Showing 333001 words to 336000 words out of 359620 words

Chapter 112 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2049

ku tafi bedroom naku kaji? Don't feel bad my son ka ji ko?." TGA zai yi magana daddyn ya ɗaga mishi hannu yana faɗin "General it's not a joke, it's a command!!." Yan da daddy ya yi maganar cikin tsawa ne yasa TGA ɗin hakura ya haɗiye maganar da yake son yi. Cikin fushi ya wuce fuuuu zuwa sama.

Kallon Aseef daddyn nasu ya yi yana mai sake ce mishi su wuce bedroom nasu. Okey ya amsa tare da riko hannun Akilar suka wuce. Bayan sun tafi ne daddyn ya dawo da kallonsa a kan Areef yana faɗin "Ina son ku sanya Michael farinciki a koda yaushe, because this two days an ɓata mishi rai over, kuma bana son hakan, na san cewa da kai da Romeo kune zaku fi kowa sanya shi farinciki, so ina da bukatar hakan daga wajenku." Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya koma bedroom nasa. Su uncle Herry suka rufa mishi baya, daddyn Rimsha ma komawa nasa bedroom ɗin ya yi yana mamakin hali irin nasu.

Dawo da kallonsa kan Jehan dake tsaye a bayansa ta bakin kofar bedroom nasa Areef ya yi. Tsantsar tsoro ne a bayyane a kan face nata, yau dai taga bala'i, dama haka Areef ɗin yake da iya faɗa? Ta tambayi kanta, ita ai ganin shiru shiru take yi mishi, bata taɓa tunanin ya iya faɗa har haka ba, ji yanda yake magana da uncle T kamar wani ɗansa, cikin faɗa da nuna tsantar isa da izza, nan take wani azababben tsoronsa ya sake kamata, ta kara shan jinin jikinta.

Har ya ƙariso in da take ba tare da ta sani ba, ta luluka can duniyar tunani. Sai da ta jita a saman kirjinsa sannan ta farga ashe ya iso gareta. Shiru ta kwanta a jikin nasa saboda dukan uku uku da kirjin nata yake yi, har ga Allah ta tsorata da ganin uncle T ga kuma bala'in da suka yi da Areef.

A wannan karon dai bata yi ƙoƙarin kwace kanta ba, sai ma kwanciya da ta yi tana mai da numfashi, kafafunta gabaɗaya sun yi mata nauyi, dan fa a gaskiya sai mai karfin zuciya ne zai iya kallon Lion da TGA suna faɗa a waje, idan kana wajen to kana iya suma dan faɗarsu bashi da kyan gani ko miskala zarratin, yanzu zasu aika mutun in da ba'a dawowa idan aka yi wargi.

Areef bawan Allah akwai saurin fahimta, ya fahimci ta tsorata sosai ne yasa ya rungumeta, dan ta ɗan sami natsuwa, jinjina mata a cikin zuciyarsa ma yake yi da har ta iya tsayuwa ta kalli bala'in TGA, ta yi ƙoƙari sosai.

Sai da ya ji ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya ne sannan ya saketa tare da riko hannunta suka koma cikin bedroom ɗin yana faɗin ta zo suje su sha fruits a tare. Sam bata yi mishi musu ba saboda har lokacin bata gama warwarewa ba.

A tare suka jera zuwa cikin ɗakin. A ɓangaren Aseef da Akila kuwa. Bayan sun shiga cikin bedroom nasu, saman bed ya zaunar da ita tare da zama a gefenta dan ya rarrasheta. Baiwar Allah tana ganin rayuwa a wajen waƴan nan masu jajayen kunnuwa, su kuma nasu kaddarar kenan, matsalar dangin miji, duk TGA yasa ta fita a hayyacinta, gabaɗaya surutan ma da ya rinƙa yi bata jinsa, tun da ya daka mata tsawa ta farko lokacin da ya shigo cikin palon, daga nan ta faɗa rashin hayyacinta na wucin gadin.

"My heartbeat dan Allah ki dai'na wannan kukan kinji ko? Ba dai kina so na ba?." Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e tana son shi. "To shikenan it's okey, ki kwantar da hankalinki, da ni kaɗai zaki zauna ba da su ba, dan haka babu ruwanki da su kin ji ko?."

Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "My shagwaɓati yanzu idan suka rabani da kai fa? Kaga kowa naka ya ce baya sona, ina tsoron su rabamu ne, seriously ba zan iya rayuwa babu kai ba." Baiwar Allah tana magana hawaye zafafe suna bin kuncinta.

Matsowa ya yi a in da ya rungumota sosai a saman kirjinsa. Murya cikin sigar rarrashi ya fara magana yana ɗan shafa bayanta a hankali hankali zuwa kasa. "My heartbeat, babu wanda zai rabamu da izinin Allah, ke tawa ce kamar yanda nake naki ke kaɗai, har mu mutu babu rabuwa, ki dai'na damuwa kinji matata farincikina?."

Hannu tasa tare da rungumo shi da kyau, a hankali ta kara shigewa jikinsa tana faɗin "Tom shikenan my shagwaɓatina." Cikin zolaya muryarsa ɗauke da zallar madarar shagwaɓa ya ce "Kina tsoron rasa fine guy ko?." Turo baki ta yi tana faɗin "Kafara ko?."

"A'a ni ban fara komai ba, kawai gaskiya na faɗa, kina tsoron rasa kyakkyawa babyn daddynsa kuma pleasure TRIPLETS ko?." Dukan wasa ta fara kai mishi a kirji nasa tana faɗin "Mun ɓata da kai tun da sharri zaka yi mini." Ta kai karshen maganar tana kokarin miƙewa daga jikin nasa.

A hanzarce ya rikota yana mai kara matseta a jikin nasa. "Am so so sorryyyyyyyy sarkin rigimata, na tuba." Ɗago kanta ta yi tare da kama kunnensa ta ja da karfi. Ƴar kara ya saki yana ɗan turo baki. "Allah ba zan kyaleki ba, kawai dan kinga kunena yafi naki kyau ko? Shi ne zaki cire mini shi?." Ya kai karshen maganar tare da karisa haurawa saman bed ɗin. Yana hawa ya jawota jikin nasa. A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, juyowa ya yi tare da yi mata rumfa da kirjinsa. A shagwaɓe ta ce "Za ka fara ko?." "Kayanki ne ko nawa?." Ya bata amsa shi ma a shagwaɓe.

"A'a kayanka ne ranka ya dade." Hararar soyayya ya wurga mata kafin ya kai hannunsa izuwa saman breast nata. A hankali ya lumshe idanunsa saboda wani daɗin da yaji ta mamaye shi. "My rigimati wai yaushe zaki barni nayi dis virgin naki ne? Ni fa ina son karɓar kayana."

Kukan shagwaɓa ta saka mishi tana faɗin "Ni to ka bari na huta mana? Wai ma yaushe aka yi auren ne? Ban gama hutawa daga gajiyar biki ba, sai ga kuma gajiyar ciwo, yau fa kwanana biyu da tashi daga ciwo, to ka bari sai na huta." Kuka ya saka mata a kan shi Allah bai yarda ba, yana son yaga yana shiga jikinta sosai.

Sanin halin kayanta yasa ta shige jikinsa sosai ta fara rarrashin shi. Akila sai Aseef, Aseef sai AKila, ba mai iya su sai junansu, haka zasu zauna suyi ta zubawa juna shagwaɓa kamar me, abin gwanin burgewa.

A kunne ya raɗa mata to ya hakura, amma next week yana son su je wajen Ammie su gaishe ta. Da murna ta ƙanƙame shi sosai tana zuba mishi godiya. Tureta ya yi tare da miƙewa zaune ya bata baya yana faɗin "Kafin mu yi aure ma kin fi so, kin fi bani kulawa, yanzu dan nace zamu je wajen Ammie ji yanda kika rikeni sosai, amma idan ba haka ba sai ki ce kina jin kunyata, ko fa wanka baki yarda mu yi tare, kuma ke kika yi mini alkawarin idan muka yi aure zaki yi mini soyayya sosai." Cikin shagwaɓa ya yi maganar tasa.

Matsowa ta yi a in da ta kwantar da kanta a saman bayansa tare da zuro hannayenta ta saman cikinsa. Murya a sanyaye ɗauke da shagwaɓa ta fara magana. "Kayi hakuri kaji my shagwaɓatina, nayi alkawarin ba zan sake ba, komai kake so zanyi maka, ba zan sake cewa ina jin kunya ba, zan kula da kai sosai." "Are you sure?." Ya yi maganar ba tare da ya juyo gareta ba.

"Yes my heartbeat, kai ne fa bugun zuciyata kuma bugun zuciyar kowa dake gidan nan, please ka dai'na ɓata rai, na san idan ka ɓata rai yaya Saif da yaya Areef ma zasu ji hakan a jikinsu." Turo ɗan red lips nasan nan ya yi tare da juyowa ya mannata da kirjinsa. A hankali ya fara shafa bayanta yana faɗin "Tom shikenan na dai'na ɓata rai, me zaki bani yau?." "Me kake so?." Shiru ya ɗan yi kafin ya matso da bakinsa dai'dai saitin kunnenta. Can kasa kasa ya furta "Abin daɗi." Lulukawa duniyar tunanin menene kuma abin daɗi ta yi.

Matsowa da bakinsa ya yi zuwa saman kumatunta, sumbatarta ya yi yana faɗin "Sarkin tunani ba, har yanzu baki dai'na tunanin ba kenan? Ni ba sai kin tuna menene abin daɗi ba, in anjuma ya yi da kai'na zan ɗauki kayana, yanzu dai tashi muje ki karisa cin abincinki.".

Zaro idanu waje ta yi, a tsananin tsorace ta ce "A'a ni ina tsoron uncle T, nama ƙoshi da abincin." Cikin nuna ko in kula ya ce "Ki dai'na tsoron Uncle T fa, dan wlh ina ga miki bashi da hankali ne, ni ko ba'a gaya mini ba nasan uncle T ɗin nan Roshan kakansu ya gado, mutun sai bakar bala'in tsiya, to ko Lion yanzu da ya musulunta ya rage faɗa, amma shi uncle T kamar busar shaiɗan ake yi mishi a kai, Allah ni nasan wannan Roshan ɗin ne ya ɓatasu, dan naji ance shi ma Roshan ɗin a lokacin shi sam baya ɗaga kafa, dan haka ke ai ba ruwanki da uncle T."

Shiru ta ɗan yi kafin ta sake fara magana cikin natsuwa da kuma sigar da zai fahimceta cikin sauki. "My heartbeat kana ji ko? Please ka dai'na cewa uncle T haka kaji? Duba yanayinsa zaka yi, bashi da wani laifi duba da irin tasowan da suka yi kenan, a addinin musulunci komai lalacewan uncle T a matsayin daddynka yake tun da kanin daddyn ne, baku da wanda ya fishi, idan har baka son uncle T to zai zama daddy ba zai taɓa jin daɗi ba, dan shi ma yana son ƴan uwan nasa, kaga yanzu misali duk yanda kake sona idan nace bana son su yaya Saif zaka zauna da Ni?." Girgiza mata kai ya yi yana faɗin "A'a ba zan zauna da kema koda kuwa zan mutu idan kika tafi, to gara na mutu da na zauna da wanda bata son TRIPLETS nawa."

"Good, to ka sani shi ma daddy haka yake son uncle T kamar yanda kuke son junanku, jini ɗaya ba wasa ba, uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa ba, ina da tabbacin daddy yana matuƙar son uncle T, kuma shi ma uncle T ɗin yana matukar kaunar daddyn, duba ga irin yanda ya girmama daddyn ɗazun, kaga umarni daddyn ya bashi a kan ya yi shiru, amma haka ya yi shirun ba dan yana so ba, hakan zai tabbatar maka da yana son yayan nasa kuma yana jin maganarsa komai wuya komai daɗi, baka ganin kullum daddyn da uncle Herry suna tare ne?." Jinjina mata kai ya yi alamar e kullum suna tare.

"To ai saboda yana sonsu ne bashi da biyunsu a duniya yasa kullum yake tare da su, in dai kuka yi wa Uncle T or uncle Herry abu, to ku sani tamkar daddy kuka yi wa, dan sai ya fisu shiga bakinciki, sai dai kawai ba zai nuna muku bane." A wannan gaɓar sai ta yi amfani da ilimi, bata ce mishi daddy ba zai nuna musu ɓacin ransa bane dan yasan irin tarbiyar da ya basu tsab zasu iya hayayyako mishi ba, sai bata ce hakan ba, duk da a zamanta da su ta lura da hakan, ta lura tun farko daddyn ne ya tabbaka babban kuskuren da ba zai taɓa gyaruwa ba, dan mawuyacin abune yanda suka girman a hakan nan ya sake cewa zai iya juya su, ina ba zai yiwu ba, bare ma da suka yi aure yanzu, ai shi dai daddy sai dai kawai muce Allah ya bashi jikoki masu jin maganarsa da bin umarninnsa, ƴaƴa kam sai dai hakuri ya ɓata komai da kansa tun farko.

Rungume sosai ya yi yana mai kara jin kaunarta a ransa, a koda yaushe tana kara mishi ilimi dan gane da addinin musulunci, wannan shi ne amfanin ka auri mace mai ilimi, ko baka mori ilimin nata ba, ƴaƴanka zasu mora. Shi dama ina ya wani san cewa da daddynsa da uncle T duk ɗaya ne, ai shi kawai daddynsa shi ne mutun tun da shi ne ya haife shi, amma yanzu ta fahimtar da shi kuma ya gane ya kuma ji daɗi.

"To muje ki karisa cin abinci ko, sai kizo ki kira our Queen, tun jiya fa take ta kiranki a waya, ta yi miki miss call sosai lokacin da bamu da lafiya, daga karshe ina rokan Allah daya sauke miki ni'imarsa mara adadi a tattare da ke my heartbeat kuma my rigimati".

Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna. "To haka zamu tafi baka bani hot kiss ba?." Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kara rungumeta sosai, dama abin da yake so kenan, rakinta yasa bai ce zai yi mata ba, yanzu idan ya ce zai yi mata sai ta tsaya ta yi ta raki, amma Alhadulillah tun da ita ta ce da bakinta ya yi mata, sai ya kwanta da ita a jikinsa kafin ya fara kissing ɗin nata.

Yau dai sam bata ji kunyarsa ba kamar yanda ta ce mishi ba zata sake cewa tana jin kunyan nasa ba, haka kuwa aka yi, fara taya shi kiss ɗin ta yi tare da rungume shi sosai.

Wani irin azababben daɗi ya ji na musamman, tun da suka yi aure sai yau ta bashi goyon bayan ɗari bisa dari. Hannu yasa ya fara wasa da breast nata dake matuƙar burge shi amma tana yi mishi rowa, to yau dai ta bashi, da kanta ma take taya shi ta hanyar gaya mishi kalamai masu daɗi. Romancing nata ya fara yi babu kama hannun yaro, haka ita ma ta zage dan kada ya kureta, amma sai dai ina ba zata haɗa kanta da shi ba, dan sufa zallar madarar soyayya wanda babu mix ko ɗigo a jininsu yake, gadon shi suka yi, kawai dan dai a yanayin yanda suka taso ne yasa basu ma sha'awar soyayyar, da ace mummynsu na tare da su, ai da dukkansu manyan ƴan soyayya ta duniya zasu zama, duba da irin soyayyar da daddynsu ya zuba lokacin yana saurayi, tamkar zasu cinye juna da mum ɗin tasu, lokaci guda kuma sai Allah ne kaɗai yasan me ya rabasu, sanadiyar hakan daddyn ya fara shan wine (giya) dan ya rage takaicin rabuwa da suka yi, hakan har ta yi mishi mummunar illah, bugu da kari kowa yasan dama su Turawa ai mayun love ne, bautawa soyayya suke na wuce misali.

Tun tana ƙoƙarin kure shi har ta kasa ta hakura ta lafe a jikinsa shiru tana karɓar saƙon da yake aika mata, ita ma dai saura kaɗan ta suma ba iya Rimsha kawai ba, ita Rimsha ma ai dan mai sauki Lion ya yi mata, kada ku manta bai cika son wasa da ita ba, yana yin komai a hankali kaɗan kaɗan da taka tsantsan, amma a hakan ma sai da ta suma, ina ga kuma ya saki jiki ya yi wasa da ita son ransa?.

To ita ma Akila kusan hakan suka kare da Aseef, har sai da ta yi mishi kukan daɗi, ya kiɗimata over, dama goyon bayanta ne da bai samu ba yasa yake ɗaga mata kafa dan baya son yi mata abin da bata so, amma yanzu ai sai ya sanyata suma saboda daɗi.

Da kyar ya hakura ya kyaleta ba dan ya so ba, sai dan kukan da take yi mishi. Kwanciya ya yi da ita a jikinsa yana shafa bayanta alamar rarrashi yana kuma mai da numfashi. Akila manya ita da ta ce zata sanya shi kuka sai ga shi daga wasan farko ita ta yi kukan.

Sai rarrashinta yake yi yana gaya mata kalamai masu ratsa zuciya, da haka har barci ya ɗauketa lafe a kirjinsa. Ganin ta yi barci ne yasa ya shafi kumatunta yana faɗin "Ƴar rigima kawai, idan baki yi mini rigima ba sam baki jin daɗi na lura." Ya kai karshen maganar tare da gyara mata kwanciya da kyau da kyau shi ma ya lumshe idanunsa alamar barcin zai yi............. Rigimati da shagwaɓati sai Allah, suna tsantsar kaunar junansu, soyayyarsu mai tsabta ce, suna matukar girmama duk abinda ɗayansu yake so, bugu da kari suna girmama juna sosai, ga kula da addini da kuma mutunta ƴan uwan juna, da nuna musu soyayya. Ba abin da zamu ce sai dai Allah ya bar su tare cikin Kaunar juna da farinciki.

A ɓangaren kasar Russia kuwa. Ganin yanda ta takure jikinta waje guda tana rawan sanyi ne yasa Lion ya jawota jikinsa, ga shi ko jacket bai saka ba bare ya rufeta da shi. Ba tare da ya kallin driver dake tukasu ba ya ce da shi ya kashe Ac'n motar. A hanzarce ya kasheta.

Ko da aka kashe bata dai'na kermar sanyi ba, ɗaukanta ya yi cancak ya dawo da ita saman cinyarsa dan ta sami damar shiga jikinsa sosai ko sanyin jikin nata zai ragu. Shi dai bodyguard dake tukasu ɗin sai satar kallonsu yake yi ta cikin mirror, sun yi matuƙar burge shi, a tunaninsa ma yaya da kanwarsa ce, duk da ya kalleta chocolate color, bai yi amfani da kalar fatarta ba, dan akwai black Americans ai, kawai sai ya yi amfani da kyan da Allah ya yi mata ya haɗasu suka zama yaya da kanwa, kwata kwata bai kawo cewa mata da miji bane, dan yanda ya ganta yar karama, ko kusa ko alama bai ma kawo mata aure kusa ba, a nasa tunanin ma bata wuce 11 years ba, dama kunsan su kamar Rimsha dai gaskiya yarinya ce sosai a wajensu, idan ana maganar aurema ko kusan kiran irinsu Akila ma baza'a yi ba bare Rimsha.

Meesha, ya ambaci sunanta. Kasa kasa ta amsa mishi da na'am, "Are you okey now?." Turo baki ta yi tana girgiza mishi kai alamar a'a. Shafa bayanta ya yi yana mamakin halinta irin na Aseef. Allah sarki Aseef ne yake yi musu wannan tsiya, idan bashi da lafiya suka yi treating nasa, idan sun tambaye shi are you okey? Sai ya ce musu no, ba ya taɓa ce musu ya ji sauki, kullum no yake ce musu, da farko sai su ɗaga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login