Showing 303001 words to 306000 words out of 381117 words

Chapter 102 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2044

tashi saiga hajiya kareema da ciki, aranar data gano tana da ciki hankalinta ya tashi sosai don haka ta fara laluben wayar talatu, rininging daya biyu talatu ta dauka   yar gari any aba batan hanya kikayi ba, tun ranar dana hadaki da wannan alhajin ban kara jin motsin ki  
Cikin furgici haj kareema ta mike tna zarya adakin tace   haba tlatu, inata kiranki tun jiya bakya dauka, kinsan irin damuwar danake ciki yanxu kuwa
  toh ay gashi nan na dauka ya ake ciki naga hankalinki ya tashi sosai meke faruwa?  talatu ta fada tana sauraronta
  talatu ciki, ciki ya shiga na shiga uku  kareema ta fada tana duban kofar shugowa dan dakin nasu
  shine kike wani tada hankali, amma dai kema wallahi kara wata karamar yarinya wallahi,  talatu ta fada tana dariya
A harzuke mummy tace   ke ba dole hanklai na ya tashi ba, ke kinsan wannan cikin shege ne, kuma yanxu da aurena da tsufana aka ganni da cikin shege akwai damuwa 
Da sauri talatu ta tari nunfashinta   waye zai gane? Nifa matsala dake wani lokacin kamar baki da kwakwalwa wallahi, ki gane mana 
Dan shuru haj kareema tayi kafin tace   ance maki banyi wannan tunanin bane,bazaiyuwu na barshi a matsayin na mijina ba saboda yau mun kusa wata rabonda mu kwanta tare 
Wata bazawarar dariya talatu tayi tace   and so what?, yanxu dai tukunna zubarwa zakiyi ko ajeshi zakiyi 
  zubarwa zanyi mana me zanyi dashi me zanyi da wani dan shege yanxu kuma  kareema ta fada
  ay shiknan, bari zan kira likita na saimuje kobe a cire shi  talatu ta fada
Sallama kareema tayi mata kafin ta kashe wayar.
Tana aje wayar khady ta shugo fuskanta dauke da takaicin abunda tajiyo ma kunnenta, a furgice mommy ta mike daga zaune ta dago ta kalleta, itama kallon nata tayi yanda take kallonta tace   chapp yanxu ke mummy cikin shege kika kwaso?,lallai ma, kullum kece meyi mana surutun kinyi asarar haihuwa, mu kasa mu kasa, munje munyi iskanci ashe kema shi kikeyi, koda yake wallahi alhakin marayun da kika&  
Afurgice mummy ta buge bakinta tace   a gidan ubanwa kikaji wannan batu 
Kallonta khady tayi tace   wanne daga ciki? Na cikin shegen kona su salima da kika sa azubar dasu saboda rashin imani 
Kwasheta kareema tayi ta mari tass, ta nuna ta da dan yatsa tace   dan ubanki ina matsayin uwarki kike fada min Magana haka  kallonta khady tayi babu kunyar idanu tace   hmm mummy Kenan, borin kunya ne ke damunki zanyi maki uzuri,amma wallahi allah saiya tambayeku keda dadi, duk halin da muka shiga ku kuka jawo mana, kuma bazan fasa fad aba wallahi alhakin marayun nan ne ke binmu mu duka shiyasa duk muka tsiyace,  ta kareshe tare da fucewa daga dakin tana hawaye, tana fita mummy ta dafe kirji tana innalillahi   wannan wace irin masifa ce na shiga uku ni kareema 
Washe gari haka mummy ta fuce daga gidan afurgice ba tare da sani kowa ba, direct asibitin da talatu ta bata address ta shige,a reception ta tadda talatu,saida suka gaisa kafin su wuce office din likitan, tunda suka zo talatu ta fada mashi buqatarsu, ba tare da bata lokaci bay ace   ayki kam in yanxu kukeso za ayi, saidai sai kun cika min hannu, bayan wannan dole sainayi mata scanning da yan gwaje gwaje saboda bana son asamu complications don wannan aikin kusan yana da risk sosai,  atake talatu tace   haba magaji baka da case 
Wata irin dariya ya kyakyace kafin yace   dillaliyar yan gwanjo ina yinki sosai 
Saida suka aje mashi kudinshi kafin ya buqaci mummy ta kwanta don yin scanning,anatse ya soma duba cikin nata, gama daya satinshi shida don haka yace   ayki zai yuwu don cikin baiyi gir&   dan shuru yayi yana gwalo idanu yana duban mahaifarta da kyau, ganin yayi shuru yasa takatu cewa ?adai 
Nunfasawa yayi ya dubesu duka yace   gaskia akwai matsala, cikin nan bazai zubu ba dole sai an haife shi,mahiafarta is weak, kuma kunsan cire ciki kamar forcing dinshi ne don ya futo bawai kamar bari bane don haka ayki bazai yuwu ba gaskia, idan kuwa akayi zata iya mutuwa 
Hankali atashe mummy tace   na shiga uku, yanxu babu yanda za ayi ya fit aba tare da wata matsala ba 
Dariya likitan yayi tace   haba hajiya lokacin da kike kwasar dadi bakiyi tunanin ciki ba sai yanxu, ai kawai kiyi hakuri ki haife shi don wallahi zaki iya mutuwa idan aka ce za ah cire shi don dole 
Mummy dai karamin hauka ne batayi bad n hankalinta ya tashi sosai, yanxu ya zatayi da wannan masifa data tunkarota, babu abunda yafi tayar mata da hankali sai tunawa da daddy, tabbas shizai fara tona mata asiri don sunfi wata hudu basu kwanta ba,tunda suka fito daga asibiti mummy ke kuka har suka shiga napep, ganin haka yasa talatu cewa   kewai kukan me kikeyi kamar tashin kiyama?, 
Cikin jin haushin talatu ta soma Magana   haba talatu, ay dole kice haka tunda ba kece a cikin situation din dana tsiinci kaina a ciki ba 
   toh ay naga kin tsaya kina bata ma kanki lokaci kina kuka ne, inma wanchan maholon mijin naki kike tsoron karya gane akwai yanda zamu toshe bakinshi, bazai taba cewa komai ba akan wannan  
Cikin jin dadi mum kareema tace   dan allah ki fada min,ya za ayi kenan 
Murmushi kawai talatu tayi tace   ki kwantar da hankalin ki indai kina da talatu bakida case 
Nan take ta fada ma mai napep inda zai kaisu, cikin yan muntina kadaan sai gasu cikin wata anguwa, saukesu mai napep yayi suka sallameshi suka wuce, saida suka danyi tafiya mai nisa har suka wuce wata maqabarta kafin su shige wani gida dake kallon maqabartar, da baya baya talatu ta shiga gidan, mummy na ganin haka itama ta shige,babu komai a cikin gidan sai katon fili dake sagaye da bishiyu, sao tsakiyan bishiyar wani tsoho zaune akan taburma, anatse suka karaso suka zauna gabanshi, talatu ce ta fara gaishesa kafin ta nuna kareema tace   malam na zango, wannan kawata ce, ga matsalolinta& ..  nan talatu ta fada mashi komai tare da buqatar da suke nema daga wajenshi, dago wa yayi ya karema karima kallo, kamar yanda itama take kallonshi, tsoho ne tukuf don har furfura ta gama cika fuskanshi, wata yar dariya yayi irin ta tsoffi yace   an gama, zaku niya tafiya 
Shuru mumy tayi tana mamaki, just like that an gama?, talatu ce ta kallshi ta aje mashi maqudan kudi tace   mun gode malam na zango 
Sallama sukayi mashi suka fito atare,kareema dai gaba daya hankalinta ba a jikinta yake ba, kallon takatu tayi tace   ban gane me tsohon nan ke nufi da an gama ba 
Kallonta talatu tayi kafin ta bude Jakarta ta janyo cingum ta wulla bakinta kafin tace   ayki ya tafi inda ya kamat yaje, ay an gama komai, da kanki zakizo ki bani labari 
Shuru dai mummy tayi bat ace komai ba har suka iso anguwarsu&


Abuja Nigeria& &
Yau sati guda Kenan, kullum madina ke zuwa wajen amr???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a,da farko amra bata sake mata ba, ganin haka yasa madina ta fara janta da hira har suka shaku sosai cikin yan kwanakin, madina wayyaiyar yarinya ce, haifaffiyar garin sokoto ce aure ya kawota nan waje wajen Abuja har mujinta ya rasu, ya barta da yaya biyu,akwai wani program da akeyi na mata inda mata ke taimakon yan uwansu mata, ta hanyar basu jari da kudi da abubuwan da zasu dogara da kansu, ammah na cikin top member na cikin kungiyar inda take contributing sosai wajen taimakaw matan nan,anan ammah ta san madina,abunda yaja hankalin ammah ga madina shine,ta fita daban cikin sauran mutane, ita burunta kawai ayi sponsoring karatunta ba kamar sauran da suke neman aba su jariya ba, nan take ammah ta dauki nauyinta da karatunta, madina na ganin haka kuwa ta miqa yayanta wajen wan babansu don daman ba iya rikesu zatayi ba koda ta koma wajen iyayenta, cikin shekaru kalilian mdina ta gama karatunta na physiology harta fara aiki a cikin wani asibiti, inda ta samu wani bangare daban na sashen mata, har take yima mutane masu matsalolin aure counselling, duk wanna achievement din nata har yanxu she believe saboda ammah ne don kwata bata taba tunanin zata kai inda take ba ayanxu ba tare da taimakon ammah ba da suke kira da hajiya uwar marayu .

Yau Friday don haka sai wajen karfe hudu ta karso gidan don saida ta gama da office, lokacin data shugo ammah na zaune a parlor, cikin girmamawa madina ta karaso suka gaisa, nan ammah ke tambayarta any progree   ay hajiya daughter taki tana da wayewa sosai, tana daukan karatu ssoai  madina ta fada tana murmushi
  madallah, nasan bazaku bani kunya ba ay, haka nake so naji, allah ya taimaka yarinyar kirki  ammah ta fada tana murmuhsii
  ameen hajiya 
  kije saman yanxu ta haura  ammah ta fada tana kallon tv
Anatse madina ta mike ta hau saman, direct dakin amra ta wuce da sallama, amra dake sanye da riga da skirt tayi saurin juyowa jin muryarta   ?nty madinaaaa, sannu da zuwa 
Murmushi madina tayi ta karaso cikin dakin ta cire mayafinta tace   washh na gaji, yauwa student, ya zaman gida fatan ki fara bashi assaignment kema 
Shuru amra tayi tana jin kunya tace   anty madina its not easy oo, kinsan na maki bayanin komai 
Kama baki madina tayi tace   haba karki bani kunya mana mrs general 
Karasowa amra tayi har inda take zaune cikin nastuwa tace   hmmm anty madina Kenan wallahi bazaki gane bane, ahaka ma da nake zuwa dakin nashi bakiji kirjina ba 
Dariya madina tayi tace   banga laifinki ba wallahi, ni har yanxu mamaki nake ashe shine mujin naki?, dole kiji tsoro sister don wallahi jiya dana ganshi saida gabana ya fadi, yana da wani irin kwarjini sosai, saidai bari kiji na fada maki wani abu 
Madina ta fada tana kamo hannunta tace   kalleni kiga, sister ke macece, mace nada wani sirrin daraja, musamman irin ku, jibeki fah san kowa kin wanda ya rasa, wallahil azeem duk gigin kanshi zaki iya saukewa trust me and trust the process, 
Sauke ijiyar zuciya amra tayi tace   wallahi tsoronshi nake ji anty madina, kinga yanxu fah kamar ya kara tsanata, baya kallon inda nake kwata kwata, baya cemin komai har gaisuwata ya daina amsawa 
Shuru madina tayi tana sauraron ta kafin tace   wace irin gaisuwa kikayi mashi? Kinyi irin wadda na koya maki ko yaya? 
Sunkuyar dakai amra tayi tana dan murmurshi   gaskia anty madina nidai bazan iyaba wallahi  amra ta fada tana sunnar dakai
  kinji matsalarki Kenan wallahi, menene abun kunya adan hugging,kinga wallahi in baki cire kunya da tsoronshi ba wallahi zaki wahala 
Kallonta madina ta sakeyi tace   dear in tambayeki mana? Bakyason kiga kuna sakewa kedashi?, 
  ina& so  amra ta amsa ta jiki a mace
  then you have to make him know your existence, you have everything da namiji mai lafiya dai bazai iya kauda kai daga ganinki ba,kuma wallahi yanxu kiyi min alkawarin zaki cire duk wani tsoronsa daga ranki, ki saki jiki kiyi abunda ya kamata inba haka ba wallahi haka zaiyi ta maki kallon hadarin kaji, don yarigada ya dandana ki, inason ya haukace akanki ta yanda bazaiyi yan seconds b aba tare da yaji motsinki a kusa dashi ba 
  anty madina zan iya kuwa? Ni ina ganin kamar yafi karfina  amra ta fada ashagwabe
Dan buge mata bagi madina tayi tace   waya fada maki namiji yana fin karfin mace, musamman mace irinki, gaki da kayan alatu allah ya baki diri da komai, ga kyawun fuska gana hali duk kin hada ke kadai 
Dariya amra tayi ta kalleta   kai anty madina da zuzuta, yanxu me zaki buqata akawo maki? 
Dan dagiwa sukayi jin an bude kofa, daga nesa salima na hangosu tace   yanxu nasan zaku koreni, waima anty madina me kike koya mata ne? nima akoya min 
Hararata amra tayi tace   toh mara kunya, futa anan 
Dariya madina tayi tana kallonsu har salima ta fita tana cewa   ina wuni anty madina,  
Amsata madina tayi harta fuce tana kunkuni, maido da kallonta ga amra tayi tace   yauwa as I was saying,wallahi saikin dage damtse ki cire wannan tsoron naki fah, yanxu dai daga ina muka tsaya jiya?  ta fada tana kallonta& ..
Sun dade sosai inda madina ta tsatsarata akan yanda zata dunga tarairayarshi, itadai kawai tana jinta ne saidai tasan cewa shidai duk wannan ba lallai yayi aiki a wajenshi ba.
Sai wajen karfe shida na yamma madina tayi masu sallama ta wuce gidanta.

Yau amra da kanta ta sauko kasan ta dora dinner, nan salima ta sauko ta tayata tare da talatu, sai wajen gab da sallar magrib suka gama, da taimakon salima suka jera komai a dining, suna gamawa suka wuce sama atre gaba dayansu.
Wani sabon wanka amra ta sake ta sauya kaya zuwa doguwar riga a shape gown data fidda shape dinta sosai, atamfa ce Holland mai zanen flowers mai kyau, anyi mata dinkin stones tundaga sama har kasa yayi mata kyau sosai, feshe jikinta tayi da turaren ta masu sanyin kamshi kafin ta tada sallah, tana nan zaune aka kira sallah isha I tana idarwa ta danyi yan addu oi ta dan dade sosai a zaune kafin ta miqe ta zare hijab din nata ta wuce gaban gado ta janyo wayarta, ammah tasa an mata sabon sim card saidai bata da number dayawa a ciki daga na ammah saina haifa da Nadine ,suma duk numbers din nasu basa shuga, gashi tayi trying tura masu message shima baya tafiya, har social media din haifa saida ta shiga ta tura mata message thrug Instagram, shima shuru babu response, haka nan ta hakura saidai kullum saita duba Instagram dinta,
Yanxu ma zaman datayi duban Instagram din ta soma yi, ganin babu response yasa ta hakura kawai ta soma duban timline dinta,da sabbin followers dinta, tana cikin yan dube dubenta ta shiga wajen suggested followers, taga handle din amar, bata dauka shi bane ba don sunan dayayi using as   A..mar, kallon profile din ta soma yi ba tare da ta shiga ba don tabbatar da ko shi dinne, ginin picture din baya fita sosai yasa ta shiga cikin account din, nan take pictures dinshi sukayi appearing guda hudu ajere, samun kanta tayi da shiga cikin hoton don tabbatar da shi dinshi, first picture din a tsaye yake a safari da kundura a saka wani bakin glass gefenshi wani tattabara ne dayayi landing a kafadarshi ya juya yana kallon tattabar, yayi masifar kyau sosai a hoton don ita kanta saida ta shagala da kallon shi, hes looking so so cute and charming, haka ta sakankance wajen kallon hotunan nashi kaf har tayi liking day aba tare da saninta ba, saida salima ta shigo dakin tace   adda dinner  kafin ta danyi firgigi ta waigo tace   gani nan 
Atare suka sauko kasan , ammah ne kawai zaune kan dining gefenta salim, zama duk sukayi atare, cikin yan mintuna kalilina ammah tace   salima jeki kira yayanku  sanin wa take nufi yasa ta miqe a tsanake ta wuce dakin nasa, da sallama ta shiga har cikin dakinsa, azaune ta hangoshi ya doka tagumi abun tausayi, kallonshi tayi kafin ta karaso har inda yake kanta a kasa tace   dinner is ready ammah tace ka fito  dan dagowa da jajayen idanunshi yayi ya kalleta yace   ina zuwa 
Wani iri taji ganin yanda yanayinshi yake gashi yanda ya bata amsa ma yasa taji babu dadi harta juyata dawo tace   is everything okay with you 
Ay kamar jira yake ya juyo ya kalleta yace   youre asking me if everything is okay?i thought kince you don t care anymore, so why are you asig huh?  ya fada yana kafeta da idanu, wani irin rashi dadi taji saidai hakan baisa ta ji zata sauke kudurinta akanshi ba don haka tace   I just ask bawai don na damu bane 
Ataqaice ya bata amsa da   okay good 
Yana kaiwa nan ya juya mata bata, rike kugu tayi tana mamakin shi kafin tace   me yake nufi da hakan Kenan?daman nasan ba sona yake ba 
Yana gab da shiga bathroom ta dago murya a hasale tace   hmm namiji Kenan daman nasan ba sona kake ba fada kawai kake abaki 
Juyowa yayi gadan gadan jin abunda ta fada yazo gab da ita yace   are you kidding me?bayan kinyi neglecting dina yanxu kuma kina questioning son da nake maki?anyways laifina ne dana kasa moving on da rayuwata dama chan nike sonki ba sona kike ba so nima zanyi kokari na cireki araina  yana kaiwa nan ya fuce daga dakin ya barta tsaye hawaye na zarya a fuskanta, rai abace ya wuce dining din ya zauna, itama saida ta daidaita natsuwarta kafin ta fito daga dakin ta zauna
Abunci suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login