Showing 90001 words to 93000 words out of 359620 words
ɗayan ya wuce wajen.
A ɓangaren Rimsha kuwa, kofar ɗakin Imran ta nufa, da sallama ɗauke a bakinta ta tsaya a bakin kofar tana jiran izinin shigowa, daga ta cikin ɗakin jelly ta amsa mata da "To ƴar anace, yaya Imran yana wanka, idan kina son yin magana da shi, sai ki jira shi a waje ai". Ta kai karshen maganar tana jan tsaki.
Har cikin zuciyarta maganar ta yi mata zafi, kuma hakan ma kaɗan ne daga maganganun da jelly ɗin ke gaya mata, yanzu ma da tasan baya cikin ɗakin ba zata je wajen ba, dan tana jin zafin maganganun jelly sosai, kuma kunsan halin jelly, number 1 ce a rashin kunya.
Rai a ɓace ta juya ta koma cikin ɗakinta, tason ta yi magana da Imran akan zuwa gyaran gashin nan nata, dan kan nata na damunta, ta kuduri niyar ba zata sake zuwa wajen Imran neman wani abin ba, dan tana zargin da gangan ɗazun jelly ta ce mishi lallai su je gidan Abbi, dan kawai ta ji yace zai kai Rimshar gyaran gashi, shi ne ta bijiro da nata dan kada a kai Rimshar, ta yanke wa kanta hukunci zata rinƙa fita da kanta ta je tunda yanzu ta yi free, zata tambayi Akila sunan anguwar da ake gyaran gashin dan ta rinƙa kai kanta da kanta kawai zai fi mata.
Tana shiga bedroom nata zuciya cike fal da tunani, toilet ta wuce dan ta yi wanka, bayan ta kammala ta shirya cikin ɗaya daga cikin ɗinkunan da Imran ya yi musu, dogowar riga ce ɗinki ya zauna mata sosai a jikinta, fesa perfume nata ta yi tare da ɗaukar wayarta ta nufi garden na gidan.
Tana zama cikinta ya fara kukan yunwa, shiru tayi tana sauraron yadda cikin nata ke ƙu,lu,lu,lu, wato kuman yunwar kenan, tunani take yi a irin rayuwar da zata shiga yanzu kuma, ji take yi tamkar ta roƙi Areef yasa a mayar da ita kusa da daddynta, ko kuma ta koma gidan Akil, wani ɓangare na zuciyarta ne ya bata amsa da ita ma Umaisha kishi take yi da ke ai, tamkar zata yi kuka tuna hakan da ta yi, a kule ta ce wai me yake faruwa da ita ne? Ko wace mace sai ta ce tana kishi da ita, to ita tace tana son mazansu ne? Abin gwanin ban tausayi, can wani ɓangare na zuciyarta ya tuna mata to ko dai ta koma gidan Abbi ne?, Nan ma ɗayar ɓangare na zuciyar tane ya bata amsa da anya zata iya yin nisa da Saif kuwa? Anya zata iya jure wuni guda ba tare da ta ganshi ba kuwa? Anya hakan zai yiwu kuwa? Bama Saif ba, shima Areef anya zata iya rabuwa da shi kuwa?, Tuna hakan yasa ta fara ruwan hawaye, ga yunwa, ba wadda zata iya gayawa tana ji, yaya Imran ne kawai, shi kuma yanzu jelly ta yi musu tsakani.
Tana cikin wannan hali sai ga jelly da Imran sun nufo garden ɗin, sunci kwalliya, Imran na sanye da kananan kaya, wato wandon jeans baka da t-shirt blue, ita kuma jelly riga da skit ne a jikin nata, skit ɗin ruwan kasa da ratsin fari, riga fari, kayan sun ɗan kamata, amma ba sosai ba, ba karya sun yi kyau sosai, yau Imran ya sanyata dole sai ta saka ɗankwali a kanta, hakan yasa bata ji daɗi ba, sai turo baki take yi, ita a dole ta ji haushi.
Ganin su yasa ta yi saurin goge hawayen fuskarta tare da ƙaƙalo murmushi dole dan kada Imran ya gane komai, tasan yana yi mata iya iyawarsa, baya bari ta shiga kunci, yanzu ma duk abin da yake faruwa tsakaninta da jelly bai da masaniya a kai, idan ya sani zai ɗauki mataki, ba zai bari hakan ta cigaba da faruwa ba, idan baku manta ba, kunsan jelly da iya makirci da kirsa, to bata yi wa Rimsha abu a in da ta san Imran ɗin zai gani ko kuma ya ji, sai ta faki idonsa take tsula tsiyarta, ɗazun ma da yake toilet ta yi wa Rimsha wannan maganar, ta san cewa ruwa na zuba, karar ruwan ba zai bari ya ji maganar ba, shiyasa ta yi.
Ganinta a garden ɗin yasa shi sakin kayatatcen murmushi yana faɗin "Rimsha yaushe kuka dawo?" "Yaya Imran yanzu ba jimawa muka dawo". Kusa da ita ya zo ya zauna "Ai mun dawo daga gidan Abbi na tambayi Areef ina kike, sai ya ce mini kun fita ke da Aseef, fatan dai kun dawo lafiya?" Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Lafiya lou Alhadulillah".
"Kina jin yunwa ko?" Ɗan satar kallon Jellyn ta yi kafin ta gyaɗa mishi kai alamar e "Am so so sorryyyyyyyyyy, gaskiya rayuwar gidan nan akwai wahala a gareki, ke baki iya cin abincinsu ba, su kuma basu son warin naki, ni kinga na iya cin abincinsu dan a kasarsu nayi karatu, amma ba komai ai kwanaki kaɗan ya rage mana a nan ɗin, zaki jure ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e.
"Good to tashi ki ɗauko mayafinki mu je gidan Akil a tare, tun da dai ke kince baki son abincin restaurant, ai aiki ya gammu da yawon zuwa gidan Akil ko gidan Abbi ɗaukar abinci". Ɗan motsa lallausan lips nata ta yi tamkar wadda take son yin murmushin, nan take dimple nata dukka biyu suka lotsa, wani irin fitinannen kyau na ɗaukar hankali ta kara, tana ƙoƙarin mikewa ta nufi cikin gida dan ɗauko mayafin nata, sai ga Aseef da Areef sun jero tamkar wasu taurari, sai walwali suke yi, Lion ya gaji da surutunsu ya haɗasu da Allah su fita mishi a ɗaki, sanin girman Allah yasa suka hakura suka kyale shi ya sha iska, ba dan haka ba, yau ba zasu rabu da shi ba.
Har wani daddaɗar nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe ganinsu, ta rasa me yasa take jin tsantsar farinciki idan ta gansu, ta rasa me yasa take jin duk wani damuwarta ya gudu da zarar ta yi tozali da kyawawan fuskokinsu masu ɗauke da annuri ta murmushi. A ɓangaren shima Areef, ganin ta a wajen yasa ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya da ta sanya Aseef juyowa yana kallon shi.
Gefenta ya je ya zauna shi kuma Aseef ya zauna a wani kujera na daban, ita kuma jelly tana ta faman kumbura kuma tu, ita a dole ta ji haushin kula Rimsha da Imran ya yi.
"Our Queen me yake damunki? Waye ya taɓa mana ke?". Cewar Areef, da kallo ɗaya ya yi mata abinku da jami'i, tuni ya fahimci akwai abin da yake damunta.
Ɗan zaro idanu Imran ya yi yana kallonta, har lokacin kuma shi dai bai ga alamar wata damuwa a face nata ba, shi ma Aseef da kallo ɗaya ya yi mata ya ga damuwa kwance a cikin idanunta, da yake idan baku manta ba, Triplets akwai baiwa, akwai kwakwalwa, sun gaji brain wajen Dr William jacop.
"Yaya Areef babu abin da yake damuna fa". Ta yi maganar tana kara ƙaƙalo murmushi a kan fuskar tata, dan ta tabbatar musu da babu komai ɗin.
Kallon Areef Aseef ya yi while shima Areef ɗin shi yake kallo, daga bisani suka juya suka kalli Imran wadda shima ya tsaresu da ido sosai, yana kallonsu, yana son sanin me yake damun kanwar tasa.
"Yaya Imran mu tafi ɗaki barci nake ji" muryar Jelly ce ta katse musu shirun da suka yi suna tunani, kallonta gabaɗayansu suka except Areef, shi dawo da kallonsa a kan Rimsha ya yi, a nan ne kuma ya fahimci jelly ce matsalar gimbiyar tasu, domin kuwa wannan magana da jelly ta yi, ta sake jefa fuskar Rimsha cikin damuwa da tunani, fahimtar hakan yasa ya ɗan yi shiru yana tunani mafita, tabbatas ba zai taɓa yarda da duk wani abin da zai sanya Rimsha cikin ɓacin rai ba, zai yarda da komai a gidan amma ban da hakan.
"Rimsha me zaki ci in sayo Miki". Cewar Imran, ya yi maganar ba tare da ya tanka maganar jelly da ta faɗa na su tafi ɗaki ba, sai dai bai gama rufe baki ba jelly ta kuma katse shi da su tashi su tafi ɗaki, ta yi hakan ne kuma dan kada Imran ya sahowa Rimsha abinci ko ya ɗauketa su fito, kishi kumallon mata, ko wace mace tana da shi, sai dai na wata ya fi na wata, ayi wa Jelly uzuri, ta ga hankalin yaya Imran ɗin ta na ƙoƙarin rabuwa biyu ne, ta ga yafi kula da Rimsha sama da ita da take matarsa, kuma take gani ita ta kasance kanwarsa, Rimsha kuma babu abin da ya haɗa su tun da bata ma san waye bappan nasu Hosain ba.
"Jelly ki bari bari na je ya sayowa Rimsha abinci ko na ɗauko mata a gidan Akil, ki je ɗakin ki kwanta ina zuwa". Babu kunya bare tsoron Allah ta sa mishi kuka wai cikinta na ciwo, shi dai Areef binsu kawai yake da ido yana karantarsu, shi kuma Aseef ganin tana kuka yasa ya tambayi Imran ɗin menene matsalar, Shi Areef duk da baya jin Hausa, zama yau da gobe da su, yasa idan suka yi magana yana fahimtar in da maganar ta dosa, sannan kuma yana karantar yanayinsu, ta hakan yake gane a kan me suke maganar.
Kanta Imran ya yi yana tambayarta ko lafiya, kuka take yi tsakaninta da Allah, hawaye wani na bin wani ta dafe cikin nata.
A hankali Rimsha ta faki idanunsu ta miƙe tana son barin wajen dan kada zuciya ya ɗebeta ta kifawa jelly mari, dan kayan haushin jelly ya isheta, sanin halinta da zuciya yasa bata son haɗuwa da Jelly'n, dan bata son suyi faɗa a matsayinsu na ƴan uwan juna.
Sosai Areef ya ji babu daɗin hakan, dan yasan Rimsha bata da wanda yafi Imran, shine farincikinta a yanzu, amma wata tazo tana kutse a tsakaninsu. Tana miƙewa ya riƙo hannunta, da sauri ta juyo duk da ta san shi ɗin ne, girgiza mata kai ya yi alamar a'a ta dawo ta zauna, ba musu ta koma ta zauna, shi kuma Imran ya ɗauki jelly a kan zai kaita ɗaki ya rarrasheta ya dawo.
Suna barin wajen Rimsha ta fara hawaye, tana mamakin jelly yarinya yar karama da ita ko a ina ta koyi wannan banza hali na kirsa da makirci oho, ɗan riƙota a gefen kirjinsa ya yi, yana goge mata hawaye tare da bata baki, da mamaki cike fal ransa Aseef ya miƙe ya dawo kusa da su dan ya ji wai shin menene matsalar.
Ɗan langwaɓar da kanta a gefen kirjin nasa ta yi tana mai jin bakin ciki a cikin zuciyarta, zama a gefenta a in da Imran ya tashi Aseef ya yi, fuskarsa ɗauke da damuwa ya fara tambayar me yake faruwa, ba ɓoye ɓoye Areef ya sanar da shi duk abin da ya fahimta, cikin sauri ta ɗago kanta daga gefen kirjin nasa, tana kallon face nasa, mamaki take yi waye ya gaya mishi abin da yake damunta, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Kina mamaki ne? Ina kaunarki ai, dole na iya gane me yake damunki, kuma duk da bana jin yarenku, ina fahimtar akan me kuke tattaunawa, yanzu dai jeki ɗauko mayafinki muje wajen cin abincin, Aseef zai ja mota, Lion ba zai hanani fita ba, dama abin da yasa yake hana fita, dan ni kaɗai ne, kada na fita wani abin ya same ni, ko kuma na fama ciwona, yanzu Aseef yana nan, babu abin da zai faru In Sha Allah, kuma daga yau kada ki sake tambayar Prof wani abu, duk abin da kikeso, Aseef yana nan idan ni ba na kusa, kin ji ko?".
Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e ta ji. "Yanzu nauyinki a kan mu yake, dole mu kula dake tamkar yadda zamu kula da kanmu, Aseef ɗauko makullin mota ka sanar da Lion zamu je restaurant, ke kuma jeki ɗauko mayafi". Kusan a tare suka miƙe Ita da Aseef ɗin, hannunta ya riƙo suka nufi cikin gida yana tambayarta shekarunta, 14 years 3 months ta bashi amsa, sai mamaki yake yi, ƴar karama da ita, lallai akwai kura.
A palon sama suka rabu, ita ta shiga ɗakinta, shi kuma ya shiga ɗakin Lion. Jim kaɗan suka fito kusan tare, sake riƙe hannunta ya yi a cikin nasa yana faɗin "Wannan abin da kuke rufe jikinku da shi, ba karamin kyau yake yi muku ba". Sai murmushi take yi ba tare da ta yi magana ba suka nufi waje.
A yadda suka bar Areef haka suka dawo suka same shi, yana ganinsu ya miƙe a kan su tafi, fitowa balcony ɗakinsa Lion ya yi dan yaga tafiyarsu, yana ji da ƴan uwan nan nasa over, har ga Allah bai so Areef ya fara fita yanzu ba, saboda jikin nasa da saura, amma shi kuma yana bala'in son yaga ya fita, ya son ganin cikin Naijan nan ya take, Hakan yasa Lion ɗin ya hakura kawai ya kyale shi su fita.
Kiran Imran a waya Areef ya yi, ya tambaye shi a wani location restaurant ɗin da suke sayan abincin yake, ba musu ya gaya musu, bai kuma tambayesu me zasu je yi a can ba, dan yasan ba makawa Rimsha zasu je sayawa abinci. Kunna goggle map Aseef ya yi a wayarsa tun kafin su bar gidan, Rimsha ta so zama a gidan baya na motar, amma Areef ya ce lallai ta dawo gidan gaba su zauna a tare, shi kuma Aseef ya tukasu.
Bata yi musu da shi ba, ta dawo kusa da shi ta zauna, duk abin da suke yi a kan idanun Lion suke yi, a kan idanunsa suka bar gidan, sai tsokanar Rimsha Areef yake yi, suna ta murmushi.
Kai tsaye wajen wani katafaren restaurant suka shiga, suna parking suka fito kusan a tare, nan take kallo ya dawo kansu, kun san mutanenmu idan suka ga Turawa, sai kallonsu jama'a suke yi, su kuwa kwata kwata basu son wannan kallo da jama'a suke yi musu, dama kuma kunsan kallo bashi da daɗi ko kaɗan, idan mutun yana kallonka gabaɗaya sai ka tsargu, sai ka fara tunanin ko dai wani abin da bai kamata bane a jikinka yasa suke kallonka.
Saman tsadaddun kujerun dake wajen suka zauna, nan take masu karɓar order suka nufo wajen nasu.
"Rimsha ki basu order abin da kike buƙata". Cewar Areef, shi dai Aseef ya yi kasa da kai yana latsa wayarsa, da alama chatting yake yi da Heartbeat nasa.
Daidai lokacin aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, umarni Areef ya yi musu a kan su yi mata takeaway ne kawai su wuce da shi gida, mangariba ya yi, sai dai abin dariya kuma abin haushin shi ne, babu mai ko biyar a jininsu, kuma ba ta yadda zasu yi su yi wa masu restaurant ɗin transfer, ko da aka kawo musu takeaway ɗin da bill ɗinsu, kallon Aseef Areef ya yi, shi ma a lokacin ya ɗago kansa dan ya kalli ɗan uwan nasa, da wani kuɗi zasu biya to? Suka tambayi kansu da kansu a cikin zuƙatansu, ita ma Rimsha sai kallonsu take yi tana kankame da laidar takeaway ɗin nata abinta.
Su kuwa masu karɓar kuɗi suna tsaye suna jira, dan kuwa ba zasu yafe ba, ice cream da suka sanyawa Rimsha ma kawai almost 10k bare azo kan saura abubuwa ga abinci.
Dariya ne ya subcewa Rimsha lokacin da ta gane me matsalar, zuba mata idanu Areef ya yi yana kallon yadda take dariyar, ba ƙaramin burge shi ta yi ba, shi ma dai Aseef dariya abin ya bashi, wai su a dole sun zo sayan abinci, sun manta ba'a Washington DC suke ba. Babbar magana yanzu ya zasu yi? Su mayar da abincin ne ko yaya za'ayi? Ga shi ita kuma Rimsha ta kankame ledar ta abinta, jira kawai take yi su biya su tafi, har ta kotsa ta fara shan ice cream dake cikin, ga shi har da pizza ta ce a sanya mata...........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E23-24
Suna a wannan hali sai ga Mark ya shigo cikin wajen, fusataccen fuskar nan tasa tamkar face ɗin shanu, yana sanye da wandon jeans black color da t-shirt maroon, faffaɗar kirjin nan nasa a buɗe irin na ogan nasa, tamkar wani zaki, ya sanya bakar glass a idanunsa, ba wasa a tattare da shi ka ɗigo, ganin shi ma kawai ya isa ya razanar da duk wata halitta mai rai.
Kai tsaye in da suke ya nufo, cikin girmamawa ya gaida su tare da miƙawa masu karɓar kuɗin rafar kuɗi ƴan dubu dubu, wadda a kallah zasu kai 100k, ko basu tambaya ba sun san Lion ya aiko shi, dan idan ba Lion ba, ba wanda ya isa ya sanya Mark fita daga gidan, ya bar bakin aikinsa, dama tun da suka fita Lion ya kira Mark ya bashi kuɗi a kan ya bi bayansu da shi, dan yasan basu da ko biyar a jikinsu, kuma yasan ba ta yadda za'ayi su yi transfer, su sun mance da hakan, amma shi tsabar kauna da kuma kula da su da yake yi bai manta ba, yana ankare dasu, shiyasa ya yi musu hakan, dan kada wata matsala ta biyo baya, Areef kawai yake jiyewa, ciwon nan nasa, tun da suka fita yake jin wani iri a ransa, yadda Areef ɗin ke jijjiga jikin nan nasa, ciwon nasa na jijjika, to shi ma haka Lion ɗin yake jin wannan jijjiga a jikinsa, tamkar ciwon a jikin nasa yake ba Areef ba, ya kyalesu su fita ne dan su yi farinciki, tun da sun nuna hakan suke so, bai taɓa hanasu abin da suke so ba, sai idan ya tabbatar da in suka yi abin zasu cutu matuƙa, shi ne zai taka musu birki, ba dan yaso ba, sai dan kada su cutu.
Tun da Mark ya miƙa kuɗin, Aseef ya riƙo hannunta suka nufi waje, shima Areef miƙewa ya yi ba tare da ya kalli in da Mark ɗin yake ba, ya bi bayansu.
Motarsu suka shiga, da gudu Aseef ya ja motar dan lokacin sallah ya yi, da mugun gudu shi ma Mark ya fito ya rufa musu baya, da motar da yazo da ita. Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa