Showing 297001 words to 300000 words out of 359620 words

Chapter 100 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1974

Juyowa ta yi tana kallonsa.

"Malam dan Allah ka barni na shiga cikin gida, wlh sanyi nake ji sosai, ga shi kuma ruwan saman nan da alama ba yanzu zai dakata ba". Ban da kallonta ba wani abin da yake yi, ga shi ba damar ta tafi ya hana ta, turo baki ta yi ta juya tana kallon gaban ta, ta ɗauke kanta daga kallon shi. Ɗan kwantar da kansa a jikin kujarar ya yi tare da lumshe idanuwansa kasa kasa ya furta "Komai kika yi kyau yake maki, kina ɗaukar alhakina sosai, please my baby ki karɓi soyayyata kin ji? I don't want to force you akan abin da baki so, kin san cewa a yau idan ina so a ɗaura mana aure ko cikin dare ne sai an ɗaura, ba mai hanawa, kin san uncle ya gama yi mini koma, ya bani ke, amma ni bana son auren mu ya kasance baki so na, bana son ayi miki dole, duk da cewa na san dole ma zaki soni idan muka yi auren, amma ba irin wannan soyayya nake da bukata ba, ina son ki soni tun kafin mu yi aure, please kada ki ce a'a a tambaya ta karshe da zan yi maki, kina so na?". Ya kai karshen maganar tare da waro idanuwansa a kan kyakkyawar fuskarta.

Shiru ta yi bata iya ba shi amsa ba, lallai ta san cewa ya haɗa komai da duk wata cikakkiyar mace zata buƙata a tattare da namiji, matsalar a nan shine ita bata yarda da soyayya ba, bata son aure, domin tana ganin irin wahalar da matan aure suke sha, ta yi rayuwa a in da tasan menene aure wato gidan Hjyr daɗi, taga yanda matan aure suke afkawa zinace zinace da halaka kansu saboda matsalar maza, shi ne dalilin da yasa ta ce ita kam ba zata yi aure ba, amma ba wai dan nata son shi ba.

Ganin ta yi mishi shiru ne ya sa ya ɗan matso kusa da ita sosai, ruwan saman na kara karfin zuban da yake yi, hannayenta dukka biyu ya riƙo cikin nasa, ba shiri ya saketa saboda wani irin ɗumi mai daɗi da ya ji daga hannun nata, barci yake ji sosai sai lumshe idanuwansa yake yi, calmly ya ce "Tun da kin kasa yin magana, idan kina so na ki zauna a tare da ni a nan har ruwa ya ɗauke, idan kuma baki sona, zaki iya fita cikin ruwan ki tafi cikin palo". Ai tun bai gama rufe baki ba, tayi ƙoƙarin buɗe kofar motar da niyar fita, a zafafe ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, dan kada ta fita ruwa ya jiƙata, mamakin hali irin nata ya fara yi, tunani yake anya ba zai kai ta ayi mata ruƙiyya ba ko wani aljanin ne ya aureta?.

Saboda daɗin ɗumin jikinta ga sanyin ruwan sama ya sa ya lumshe idanuwansa tare da kara kankamata a saman kirjin nasa yana sauke numfashi a hankali hankali.

Kasancewar ya kankameta sosai ba halin ta kwace kanta, kasa kasa ta ce "Malam ka sake ni bana so". Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe, shiru ya yi bai tanka ta ba, dan bashi da abin da zai ce mata, jikinsa duk ya kara mutuwa dalilin kwanciya da ta yi a jikin nasa, ga kuma wani bala'in daɗi na ɗumin jikinta, abin ba'a magana, har wani barci mai matuƙar ni'ima ce take ƙoƙarin ɗaukarsa.

"My Jehan please kada ki azabtar da bawan Allah da bai san komai ba sai tsantsar soyayyarki, even for the sake of uncle ki soni kin ji? Amma kuma ina da tambaya meyasa baki so na? Shin bancancanci a soni bane?". Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa, da kyar muryar tasa take fita, tamkar mai magagin barci.

Tamkar a mafarki haka yaji zazzaƙa kuma daddaɗar muryarta tana faɗin "Ka wuce ma mace ta tsaya yi maka wata magana na bata sonka ko makamancin haka, kuma ai ni ban taɓa cewa bana sonka ba, soyayya da aure ne ni bana so, amma ina sonka tamkar yanda nake son Rimsha".

Duk da bata furta mishi so irin na mata da miji ba, tabbas ya ji daɗin kalamanta hakan yasa ya kara matseta a jikinsa sosai tare da ɗan rankwafo da kansa a kanta yana ɗan ɗaura hannunsa a saman bayanta.

"Meyasa baki son soyayya?". "Saboda soyayya karya ce, yau idan ka ce kana sona muka yi aure, after some days or months, mind naka zai canza daga kai'na zuwa kan wata or something else, like dai baban Maryam na gidan hajiyar daɗi, shi ne kawai yasa ni ban yarda da soyayya ba, is better for me na zauna da daddyna". Tabbas ya fahimci tsantsan yarinta ce a cikin maganar tata, dan abu ya faru da wata kawai sai ki yi tunanin kamar da kowa ma haka ne, baga misali a kan mummynki da daddynki ba, shi ya dai'na sonta ne?, Amma sai bai nuna mata hakan ba, sai ya yi amfani da yarintar tata dan ya canza mata tunani.

"Yes kina da gaskiya, haka ne duniyar yanzu, amma ni yanzu dai ki yarda mu buga wani game kin ji ko my diramati?". Yana magana yana ɗan shafa bayanta. "Tom shikenan na yarda, amma na minti nawa?".

"One week ma it's okey for me". Ɗan zaro idanu ta yi tana faɗin "Game ne har one week? To da wayar waye zamu buga". Ɗan jan dogon hancinta ya yi yana faɗin "Ba da waya ba, a reality zamu buga game ɗin, soyayyar wasa na sati ɗaya zamu yi, zaki kasance ke girlfriend ɗita ce for only one week, duk abin da na ce zaki rinƙa amsa mini cikin so da kauna, and then zaki rinƙa yi mini like ni boyfriend naki ne a zahiri, ko da baki taɓa jini na ba, for example idan zan fita na ce mini zan fita, you can pray for me and tell me some romantic words like yanda girlfriend take yi wa boyfriend nata, kin gane ai?".

Shiru ta ɗan yi tana tunani abin. "Sarkin tunani, kowa ai yana bedroom nasa ko? To haka zamu kasance, idan dai mun haɗu a palo ne zamu yi soyayya like boyfriend and girlfriend, idan muka kai one week muna buga game ɗin nan, to daga lokacin zan dai'na kulaki, zan dawo yayanki not masoyi, do you agree?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "One week kawai ko? Daga nan kuma zaka dai'na takura mini kana kulani ka yi alkawari?" Hannunta ya riko cikin nasa yana faɗin "Yes nayi alkawari zan dai'na takura miki kuma zan dai'na kulaki". Jinjina kai ta yi tana son tashi daga jikin nasa.

Hannunsa dukka biyu ya ɗaura a saman bayanta yana faɗin "Ina zaki je kuma? Ai yanzu kin zama girlfriend na for one week, so a jikina zaki kwanta mu yi hira". "Dama girlfriend and boyfriend suna kwanciya a jikin juna ne?" Ta tambaya tana ɗago kanta dan ta kalli face nasa. "Yes mana baki sani ba? To mu a kasarmu haka ake yi". A takaice ta ce mishi "To mu kuma a kasarmu ba haka ake yi ba, kuma nan kasarmu ne ba naku ba, dan haka dokarmu zaka bi!". "Okey na ji zan bi dokarku, amma for now dai ki kwanta shiru mu ɗan yi soyayya kafin ruwa ya ɗauke mu shiga ciki sai ki dai'na zama a jikin nawa". Ya kai karshen maganar tare da mayar da kan nata ya kwantar a saman kirjin nasa yana ɗan shafa...........

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊


*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581*

75


Ya kai karshen maganar tare da mayar da kan nata ya kwantar a saman kirjin nasa yana ɗan shafa bayanta zuwa saman kanta. "No ni ban yarda ba gaskiya, ni dai ka bari na tashi". "Talk to me like my girlfriend not like sister kin ji ko? Ko kin manta mun fara game daga yanzu ne?".

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To shikenan amma ai ni haka na iya magana". Jinjina kai ya yi yana faɗin "Okey i will going to teach you how to talk to me like your real boyfriend or your husband okey?". Gyaɗa mishi kai ta yi tana dai son ta tashi daga jikin nan nasa dan sam hankalinta bai kwanta da kwanciya a jikinsa or taɓa jikinsa ba.

Katse mata tunani ya yi da cewa "Idan muka je ciki zaki busar mini da gashi na with hand dryer?". Ɗan zaro dara daran idanun nan nata ta yi tana faɗin "Kai a'a gaskiya". Ɗan shafa kumatunta ya yi kafin ya ce "A gaban uncle fa za'ayi hakan kin yarda?". Nan ma shiru ta ɗan yi kafin ta ce "E to tunda a gaban daddy ne in dai bai ce komai ba, bai hana ba na yarda". "Serious?". Jinjina mishi kai ta yi.

"I really love you my baby". Ya faɗa yana murmushi, shiru ta yi bata bashi amsa ba, "To ya bazaki bani amsa ba? Ba nace miki I love you ba, kema ya kamata ki ce mini I love you too my baby, ko kin manta yanzu ke girlfriend ɗita ce?". A sanyaye ya yi maganar. "I love you too my baby". Ta faɗa a normal yanda take magana, girgiza mata kai ya yi yana faɗin "Not like that mana baby, ki faɗa da salon soyayya kamar yanda na gaya miki, idan ba haka ba ni ba zan yarda ba".

Ɗan turo baki ta yi tana faɗin "Allah ni ban san ya zan yi ba, ni fa a haka na iya maganata". Tabbas ta san yanda ake magana cike da soyayya, ta yi zaman gidan Hajiyar daɗi idan baku manta ba, kuma tun ainahi ita mai yawace yawace a media ce, babu wani abin da bata sani ba, kawai yi mishi ne ba zata yi ba, dan tana ganin like shirmene ka zauna kana wani kwantar da murya dan yin magana da wani, kana wani kirkiro salo na karya da banza.

"To shikenan ki rinƙa yi a hakan ma yana yi mini daɗi". "Da gaske?" Ta faɗa a sanyaye, ɗago idanu ya yi yana kallonta, har cikin ransa ya ji daɗin yanda ta ce da gasken, dan ta yi maganar a sanyaye kamar ba ita ba, da alama ta fara kwaikwayon yanda yake magana ne.

"Zaki rakani unguwa anjuma?". "Unguwar ina kuma?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Wajen masoya". Jinjina mishi kai ta yi alamar e zata je, "Yauwa my baby sarkin rigimata wani irin kwalliya zaki yi mini?". Da kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta tuna game suke yi, dan haka sai ta ce "Wani iri kake so?". Wani irin azababben daɗi mara misaltuwa yake ji, matso da ɗan bakinsa zuwa wajen kunnenta ya yi, a hankali kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana "Kin san fa ke kyakkyawace ko baki yi kwalliya ba, komai naki natural ne, dan haka ki saka mini wannan kayan naku masu zanen nan, wanda ranar kika saka, yana nan something like drawing aka yi a jiki da wasu abubuwa da aka saka miki a gaban rigar kin gane shi?".

Sarai ta gane atamfar Rimsha da Imran ya bada aka zuba mata ɗinki riga da sket mai bala'in kyau da ta saka ranar yake magana, amma saboda ta wahalar da shi sai ta ce mishi ita bata gane ba, haka ya zage yana ta faman yi mata kwatancen atampha, amma sai ta tununa sam ita bata gane ba, daga karshe da yake yana da basira sai ya gane wahalar da shi kawai take yi, bawan Allah shi bai san atampha ba, matan kasarsu da kananan kaya suke amfani, ba ruwansu da atampha, shi kuma yana yi mishi kyau tun ranar da ya fara gani a jikin Rimsha, hakan yasa yake so ta saka mishi.

Da ya fahimci cewa ta gane nufinsa kawai wasa da hankali take yi tana wahalar da shi, sai ya yi ƙoƙarin jan dogon hancinta da karfi dan shi ma ya rama, da sauri ta miƙe daga jikin nasa dan ta gudu zuwa waje ta nufi cikin palo dan ruwan saman ya tsagaita, kuma ta ga nufinsa jan mata hanci zai yi, da zafi idan ya ja mata, shi ne zata gudu.

Ina rikota ya yi yana faɗin "Ina zaki je? Wato dama wahalar da ni kike son yi ko?". Girgiza mishi kai ta yi tana ɗan murmushi, zubawa mirmishi nata idanu ya yi yana kallo, ko ba komai yau kawai ya yi nasara da har ya sakata tana murmushi kuma ta ɗan saki jiki da shi tana wasa, kai wannan abin ya yi mishi mugun daɗi wlh.

"Kayi hakuri to". Girgiza kai ya yi yana faɗin "Idan zaki yi mini magana ki rinƙa cewa baby, ai haka lovers suke yi, ko kin manta muna game ne?". Girgiza kai ta yi kafin ta ce "To shikenan ka yi hakuri babyna". Wani irin azababben daɗi ya ji tana ratsa shi, bawan Allah yana tsananin sonta, tamkar yanda Akila ta kasance kaddarar Aseef ce ita, ta zama kamar wata bugun numfashisa, to haka shi ma Areef Jehan take bugun numfashisa, dama su basu iya so ba, idan suna son abu gabaɗaya suke tafiya mishi.

"Mu je cikin gida ko?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ɗan sumbatar lallausan kumatunta ya yi yana faɗin "To muje tun da ruwan ya tsagaita". Ya kai karshen maganar tare da sakinta, da sauri ta fita ta yi gaba abinta, fitowa ya yi shi ma ya bi bayanta yana kare mata kallo hannunsa na rike da wayar daddy da kuma nasa.

A palon sama suka isko daddynta yana zaune shiru ya buga uban tagumi, kusa da shi suka zauna, tamkar abin haɗin baki suka sanya shi a tsakiya, ya ji matukar daɗin ganinsu a tare haka, ƙoƙarin kwanciya a cinyar daddyn ta yi, da sauri ya rigata kwanciya yana bawa daddyn labarin sun je basu san hanyar gidan Abbin ba sunka dawo.

Shi kuma daddyn tambayarsa ya yi me ya jika mishi gashin kansa? Ko dai ya shiga ruwa ne? Miƙewa zaune ya yi yana faɗin "Uncle kada ka tambaya ka ji? Ban san me zan ce maka ba, ba zan iya yi maka karya ba, kuma bana son na gaya maka gaskiya, iya abin da na san zan iya cemaka shi ne ba wata matsala bane kawai, ka ji my uncle?". Shafa kan nasa daddyn ya yi yana ɗan kallon Jehan ɗin, ita ma gashin kanta a jike, a matsayinsa na babba ya fahimci in da suka dosa, ya san wace ce Jehan yanzu gardama ta yi mishi ta sanya shi shiga cikin ruwa, tuna hakan yasa sam bai ji daɗi ba kuma ya kudurta a ransa sai ya yi mata faɗa sosai, dan ya lura rainin da ta yi wa Areef ɗin nan yana neman ya yi yawa, so yana da kyau ya tsawatar mata.

"Uncle baby ta ce zata busar mini da gashina with hand dryer, amma ta ce sai da izininka, ka bamu izini?". Ya yi maganar yana miƙewa tsaye, jinjina mishi kai daddyn ya yi yana faɗin ya basu izini, ya san waye Areef, so baya damuwa dan za su keɓe da ita, Jehan ai matarsa ce, ita ce dai bata sani ba, kuma ya ce kada a gaya mata sai ya gama tsokanarta son ransa, amma matarsa ce tun ranar da suka fita da shi da daddyn zuwa gidan daddyn na nan Kadunar, a lokacin sun biya gidan Abba, a nan ne daddyn yake sanar da Abba ya yi wa Jehan miji, ya kuma aurar da Rimsha, da yake Abba mutun ne shi ma mai son farincikin ƴan uwan nasa, ya ji daɗi sosai, lokacin su daddyn Jelly suna gidan a in da Abbi ya ce to a ɗaura auren kawai dan su ba ruwansu da bidia, ya tambayi Areef ɗin a ɗaura? Ya ce e a ɗaura tun da su Abba sun ce a ɗaura, sai dai baya son a gayawa kowa har sai in Lion ya dawo, dama ya bari sai ya dawo ne za'ayi auren, amma tun da sun ce to a ɗaura sai a bar maganar iya tsakaninsu, shiyasa a ƴan kwanakin nan yake taɓa jikinta yake kuma wasa da ita fiye da a baya, a baya sam baya taɓa jikinta kuma baya bata umarni, yanzu kuwa kun dai gani da safe in da ya yi mata magana cikin bada umarni da nuna isa, shiyasa kuma daddyn ya ce ya kaita gidan Abbi da kansa, domin kuwa yasan TRIPLETS da kishi, Areef ba zai yarda wani ya ɗauketa zuwa gidan Abbin ba, so matarsa ce halak malak kawai wasa da ita yake yi son ransa, yana son su saba ta kuma faɗa tarkon sonsa sosai.

(TRIPLETS gidan mamaki, kullum cikin bazata nake baku ko? To ga auren Areef ma ya zo muku a bazata😌🙄 ku jira akwai saura bazata da yawa masu tashin kai su birkita muku lissafin kwakwalwa fiye da baya suna zuwa, ku dai'na wahalar da kanku wajen cankan me zai faru a gaba a cikin littafina, dan fa ni ɗin ta daban ce,👊😹 haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login