya koma ainahin Lion ɗin nasa, sai ya wani kara ɗaure fuska na wuce misali, ga uban nuna isa da izza babu abin da ya ragu.

Ɗaukar trolley ya yi zuwa ciki, gabaɗaya sojojin sun yi mamakin me zai yi da trolley,? Saboda sun san wanene shi, baya sayan kaya a hanya, idan zai yi tafiya yana shirya komai da zata ishe shi, harta ita kanta soja mace da ta kawo trolley bata san menene a ciki ba, ita dai an kawo mata trolley har cikin office nata aka ce ta shiga jirgi zu je zata kaiwa GAR, amma bata san me a ciki ba, duk abin da yake ciki wannan kyakkyawa tsadadden kuma haɗaɗen trolley to Josephine ne ta sayo shi, ita ta je da kanta ta yi sayayya, a lokacin da zata je ita da kanta bata san me zata je saya ba, ita dai tana zaune sojoji biyu suka zo har cikin gida suka ɗauketa zuwa super market, sai da suka shiga super market ɗin ne Lion ɗin ya yi mata massage a kan ga abin da zata ɗauka mishi a super market ɗin, ta sha ruwan mamakin ganin saƙonsa, bata taɓa tunanin ya san da numberta a duniya ba, dole dai ba dan ta so ba ta yi wannan sayayya na abin da ya rubuta mata tas, bata yi mamakin ganin ya rubuta mata ta ɗauka mishi kayan mata har da su pad ba, domin duk wani motsin yaran nata tana iya sani, amma ba kowani lokaci ba, time to time haka dai, Lion shi ne yake yawan zulle mata sosai dama, dan ya fi TRIPLETS nasa riko da addini fiye da tunanin mai tunani, bata iya bincikar halin da yake ciki, kuma bata taɓa iya gane mishi, kullum a siffa ɗaya yanayi ɗaya take ganin shi, Aseef kuwa bawan Allah da yake yanzu ma yake koyan karatun addinin bai yi nisa ba, sai ya zamana duk wata bala'i take farawa ta kansa, shi kuma Areef Allah yana kare shi daga duk wata sharri saboda kyakkyawar zuciyarsa ta zinari kuma shi ma yana da riko da addini sosai duk da bai kai Lion ilimin addinin ba, amma yana iya ka bakin kokarinsa, Lion shi ne ya zurfafa bincike sosai a kan addinin musulunci shiyasa ya fisu ilimi na wuce misali.

So Josephine bata yi mamaki ba dan ya ce ta zaɓo mishi kayan mata, ta san yana tare da mace, abin da ya bata mamaki a nan shi ne karfin izzarsa da nuna isa irin na yaron nata, wato shi ko ana so ko ba'a so idan yana son abu to fa sai an shi, gata dai a nata wawtar wai ita take juyasu, amma shi kuma shi ne yake ainahin controlling nata ko tana so ko bata so, bata isa ta ɗaura wata magana a saman nasa maganar ba, idan ya yi magana dole ne a yi, yanzu dan tsabar isa irin nasa tana zaune a gidanta yasa aka ɗaukota aka kawota super market, kuma ba yanda ta iya dole ne ta yi wannan sayayya idan tana son zamanta lafiya, kuma duk abin da ya rubuta dole haka zata ɗauko mishi su masu kyau ko ranta ya ɓaci a banza, ita dai tana ganin gararin rayuwa, sun haifi ƴaƴan amma ƴaƴan su ne suke juyasu, ko da yake ba laifin ƴaƴan ba ne, laifin su ne dan su suka basu tarbiya irin haka, so dole su ɗauki koma me yaran zasu yi a yanzu, dan sun makaro tunfarko, itace tun yana ɗanye ake tankwara shi, idan aka kuskura aka bari ya bushe to ba zai tankwaru ba sai dai ya karye, Allah ka bawa ko wace mace ikon bawa ƴaƴanta tarbiya irin na koyarwar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dan amfanuwan kanta.

A takaice dai Josephine ce ta yi dukkan sayayyar cikin trolleyn nan, bayan ta kammala ta shirya su cikin trolleyn sai ta bawa soja mace dake biye da ita ta ɗauko suka fito, sojan ta wuce office nasu ita kuma Josephine ɗayar sojar ta mayar da ita gida aka cigaba da tsaronta, dan Lion ya hanata fita ko nan da can, kullum tana gida zaratan sojoji biyu suna gadinta.

Wajen da trolleys nasu yake ya nufa ya ajiye trolley, kusa da ita ya dawo, sai zuba barci take yi abinta, hankali a kwance, ɗan zuba mata waƴan nan dara daran blue eyes ɗin nasa ya yi na ƴan mintoci kafin ya sanya hannu ya saɓeta a kafaɗarsa tamkar wata ƴar baby ya nufi toilet da ita. Daddaɗar kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo a hancinta lokacin da ta farka sanadiyar jin da ta yi an ɗauketa, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata a saman face nasa, hankalinsa baya a kanata haka zalika kallonsa, yana kan wajen da yake son zaunar da ita, amma ya san tana kallon shi.

Hannu tasa ta saƙalo wuyarsa tana ɗan turo baki, jin saukar hannun nata a wuyarsa ne yasa ya sauko da idanunsa kanta, cikin sauri ta runtse nata idanun, tsayuwa ya yi daga tafiyar da yake yi ya zuba mata idanu. "Open your eyes". Ya faɗa a tsakanin sanyaye.

A hankali tamkar mara gaskiya ta ɗan buɗe idanun nata tana kara turo mishi baki.

Zuba mata ido ya yi na ƴan mintoci kafin ya ɗaurata a saman chair dake cikin toilet ɗin. Ɗan ɗaukanta da ya yi har ta ɓata mishi jiki, da yake idan baku manta ba shi rabin kayansa dukka fararene, shi ne yasa take saurin ɓata shi. Wucewa ya yi ya haɗa ruwan wanka sannan ya nufi hanyar fita yana ce mata ta yi wanka ta zo ta sanya kaya, okey ta amsa mishi da shi, ficewa ya yi zuwa ɗayar ɗakin shi ma dan ya yi wanka.

Ta riga shi fitowa daga wankar, ko da ta fito taga sofar da ta kwanta a kai ya ɓaci da jini, sai ta ɗauko towel fari mai kyau irin na goge sumar kai idan an yi wankar nan, ta ɗauko sabulai masu kamshi sosai, ta zo ta zuba tare da ruwa kaɗan ta goge tas, nan take wajen ta fara zuba kamshi sosai saboda karfin kamshin sabulan, bata sanya kaya a jikinta ba har sai da ta gyare musu ɗakin tsab, air freshener har kala uku ta fesa musu sannan ta ɗan kara gudun Ac, wani haɗaɗɗen kamshi tare da sanyin Ac mai ratsa zuciya ne yake tashi a ɗakin.

Lotions nasa ta je ta fitar tare da zama ta fara shafawa sai ga shi ya shigo ɗakin cikin shigar wando three quarter fari tas da kuma polo t-shirt sky blue, ya yi matuƙar kyau tamkar shi ya yi kansa, ya ɗaure dark black curly hairnsa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa, face nasa har wani kyalli yake yi, soft skin ɗin nan nasa ya kara kwanciya luff tamkar bai taɓa taka kasa ya fita waje ba, sai wani sheki fatar tasa take yi, alama ce ta ya kara samu kwanciyar hankali over fiye da na baya.

Sosai yau ta zuba mishi idanu tana kallo shi, ya yi wani irin azababben kyau ne na wuce misali, ji take yi tamkar ta tashi ta je ta rungume shi ta kuma sumbaci ɗan bakin nan nasa, dan kuwa lips nasa har wani kyalli suke yi tamkar ya sanya musu lips balm, sun kara ja sosai. Ya tsaya a tsakiyar bedroom ɗin yana ɗan latsa waya. Kasa jurewa ta yi da sauri ta miƙe ta zo ta faɗa jikinsa.

Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke a tare kafin ya buɗe hannunsa ya rungumeta da kyau a saman faffaɗar kirjinsa, sam ta manta ma da cewa towel ne a jikin nata, ga gashin kanta bai gama bushewa ba, akwai ruwa ruwa a jikinsa, shi ma gashin kansa da ɗan ruwa a jikinsa, dan bai busar da shi ba, da ya goge da towel kawai sai ya barta dan yana son ya zo ya bata pad kada ta saka kaya ta sake ɓata jikinta, yasan idan ba shi ya zo ya bata da kansa ba, to ba zata taɓa trolley ɗin ba, kayanta kawai zata ɗauka dan bata da shisshigi a kan abin da bai shafeta ba.

Lumshe idanunsa ya yi yana shaƙar daddaɗar kamshin air freshener da ta fesa musu ga kuma sanyin Ac dake ratsa mishi zuciya, shi kaɗai yasan me yake ji.

Hannu ya ɗaura a saman bayanta kasa kasa ya ce "Muje na baki kayan sakawa". Ya yi maganar a tsananin sanyaye kamar dai kullum, ya kuma yi maganar yana waro idanunsa a kanta. Sakinsa ta yi ta nufi wajen trolleys ɗin tana faɗin "Noori yau kai ne zaka zaɓa mini kaya?". Tana magana cikin tsantsar yarinta, hakan ba ƙaramin burge shi take yi ba, sai dai shiru ya yi bai yi magana ba, ya kariso wajen trolley ɗin.

Wanda sojan can ta kawo mishi ya kwantar a in da ya zuge zip ɗin ya buɗe, manya manyan teddy guda biyu farare kal kal masu matukar kyau da kuma girma sosai ya fara cin karo da shi a cikin trolleyn, kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa, shi dai bai cewa Josephine ta saya mishi teddy ba, ita kuma ta saya mishi ne dan ta nuna mishi cewa Rimsha fa baby ce da bata wuce ta yi wasa da teddy ba, sako ta aiko mishi a fakaice, ya gane nufinta sarai amma sai ya yi tamkar bai gane ba.

Yana ciro teddy ya ajiye a gefe Rimshar ta kariso wajen da sauri tana zuba uban murmushi cike da murna ta ɗauki teddy ɗaya, ta ji tsantsar farinciki, rabonta da su tun a Abuja lokacin da daddynta yake sayo musu suyi ta faɗa ita da Jehan akansu. Zancen Josephine ya tabbata, Rimsha fa yarinya ce da bata wuce wasa da teddy ba, ga shi kuwa ta ɗauki abinta tana ta murmushi har da yi wa teddyn magana tamkar da mutun take tare.

Girgiza kai kawai ya yi ya cigaba da duba kayan ba tare da ya fitar dasu daga cikin trolleyn ba, yes komai ya yi, yanda ya rubuta haka ya sayosu, wata ƙatuwar leda mai ɗauke da pad a ciki ya fitar tare da ɗauko kwalin pant guda ɗaya, miƙa mata ya yi yana faɗin ta ajiye teddyn nan ta je ta shirya, karɓa ta yi tana kallon pad ɗin da mamaki, ita fa bata san taya ma ake sanya always a jikin pant ba, bata taɓa ganin yanda ake yi ba, shiru ta tsaya ta kasa motsawa, gyara kayan cikin trolley ya yi tare da jan zip ɗin ya rufe, sannan ya miƙe tsaye da nufin ya bar wajen.

Ganin tana tsaye tana ta kallon always ɗin ne yasa ya ɗan zuba mata idanu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login