Showing 78001 words to 81000 words out of 359620 words
dan saboda baya son ja in ja da Areef ɗin, duk abin da zai yi yana yin shi ne da lissafi, baya taɓa yi wa TRIPLETS nasa faɗa ko magana mara daɗi a gaban wani, dan baya son kowa yasan tsakaninsa da ƴan uwansa, ko ranar da ya ce Mark ya sanyata tsalle kwaɗo Areef ya hana, yana sane, abin da yasa bai yi magana a lokacin ba, baya son su Mark su raina TRIPLETS nasa, yana son tamkar yadda kowani securitynsa zasu ji maganarsa, to haka zasu ji maganar TRIPLETS nasa, yasan cewa idan ya yi magana a lokacin Mark zai raina Areef ɗin, zai zama idan Areef ya yi magana ba zai ɗauki maganar da muhimmanci ba, hakan yasa ya yi shiru sai da Areef ɗin ya shigo ɗaki ya same sa ne ya yi mishi faɗa tare da gaya mishi baya son ya rinƙa shiga irin wannan magana, idan ya bawa wani punishment to baya son su rinƙa saka baki, haka kuma ya saba yi musu, daga shi sai su yake yi musu faɗa, ko Imran baya bari yasan tsakaninsa da TRIPLETS nasa, yanzu ma yana jiran Areef ɗin ne ya dawo, kuma ma abin da yasa bai karfafa dole sai ya sanya mata chemical ɗin ba, saboda yasan zanen ba na yanzu bane, rikicewa da shiga ruɗu ne yasa ta ce na yanzu ne, amma a matsayinsa na babban soja ya san tabbas ba na yanzu bane, an jima da yin shi, to shiyasa bai karfafa dole sai ya zuba mata ba, ku kunsan da ya karfafa wane Areef ya karɓeta daga hannunsa, ba'ayi wadda zai iya karɓarta ba, bugu da kari fuskarta, wannan fuska tata ta sanya shi cikin tunani, akwai wani ɓoyayyen sirri a tarrare da face ɗin tata a cewarsa, bai kawo cewa son shi ne yasa ta yi zanen sunan ba, dan a yadda yake ganinta, kallon karamar yarinya yake yi mata, bata san menene ma soyayya ba, kuma kuma masu karatu kunsan a lokacin da ta yi wannan zanen ta yi ne ba dan tana son shi ba, ta yi ne kawai dan yana burgerta, a lokacin bata iya banbance soyayya da burgewa ba.
(Amma kuma da ta tara hannunta da gaske fa zai zuba mata chemical ɗin nan, gaskiya Lion halinsa sai shi, baka gane gabansa bare bayansa🤔)
Kai tsaye ɗakinta Areef ya wuce da ita, zaune ya isko Akila tana aikin latsa waya, ganinsa ɗauke da Rimshar yasa ta miƙe tsaye tana tambayarsa ko lafiya, bai ce da ita komai ba, ya wuce ya kwantar da ita a saman gado tare da zama a gefenta yana kallon yadda jikinta ke uban kerma tamkar mazari.
Gently ya fara magana "Rimsha ya isa haka nan, ki dai'na wannan kukan, yanzu ki tashi ki gaya mini gaskiya me ya faru tsakaninki da Lion? Me ya haɗa ku?". Ta ɗauki tsawon a kallah minti goma kafin ta iya dawo da natsuwarta, da kyar ta tattaro sauran muryar da ya rage mata, cikin shasshekar kuka ta fara magana "Yaya Areef ba zan ɓoye maka ba, dan ya kalli zanen dake a kan kirjina ne ya ce zai zuba mini chemical na goge shi". "Zan iya ganin wani zane ne?" Ya tambaya yana kallon kirjin nata, sai yanzu ya lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa, abin ku da Turawa, kwata kwata basu san menene kunya ba a rayuwarsu, Akila kam ta zuba musu idanu kawai tana kare musu kallo.
Da kyar ta iya miƙewa zaune tare da sanya hannu cike da kunya ta ɗanyi kasa da vest ɗin jikinta kaɗan zuwa rabin tudun tula tulan nata, ta nuna mishi zanen, zuba wa zanen idanu ya yi yana karantawa.
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Lallai da kuwa Lion ya tabka babban kuskuren da ba zai iya gyarawa ba a rayuwarmu, yanzu idan ma ban da shi da neman magana, ko in ce da san gallazawa rai, ai yasan wannan zane daga ido ma ba ta yanzu bace, kowa ya ga wannan zane yasan ta jima, abinda har ta fara bin fatar jikinki, amma ba komai ina mai baki hakuri a madadinsa, kuma In Sha Allah daga yau kin dai'na zuwa in da yake, Aseef yana nan zuwa gobe, dama shi ne mai kai mishi abinci, zaki huta my sister, rabu da shi Allah yana ganin mu ai". Ya kai karshen maganar yana jawo mata zip ɗin rigar tata sama, sam bai ji daɗin abin da ɗan uwan nasa ya yi ba, yasan da cewa yana sane zanen ya jima, kawai bakar mugunta ce sai ya gallazawa ƴar mutane Baiwar Allah, amma ba komai zai gane kurensa, zai ɗanɗani ƙuɗarsa ne.
Bayan ya gama ja mata zip ɗin rigar ya goge mata hawaye tas kafin ya miƙe tsaye yana mai dawo da kallonsa a kan Akila da ta tsare shi da idanu. "Heartbeat sarkin rigima, yanzu kuma wani sabon rigima zaki yi mini?" Ya yi maganar cikin zolaya, kuma duk cikin harshen turanci suke magana.
Ɗan rufe fuska ta yi da hannunta tana murmushi bata ce komai ba, wucewa ya yi ya fice daga ɗakin ya koma wajen ɗan uwan nasa.
Yana fita ta koma ta kwanta ƙwaƙwalwarta na tariyo mata abin da ya faro, kwayar idanunsa kawai take gani cikin nata, matsowa kusa da ita Akila ta yi ta shiga rarrashinta tare da bata baki.
A ɓangaren Areef kuwa, abinci ya je ya zubawa ɗan uwan nasa, a tare suka ci suka ƙoshi, da kansa ya tattare kayan ya fitar tare da dawowa ya ɗauki chemical ɗin ya mai da shi mazauninsa, a lokacin shi kuma Lion already ya koma saman bed nasa ya kwanta, abu biyu suka tsaya mishi a zuciya tun zuwan shi NIGERIA, na farko Yarinyar da ta kira sunansa kai tsaye a ranar da ya sauƙa gidansu Imran, har cikin ransa yanzu da ya ga sunansa a kirjin Rimsha zuciyarsa ya bashi ita ce wannan yarinya, abu na biyu kuma fuskarta, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to waye kenan? Wan can dai ba yarinya ba ce tare da Josephine, dattijuwa ce, kada ku mance kowa da yadda yake kallon mutum, wani zai ga kayi mishi kama da wani na shi, kai kuma ba zaka ga kamannin ba, to shi dai tabbas ya ga mai irin wannan fuska tata sak a tare da Josephine, sai dai ya rasa a ina ne ya taɓa ganin nasu tare, shiru ya yi yana faɗaɗa tunaninsa a ina ne ya ga hakan.
Gefensa Areef ya zo ya zauna tare da ɗan taɓa shi, juyo da dara daran blue eyes nasa ya yi izuwa kan Areef ɗin, shiru bai ce komai ba, cikin natsuwa Areef ya fara magana. "My blood na san kana son farincikin mu fiye da naka, na san kana son abin da muke so, na san baka da wani burin da ta wuce ka ganmu a cikin farinciki, duk in da muka je muna alfahari da hakan, muna jin daɗin hakan, dan Allah yau ina neman Alfarma a wajenka, ba dan ni zaka yi ba, please and please dan girman Allah zaka yi, ina son ka rinƙa danne zuciyarka a kan sister, wlh tana da problem a kanta, ta shiga ta shin hankali, ko in ce taga tashin hankali da ya wuce shekarunta, ya wuci girman ƙwaƙwalwarta, hakan yasa take da yawan razana, to please tana tsoronka kamar ta mutu, tana tsoron ganin kwayar idanunka, idan har ka cigaba da kallonta ma kawai wlh kana iya ɗaukar gawarta, ni zaka yi wa, ina kaunarta, ina kaunarta fiye da tunaninka, idan tana farinciki nima ina yi, idan ta yi kuka, ko ban yi a zahiri ba, ina yi a cikin zuciyata, kasan dai bawa baya sanyawa kansa soyayya ko? To ba ni na sanyawa kaina sonta ita da mahaifinta ba, Allah ya jarrabeni da hakan, ka taimaka mini tun da Aseef zai zo gobe, ina son sister ta daina kawo maka abinci, ta daina zuwa kusa da kai, yanzu haka dole Prof ya ɗauketa zuwa asibiti, idan ba haka ba, akwai gagarumin matsala". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar murya mai ɗauke da damuwa ainun, tabbas duk abin da yake damun Rimsha ya sani, baiwar Allah bala'in da ta rinƙa gani na Daular Mutuwa ya birkita mata kwakwalwa, ko shi Dr Nawid bai gano ainahin damunwanta ba, wlh bala'in dake Daular Mutuwa ya fi karfin ƙwaƙwalwarta ya ɗauka, hakan ya haifar mata da razana, Areef ya gano hakan ne ta hanyar dubata da ya taɓa yi da bata da lafiya, hakan yasa take yawan suma, kuma Areef ya yi gaskiya idan ta cigaba da zama inuwa ɗaya da Lion to wata rana za'a iya ɗaukar gawarta a wajen.
Shiru ya yi bai tanka ɗan uwan nasa ba, shima Areef ɗin shiru ya yi, almost 30 mins suna haka kafin Lion ya ce "Haka kake so?" Gyaɗa mishi kai ya yi alamar e, jinjina kai ya yi alamar to ya yi accepted, wani irin farinciki ne ya dira mishi a cikin zuciyarsa, da sauri ya rungumi ɗan uwan nasa yana zuba mishi ruwan godiya tare da ruwan Albarka, shikenan yanzu Rimsha ta tashi daga ƴar aiki, ta yi free wow abin ya yi daɗi, yau saboda Areef Lion ya canza magana, saboda faricniki TRIPLETS kai abin ya kayatar.
Sun jima suna hira, ko da sunan wasa Lion bai sanar da Areef face ɗin Rimsha ya yi mishi kama da na wata da ya taɓa gani tare da Josephine ba, ya bar abin a ransa zan yi bincike a kan idan ya sami lokaci, yau dai kwanan faricniki Areef ya yi, shi kuma Saif mafarkin Josephine kamar kullum ya kwana yana yi.
A ɓangaren Rimsha da Akila kuwa, Rimsha dai barci ɓarawo ne ya yi awon gaba da ita, ita kuma Akila sai da suka yi waya da Umaisha kafin ta raba dare da sahibin nata suna hira, sai Misalin karfe 2 na dare suka hakura ba dan sun so ba, ko kaɗan a hirar tasu bata kawo mishi zancen cewa ta gane shi ko makamancin haka ba, shima bai kawo mata zancen ba, sun dai zuba soyayyarsu kamar yadda suka saba.
Wayar da suka yi da Umaisha ba komai bane face magana a kan yajin da Akil ya yi, mu koma baya kaɗan mu ji tattaunawar tasu kafin mu cigaba da tafiya.
Kiranta Umaisha ta yi, tamkar zata yi kuka ta fara magana "Hello Heartbeat". Cike da kulawa Akilar ta ce "Aunty Umaisha ta yaya Akil, to ya ake ciki ne? Ya naji muryarki haka? Ko dai babyna ne yake addaba miki? Kin san nina yi mishi huɗuba ai, na ce ya tabbatar yana takura miki sosai, ya yi ta naushinki a ciki har sai kin yabawa aya zakinta". Tana magana tana murmushi, turnuke fuska Umaisha ɗin ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce "Ni Heartbeat ba wannan ba, dan girman Allah wata alfarma nake nema daga gare ki". Da sauri ta ce "Wace alfatma kuma?"
"Dan Allah heartbeat ki kira mani shi a waya, ki ce mashi wlh na tuba bazan kara ba, tun fa da safe ya yi fushi ya fita, kuma wlh kafin ya fita sai da ya ce mini ya yi yaji sai ya yi sati biyu ko wata ɗaya zai dawo, na ɗauka wasa yake yi kuma raina a ɓace na ce mashi kada ma ya dawo ma in yana so, ashe wlh da gaske yake yi, yanzu na kirashi yafi miss call hamsin ya ki ɗagawa, kuma wlh ni nasan yana ganin kirata, ɗauka ce kawai ba zai yi ba, na yi mashi massages har na gaji babu reply, dan girman Allah ki kirashi nasan zai ɗauki kiranki, ba zan taɓa iya yin barci ba har sai ya dawo". Kwashewa da dariya Akila ta yi har da riƙe ciki, iskanci Umaisha da Akil ya wuce misali.
"Heartbeat ki tausaya mini ko dan saboda babynki". Tana magana murya a dashe taci kuka ta ƙoshi, ita kuma Akila tsabar shakiyanci tana binta da to na iyashege, sai da Umaishar ta gama maganarta tas, sannan Akilar ta ce "Kai amma yaya Akil ya iya, wato ma shi ne ya yi yaji kenan? Wayyo cikina, ai kaɗan ma kika gani, ba ke duk abin da na gaya maki baki ɗauka ba, wlh yaya Akil ustadz ne, koyi da annabi yake yi, shiyasa shi ya yi yaji ya bar miki gidan, nasan yana masallaci a yanzu, ya tare a can, abin da zai faru kawai ki jira sai ya cika wa'adinsa da ya ɗebe". Ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariyar shakiyanci, katse kiran kawai Umaisha ta yi, dan ta lura Akila zata kara mata zafi a kan zafi ne.
Bayan ta katse kiran ne Akilar ta jawo bargo ta shiga kafin nan ta rubutawa Akil massage a kan halin da Matarsa ke ciki, bayan ya tura mishi ne bai fi da minti goma ba masoyin nata ya kira, shi ne suka fara hira har karfe biyu na dare, to kun ji yadda a ka yi.
Washegari karfe 8 na safe, Akil ya zo ya ɗauki Akila ya mai da ita gida, kamar yadda Imran ya faɗa, sun sha kukan rabuwa da Rimsha kamar ba gobe, sai da Areef ya ja Rimsha zuwa cikin gida, ita kuma Akila Imran ya turata cikin motar Akil suka nufi gida.
Ɗaki Areef ya mayar da Rimsha tare da yi mata albishir a kan daga yau ta bar aiki, school kawai zata rinƙa zuwa ta dawo, sai wanka da tsala kwalliya, sai kuma barci, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, dama kamar zata yi kuka, daurewa kawai take yi tana yin wannan aiki, amma badan haka ba, Allah ne kaɗai yasan yadda take ji a duk san da ta ɗauki abincin da nufin ta kai wa Lion.
Ganin sai murmushi take baki yaki rufuwa ne yasa shi ya miƙe tare da ficewa daga ɗakin yana mai jin tsantsar kaunarta a ransa.
Bin bayansa da kallo ta yi har ya kure wa ganin ta ya fice daga ɗakin, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare buga uban tagumi, ta rasa me yake damunta, daga jiya zuwa yau, a hankali hankali soyayyar da take yi wa Saif yana juyawa ya koma kan Areef ne ko Aseef ne ta rasa, ita kanta ta rasa me yake damunta, ko wace zuciya tana son mai kyautata mata, tabbas son da take yi wa Saif kaso 40 cikin ɗari ya dawo kan Aseef da Areef, sai dai a cikinsu ta rasa tantance waye ne take yi wa son aure, waye kuma take yi wa son kyautatawar da suke yi mata, shekarunta bai kai ta iya tantance hakan ba, ba karya suna bata kulawar da ko motsi ta yi sai sun tambayeta akwai wani abin ne idan suna kusa, shi kuma Aseef idan suna yin video call kenan, ba su taɓa barinta ta zauna shiru har ma ta yi wani tunanin da zai sanyata bakin ciki, tabbas tana son su ba kaɗan ba, ba zata iya yin wuni guda bata ga Aseef or Areef, idan bata yi Video call da Aseef ba, to zata kalli Areef, musamman ma shi Areef ɗin wanda suka yi mugun sabo na kin karawa, kuna ganin dai yadda suke da ita, kuma idan ba ku manta ba, shi Areef ɗin shi ya fara bata kulawa kafin Aseef ya biyo bayansa, shi ya kula mata da daddynta tamkar ɗan uwan shi, wannan matsala tata tana neman zama mata gagarumar matsala, domin ta rasa wa take so so na aure, waye kuma yake yi wa son kyautatawa a cikin TRIPLETS.
Yana fita abinci ya je ya ɗaukawa ɗan uwan nasa daga kitchen zuwa ɗakinsa, kamar dai kullum a tare suka ci abincin cikin nishaɗi da kaunar juna, bayan sun kammala suka koma saman bed dan su cigaba da hira, bayan Areef ya gyare wajen kenan, Allah sarki karfi da ya ji Areef ya koyi aikin da bai kamata ace shi ne yake yi ba, before bai iya ba sam, yanzu kuma Alhamdulila yana ƙoƙartawa ya yi.
Misalin karfe biyu na rana, taci kwalliya kamar ba gobe, ta sanya ɗaya daga cikin ɗinkunan da Imran ya ɗinka musu, wata shegiyar ɗinkin riga da skit a kayi mata, kayan sun zauna tsam a jikinta tamkar dan ita aka yi shi, ya bi shape ɗinta sosai da sosai, bata iya ɗaura ɗankwalin atampha ba, sai kawai ta yafa abinta a saman kanta, ta yi kyau iya kyau.
Palon sama ta fito ta zauna tana jiran Imran ya fito zai kai ta wajen gyaran gashi, yau tana ji tamkar ta yi kumshi idan suka je gyaran gashin tun da yanzu ta daina yi wa Saif aiki, farinciki a wajenta ba'a magana, tana zaune shiru ga wayarta na a gefenta, ko me ta tuna sai kuma idanunta suka cika tap da kwallah, wayar tata ta laluɓo.
Kunna hasken screen ɗin wayar ta yi, bayan ta cire password ɗin contact ta shiga, number Anaya ta fara kira, bugu ɗaya Anaya ta ɗaga dan lokacin ta dawo daga school, murya a gajiye ta ce "Rimsha ina wuni?". Tamkar zata fashe da kuka ta ce "Anaya, Anaya yau GAR ya kallah mini......." Sai kuma ta kasa karisawa ta yi shiru.
"Rimsha waye kuma GAR? Me kuma ya kallah miki ɗin". Girgiza kai ta fara yi tamkar Anaya ɗin na a gabanta "Babu komai Anaya zamu yi waya anjima". Ta kai karshen maganar ba tare da ta jira Amsar da Anaya ɗin zata bata ba, ta yi maza ta katse kiran.
Ajiye wayar a gefenta ta yi tare da buga uban tagumi tana tunani, abin da Lion ya yi matan nan, ya yi mata zafi ba ɗan kaɗan ba, kuma dai kunsan yadda take tattalin tula tulan nan nata, bata son ko iska su sha, idan zata sanya kaya sai ta rufesu da vest, bata bari ko alamarsu a gani, kawai ya zo ya wani buɗe mata su ya kalle kamar nashi ko an aike shi, yau da tana da dama sai ta kifa mishi maruka ko biyar ne haka, kila ta huce takaicin da take ciki, idan ta tuna