Showing 228001 words to 231000 words out of 359620 words

Chapter 77 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1962

ta yi shiru tana kallon sama, yanayin kwanciyar da ta yi kuma yasa wani ɓangare na daga cikin zanen sunansa da ta yi a kirjinta ya fito, saboda ta kwanta ne a mike tana kallon sama, so kunsan yadda wuyar normal abaya kuma take, tana da ɗan girma, bare ita da bata gama cika sosai ba, wuyar ta yi mata yawa kaɗan.

Sam bata ji shigowarsa cikin ɗakin ba sai ganin inuwar mutun ta yi a wajen mirror ta wutsiyar idanunta, da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "Yaya Saif in kawo maka abinci?". Ko sannu bai ce mata ba, miƙewa ta yi zata fice daga cikin ɗakin, zazzakar muryarsa ne ya daki dodan kunnenta. "Yaushe zaku gama exams?" Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba, amma yana kallonta ta cikin mirror, ita ce dai bata kallon face nasa sai bayansa.

"Saura kwana uku ne yau nake tunani". Ta bashi amsa, Jinjina mata kai ya yi dan yana son barinta ta kammala Exams nata kafin su yi tafiya, baya wasa da karatu, yana ɗaukar ilimi da daraja da mahimmanci over, shiyasa baya yi mata wasa da karatunta. "Yaya Saif in kawo maka abinci?". Ta sake tambayarsa. "Ki kai mini garden". Ya faɗa tare da wucewa ya nufi toilet. Wani irin daɗi ta ji yau ta yi magana har sau biyu da shi kuma dukka ya amsa, da idan ya amsa sau ɗaya ko zaka shekara kana sake yi mishi magana ba zai sake amsawa ba.

Palo ta nufa, sai nasiha ta tarar su Abba suke yi wa Akila da Aseef, kasa kunne ta yi tana jin abin da suke faɗe da ta shiga kitchen ɗin, sai kuka Akila take yi ta kwanto kanta a cinyar Abba, faɗa sosai suka yi mata, har ta daddyn Jelly sai da ya yi mata faɗa, sannan suka dawo kan Aseef ɗin shi ma suka yi mishi nasiha sosai a kan aure, sosai ya natsu yana jin su har suka kammala, cikin sanyin murya ya ce "Nagode sosai uncles, kuma nayi muku alkawarin In Sha Allah zan kula da Heartbeat sosai, zan kula da duk wasu hakokinta da ya rataya a kai'na, ba zan iya biyanku ba abin da kuka yi mini, sai dai nayi muku addu'ar samun rahmar Ubangiji a duk in da kuke, bani da wasu kalmomi da zan yi muku godiya da shi face addu'ar nan dai".

Areef ne ya karɓi zancen da cewa "Gaskiya mun gode sosai da irin halakci da kuka nuna mana, we really appreciate Allah ya biya ku da mafificin alkhari". Amin suka amsa da shi kafin su ce daddyn Rimsha ya rufe musu taron da addu'a zasu tafi, shi dai Lion duk abin da suke yi yana ciki abinsa, bai ma san suna yi ba, ya yi wanka yana shiryawa cikin kayan barci, abin da ya faru tsakaninsa da Rimsha ne yake ta yi mishi yawo a kwakwalwarsa, idan ya tuna ya hura mata iska a baki sai zuciyarsa ta amsa, lallausan laɓɓanta sun tsaya mishi a rai sosai, kamar yadda Malika ta yi tunanin zai faru, hakan kuwa ya faru, sun tsaya mishi a rai ba kaɗan ba.

Ita kuma Rimsha da ta gama jin nasihar sai ta kwashi kayan abincin ta wuce garden da su, bayan ta kai ne ta dawo ta yi wanka tare da shiryawa cikin kayan barci riga mai dogon hannu da kuma wando dogo, sai ta ɗauki hijabi ta sanya a saman kayan bayan ta gama fesa perfume a jikinta, sai zuba kamshi take yi, ta yi kyau abinta sosai.

Garden ɗin ta koma, har lokacin bai zo ba, zama ta yi saman sofa dan ta jira shi, su kuma su Abba, bayan sun kammala addu'a da duk wani nasiha da zasu yi, suka yi musu sallama, har wajen motocinsu dake wajen gate daddyn Rimsha da Areef suka rakasu, sun bar Akila da Aseef a palon, sai kuka take zubawa.

Ba zai iya miƙewa ya je kusa da ita ba bawan Allah, jiri yake gani, dan haka sai ya rinƙa rarrashinta daga in da yake zaunen har su Areef suka dawo suka same su, daddyn Rimsha ne ya rungumota ya rinƙa bata hakuri yana rarrashinta, shi kuma Areef ya taimakawa Aseef ɗin zuwa bedroom ɗin Lion dan su bashi abinci da kulawa ta musamman dan tabbas akwai ciwo a jikinsa.

Suna shiga bedroom ɗin shi kuma Lion yana fitowa shirye cikin kayan barci masu kyau da tsada, riga ce da doguwar wando masu bala'in laushi, sai dai ya ɗaura jacket a saman kayan nasa, dama haka yake yi in dai zai ke garden, yana sanya jacket saboda cikin dare sanyi mai ratsa kashi yana sauka a wajen. Ko sannu bai ce musu ba ya wuce zuwa palon kasa sai zuba daddaɗar kamshi yake yi.

A nan ya wuce Akila da daddyn Rimsha ko kallon in da suke bai yi ba. Da sallama kasa kasa ya shiga garden ɗin, tana zaune tana taunar chewing gum da Anaya ta bata dayawa a school yau, shi ne ta zubasu a cikin jakarta take aikin tauna guda biyu, shakar daddaɗar kamshin perfume nasa ta yi tare da lumshe idanu.

Saman sofa ya zauna ba tare da ya yi mata magana ba, miƙewa ta yi ta dawo kusa da shi ta zauna tare da fara zuba mishi abincin, bayan ta zuba mishi ta tura mishi ne ya ce ta je ta kawo mishi laptop nasa a bedroom nasa, okey ta amsa mishi da shi tare da miƙewa.

Kunna wutar screen ɗin wayarsa ya yi ya duba time 9:30pm jawo abincin ya yi ya fara ci cikin natsuwa da class, a haka ta dawo ta same shi, kusa da shi ta ajiye mishi laptop ɗin tare da komawa saman sofa ta kwanta tana tunanin yadda zata kaya a ranar da zasu gama exams, suna da party a school ɗin nasu, tasan daddynta, yaya Areef, yaya Aseef duk zasu je, amma ta so ace Lion ma zai je, sai dai ko a mafarki ta san ba zai taɓa yiwuwa ba, dan kuwa bata ga mai sanya shi zuwa ba, bama wanda ya isa ya tinkare shi da maganar, amma bata da burin da ya wuce ya je ɗin.

Wayarta ne ya fara kara, dubawa da zata yi sai ta ga new number ne, kamar ba zata ɗauka ba, sai kuma ta ɗauka, karawa ta yi a kunnenta a sanyaye kasa kasa ta ce "Hello". "Kin fara barci ne Rimsha". Daga ɗayan ɓangaren uncle Faisal ya faɗa, "Aa uncle ban yi barci ba ina wuni". "Lafiya lou ya karatun exams?" "Lafiya lou Alhadulillah" ta bashi amsa tana kallon yadda Lion yake cin abincinsa cikin kwanciyar hankali.

"Yau dai nayi sa'a da kika ɗauki kirana, ban san meyasa baki son ɗaukar kirana ba Rimsha". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Babu komai uncle ai wayar ce bata hannuna shiyasa, amma kai ma kasan ai ba zan ki ɗaukar call naka ba, kuma.......". Bata kai karshen maganar ba ta tsaya cak sakamakon ido da Lion ya wurga mata, ga shi dare ne idanun nasa sun kara kyalli, nan take ta nemi natsuwarta ta rasa, duk tabi ta dibirbir ce, bai ce da ita komai ba, ya dai tsareta da idanu yana kallon face nata, duk da ta kawar da kallonta daga kansa, amma ta kasa cigaba da yiwa uncle Faisal ɗin magana, sai hello, hello yake ta cewa, amma ta kasa amsawa.

Almost 2 mins suna haka, bai kawar da kallonsa daga kanta ba, ita kuma bata cigaba da wayar ba, shi kuma uncle Faisal bai katse kiran ba, dan a cewarsa idan ya katse da wuya ya sake samu ta ɗauki kiransa, so gara ya saurara ya ji.

Hannu Lion ɗin ya miƙa mata a kan ta bashi wayar tata ba tare da ya yi magana ba, ba musu ta miƙe ta karisa gabansa, cikin natsuwa ta miƙa mishi wayar, karɓa ya yi tare da cewa ta zuba mishi ruwa.

Mamaki take yi, ta fara tantama a kan Lion gaskiya, duk yadda aka yi yana jin Hausa, domin kuwa duk maganar da suka yi da uncle Faisal da hausa suka yi shi, idan ba ya ji me suka ce ba, me zai sa ya karɓi wayarta? To me ma zai yi da wayar? Sai tambayoyi take jerawa kanta har ta gama zuba mishi ruwan ta miƙa mishi.

Shi kuma bai bi ta kan call ɗin da suke yi ba ya ajiye wayar a gefensa tare da karɓar ruwan ya kafa a bakinsa, abin da ya faru tana can tana waya ya ce ta bashi ruwa bata ji ba, shi ne ya ɗago ya tsareta da idanu, da ya ga bata da niyar zuwa ta zuba mishi ruwan, sai ya ce ta kawo mishi wayar daga yau ya kwaceta kenan.

Sai magana uncle Faisal yake yi, Lion ɗin ya ajiye wayar ma bai kula ta ba, zata kwashe kayan abin ne ya ce mata ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage, dama tana jin yunwa sosai, dan haka sai ta zauna ta fara ci, shi ma Lion ɗin yasan tana jin yunwa sosai ne shiyasa ya ce ta zauna ta ci, yasan duk wanda yake gidan nan yau to da yunwa ya wuni, dan basu da kwanciyar hankali, basu bi ta kan abinci ba sam.

Tana tsaka da cin abincin ne Brady ya shigo cikin garden ɗin da gudu, wani irin girgiza ya yi na ganin Lion, da gudu ya haye jikinsa, da gani yana cikin tsantsar farinciki, shafa jikinsa Lion ɗin ya fara yi yana ƙoƙarin ɗauko wayarsa kira ya shigo wayar Rimshar, number uncle Faisal ne.

Da farko kamar ba zai kula ba, sai kuma ya yi picking call ɗin tare da sanya wayar a hand-free, daga ɗayan ɓangaren uncle Faisal ya fara magana "Gimbiya sarautar mata, yau rana ta ce mai sa'a, ban yi tunanin zaki sake ɗaukar kiran ba, gaskiya naji daɗi kuma nayi sa'a, ɗazun ya akayi kika yi shiru muna magana?" Wannan karonfa uncle Faisal da turanci ya yi maganar tasa dukka.

Ɗago ido Lion ya yi yana kallon Brady, ita kuma kwarewa ta yi ta fara tari kamar wata mara gaskiya, ɗaukar wayar ya yi tare da bin number uncle Faisal ɗin da kallo, kallo ɗaya ya haddace number a kansa, sai hello uncle Faisal ɗin yake ta faɗa, katse kiran ya yi tare da yunkurin miƙewa zaune, dan ya fi karfin ya yi magana da uncle Faisal ɗin, tsabar tsadar maganarsa ba kowa yake samu jin voice nasa ba, wani abin ba sai ya yi magana ba yake ɗaukar mataki a kai, in ji sojojinsa suka ce shirunsa ma magana ce.

Sauka daga jikinsa Brady ya yi dan ya bashi damar miƙewa.

"Waye shi?!" Shi ne tambayar da ya wurga mata, wani irin haɗiyar wahalallen yawu ta yi, "Uncle namu ne" da kyar ta iya bashi amsar, tunani ya fara yi a ransa, au dama su uncle ɗin an tura musu yara ne dan su yi ta kiransu a waya suna gaya musu wasu maganganu marasa kan gado? Dama ba karatu suke koya musu bane ko yaya? Yanzu shi da girmansa yana malami ne zai kira karamar yarinyar da yake koyarwa yana faɗan hakan? Anya malan ƴan Nigerian nan kansu ɗaya kuwa?.

A fili kuwa ɗaure fuska sosai ya yi dama fuska ba'a magana, kullum a ɗaure take. "Dama ba karatu kike zuwa yi a school ɗin ba kenan?". Ɗago kai ta yi dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, ganin yadda fuskarsa take ne yasa ta miƙe a guje dan ta bar wajen, saboda kada ya naɗa mata duka, ai yanzu tsoronsa ya kara ninkuwa a ranta tun shekaran jiya da ya kusa kasheta, ba dan Areef ba da yanzu idan bata cikin kabari to tana gadon asibiti.

Wani wawan damka ya kai mata a ciki tare da jawota baya, tafiya ta yi luuuu sai saman faffaɗar kirjinsa ta faɗa, wash ta furta da karfi, shi kuma hannu yasa ya damko wuyarta ta saman hijabin, rai a matukar ɓace ya ce "Me kike zuwa yi a school?" Girgiza mishi kai ta fara yi ta ji shaƙa, nan take ta fara ganin wasu hayaniya suna gilma mata ta cikin idanu, shi kuwa ransa kara ɓaci yake yi idan ya tuna cewa yanzu idan ta je school kenan tsayawa take yi da maza suna hira, har da basu number wayarta, wato ta yi girman da zata yi hira da namiji? To ta ce mishi menene ma?.

Tuna hakan yasa ya kara shaketa da karfi har sai da harshenta ya fito waje sosai, "Me kike zuwa yi a school?!" Ya sake tambayarta idanunsa sun riƙiɗe sun yi jawur da su, sai ƙoƙarin bubbuga hannunsa take yi dan ya saketa kada ta mutu, idanuwanta sun yi jawur kamar jini, sun ciko da kwallah tab, azababben kishi ya rufe mishi idanu zai yi kisan kai a banza.

Ganin zata mutu da gaske ne shi kuma bai ma damu ba yasa Brady ya fara daka mishi haushi yana kokarin cire hannunsa daga wuyarta, tabbas da ya kara minti ɗaya shake da ita ba makawa mutuwa za ta yi, dan kuwa ta shaku ba karya, ya matse wuyarne na wuce misali ta yadda ko numfashi baya wuce nata.

Sai da ya tabbatar ta galabaita ta kusa mutuwa sannan ya saketa yana wani huci kamar mayinwacin zaki.

Kokarin kama shi ta fara yi dan ta miƙe ta sauka daga jikinsa, ruwa kawai take son sha, yau a karo na biyu ta ji kamshin lahira dukka kuma a hannunsa, ranar ta farko shaketa da ya yi a bedroom nata lokacin da ta ɗauki kiran daddynsa, sai dai fa shakar yau ta fi shan azaba, dar har sai da harshenta ya zazzago waje, ta kusa bakuntar lahira.

Damko wuyar rigarsa ta kirjinsa ta yi cikin fitar hayyaci tana kokarin mikewa ta kasa, ta riƙe wuyarta da hannu ɗaya, sai ruwan hawaye take yi, babu karya ta azabtu na wuce misali.

Duk azababben bakin kishin da yake ji, bai hana ya ji tausayinta ba ganin halin da take ciki, ciza laɓɓansa ya yi tare da ɗauko ruwa a cikin kayan abincin ya buɗe bakin robar, tallabo kanta ya yi a gefen kirjinsa ya kafa mata robar a bakinta, sha ta fara yi babu kama hannun yaro, sai wani irin numfashin take yi, ta fita a hayyacinta sosai, komai bibbiyu take gani, harta shi kansa bibbiyu take kallonsa. Allah sarki ita kuma nata kaddaran kenan, wannan azababben bakin kishin nasa, da shi take azabtuwa matuka, idan ya damketa sai ta ji kamshin lahira.

Sai da ta shanye ruwan tas kafin ya cire mata robar daga bakinta, yana cire mata ta lafe a kirjin nasa tare da runtse idanunta tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da alama har yanzu bata dawo daidai ba.

Sake kiran wayar tata uncle Faisal ya yi a karo na uku, wani irin wurgi ya yi da wayar ta daki jikin glass dake kewaye da wajen ta tarwatse, jin hakan yasa ta yi kokarin barin jikin nasa, rikota ya yi da karfi yana sake tambayarta me take zuwa yi a school dama?.

Ganin hakan yasa ta kwanta a kirjin nasa kawai tana kuka kasa kasa mara sauti mai tsuma zuciyar mai sauraro, sai dai sam shi kam bata tsuma mishi zuciya ba gaskiya, azababben kishi ya rufe mishi ido.

"Yaya Saif wlh bana kula shi, shi ne nan yake yi mini magana, kuma ni bani na bashi numberta ba, wlh Anaya ce ta bashi, ka kira shi ka tambaye shi ko ya kirani bana ɗauka, wlh ni karatu nake zuwa yi a school ba wani abu ba, zaka iya tambayar Mark ka ji, Allah banda karatu babu wani abin da nake yi". Da kyar take yin maganar muryarta na gargada, ta kai karshen maganar tana sakin kuka mai sauti sosai, ta wahala sosai ƴar kaniya.

(Tab uncle Faisal ma kenan, to ina ga ya ji labarin Mr Emmanuel kuma da abin da yake yi musu kuma?🤔 Ina ga lahira ne kawai zata yi bako)

Har cikin ransa ya ji sanyi dan ya yarda da maganarta, yasan bata yin karya, idan kaji ta yi karya to da kwakkwaran dalilinta na yin hakan, so ya yarda da abin da ta faɗa yanzu, ya kuma ji sanyi sosai a ransa, dan haka sai ya sauke Nauyayyar ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, sai a lokacin ne kuma ya fara jin sautin kukan nata yana ratsa shi, har cikin ransa ya ji ba zai iya jure kukan nata ba, waro idanuwansa ya yi a saman face nata, idanunta a datse gam.

Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallonta, nan take tunanin laushin laɓɓanta ya dawo mishi cikin ƙwaƙwalwarsa, kai kallonsa saman Lips ɗin nata ya yi yana jin wani irin yanayi a jikinsa, ji yake yi tamkar ya kai hannu ya taɓa su, ga shi yadda take kukan hancinta ya toshe saboda tana kwance ga kuma kuka, dole ta baki take numfashi, so time to time tana motsa laɓɓan nata dan fitar da numfashi, duk kuma time ɗin da ta motsa su sai dimples nata sun lotsa, ba karya suna kara tafiya da imaninsa ba kaɗan ba, duk abin da yake saman face nata ba karamin kyau yake yi mishi ba.

Motsa laɓɓanta ta yi dan ta ja hanci, nan take dimples nata suka yi wani irin lotsawa sosai, bai san time da zuciya ta ɗebe shi ya sanya yatsarsa ɗaya a cikin ramin dimple ɗin nata ba, suna yi mishi tsantsar kyau, sam shi ma yanzu baya cikin hayyacinsa, ya yi nisa a kallon abubuwan da suke burge shi, bugu da kari gata kwance a kirjinsa, ai dole ma ta sanya shi shiga wani duniya. BAKA GA KOMAI BA, AN GAYAMAKA MATA WASA NE?

Ɗan motsa latsan nasa ya yi a cikin ramin dimple ɗin nata yana mai jin wani irin yanayi, bata san lokacin da ta tsayar da kukun nata ba jin hannunsa a face nata, tana tsoron ta waro idanu su haɗa ido da shi, dan haka sai ta danne duk da cewa tana son kallon meyasa ya sanya yatsansa a dimple ɗin nata, a hankali ya ɗan shafa kumatunta tare da shafo hawayen nata, shiru ta natsu tana jinsa, bawan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login