Showing 96001 words to 99000 words out of 359620 words

Chapter 33 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2016

daɗi kawai take yi.

Da yamma misalin karfe biyar suna zaune jugum jugum, sai lumfashi sama sama Aisha take yi, ga jikin nan nata ya yi zafi jau kamar wuta, duk suna kanta sai sannu suke yi mata, tana kwance cikin baff ɗin wanka, sai rawan sanyi take yi, ga shi babu abin da zasu rufata da shi, sai addua'o'i Jehan take ta faman tofa mata, da kyar take iya motsa bakinta, can kasa kasa ta ce "Jehan wlh kin cuceni, da ban biye maganarki ba, ai da yanzu ina zaune lafiya ta Lou cikin jin daɗi, amma yanzu ga shi zan mutu a cikin toilet saboda bala'in yunwa da kishin ruwa, ga wahala ta sanyi babu wajen kwanciya bare rufuwa, sai dai mu kwanta a tiles haka, dole sanyi ta kama mu, yanzu waye gari ya wayanwa?". Tana magana siraran zafafan hawaye na bin kuncinta ta gefe da gefen kunnenta.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara magana a nutse, duk yunwa ya kwakulesu, da kyar ita ma voice nata yake fita, "A'isha ban cuce ki ba, kuma abin da ya faru a yanzu kamata ya yi ma ya zama miki darasi, kamata ya yi ma ki ɗauki haske, yanzu tsakaninki da Allah kuɗi zai kai naira nawa kika kawowa wannan tsinanniyar gidan? Na san ba zaki iya kirgawa ba, duk da wannan kuɗi da kika kawo musu, bai sa sun ji tausayinki sun san suna karuwa dake ba, bai sa sun agaza miki sun yafe miki ba, ina son ki sani A'isha, sun gama dake ne, yanzu baki da amfani a wajensu, sun san cewa yanzu ba'a yayinki, sun gama ɗebar abin da zasu ɗeba a tattare dake, yanzu kin tashi aiki, ke da bakin ki a nan kika gaya mini, idan mace ta ragwargwaɓe zuwa suke yi su jefar da ita a wani garin, hakan yana nufin kenan idan mace ta gama biya musu bukatarsu to bata da amfani a wajensu, ki godewa Allah da ya nuna miki da idanunki kika gani tun da sauran numfashinki, wlh Aisha bariki bata da wata amfani, jiya dai kinga yayinki ake yi, kowa rububinki yake yi, yau kuma fa? Kowa ya gujeki, saboda komai naki ya kare, da zama kikayi, kika hakura kika yi aure, wlh koma ya zaki koma, sai an ganki da daraja tun da a ɗakin mijinki ki ke, yanzu fa? Ina mai tabbatar miki idan kika mutu, tamkar idan dabba ya mutu haka zasu ɗauke ki su jefar, kin sani ba wai baki sani ba, ke da bakin ki kike bani labari, to yana da kyau ki sani, duk wata ƴar bariki or ɗan bariki, mutuwar walanci suke yi, a lalace suke karewa, yana da kyau ki nitsar da tunaninki waje guda, ki san abin da kike yi, baa yin kuɗi da jiki, duk wanda ya ce miki ana yi karya yake yi miki, kuɗin ba zasu yi albarka ba, ni ina son ki tuba ne, ki koma ga Allah, ina miki sha'awar samun rahmar Ubangiji, yanzu sai Allah ne kaɗai yasan me yake damunki, wata kila wani cuta wani kafurin mutun ya sanya miki, kinga kuma su ba damuwrasu bane, idan cuta ta kamaki, ki mutu dan kanki, su dai tun da kin biya kuɗin da suka saye ki, to babu ruwansu, wlh yana da kyau duk masu shirin faɗawa irin wannan rayuwa ta bariki su sani babu wata nasara a saɓon Allah, babu in da zaka je, babu kuma abin da zaka cinma matukar zaka kauce hanyar Allah Manzonsa, duk wuya duk daɗi, ka tsaya a faɗar Allah da Manzonsa, to a nan ne zaka ci riba biyu, wato duniya da lahira, wlh ko yau na mutu, ba zan taɓa danasanin zuwata duniya ba, saboda ina iya kan bakin ƙoƙarina wajen ganin na tsaya a kan koyarwar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ban taɓa batawa iyayena rai ba, bantaɓa bari Sallah ya wuce ni ba, azumi, sadaka, dukka ina iya bakin ƙoƙari, har na rabu da iyayena albarka suke saka mini, to me yafi wannan a duniya? Ni nasan jarabawa ce Allah ya jarrabeni da shi na zuwa na wannan gidan, idan da na gaya miki ni ƴar wace ce, ke da kanki zaki ce eh tabbas jarabawa ce Allah ya jarrabeni da shi, kuma ina ƙoƙarin naga na ci wannan jarabawa, bana neman taimakon kowa sai na mahaliccina, baya barci, yana kallon duk abin da yake faruwa damu, da izininsa kuma zai kawo mana mafita, zai dafa mana, dan addu'a bata faɗuwa kasa banza, sai dai jinkirin amsawa, to ina mai........".

Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamon buɗe kofar da ta ji ana yi, cikin sauri suka miƙe tsaye da kyar, wani irin jiri ne ya ɗebesu saboda bala'in yunwa, cikin sauri ta dafe bango dan kada ta faɗi kasa, da kyar da kyar suke jan numfashi, idanu duk sun rena fata, dama Jehan akwai dara daran idanu, da ta rame sai suka kara fitowa kwala kwala da su.

Zinariya ce ta buɗe kofar, kamar kullun kajeren jeans fashion trouser ne a jikinta, sai riga mai hannun vest baki, tasha wannan uwar make up ɗin nata, ga uban attachment da ta zuba a kai kamar wani bukkar shaiɗanu, fuska kamar an ɗaye bayan kadangare, saboda bleaching ta cinye fatar, naman fuskar ta yi jawur, sai kuma ta rinƙa damɓara uban Foundation, abin kamar kayi ta kwara amai idan ka gani, ga wani uban hujin hanci da ta yi, sai ta wani tabka katon ɗangunne kamar na Indiyawa, to su indiyawa yana musu kyau idan suka sanya, ita kuwa, sai ya yi mata wani sundumdum a fuska kamar garman shanu, abu ba kyan gani, babban abin haushi kuma abin amai shi ne eyelashes da suke labkawa, abu kamar bindin kaza, a tsaitsaye yana zagin wadda suke kallah, harta Hajiyar daɗi irin dressing nata kena, kayan haushi, kamar ya finciko wannan uban ɗan kunnan na hancin nan nasu ka tuge har da hancin kowa ma ya huta shegu, sai uban warin man bleaching suke yi, kamshin turaren da suka sanya daban, warin man bleaching daban, dama kuma haka yake yi, shegen wari masu bleaching nan suke yi, ko sun sanya turare baya kau da warin, sune basu ganewa, na kusa da su kuma basu gaya musu gaskiya, dan tsoron kada su ɓata alakar dake tsakaninsu, hmmmm ai duk abin da Allah ya haramta ka ce zaka yi, to fa kana tsaka mai wuya, ka rinƙa faɗawa wahala da masifu kala kala, Allah dai ya karemu, yasa mu tsaya a iya in da Ubangiji ya tsai damu Amin.

Kallon banza ta watsa musu kafin ta ce "Ku wuce ku fito". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta nufi waje, "Ai na ɗauka barinmu zaku yi mu mutu a ciki, ban yi zaton zaku buɗe mu ba ai". Cewar Jehan da baki baya shiru, da kyar maganar yake fita, amma sai ta yi tsiwa.

"Ke kada ki kuskura ki ce zaki gaya mini wata magana a nan, wlh yanzun nan sai mu saɓa miki kamanni, ke wato bakin ki ba zai yi shiru ba ko?, To wlh ki sani nan bariki kikazo, akwai iyayen iyayenki a rashin kunya, yanzu zamu gyara miki zama, ku yi maza ku fito min nan tun ban ci uban yarinya ba dan ubanta!". Tana magana tana hura hanci takar balo balo, dama ga hancin ba'a magana.

"Babu in da zanje, kuma da kike wannan magana dama an gaya miki ni mara tarbiya ce irinki da zaki ce kunfini rashin kunya, wlh ina mai baku shawara da kuji tsoron Allah, ku sani akwai mutuwa, dan ba zance muku akwai tsufa, saboda kun rigada kun tsufa kun tsofe, ke a yadda kike yanzun nan saboda Allah ba kamata ya yi a ce ewar haka kina saman dadduma kina addu'a Allah yasa ki cika da imani ba, duk kin tsufa kin zagwanye, kadangarun bariki sun zuke miki ruwan kai da jinin jiki, amma har yanzu sheiɗan na zugaki na cewa kina da mamora ko? To wlh ki sani babu wata mamora da ta rage a jikinki face azaba da kika tana da wa kanki da kanki, ke da kanki idan zaki gayawa kanki gaskiya ki ajiye zancen sheiɗan a gefe, kin san cewa bai wuci taku biyu ya rage miki zuwa kabari ba, shekarunki nawa a duniyar nan? Kin taɓa waigawa ki duba a waƴan nan shekarun na baya da kika yi me kika aikata na alkhari? Wai ko dai kema kina ɗaya daga cikin waƴan da suke tunanin sun zo duniya kenan babu komawa? To idan ma kina ɗaya daga ciki ki sani dai duniya kam akwai ranar barinta, mutuwa gaskiya ce, yanzu ma tana iya ɗauke ki, bata jira sai an shirya, da a shirya da kar a shirya duk sai ta ɗauka idan lokacin ya yi, babu kuma uban da ya isa ya hanata ɗauka, to tun da sauran ni'ima ta numfashi da Ubangiji ya yi muku is better for you da ki tuba, ki tuba ki koma ga Allah, Allah gafurur rahim ne, zai karɓi tubanki!!".

A fusace ta juyo ta dawo cikin toilet ɗin, ranta a matukar ɓace ta ɗaga hannu zata zabga mata mari, nan take zuciyarta ya tuna mata da Hajiyar daɗi na dawowa gobe, hakan ce kuma tasa ta buɗe su, idan Hajiyar daɗi ta dawo da sami wani tabo a jikin su ukun nan, wato JEHAN, ADIVA, MARYAM, su da aka kawo sabbin, basu biya kuɗinsu ba, to sai ta yi wa su Zinariyar mummunar hukunci, dan kuwa ita bata ɗaukar asara, bata yarda da asara ko mai kankantar sa, shiyasa suka yi sauri tun yau suka buɗe su Jehan ɗin, zasu duba lafiyarsu da sauran abin da ya dace kafin hajiya ta iso ta same su lafiya, daga nan kuma su umarce su da kada su kuskura su gayawa hajiya abin da suka yi musu, idan ba haka ba wlh sai sun bi dare sun kashe su. BARIKI KENAN, BABU MUTUNCI KO KAƊAN.

Tuna hakan yasa bata bari Jehan ɗin ba, ta juya rai a ɓace ta koma cikin ɗakin tana jiran fitowarsu, da kyar Maryam da Adiva suka iya jan kafafunsu suka fito cikin ɗakin, ita kuma A'isha ko motsin kirki bata iya yi, komawa kusa da ita Jehan ta yi ta zauna, sai jiransu Zinariya take yi, amma shiru Jehan taki fitowa, daga karshe dai ta taso ta dawo cikin toilet ɗin, cike da bada umarni ta ce "Ke Jehan ki wuce mu tafi".

A kule rai a matukar ɓace ta ce "Babu in da zanje marasa imani kawai, wlh in dai baku ɗauki A'isha kun kaita cikin bedroom kun kwantar da ita a gadonta ba, to sai dai mu mutu ni da ita a nan!". Basu da zaɓi dole su fito da Aisha ba dan sun so ba, da farko basu yi niyar ko kallon in da take ba, amma da Jehan ta kafe akan sai sun fitar da ita zata fito ita ma, dan dole suka yi hakan dan gudun su yi laifi wajen Hajiya.

Bayan sun fitar da ita zuwa saman gadonta ne ita ma Jehan ɗin ta fito, dama sai da Zinariya ta kira wata wai tattabara tazo ta tayata fitar da A'isha, to suna fitar da ita tattabara ta koma bakin aikinta, ita kuma Zinariya ta tasasu a gaba tamkar wata uwarsu tana basu umarni kamar haka.

"Wlh ko da gigin wasa, idan wata ta kuskura ta sanar da hajiya abin da ya faru da ku, to sai na lahira ya fi ku jin daɗi, shekarunku sun yi kaɗan da su ɗauki azabata, zan iya kashe rayinya wlh".

Cike da confidence babu tsoro ko kaɗan a tattare da ita Jehan ta mai da mata da martani kamar haka "Saboda ke ce uwar mu ba, ai dole ki saka mu a gaba kina wani bamu umarni, ke bari ki ji in gaya miki fa, a bariki babu uwa, a bariki babu babba, duk wanda ya taka, kai ma ka taka shi, ko da kuwa shi ya koya maka bariki, kina tunanin bansan komai dan gane da bariki bane? To idan haka kike tunani ki canza, kowa babban kansa ne a bariki, kowa ga shin kansa zai ci, bari ki ji nayi yawo a Media fiye da tunaninki, sannan ke daga ganina baki ga kalar jahila ba, babu wadda ta isa ta zana mini ga abin da zan yi, tun asalina abin da nayi niya nake yi, to kuma a haka zan rayu a cikin gidan nan, da kuma kike maganar zaki kashe mu idan muka faɗa, an gaya miki rayukanmu a hannunki yake ne? Babu wanda ya isa ya kashe wani har sai kwanansa ya kare, duk wanda kika ga an kashe, to kwanansa ne ya kare, ko ba'a kashe shi ba zai mutu a wannan lokaci, sai maganar azabtar damu da kike yi, ke baki san mu kafuwar Allah bane? Duk azaban da kuka yi mana, kuka kullemu a cikin toilet babu ci har na tsawon kwana uku da wuni ɗaya, kuka buɗe mu babu abin da ya same mu, daga nan ya kamata ki sani kafuwar Allah ne ba na ɗan adam ba, sannan kina da wuta da aljanna ne? Tun da baki da ko ɗaya ai shekenan duk wani azabanki na banza ne, ni ba zan gaji da gaya miki ki ji tsoron Allah ki sani akwai lahira, akwai ranar da zaki biya duk wani abin da kika yi, ranar da babu uban da ya isa ya tare miki, kuɗi ba zasu tsinana miki komai ba a wannan rana, kina da sauran lokaci da zaki iya tuba, to kada ki bari dama ya kubce miki, sai magana ta karshe, wlh zaman ki lafiya a gidan nan shi ne ki dai'na nuna mana wani izza kamar ke kika haifemu, idan ba haka ba, na yi miki alkawarin wlh ni zan sanya ki ki fara danasanin zuwanki duniya a rayuwarki, da ni kike magana JEHAN NAWAZUDDEN SALMAN SULTAN, ni kai'na wani lokaci tsoron kai'na nake ji, dan haka zaman ki lafiya ki fita harkata, idan kuma kika ki, wlh na juyo muka sanya kafar wando ɗaya, Allah sarki, sunanki sorry". Duk wannan magana da Jehan take yin shi fa, bala'in tsoro ne cike fal a ranta, kamar yadda kuka sani ne, kwarin gwiwar a iya baki ne kawai, ita dai kawai ta yi Imani da cewa duk tsoron mutun da kake ji, idan ka dake ka nuna baka shakkarsa ba kuma ka tsoronsa, to tabbas sai fara shakkarka har ma ya ji tsoron naka, kuma haka ne, rayuwa idan ka nuna kana tsoron abu, to tabbas yafi tsoratar da kai, amma idan ka dake, ka nuna jan wuya, to fa ba makawa zai fara tsoronka, zai yi ta tunanin ko ka taki wani abin ne.

Duk rashin kunya irin ta Zinariya yau dai sai da ta ji tsoron Jehan ya kamata, mamaki take yi tare da tunanin anya ba wani abu Jehan ta taka ba kuwa? Abin ya fara ɗaure mata kai, shiru ta yi bata sake ce da su komai ba, wannan shi ne gaba ma da gabanta.

Suna a wannan hali Yar gwal ta shigo ɗakin ɗauke da abinci kala biyu, na Jehan daban, nasu Adiva daban, nan ma ba karamin dirama suka sha ba, dan Jehan ta ce wlh idan sun ga ta ci abinci, to tare da su Adiva zata ci, ba zata ci wannan abincin da suke bata ita kaɗai ɗin ba, domin kuwa tun da suka kafe sai taci shi tun farkon zuwanta, daga nan tasan tabbas akwai wani abu a cikinsa, ba haka kawai ba, to kuma ba zata ci ba, ba yadda basu buga ba, ta kafe ta ce sai dai yunwa ya kasheta, ƴar gwal har ta fara yunkurin ƙoƙarin zata dake ta, Zinariya ta dakatar da ita, ba dan sun so ba, sai dan saboda kada yunwa ya kashe Jehan Hajiyar daɗi ta sanya su biya, haka suka hakura suka fita da abincin Jehan ɗin, suka ce taci nasu Adivar, hakan kuma ya kara tabbatarwa da Jehan tabbas akwai abin da suka zuba a ciki, idan da babu komai ai da zasu juye musu abincin ne su haɗa musu su ce su ci, amma sun koma da shi, to akwai wani abu a kasa. Allah dai ya kyauta.

Suna fita su Adiva suka fara cin abincin hannu baka hannu kwarya, bayin Allah sun wahala, ita ma Jehan ɗin hannu baka hannu kyarta ta fara cin abincin, jolof rice ce, ta ji kayan haɗi ba karya, ko wanka basu tsaya yi ba, sai da suka kusan cin ye abincin, Jehan ta ɗauki tray ɗin ta dawo kusa da A'isha dake kwance tamkar babu rai a tattare da ita, dan ta bata abincin a baki.

Zama ta yi a gefenta tare da fara ambatar sunanta a nutse, "A'isha, A'isha". Shiru bata amsa ba, taɓata ta fara yi tana mai cigaba da ambatar sunanta, nan ma shiru bata amsa ba, a razane ta fara jinjigata da karfi tana kiran sunanta, da sauri suma su Adiva suka yi kanta dan su ga menene ya same ta, ina shiru bata ko motsi, da gudu Jehan ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje.

Bata zame ko'ina ba sai office ɗin Zinariya, zaune ta iskota saman kujera tana shan lemun kwalba mai sanyi, a ruɗe ta gaya mata abin da yake faruwa da A'isha, babu ko tsoron Allah a cikin zuciyarta bare tausayi ta ce "To ina ruwana dan bata motsi? Ta mutu mana idan ta ga dama". Hankalinta kwance ta yi wannan magana.

Tsabar bakin cikin Jehan bata san lokaci da ta yi wani irin mahaukacin kukan kura ta damko wuyar rigarta ba, idanunta sun rufe, rashin imanin gidan nan ya wuci tunanin mai tunani, zuciyarta tafasa yake yi tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ga idanunta dama sun kara girma sabida rama, yanzu kuma sun yi jawur kamar wuta, zarosu waje ta yi sosai tare da shaƙe wuyar Zinariyar da iya karfinta na karshe, cikin tsawa ta ce "Tabbas idan A'isha ta mutu wlh ba zan barki ba, baku da imani, baku


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login