Showing 21001 words to 24000 words out of 359620 words
kasa kasa cikin sanyin murya, kuma ya yi maganar ba tare da ya ɗago ya kalleta ba.
Cikin sauri ta miƙe ta fice daga wajen, shi dai Areef bai ce komai ba, shi ma Imran ba bakin magana, da ma Allah yasa bai haɗa mata da mari ba ai da sauki.
Tana fita bedroom nata ta koma, suka cigaba da hira da Akila, a nan AKILA take gaya mata Hjy Batula zata aiko mata da wasu kayan karin girman breast wadda ta haɗawa jelly, suna da kyau sosai, Hjy Batula ɗin ta ce zata bawa yaya Imran ko yaya Akil su kawo mata, idan sun kawo mata, zata ɗebawa yaya Imran ya kawo mata ita ma ta yi amfani da su, sosai Rimsha ta ji kunya, ta kuma amsa da to, sannan ta daɗa da cewa ta haɗa mata da su kanunfari, citta, kimba, da kuma su na'a'na'a, dan tana son ta rinƙa haɗa tea nata irin wadda mummynta take yi wa daddynsu mai shegen daɗin nan, bata son green tea ɗin su Lion, bata saba sha ba, sai ta ji babu daɗi, ga shi ita ma'abociya shan tea ɗin ne, to Akila ta amsa mata, tare da gaya mata zata bawa driversu ya sawo mata kayan a kasuwa, idan ya kawo mata, sai ta bawa yaya Akil ko yaya Imran su kawo mata, sai murna Rimsha take yi, sun sha hira kamar ba gobe, sosai Akila ta kara zugata akan ta rinƙa shan wanka da kwalliya, kada ta yarda Lion ya bar Nigeria ba tare da ta sato masu zuciyarsa ba, sai murmushi take yi jin Akila ta sosa mata in da yake yi mata kai kayi, ita kuma Akilar ta zage sai kara gaya mata lagon maza take yi, abin da bata sani ba shi ne, LION duk duniya abu ɗaya ya bari a kasani a matsayin rauninsa, wannan abu kuma ba komai bane fashe kaunar TRIPLETS nasa, kaunar ƴan uwansa kawai ya bari jama'a suka sani, bayan haka ko uban da ya haife shi, bai san me raunin ɗan nasa ba, shi Lion bai ma yarda yana da rauni ba a duniya, domin a nashi ganin komai ma zai iya yi, kuma zai iya jure komai ciki kuma har da rashin TRIPLETS ɗin nasa da jama'a suke ganin kamar shi ne rauninsa. TO FA ZAN SO GANIN MENENE RAUNIN LION GASKIYA.
Idan muka koma ɓangaren gidan Abbo kuwa.
Misalin karfe 5 na asuba Nawid ya farka, abin mamaki sai ya ga bata a kan gadon, a hankali ya miƙe tare da zuro kafafunsa kasan gadon, ya kunna wutar ɗakin, nan take haske ya gauraye ɗakin.
Can saman dadduma ya hangota, tana zaune tana karatun Al Qur'ani mai girma, baiwar Allah Akil ya riga da ya saba masu, ɗan zamanta da Akil ta koyi abubuwa da dama dan gane da addini, ciki har da su askar, yin karatun Al Qur'ani mai girma, tashi barci kafin lokacin sallar asuba domin ta gabatar da nafila na raƙatainil fajir, sannan ta gabatar da karatun Al Qur'ani, yin sallar dare, da dai sauransu, ba ƙaramin natsuwa da cigaba ta samu ba.
Miƙewa ya yi ya nufi toilet, wanka ya farayi, ya ɗauro alkawala, kusa da ita ya zo ya tsaya, ganin shi yasa ta miƙe hannunta riƙe da Al Qur'ani ta nufi saman sofarsa ta zauna.
Tsayuwa ya yi ya gabatar da sallar raƙatainil fajir, sannan ya nufi masallaci, ita kuma ta dawo saman dadduma dan gabatar da sallar Asuba.
After some minutes, bayan ta idar da sallah ta yi karatu har rana ya fito, ta yi askars ɗinta, ta miƙe ta nufi waje.
Tana ƙokarin fita shi kuma yana ƙoƙarin shigowa, karo suka ɗan yi, da sauri ta yi baya tana sunkuyar da kanta kasa.
Zuba mata idanu ya yi yana kallonta sosai.
Kasa ta yi da kanta, cikin sanyin murya da girmamawa ta fara magana "Ina kwana yaya Nawid?". Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya amsa mata tare da tambayarta ya kwanan bakunta, cike da kunya ta amsa mashi da lafiya, gabaɗaya kunyarsa take ji, domin ta tashi barci ta tarar ya rabata da kayan jikinta.
"Ina zaki je yanzu da sassafen nan?" Ya yi maganar yana kara tsareta da ido. "Wajen Ummi zanje". "A nan ɗin na takura maki ne?" Ya yi maganar cikin zolaya.
Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin a'a. Wucewa ya yi, ya shige cikin ɗakin. "Zo ki yi kwanciyarki sai zuwa anjima sai kije, yanzu ko da kinje ma, tana barci, bata kai ga tashi ba". Kamar zata yi kuka, haka ta juyo ba dan ta so ba. Saman sofa ta zauna tana wani rakuɓe rakuɓe.
Da mamaki yake kallonta, ya rasa meyasa take gudun shi haka, tabbas ƙwaƙwalwarsa tana gaya mashi akwai dalili, domin kuwa shekaruntan nan ta wuce a ce sai an zauna ana yi mata wani karin bayani game da aure, 21 years take da shi a duniya yanzu.
Tsareta ya yi da ido, yana son karantarta, domin ya gane menene matsalarta. "Tashi ki zonan". Shi ne abin da ya faɗa.
Ba musu ta tashi ta koma kusa da shi ta zauna.
"Meyasa kike guduna har haka ne A'AFIA?". Kasa ta yi da kanta. "Babu komai yaya Nawid" ta yi maganar cikin sanyin murya.
Hannunta ya riƙo a cikin nasa. "Ni yayanki ne, kada ki mance da Ummi da Aunty Khadijah ƴan uwa ne, dan Allah ki gaya mani menene yake damunki Kin ji? Kada ki damu, kuma kada ki ɓoye mani komai".
Ɗan satar kallon shi ta yi ta kasan ido. "Da gaske yaya Nawid babu komai". Gefensa ya nuna mata ba tare da ta sake magana ba, ba musu ta karisa hayewa saman gadon, ta kwanta a gefen nasa, shi ma kwanciya ya yi, ya sanya kansa a saman pillow da ta kwantar da nata kan.
"Ba zan ɓoye maki ba, a lokacin da aka bani aurenki, kwata kwata babu sonki ko kaɗan a raina, amma daga daren jiya zuwa yau, Allah ya jarrabeni da sonki, ina fatan kema kin na sona?". Ya yi maganar can kasa kasa maƙoshinsa.
Ɗan juyowa ta yi kaɗan "Ina son ka nima yaya Nawid". "Da gaske?" Ya faɗa cikin zolaya, gyaɗa mashi kai ta yi alamar e.
"Kada fa dan kinga idona ne yasa kika faɗi hakan, fatan Allah yasa babu wani a zuciyarki". Nan ma cikin zolaya ya yi maganar.
"Yaya Nawid ba wai dan ganin idonka bane, wlh da gaske ne ina sonka, kuma ni wlh ban taɓa yin soyayya ba, bani da saurayi ko a school, ni koma a ina bana kula kowa, zaka iya tambaya ma ka ji".
Hannu ya kai ya ɗan ja hancinta yana murmushi "To waye zan tambaya ɗin?" "Nima ban sani ba, kawai dai ka tambayi koma waye".
Kara juyowa ya yi da kyau ta yadda zai sami damar ganin fuskarta sosai. "Ni ba sai na tambayi kowa ba, domin kuwa, na taɓa kamaki kina soyayya, a kan idona kika sace wa wani sarauyari bawan Allah zuciyarsa da kallo ɗaya".
Zaro ido waje ta yi "Yaya Nawid a ina aka yi hakan? Kuma ni Aafia ɗin ce na yi hakan?" Ta kai karshen maganar tana yin narai narai da idanu kamar zata yi kuka. Ɗaure fuska sosai ya yi "E mana, ke ɗin dai, ai a gabana aka yi komai".
Shiru ta ɗan yi tare da nutsa ƙwaƙwalwarta a cikin tunani, ita dai tasan wlh bata taɓa tsayawa da wani saurayi ba, bata taɓa soyayya ba, Rufee ta yi ƙoƙarin koya mata soyayya, ta yi ƙoƙarin haɗata da maza, amma idan baku mance ba, ta ki yarda, bata kula kowa, karatu kawai take yi, bata shiga harkar kowa.
"Yaya Nawid ni wlh ban tuna yaushe aka yi hakan ba, ni ba zan yi musu da maganarka a kan cewa ba haka bane, amma dai abin da zance kila daga ɗan nesa ka gani, to kila mai kama da ni ce sai kaga kamar ni ce...."
Katse ta ya yi da cewa "Ba wata mai kama dake, ke ɗin ce ba wata ba". Shiru ta yi na ɗan lokaci. "Tom shikenan Yaya Nawid na yarda ni ɗin ce, amma ka yi hakuri".
Shafa face nata ya yi. "My beautiful wife, jiya ba kin sace zuciyar mijinki da daddare a nan ba, to ai shi ne saurayin da kika sace wa zuciyar, kuma ai kinga a gabana aka yi komai ko?". Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.
Tsareta da ido ya yi, yana kallon yadda take murmushin gwanin ban sha'awa. Ganin yana kallonta sosai ne yasa ta ɗan sauƙe idanunta kasa. "Kunyata kike ji?" Dawo da kallonta kan face nasa ta yi, ɗaga mata gera ɗaya ya yi yana kashe mata ido ɗaya.
Kara faɗaɗa murmushin kan face nata ta yi, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ganin ta yi murmushi, kuma ta ɗan saki jikinta.
"Gaskiya fa ina kara yi wa Allah godiya, sannan ina kara yi wa Abbina godiya da ya mallaka mani ke, ya zama dole gobe muje mu gaida shi, na ji daɗin bani ke da ya yi". Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi.
Hannun nata ya kama tare da zame shi daga kan face ɗin nata. "Ki daina hana ni ganin fuskar matata, ko fuskarki ce?" Ya tambaya yana ɗaga mata gera ɗaya.
Kin yarda ta yi, ta dage sai ta rufe fuskarta, shi kuma ya ce a'a bai yarda ba, haka suka kama kokawar wasa, daga karshe dai ya yi nasarar kame hannayen nata dukka biyu, ya riƙe cikin nashi, tare kuma da mannata da jikinsa yana murmushi, ita ma sai murmushi take yi.
"To dai na fiki karfi sai ki rinƙa bina a hankali, idan ba haka ba, zaki sha wahala". Cikin zolaya tare da so da kauna ya yi maganar.
"Ai daman Yaya Nawid ka fini karfi mana, bama haɗi ai". Sake hannayen nata ya yi tare da jawota sosai ya matseta a jikinsa, matso da bakinsa ya yi saitin kunnenta, ya fara zuba mata kalaman masu shegen daɗi.
Tuni ya mantar da ita wani bakin ciki, cikin kankanin lokaci ya sanya ta saki jiki da shi, tun tana mai da mashi da martani ɗai'ɗai, har ta fara zuba mashi nata salon kalaman kamar, yadda yake zuba mata shi ma, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, wani irin yanayi mai cike da annashuwa ya tsinci kansa a ciki, har cikin ransa yake jin breast ɗin nan nata da suke sokinsa a kirjinsa, dannewa kawai yake yi, ita kuma ta saki jikinta da shi.
Haka suka kasance har karfe 7 na safe, sannan ya ce ta tashi su je wajen Ummi, daga nan sai suje kitchen ya tayata yi masu girki. "Yaya Nawid ka iya girki ne?" Ta tambaya da mamaki akan face nata.
"Prof ya iya girki ne ko bai iya ba?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kamar dai bai iya ba". Kashe mata ido ɗaya ya yi. "Duk wan da ya ce maki Prof bai iya girki ba, to ya gaya maki ne kawai dan ya ji daɗin bakinsa, amma Prof ba abin da bai iya girkawa ba, sai dai kawai baya son yi ne, amma ba dai ya yi aure ba? Zai yi ne ma ba wanda ya sani, nima da ai bana shiga kitchen, ko hanyarta ma ban sani ba, ban san me da me ma a cikin kitchen ɗin ba, amma yau ba gashi saboda ke zai shiga ba". Ya kai karshen maganar tare da sakinta ya miƙe zaune.
Miƙewa ita ma ta yi, ta riga shi sauƙowa kasa, hannunta ya kamata suka nufi wajen, sai hira yake zuba mata, ita kuma sai murmushi take abinta, dama akwai tsohon soyayyarsa a cikin zuciyarta, yau soyayyar ta dawo mata sabuwa.
A palo suka isko Ummi, har ta gama haɗa breakfast, ta jere saman table tana jiransu su tashi barci. Ganinta yasa A'AFIA ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata, cikin sauri ta karisa wajenta, miƙewa Ummin ta yi, ta tarota tare da runhumeta tana sakar mata wani ƙayatatciyar murmushi, sai murmushi shi ma yake yi, bakinsa yaki rufuwa.
A tare suka zauna a saman sofar da ta tashi ta koma ta zauna, har lokacin bata saki surukar tata ba, shi ma wucewa ya yi ya zauna, sai murmushi suke yi, suka gaisa, har lokacin kuma, duk cikinsu ba wanda ya iya tunawa da Abbo, ya rufe masu baki, tamkar an goge masu shi a kwakwarsu.
A tare suka hau saman table dan yin breakfast. Bayan sun kammala ne A'AFIA ta miƙe ta tattare kwaninkan ta gyara komai, sannan ta nufi bedroom ɗin Nawid wadda ya kasance nasu a yanzu, ita da shi kenan, yanzu ta iya wasu aikace aikacen gida kaɗan, ciki har da girki, kuma zamanta da Umaisha da Akila ta ɗan koya.
Ita kuma Ummi suka cigaba da hira da shi.
Tana shiga bedroom ɗin ta fara tattare masu ɗakin dan ta gyara, sai da tattare ko'ina, sannan ta fara ƙoƙarin canza masu zanin gado.
Tana faman cire bed sheet ɗin, bata ji shigowarsa ba, sai kawai taga ya sanya hannu yana tayata, da mamaki take kallonsa, kamar AKil, domin shi ma Akil, cire kayansa yake yi, ya sanya na shan iska, ya gyara masu ɗaki, ya kuma wanke toilet, sannan ya raka Umaisha kitchen, tana aiki yana shafe mata tula tula, da yake yanzu Umaisha ɗin take yin girki, sun dai'na sayen abinci, Rimsha ta koya mata wasu, sannan shi ma ya saya mata littatafan girki kala kala, dan kawai ta rinƙa yi masu girki, to a nan Aafia ma ta ɗan koyi aiki.
"Meyasa kike kallona haka?" Ya tambaya daidai lokacin da ya karisa cire bed sheet ɗin, ya ɗauka ya nufi wajen zuba kayan datti.
"Babu komai" . Jinjina mata kai ya yi. "To jeki ki yi wanka, bari na shinfiɗa mana wani bed ɗin, idan kin fito sai na shiga na yi Nima, ko dai nazo muje mu yi a tare ne?" . Ya yi magana ta karshen cikin zolaya.
Da sauri ta nufi toilet ɗin tana girgiza mashi kai alamar a'a, dariya ya yi. "Matsoraciya kawai". Ya faɗa yana ciro masu wani sabon bed sheet daga cikin drawer kayansa.
Ko sannu ba ta sake ce mashi ba, da haka ta wuce toilet abinta, binta ya yi da kallo har sai da ta shige, sannan ya zo ya fara aikin gyara gadon, a hankali yake jin kaunarta na karuwa mashi a cikin zuciyarsa.
After some minutes ta fito wanka, sai ɗari ɗarin fitowa take yi kada ta same shi a ɗakin, domin kuwa towel ta ɗauro, bata iya ta yi wanka ta sake mayar da kayan dattin da ta cire ba. Ta yi Sa'a kuwa, baya ɗakin.
Ganin baya nan yasa ta ji wani irin daɗi ya kulluɓeta, gaban mirror ta wuce, sauri sauri ta fara shafa mayukansa da ta gani a wajen.
Tana tsaka da shafa mai ta ji saukar hannunsa a kugunta, har ga Allah bata ji shigowarsa, kofar nasa bata kara, idan an taɓata, wani irin ɗaukewa na wucin gadi numfashinta ya yi, cak ta tsaya da shafa mai ɗin da take yi.
Kwanto da kansa ya yi a saman kafadarta, tare da sanya hannunsa ɗaya, ya karɓi Lotion na hannunta da take shafawa, zubawa a hannunsa ya yi, a nutse ya murza man a hannayensa, har lokacin kansa na kwance a saman kafaɗarta, a hannunta ya fara shafa mata man, kafin ya ɗan raba jikinsu, ya fara shafa mata a suk gaɓɓan da ake shafa mai, mutuwar tsaye ta yi, ta kasa ko motsawa.
Ya zo daidai wuyarta, yana ƙoƙarin kwance towel na jikinta dan ya shafa mata man, cikin sauri ta kankame towel ɗin, ɗago ido ya yi, ya kalli face nata, cikin sauri ta kawar da kallonta, sake mata towel ɗin ya yi, ya shafa mata man a face nata yana murmushi.
"Am so sorry gimbiyata, na yi aikin da baki saka ni ba ko? To ki yi hakuri na taya ki ne kawai, tun da an hanani shafawa kirjin mai Shikenan, na bar maki, shafa masu ga kayan sawarki nan na karɓo maki daga wajen Ummi". Yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi toilet dan shi ma ya yi wanka.
Bin shi da kallo ta yi, har sai da ya zo zai shiga toilet ɗin, sannan ya ɗan juyo, cikin sauri ta kawar da kallonta, murmushi ya saki kawai, sannan ya shige abinsa, yana juyawa ta dawo da kallonta kansa, har sai da ya shige ta daina ganinsa, sannan ta cigaba da abin da take yi, sai tunanin yadda ya shafa mata Lotion ɗin take yi, har cikin ranta ta ji daɗin hakan, musamman yadda taga yana zuba irin wannan murmushi haka, abin ya tsaya mata a ranta.
Wucewa ta yi ta ɗauki kayan da ya ajiye mata a saman gado, wani irin kunya ta ji lokacin da ta kalla har da breziya da pant ya kawo mata.
Ɗauka ta yi ta fara sakawa da sauri sauri, doguwar rigar Abaya ce, pink color tare da mayafinta. Tana gama shiryawa Ummi ta buga masu kofar ɗakin, cikin sauri ta karisa bakin kofar ta buɗe, miƙa mata wayarta Ummi ta yi. "Ga shi nan tun ɗazun ake ta kiran ki". Cikin girmamawa ta karɓa tare da yin godiya, juyawa Ummi ta yi ta koma nata bedroom ɗin, ita kuma ta dawo cikin ɗakin.
Umaisha ce ta kira a wayar, cike da zumuɗi ta bi kiran, tare da zama a gefen gado. Bugu ɗaya Umaisha ta ɗaga.
"Hello Umaisha!" Ta yi maganar cike da so da kuma kaunar ƴar uwar tata, "Aunty Afi ina kwana?" "Lafiya lou Umaisha yasu yaya AKil?" "Suna lafiya, ya Yaya Nawid da kuma Ummi?".
Nisawa ta yi tana mai kara faɗaɗa murmushinta "Wlh kowa yana nan lafiya Umaisha, amma lafiya kika kirani da sanyin safiya haka? Ya kuma aka yi yaya Akil ya kyaleki kika yi kira da sanyin safiyar nan".
Shiru kaɗan Umaisha ta ɗan yi kafin ta ce "Wlh Aunty Afi satar hanya na yi na kiraki, yanzu haka yaya Akil yana ɗaki yana kwance, nace mashi ina zuwa ne, shi ne nazo kitchen na kiraki, yanzu dai muyi magana da wuri Kinji? Dan kinsan halinsa sarai, yanzu idan ya ji na kira wani da safe haka, faɗa zai yi Mani, zai ce na takurawa ƴan gida suna barcinsu.
"Okey to menene faɗi