Showing 273001 words to 276000 words out of 359620 words

Chapter 92 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2033

ɗin ya dawo, domin ya samawa daddyn ƴanci, ya gaji da kallon abin da Lion yake yi mishi, shi ne daddyn ya ce to zai koma gidansa na nan Kadunar, amma ya yi wa Areef alkawarin za'a ɗaura aurensa da Jehan kafin ya bar gidan, so zai tafi ya barta a nan, hakan tasa Areef ɗin ya ji daɗi ba kaɗan ba, to shi ne suka je ganin gidan suka kuma saka masu decoration na gida suka zo suka gyara komai, a ka wanke ko'ina da ina.

Areef da daddy sai hira suke yi, ita kuma Jehan tana kallon India film a Tv, Areef ya tada kai da cinyar daddy suna zuba hira kamar wasu abokai, a hankali daddyn ya kwantar mishi da kansa a saman sofa tare da mikewa yana faɗin yana zuwa bari ya yi wanka ya yi shirin barci dan barci yake ji, okey Areef ɗin ya amsa mishi da shi yana hararar Jehan dake kallon shi, ita ma hararar shi ta yi tana turo baki, motsa laɓɓansa a hankali ya yi ya furta zan kamaki ne, kallon up and down ta yi mishi tare da murguɗa baki, shi dai daddy sa kai ya yi ya wuce abinsa, dan shi diramar tasu ma wlh daɗi take yi mishi, abin yana burge shi.

Daddyn yana barin waje suka mai da hankalinsu gabaɗayansu a kan Tv, dama ita already kallon take yi, shi kuma tafiyar daddyn yasa dole ya yi kallo lafin ya dawo, dan yasan ko ya yi mata magana ba zata amsa ba, to ba sai ma ya yi mata ba, su yi kallo kawai dan bai jin tsokanar yau.

Kamar da ga sama aka hasko masoyan Indiyawa suna kissing na juna a cikin Tvn, juyowa ya yi yana kallonta yayin da ita ma ta juyo ta saci kallonsa, tamkar ta nitse cikin kasa saboda kunya, gera ɗaya ya ɗaga mata alamar yane, kallon sama da kasa ta yi mishi tare da kawar da kanta gefe dan bata son ma ta sake kallon Tvn tun da sun sako abin kunya, dama ba'ayi hakan bama ya ta kare da ɗan iskan nan a cewarta.

Zazzaƙar muryarsa ne ya katse ta da cewa "In zo nima ki yi mini?". A sukwane ta dawo da kallonta kan nasa, me zata yi mishi kenan? Ta tambayi katan, tana tsaka da tunani sai ganin shi ta yi ta miƙe ya nufota yana faɗin "Kiss mana, shi zaki yi mini". Ai bata san lokacin da ta mike da gudu ta bi bayan daddynta ba, sai dai ina bata kai ga shiga ɗakin daddyn ba ya sha gabanta yana faɗin "Allah ba zaki je waken uncle ba, sai dai ki tafi bedroom naki ko kuma ki yi mini kiss". Tamkar ta shakesa haka take ji saboda haushi.

"Amma baby wlh lips naki zai yi daɗin kiss ba kaɗan ba, bari dai na gwada mu ji". Yana magana ya matsowa kusa da ita, a sukawane ta juya ta shige cikin bedroom nasu tana ɗaure fuska, murmushi ya yi yana faɗin "Ba yanzu ba, amma gaba tabbas zan yi hakan, yanzu dai tsona ce kawai". Ya kai karshen maganar tare da nufar ɗakin daddyn, dan basu gama hira ba, yana shiga ya haye saman bed ya kwanta, ita ma saman gadonta ta haye ta kwanta tana tunanin idan anjima kaɗan ta yi in Areef ɗin ya koma bedroom nasa zata je ta gayawa daddy wlh ya rabata da Areef ko kuma ta bar gidan nan.

Da wannan tunani ta miƙe ta yi wanka ta shirya cikin kayan barci riga da wando, ta yi kyau sosai na wuce misali, sai zuba kamshi take yi, dama kunsanta akwai ta da son kamshi kuma bata son datti ko kaɗan, saman bed nata ta kwanta har karfe 11 na dare, sannan ta miƙe ta lallaɓo a hankali kamar wata ɓarauniya ta nufi bedroom ɗin na daddy.

Tazo zata shiga ɗakin kenan shi kuma yana fitowa, a bakin kofa suka yi karo, bata kula shi ba, ta sa kai zata wuce cikin ɗakin, hannu yasa ya tare kofar ɗakin tare da gyara tsayuwarsa a wajen ya tare mata hanya.

Idan da sabo ta saba da iskancinsa dan haka sai ta ce "Malam ka bani hanya zan wuce ne". Tsare ta ya yi da idanuwan nan nasa, ya wani kashe su kamar wanda ya yi shaye shaye, sai mata wani irin mayen kallon yake yi from head to toe ba tare da ya yi magana ba.

Ganin ba shi da niyar yin magana kuma bashi da niyar bata hanya ne yasa ta ce "Wai kai dan Allah me na maka ne kake addabama rayuwata?".

Sai da ya ɗauki good 2mins yana ta mata wani shegen kallon kafin ya matso kusa da ita sosai, murya kasa kasa ya fara magana "Saboda kin ki kice mini I love you, sannan kuma kin ki ki fara kirana Babyn baby, dan haka ba zan daina takura miki ba". Da wani irin kallon banza ta juyo da kallonta kanshi, ji tayi kamar ta wanka wa lallausan kumatun nan nasa mari, ga kumatun ya yi jawur luwai luwai zai yi daɗin mari, amma ba zata iya ba, a zahirin gaskiya daurewa take yi kawai tana magana da shi, amma bala'in tsoronsa take ji kamar zata mutu daga ta ciki, ga bala'in kwarjinin da yake yi mata.

Jin ta yi shiru ne ya sa ya sake matsowa da ɗan bakin nan nasa saitin kunnanta kamar mai raɗa. "Baby kin girma daidai yanda nake so fa, komai ya cika daidai, kinga twins ball's ɗin nan naki, daidai haka nake so, sun isheni". Da sauri ta ɗago tana kallon shi, kashe mata ido ɗaya ya yi yana wani ɗaga gera guda, ɗan juyawa ta yi ta kalli kofar ɗakin daddyn, shi ko kunyar daddy ya ji abin da yake faɗa ma baya ji.

Ganin tana kallon ɗakin ne yasa ya kara matsowa kusa da ita sosai, ta yanda har suna iya juyo numfashin juna "Daddy ya san ke matata ce ai, ya bani ke, dan haka normal ne, yanzu dai bani hot kiss kamar wanda muka gani ɗazun a Tv, zan je na kira Lion mu ga juna daga nan nayi barci"

Harara ta banka mishi tare da faɗin "Bani hanya na wuce!". Dafe saitin zuciyarsa ya yi yana faɗin "Wash Allah kin kashe ni da kika yi maganar nan, wai ni baby me nayi miki ne da baki so na?".

A kule ta ce "Saboda kai ɗan iska ne, kuma wlh ko ka bani hanya na wuce, ko kuma na yi maka ihun kwarto a tsakar daren nan".

Wani irin cool murmushi ya saki yana shafa kansa ya ce "Good idea kin ga daga nan sai a ɗaura mana aure, na yi mata a sama, amma shawaran nan ta yi bari ki ga na yi miki kwartancin ma da wuri yadda za'a fi yin saurin ɗaura aure". Ya kai karshen maganar yana jawota jikinsa. Kware baki ta yi zata yi ihu da gaske, cikin sauri ya toshe mata bakin da hannunsa ɗaya, dan baya son ta tashi daddy daga barci, bawan Allah ya jima da yin barci abinsa.

Kasa kasa ya ce "Idan kika yi ihu Allah sai na yi maganinki a cikin daren nan, tukunnan ma me ya fito da ke? Kuma me zaki je yi wajen uncle?". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga bakin nata.

Wani irin yanayi take ji yana ratsata, namiji bai taɓa taɓa jikinta ba, sai wannan ɗan bala'in a cewarta, sai kokarin kwace kanta take yi, shi kuwa da hannu ɗaya ya riƙe kugunta ya mannata da kirjinsa, ta kasa kwacewa.

"Ki natsu ki gaya mini me ya fito dake? Kuma me zaki je yi wajen uncle?". Ta san halinshi sarai idan bata ba shi amsa ba to ko kwana za su yi a nan ba zai sake ta ba, hakan yasa ta turo baki rai a ɓace ta fara magana.

"Ni da daddyna shi ne kake tambayar me zan je yi a wajen shi? To ganin shi zan je yi" girgiza kai ya yi yana ɗan raba jikinsa da nata, dan ta fara jefa shi cikin yanayi. "No correct amsar abin da ya fito da ke zaki gaya mani, idan ba haka ba yau a cikin bedroom na zaki kwana". Kamar ta shakesa saboda haushi, kumatu a kunbure ta ce "Karar ka zan kai mashi, dan ya rabani da kai, ka addabawa rayuwata, na ga ji".

Sake ta ya yi yana murmushi ya ce "Au haka ne dama? Lallai kice na kara takura miki kenan? Tom gara da mum tana nan idan kika kaimata karata shi ne wata kila zan ɗan barki ki huta na kwana biyu, amma uncle kam kara hura wuta zai yi, kisani daga yau kullun da safe sai kin zo bedroomna na ganki tukunnan kafin ki ga kowa, nine mutun na farko da za ki fara gani kafin kowa, kin ji na gaya miki, sannan ina miki albishir da ki sani takura yanzu na fara yi miki ba fashi, daga yanzu sabbin salo zan fitar in ga mai kwatarki my babyn babynta". Ya kai karshen maganar yana ɗaga gera ɗaya.

Kallon sama da kasa ta yi mishi rai a ɓace ta ce "Allah zai saka mini kuma wlh ban....." Bai bari ta karisa ba ya yi sauri sake jawota jikinsa yana faɗin "Kina karisawa sai na yi miki abin muka yi ido huɗu dake da ni a Tv ɗazun". Tuna abin yasa ta yi sauri kama bakinta ta yi shiru ba ta yi magana ba, zuba mata wayan nan idanun nasa ya yi yana kallon face nata.

"Jehan why are you so beautiful like my uncle? Gaskiya kina caza mini kai sosai, anytime tunanin ki ne kawai yake zuwa mani cikin brain ɗina, seriously i really love you, ni na gaji da abin da kike yi mini, ina son ki gaya mini why baki so na? Why kika tsani gani na? Me na yi miki? Ko akwai irin type na mijin da kike so ne? Please tell me the reason, idan ba haka ba zaki cutar da ni sosai".

Karo na farko da ya fara yi mata magana cikin natsuwa da kuma serious akan abu, babu tsokana ko muryar raha a cikin maganar, in a serious matter ya yi maganar, hakan yasa ta ɗago tana kallon fuskarsa, shi ma ita yake kallo babu ko kyaftawa, alamar amsa kawai yake jira.

"I don't know the reason why, but ba kai kaɗai ba, ni bana son kowa, banyarda da soyayya ba". Matso da fuskarsa ya yi daf da tata har suna iya jiyo numfashin juna, kwata kwata sun mance ma a kofar ɗakin daddy suke wannan diramar ta su. Ƙoƙarin kawar da kanta gefe ta yi, amma sai ya hanata ta hanyar haɗe goshinsa da nata, hancinsu yana gogan na juna. "Zaki yarda mu yi wani game da ke?" Ya yi maganar kamar mai yin raɗa, cikin sanyin murya.

Zubawa laullausan laɓɓansa idanu ta yi tana kallon yanda yake motsasu idan zai yi magana, gasu jawur kamar ya sanya jan jan baki, ga laushi kamar me, sai sheki suke yi tamkar an sanya musu lips balm.

"Kiyi magana mana!". Ba ƙaramin tafiya da imaninta lips nasa suka yi ba, abin ya ɗauki hakankalinta, "Jehan why kika yi shiru? Talk now, zaki yarda mu yi game?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a bata so, raba fuskokin nasu ya yi tare da ɗan ja baya yana faɗin "Okey jeki ki kwanta ki kyale uncle ya yi barci, da safe sai ki zo ku yi magana ko?". A wannan karon ma a nutse da ainahin voice nasa ya yi mata magana.

Juyawa ta yi ba musu ta nufi bedroom ɗin nata, har ta kusa shiga sai kuma ta ɗan juyo dan ta saci kallonsa, har cikin zuciyarta take jin daɗin kallon kyakkywar face nasa. Tana juyowa suka haɗa idanu, dan kuwa ita ya tsare da kallo. Cikin sauri ta juya tare da karisa shiga cikin bedroom ɗin nasu, cool murmushi shi kuma ya saki tare da wucewa nashi bedroom ɗin yana mai jin tsantsar kaunarta a cikin zuciyarsa, ƴar diramarsa, har kewarsa ta yi yau, ya fahimci matsalarta a yanzu, ba wai bata son shi ba ne, no bata san menene ma soyayyar ba, bata taɓa yi ba, bata san ya ake yi ba, bata da wasa da dariya bare wani ya iya gane idan ta shiga feeling na soyayya, ba wanda yake gane ina ta dosa saboda rashin sakewa da mutane da bata yi, hakan yasa yake yawan tsokanarta dan ta saba da wasa da dariya, so yake yi ya canza mata rayuwar da ta taso a kanta, wannan shi ne dalilin tsokanarta da yake yawan yi.

A ɓangaren ƴan rigima kuwa, sai bayan sun yi sallar isha sun ci abinci ne Aseef ya kira Lion Video call dan su ga juna, yau dai tare suka ciyar da juna abinci shi da rigimatin nasa, a baki ya rinƙa bata ita ma tana bashi, yau sam sun ƙi zuwa dining table su ci abincin, su Areef ne kawai suka haɗu da su daddy aka haɗe gabaɗaya a table, shi Aseef ya ce a ɗaki zasu ci dan a saman table ɗin Akila zata bashi kunya, zata ki yarda ta karɓi abinci a baki idan ya bata, zata ce tana jin kunyar daddy alhalin shi kuma daddyn bai san kunya ba, su ba ruwansu ko kiss Aseef zai yi mata a wajen ma, kai idan ta kama ma abin da ya fi kiss ma su yi ba abin da ya dami su daddy, amma ita ta kafe sam kunyar daddy take ji, shi ne ya ɗauko musu abincin zuwa bedroom ɗin nasu, bayan sunci sai suka yi wanka suka yi shirin kwanciya, yau dai shi ya zaɓa mata kayan barcin da yake son ta saka mishi, ba dan ta so ba ta karɓa sai dan ba zata iya cigaba da yin musu da shi a koda yaushe ba.

Wasu shegun riga ne mai ƙaramin hannu zuwa cibiya da ƴar wando zuwa cinya, jikin kayan suna da tsantsi sosai, sai yabawa kyan da ta yi yake ta yi har suka haye gado ya kira Lion don su gaisa, suna tsaka da hira da Lion ɗin ne ya ce mata ta zo su gaisa, ganin kayan jikinta ta yi kafin ya jawo bargo zuwa kirjinta, sannan ya juyo da wayar kanta, good evening ta ce mishi cikin girmamawa, amsa ɗaya ya bata kafin ya ce da Aseef ɗin good night, bai jira amsarsu ba ya katse kiran, murmushi Aseef ɗin ya saki yana faɗin "My rigimati Allah kin ciri tuta da har Lion ya amsa miki gaisuwa, dama da gangan na ce kizo ku gaisa dan naga shin zai amsawa matata ne ko ba zai amsa ba, amma kuma kin saka shi ya ce mini good night bamu gama waya ba, ban fa gaji da ganin shi ba".

Turo bari ta yi tana faɗin "Allah Heartbeat kai ko, yanzu haka dama kake zama ka yi ta zubawa yaya Saif shagwaɓa ko? Ji yanda ka rinƙa yi mishi magana kamar da ni kake magana". Kasa kasa ya ce mata "To ai ni autansu ne, kuma ni pleasure su ne, dole su biye mini yanda nake so". "To ai yanzu yaya Saif zai dai'na shagwaɓaka tun da shi ma ya samu mai shagwaɓa shi". Murmushi ya yi yana faɗin "Ai ni har abada ba zasu dai'na shagwaɓa ni ba, matsayin sister daban, matsayi na daban kin gane ai?". Zata sake yin magana ya jawota jikinsa kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana "Ki bar maganarsu Lion, yanzu maganata zaki yi, me zaki bani yau kuma?" "Me kake so?" Ta yi maganar a shagwaɓe, a kunne ya raɗa mata abin da yake so ɗin, zaro idanu ta yi zata yi magana ya yi maza ya haɗe bakinsu tare da jan bargon gabaɗaya ya rufesu har kansu. ASUBA TA GARI.

A ɓangaren Lion kuwa, barci ya koma saboda barcin ne a idanunsa sosai, sai shakar daddaɗar kamshin perfume nasa take yi ta lafe a saman kirjin nasa har ita ma barci ya ɗauketa, basu suka farka ba sai karfe biyu, ita ce ta fara farkawa, a hankali ta waro idanunta waje, da yake ta sha barci dai idanun suka yi ja, zubawa kyakkywar fuskarsa idanu ta yi tana kallon yanda yake sauke numfashi a hankali hankali cikin natsuwa.

Cikin sanɗa ta lallaɓa zata sauka daga jikin nasa, cap ya rikota domin kuwa tun farkawarta shi ma ya farka, a hankali ya waro idanuwansa a saman face nata, runtse ido ta yi tana sakin cool murmushin da bata san dalilin yin shi ba, haka kawai ta ji murmushin ya zo mata.

Sakinta ya yi tare da yunkurawa zai miƙe, sauka ta yi daga jikin nasa ta diro kasa daga saman gadon ta nufi toilet, wayarsa ya ɗauko dan ya duba time, 2:02pm, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya zuro kafafunsa kasa, duk jikinsa a mace, toilet ɗin shi ma ya nufa dan ya yi wanka tare da ɗauro alwala dan gabatar da sallar azahar.

Kai tsaye ya shige cikin toilet ɗin, wani ihu ta kurma tana daga cikin baf ɗin wanka, sam bata yi zaton zai shigo ba, ko da ya shigo kuma bai bi ta kanta ba, bai ma san tana cikin baf ɗin ba sai da ta kurma ihun ne ya kai kallonsa wajen, ɗan zuba mata idanu ya yi ta takure jiki waje guda ita a dole ta ɓoye jikinta, girgiza kai kawai ya yi tare da wucewa ya ɗauki brush, dan shi mamaki ma yarinyar nan take bashi, ko me zata ɓoye oho mata.

Ta kasa cigaba da yin wankar tata, shi kuma bai sake bi ta kanta ba ya yi brush ya kammala sannan ya ɗauko wani baf na wanka irin tafi da gidan kannan, baf ɗin yana da bala'in kyau sosai tamkar ainahin baf yake, sake baki ta yi tana kallon ikon Allah, tunanin take yi a cikin zuciyarta ba dai wanka zai yi ba shi ma?.

Bata ankara ba tana can tana tunani sai ta ga ya haɗa ruwa yana cire kayan jikinsa, shi ko ajikinsa ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login