Showing 45001 words to 48000 words out of 359620 words
dake tsakiyar ɗakin ta ajiye masu abincin tare da miƙewa ta nufi drawer kayansa dan fitar mashi da kayan sakawa.
Kananan kaya na shan iska ta fitar mashi, a saman bed nasu ta ɗaura kayan, ita ma ta kwanta a gefen kayan tana jiran fitowarsa.
After some minutes ya fito ɗaure da towel a kugunsa, tsayuwa ya yi a wajen drawer kayansa tare da zuba mata ido, ita kuwa tana jin fitowar shi, amma taki ɗagowa ta kalle shi.
"Mrs Nawid yanzu dai ba za'a taya ni sanya kaya ba?". Gyaɗa mashi kai ta yi tana daga kwance, har lokacin kuma taki ɗago kai.
Bai sake magana ba ya kariso wajen gadon, kayansa da ta ajiye mashi ya ɗauka yana mai bin kayan da kallo, har cikin ransa ya ji daɗin kayan da ta fitar mashi, hakan ya nuna lallai tana da kula sosai, a ɗan zamansu kwana biyun nan, har ta fahimci irin kayan da yake son sanyawa idan yana gida, abin ya sanya ya kara jin sonta a ransa.
Toilet ya koma dan baya son yin duk wani abin da bata so, yasan ba zata ji daɗi ya sanya kaya a cikin ɗakin tana ciki ba, tun da ba sabawa sosai suka yi ba, hakan yasa ya wuce toilet abinsa, kuma shima a yanzu dai ba zai iya sanya kaya a gabanta ba.
A yadda ya barta a haka ya sake fitowa shirye ya sameta, gaban mirror ya tsaya domin ya shafa mayukansa.
"Mrs Nawid ki zo ki taya ni shafa mai, idan ba haka ba, Allah zan yi maki alluran barci, dan tun da ba tayani aiki zaki nayi ba, gara kawai idan na dawo na rinƙa yi maki alluran barci sai nayi aikina ni kaɗai, kuma bayan haka zan ɓata dake tun da kina da son kai, ni in tayaki aiki, ke kuma baki son tayani ko?". Cikin zolaya ya yi maganar yana mai taje gemunsa.
Miƙewa ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon, kafin nan ta miƙe gabaɗaya, gabansa ta isa ta tsaya tana mai ɗauko Lotion da yake amfani da shi.
Da mamaki yake kallonta, bai yi zaton zata shafa mashi ɗin ba, ya zolayeta ne kawai, ashe dai zata yi mashi ɗin, a lallai yau rana ce ta Sa'a a gare shi.
"Zan iya rungume matata?" Ya faɗa kasa kasa, shiru ta yi Mashi, mamaki ma yake bata, wai komai zai yi mata sai ya tambayeta sai ka ce ita ta aure shi ba shi ya aureta ba.
Ɗan shafa gefen fuskarta ya yi yana mai kara faɗaɗa murmushin kan fuskarsa, ita ma sai murmushi take yi ta wani yi kasa da kai tana murza mai a hannunta.
Jawota jikin nasa ya yi, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Dama kin ce na koya maki kiss da sumbata ko?". Shiru ta yi mashi tana runtse idanunta. "To buɗe idanu mu kalli juna sai na koya maki daki daki ta yadda zaki fi iya ɗauka da kyau".
Ƙin buɗe idanun nata ta yi, har lokacin kuma tana Murmushi. A hankali ya rankwafo da kansa tare da haɗe fuskokinsu waje guda, jin tana iya shakar numfashinsa ne yasa ta razana sosai, nan take abin da ya faru a baya ya dawo mata sabo, a kiɗime ta fara ƙoƙarin kwace kanta daga gare shi, kara kankameta ya yi, dan shi bai kawo komai a ransa ba, ya yi zaton bata saba bane yasa take son guduwa.
Ba tare da ya yi magana ba ya ɗaura bakinsa a saman tata, a nutse ya fara kissing nata, tun tana mutsu mutsu tana neman kwace kanta, har ta hakura ta natsu tsit a jikin nasa, shi kuwa lafiyayyar kiss yake bata tare da kara matseta a jikinsa, sai faman sauƙe numfashi da sauri sauri yake yi, hankali ya kwanta, abin nema ya samu.
Sun ɗan jima a haka, ta natsu shiru, duk wasu ƙofofi da gaɓɓai na jikinta suna karɓar wannan daddaɗar saƙon da yake aika masu da shi, tuni ya sanya ta fara fita a hanyacinta. Can ta yi nisa bata jin shi sosai, kamar daga sama ta ji sauƙar hannunsa a kirjinta, wani irin bugu kirjinta ya bada, ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi.
Can kasa kasa ta jiyo muryarsa bayan ya zame bakinsa daga nata. "Please kada ki hanani taɓawa, na yi maki alkawari ba zan kai hannuna ciki ba, a iya rigar kawai zan shafasu, bana son ɓacin ranki, idan har baki son na taɓa to na hakura". Allah sarki shi kuma yana ƙoƙarin saka ta farinciki ne dan yana tunanin tana cikin kunci anyi mata auren dole, auren da bata shirya ba, bata san shi ba rana ɗaya kawai aka haɗa auren, ranar da ta fara ganin shi, a ranar ta zama mallakinsa, hakan yasa yake binta a hankali dan ya koya mata son shi, a nasa tunanin fa kenan, abin da bai sani be shi ne, ta jima tana dakon soyayyarsa.
Jin abin da ya ce yasa tayi shiru ta natsu, dan kyautatawa iya kyautatawa yana yi mata, koda yaushe bashi da wata burin da ta wuce ya ganta tana murmushi tana farinciki, dole ita ma ta yi ƙoƙarin sanya shi farinciki.
Kamar yadda ya faɗa hakan ya yi, bai saɓa maganarsa ba, suna daga cikin rigar ya rinƙa matsasu yana wasa da su, ya kankameta sosai a jikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji, shekarunsa 28 to 29 a duniya yanzu.
Sun jima a haka kafin ya saketa ya juya ya nufi toilet ba tare da ya bari sun haɗa ido ba, da alama kunyarta yake ji. Ita kuma, da kyar ta koma saman gado ta kwanta tare da lumshe idanunta tamkar mai yin barci, ban da ajiyar zuciya babu wani abu da take sauƙewa.
After some minutes.
Wanka ya sake yi tare da shiryawa cikin wasu kananan kayan, sai dai a wannan karon ba ita ta fitar mashi da kayan ba, shi ya zo ya fitar da kansa, ita tun da ta kwanta ta kasa sake motsawa.
Bayan ya kammala shirinsa tsab, ya kariso gaban gadon, a hankali ya zauna kusa da ita tare da sanya hannunsa ya fara shafa gashin kanta, da yake kwanciyar da ta yi yasa ɗan kwalinta ya zame kasa, gashinta ya bayyana.
"Tashi muje na baki abinci ko matata?". A nutse ya yi maganar, har lokacin taki buɗe idanunta, dan bata san da wani ido zata kalle shi ba.
"Yaya Nawid naƙoshi". "Ban yarda ba, kiyi hakuri kin ji? Na san abin da nayi maki ne yasa kika ce haka, to na tuba bazan sake ba, yanzu dai yinwa nake ji, please ki tashi muci ko?".
Shiru ta ɗan yi Mashi kafin ta ce "Yaya Nawid da gaske ba zan iya ci ba, kai kaci kawai". Ɗan kwantowa kaɗan ya yi tare da ranƙwafo da kansa daidai saman tata, har suna iya jiyo numfashin juna. "Idan baki ci ba, wlh nima ba zan ci ba, dan Allah kiyi hakuri, na ce maki ba zan kara ba kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana mai gangaro da hannunsa zuwa saman wuyarta.
"To yaya Nawid ai kunyarka nake ji ne, ni gaskiya ba zan iya buɗe idanuna na kalleka ba" Murmushi ya yi tare da cewa "To tashi kizo, nayi alkawarin ba zan kalleki ba, zan rufe idanuna ko kuma na kawar da kaina a duk lokacin da na kawo maki spoon ɗin abincin bakinki". To ta amsa da shi tare da miƙewa zaune, shima miƙewa ya yi suka sauƙo daga saman gadon zuwa kasa.
Ita ta zuba masu abincin, sai kallonta yake yi, ya kasa cika alkawarin da ya ɗauka na ba zai kalleta ba, ita kuma taki yarda ta kalle shi.
Bayan ta gama zuba masu, sai ta zauna a gefensa kamar yadda suka saba zama.
Ɗaukar spoon ya yi tare da ɗebar abincin ya kai mata saitin bakinta yana mai tsareta da ido.
"Ni yaya Nawid zan ci da kaina". Ba musu ya juya abincin izuwa bakinsa, ɗaukar nata spoon ɗin ta yi suka fara ci a tare, abin gwanin ban sha'awa da burgewa.
Bayan sun kammalaci, ta miƙe ta kwashe kayan abincin zuwa Palo, lokacin da ta dawo, ta samu yana waya, shiru ta tsaya kusa da shi tana jin muryar macen da ke fitowa daga cikin wayar tasa, wani irin kululun bakin cikine ya turnuke mata maƙoshi, bata bari ya kammala wayar ba ta fusge tare da bin screen ɗin wayar da kallo.
Bata kai ga kallon sunan da ya rubuta ba, sai gani ta yi ya miƙe yana ƙoƙarin kwace wayar, da gudu ta nufi waje bata bari ya kwace wayar ba.
Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ta fara kishin shi, kenan ta fara son shi, dan shi idan baku manta ba, yana ganin kamar dole aka yi mata, kuma hakan ya sa ya zage yake koya mata son shi.
Da sauri ya bi bayanta, a palo ya sameta zaune kusa da Ummi, tamkar ba ita ce ta karɓe mashi waya yanzu ba, kai kallonsa ya yi izuwa kan hannayenta, babu wayar mamaki ne ya kama shi, ko'ina ta kai wayar oho.
"Zo mu tafi ina da magana dake". Ya faɗa yana satar kallon Ummi, make kafaɗa ta yi alamar ba zata zo ba, kashe mata ido ɗaya ya yi tare da ɗan karkata mata kai alamar ta yi hakuri ta zo suje.
Gyarawa ta yi ta kwantar da kanta a saman cinyar Ummi tana mai da kallonta izuwa saman Tv da Ummin ke kallo, ba zata zo ɗin ba kenan.
"To shikenan bani wayata fita dama zan yi, kiran da ki ka ga anyi mani nan, wata patient a ka kawo a asibiti, abin na gaggawa ne, kuma ni kaɗai ne zan iya dubata, dan haka zan je wata kila na dawo yau, wata kila sai safiyar gobe". Ya kai karshen maganar yana miƙa mata hannunsa akan ta bashi wayar.
Ɗan satar kallon Ummi ta yi kafin ta miƙe tsaye ta nufi hanyar ɗakin nasu ba tare da ta yi magana ba, murmushi ya saki while ita ma Ummi murmushin ta yi, tana faɗi a ranta cewa, ai ba zata sake shiga tsakaninsu ba, jiya haka suka yi mata, a kitchen suna aiki ya shigo wai zai taya su, A'AFIA na ɓare maggi zata saka a miya, da ya sanya hannu zai taya ta, sai ta ce "Ummi ki ce yaya Nawid ya bar mani kayana bana soz bai iya ba, baya ɓarewa dukka, yana barin sauran Maggi a ciki". Ita kuwa Ummi sai ta shiga, ta ce ya bar mata kayanta, ai kuwa kafin ta gama ɓare maggin nan ita da kanta ta ce "Yaya Nawid to ɗauka muyi bibbiyu". Daga nan Ummi ta fita harkarsu, bata shiga faɗarsu, yanzu ma da ta shiga ta ce A'AFIA bazata je ɗakin ba ko makamancin haka, ai da sun sake bata kunya, tun da ga shi dai ta miƙe ta wuce ɗakin dan kanta, so ba'a shiga tsakanin mata da miji, idan ma mace ta kawo maki kukanta akan mijinta, kiyi mata addu'a kawai ki bata hakuri, wlh idan kika kuskura kika tayata zaginsa da faɗar laifinsa, tofa zata iya biye maki a lokacin tun da sun yi faɗa da mijin, amma kuma da zarar sun shirya, ki tabbatar abin da kika faɗa na zaginsan nan tsab a kunnensa zata gaya Mashi, idan munafuka ce ma, wlh sai ta kara da karya, kuma zata yi ta riƙe ki a rai na kin zagi mijinta, haka dayawan mata suke, Allah dai yasa mu dace mu kuma gyara.
Bin bayanta ya yi, a tsakiyar gado ya iskota ta kwanta ruf da ciki tare da kifa kanta a kan pillow.
Saman gadon ya haye shi ma, a hankali ya sanya hannu ya ɗago kanta, Subhanallah zaro idanuwansa waje ya yi yana kallon yadda take hawaye sharɓa sharɓa.
"Aafia lafiya kike kuka? Me ya faru kuma?" Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da damuwa tare da kulawa a gareta sosai.
Shiru ta yi mashi ba tare da ta yi magana ba. "Dan Allah matata ki gaya mini, shin nayi miki wani laifi ne?" Ya kai karshen maganar tare da ɗagota da kyau ya mannata da kirjinsa.
"Yaya Nawid kwana fa ka ce zaka je kayi a asibitin, kuma fa ai naji mace ce fa ta kira ka, daman kenan akwai number mata a wayarka?". Allah sarki da yake ta jima tana som shi, hakan yasa take bala'in kishin kayanta, shi kuma bai san hakan ba.
"Am so so sorryyyyyyyyyy Matata, na tuba, yanzu dai to tashi muje Asibitin tare domin ki ganewa idanunki, ayi komai a gabanki, mu je tare kuma mu dawo tare ko, amma ki yi shiru dan bana son kukanki". Cikin sauri ya ɗago tana kallon shi, jin ya ce zasu je hospital a tare, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta tsare shi da ido ne yasa ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abin da ya ce.
Cikin sauri ta diro kasa saga saman, ta nufi waje tana murna, miƙewa shi kuma ya yi ya hau shirin zuwa hospital ɗin.
Tana fita ɗakin jelly ta wuce, har lokacin Ummi tana Palo tana kallonta. Hijabin jelly ta ɗauko tare da wasu kayan, doguwar riga abaya fara tas, da mayafinta, ta sanya rigar, ta ɗaura mayafin a matsayin ɗan kwali, ta ɗaura ɗan hijabin please call me ɗin a saman, shi ma hijabin fari ne tas, ta yi kyau sosai abinta.
Lokacin da ta dawo ɗakin shi ma ya kammala shi, hannunta ya riƙo a kan su tafi, karɓar jakar hannunsa ta yi tare da rataya shi a kafaɗarta, suka nufi waje.
A Palon suka tsaya suka yi wa Ummi sallama, addu'a ta yi masu tare da fatan nasara da kuma a dawo lafiya, sosai dai ta yi masu addu'a, sai Amin Amin suke amsawa da shi.
Suna fita harabar gidan ya ɗan rungumota a jikinsa, lokacin kuma karfe 6 daidai gari ya ɗan yi duhun mangariba.
Da kansa ya buɗe mata gidan gaba na motar ta shiga, bayan ya mai da marfin ya rufe, ya zagayo ta mazaunin driver, ya shiga ya zauna.
Zuba mata idanu ya yi ba tare da ya kunna motar ba, jin shiru bai tashi motar ba yasa ta ɗan ɗago dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, ƙasa ta yi da kai tana Murmushi.
"Me ya yasa ki murmushi?". Girgiza kai ta yi alamar babu komai. Matsowa kusa da ita ya yi tare da rankwafo da kansa sai tin tata. "Kin taɓa ganin anyi abu babu dalili ne?". Nan ma dai girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.
"To menene dalilin?" Nisawa ta yi kafin ta ce "Saboda kayi kyau sosai ne yasa nake murmushi, amma kuma....." Sai ta yi shiru. "Amma kuma menene? Ki karisar da maganar mana?" "Amma kuma bana son wata ta ganka a haka, bana son taga kyan da kayi". "Kenan kishi kike yi?" Girgiza mashi kai ta yi alamar A'a.
"Menene wannan idan ba kishi ba?" "No yaya Nawid ba kishi bane, kawai ina kula da kai ne, wai ka manta amarka a ka bani ne?" Zaro ido ya yi yana kallon yadda take zaro magana kamar ba ita ba, eyee wato Amanar shi aka bata, kai jama'a, wasa wasa ita ma ta iya magana sosai.
"E kam gaskiya ne, tun da amana ta a ka baki, dole ki kula da ni sosai, yanzu dai bani sumbata sai mu tafi ko? Lokaci na kurewa". Kara faɗaɗa murmushinta tayi tare da matso da ɗan bakinta sai tin kumatunsa da nufin ta sumbace shi.
Sai da ya bari ta kawo bakinta, sai ya juyo da face nasa ta sumbace sa a saman lips nasa, tana ƙoƙarin zamewa ya riƙota tare da zura harshensa a cikin bakin nata, ya fara kissing nata.
Sun ɗan jima a haka kafin daga bisani ya saketa tare da kunna motar yana wani lumshe idanu, kumawa ta yi ta jingina da jikin kujerar motar, ita ma ta lumshe idanunta kamar mai barci, wani azababben son shi ne ke kara ninkuwa a cikin zuciyarta.
A hankali yake tukin, duk bayan minti sai ya juyo ya kalleta, har lokacin idanunta a lumshe. Kasancewar suna tuƙi a hankali sai ya sa basu isa Hospital ɗin da wuri ba.
Har suka isa kuma, ta ki yarda su haɗa ido, a tare suka fito suka jera zuwa ciki, sai janta da hira yake yi, tun bata biye mashi sosai, har ta fara biye mishi, dayawa daga cikin nurses ɗin sun yi zaton kanwasa ce, domin basu san ya yi aure ba, kuma akwai kama ta jini a kan fuskokinsu, idan baku manta ba, da Hjy Turai da Hjy Hadiza ƴa da kanwa ce, dole za'a samu kama ta jini.
Kai tsaye office nasa ya wuce. Bai kai ga shiga cikin office ɗin ba wasu nurse guda biyu suka nufo shi da sauri, basu bari sun gama karisowa ba suka fara gaya mashi halin da matar da zaayiwa aiki take ciki.
Dawo da kallonsa kan Aafia ya yi, cike da kauna ya ce "Ki shiga office ki jirani ko, Bahijja ki raka ta, ki zauna ki kula da ita, ke kuma Ameera muje zuwa ɗakin da aka kwantar da matar". Ya kai karshen maganar tare da wucewa gaba. Wadda aka kira da Ameera ta bi bayan shi, ita kuma Bahijja ta yi gaba tana faɗin "Ke muje ko?".
Binta da kallo Aafia ta yi kafin ta maido da kallonta izuwa kan mijin nata, bata kula Bahijja ba har sai da ya kurewa ganinta, sai binta da kallon banza da raini Bahijja take yi, dan bata taɓa tunanin Aafia matar Dr bane, tun da basu ji labarin auren nasa ba, abu ne da aka yi shi lokaci guda.
Sai bayan ya kurewa ganinta ne ta tura kofar office ɗin ta shige, bayanta Bahijja ta bi, ta je zata zauna a ainahin kujerar da yake zama, Bahijja ta daka mata tsawa akan wai ta dako kujerar da patient suke zama ta zauna, kujerar Dr iya shi kaɗai ne yake zama a kai.
Da yake Aafia ma yar yi ce, ko kallon in da take bata yi ba, domin Bahijja bata kai ta ɗaga idanu ta kalle ta ba, wucewa ta yi ta zauna a saman ainahin kujerar tasa.
"Ke baki da hankali ne? Ina matsayin P.A na oga zan yi maki magana ki ki kulani, kanki ɗaya kuwa? Na