Showing 339001 words to 342000 words out of 381117 words

Chapter 114 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1967

ba suka wuce office din doctor.

Da sallama suka shiga cikin office din ammah ce a gaba sai amra dake biye da ita tare da salima.
Zama sukayi gaba dayansu baya sun gaisa da doctor din.
 Sannu madam ya nauyi? Hope baby is kicking
Doctor ya fada yana kallon amra
Murmusawa kawai tayi batace komai ba, maida kallonshi yayi kan ammah yace  Bari mu fara scan ko? Saimug ko edd dinta yayi gaba ko ya dawo baya
Mikewa amra tayi ta wuce inda doctor kw dubata, hawa tayi kan gadon kafin ya soma dubata, yana gamawa yayi printing scan din.

Mikamaa ammah paper yayi kafin ya soma magana  alhamdullah hajiya, ta shiga wata Tara ciff and edd dinta yana nuna in the next 7 days baby will be ready to come to the world, yanxu form now ya kamata ta dage da exercise sosai zai taimaka mata sosai
 Alhamdullah I Alhamdulillah thank you doctor
Ammah ta fada tana murmushi.

***
Suna fitowa daga office din doctor motar suka shige, suna shiga ammah ta kunna motar suka bar cikin asibitin, kowannen su fuskanshi dauke da murmushin jin dadi, musamman ammah, amra dai mamaki ma ya hanata tunanin komai, she can t believe itace zata haihu, allah mai ko kenan.

Suna isowa gida amra ta wuce daki saboda wani irin ciwon baya daya riketa sosai, yau kwana biyar kenan tana fama dashi yazo ya dawo haka yake mata, abunda yasa bata fada ma doctor ba kuwa shine normallly tana yin haka tun kafin cikin ta ya tsufa so yanxu daya fara mata hakan sai tayi tunanin it s normal.

Karfe Tara nayi ammah ta shugo dakinta da sallama, a zaune ta taddata tana rike bayanta,  daughter Yadai
Ammah ta fada tana zama gefenta don yanxu bata wuce minti talatin bata leko ta ba,  ba komai ammah, na gaji ne kawai da zaman
 Toh ki miek ki zagaya gidan zai saki Insha Allah
 Tohm ammah
Tana kaiwa nan ta mike ta nufi hanyar futa daga dakin, kasa ta sauka ta zagaye parlor kafin ta hau sama, tana haurowa ammah na fitowa daga dakinta,  daughter Ina zuwa, Ay kin gama kwanan dakinki yanxu, wuce muje part dina
Kanta a kasa tace  Toh ammah
Part din ammah suka wuce inda ammah ta bata gadon ta gaba daya tace ta kwanta abunta, kwanciya amra tayi har barci ya kwashe ta,

Mikewa ammah tayi ta luluba mata duvet kafin ta wuce bathroom ta dauro alwala don kusan karfe goma na dare, alwala ammah tayi tana dauro wa ta fito daga toilet din ta shimfida sallaya ta fuskanshi kibla, ta dade sosai tana addau Har barci ya kwashe anan zaune.

Karfe uku daidai kuwa Tayi saurin bude idanunta don jin wani abu daya taho mata daga mararta lokaci guda, da kyar ta zauna akan gadon tana cije lebe ta,
Ta dade sosai a zaune tana danne abun da takeji, abun dai gaba gaba yakeyi don haka yana turnikota ta kwala uwar kara  innalillahi wayyo bayana
Cikin sauri ammah dake shirin sallame sallar daren da takeyi tana sallama ta mike cikin sauri ta karaso inda amra ke kwance, tana zuwa inda take taga ruwa na fita daga kasa ta don tayi sharkaf  subhanallah, daughter abun yazo gadan gadan
Cikin sauri amra ta dago ta kalli ammah  wayyo ammah bayana marana Zan mutu
 Shii babu abunda zai faru my dear Ina zuwa
Mikewa ammah tayi ta dauka wayarta kan dresser ta fara dialing number Aman. Aman dake barci karar wayarshi ta karade dakin, cikin sauri ya dauka wayar ya Kara a kunnenshi Ganin sunan ammah baima tsaya ya gama jin abunda take fada ba ya kashe wayar ya mike tsaye ya zari keys dinshi ya futo daga dakin, yana fitowa saiga ammah ta futo da amra, mayafin daga lulluba mata ma ya koma gefe, kasa suka sauko ahanakli inda amra ke kururu tana wayyo Zan mutu, babu abunda ammah keyi mata sai addua
 Kai Aman zo riketa bari na dauko delivery bag
Da sauri ya karaso ya rike amra dake faman dafe ciki.
Ammah na saukowa suka ta amshi amra kafin ya fuce ya fidda motarshi daga parking space.

Da taimakon Aman ammah ta saka amra a cikin motar, kusan karfe hudu kenan, suna shiga motar aman ya fushi mairam aguje suka bar compound din.
Yanda yake mugun gudu yasa suka iso in few minutes, suna zuwa Aman ya wuce reception ya fada masu akwai emergency nan zauka fito a gado Har wajen mota aka fidda amra aka saka ta Har lokacin hannunta na cikin na ammah  wayyo ammah Zan mutu kawo take fada
 Bazaki mutu ba daughter, Allah ya sauke ki lafiya
Agaggauce aka shige da amra cikin delivery room inda ammah da Aman suka kasa sukuni hankali su a tashe, da kyar Aman yasamu ammah ta zauna ya dunga tausasa ta saboda ciwon zuciya ta.

Suna nan zaune Har wajen karfe biyar shuru, awa saya da rabi kenan, at that point hankalin ammah ya gama Tashi sosai, babu abunda yake sai rokon Allah ya kawo ka amra sauqi.
Suna nan zaune saiga doctor ya fito tare da nurse fuskansu dauke da murmushi, mikewa ammah tayi tare da Aman sukayi saurin karasowa inda doctor yake, hannu ya miqa ma Aman don Duk a tunanin shi shine mijin amra, yana Mika mashi hannu yace  congratulations sir, ta haihu lafiya, the mummy and the babies are perfectly fine
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke atare nan ammah tace  were she zamu iya ganinta?
 Yea zaku iya but kudan bamu minti goma a gama gyarasu, don Ana gyarata.
Cikin zumudi ammah tace  Alhamdulillah alhamdullah, don ita ta amra ma take kawai don lokacin da take ce mata zata mutu ba karamin tashin hankali ta shiga ba.
After like 10min saiga nurse ta fito  Ma zaku iya shugowa, mun kaita recovery ward
Nan nurse tayi masu jagora jikin ammah Har bari yakeyi tana son zuwa Ganin amra da abunda ta haifa don doctor bai fada masu ba.
Nurse dince ta bude dakin ahanakli, tundaga nesa ammah ta hangota tana sanye cikin gown din marasa lafiya hannunta biyu rike da towels, nan take ammah ta soma hawaye Har tana neman faduwa kasa, nan Aman ya tallabota Har suka karaso dakin, ammah na karasowa tayi turus ta tsaya gaban gadon, gaba daya kafafunta Gaza daukanta sukayi nan take ta zube a kasa tayi sujjada tana dagowa ta daga hannu, it was a very emotional moment Aman ma kasa dauke idnaunshi yayi akan amra da babies dun dake gabanta ta rike guda biyu a hannunta sai guda daya akan gadon, dukda bak ga fuskansu ba but ya hango cute hannayen yaran farare tass, da sauri ammah ta mike ta karaso gabanta ta shafa fuska ta ta sumbace ta. Ammah na kuka amra na kukan murna, gaba dayansu aka rasa wanda zai taddashi wani  barakallah daughter Allah yayi maki albarka, Allah ya Raya mana su  abunda ammah ke fada kenan kafin ta saketa ta koma wajen babies din, takowa Aman yayi ya dauki wanda ke kwance akan gado while ammah ta rike daya amra ma ta rike daya, nan take ammah ta dunga jeroma yaran kisses tana hawayen farin ciki, suna cikin wann moment din saiga doctor ya shugo yana shugowa yayi congratulating dunsu tare da shaida masu gender na babies din,  hajiya daman kince kyautar Allah irin wannan ba a yi mashi shishigi, madam ta samu triplet 2 boys and a baby girl
 Allahu akbar ammah tayi kabbara tana gamawa ta juyo ta kalli doctor  hajjin bana dakai za aje doctor
 Thank you so much ma thank you!! Abund adoctor ke fada kenan,  anjima zamu sallameta Insha aallah, madam is brave, bamu taba tsammanin hakan ba,
Godiya sosai ammah tayi mashi kafin ya fuce ya barsu suna kukan murna&
Kallon babies sun Aman yayi yace  ammah naga suna kama dake
Dariya sukayi gaba dayansu inda ammah ta kalli babies sun for the countless times tace  gaba dayansu babu wanda yake kama dani, wannan ubansu suka dauko gaba Dayan su, kaga nan ta fada tana nuna mashi wani dan mole din kumatunsu su duka don identical triplets ne,  kaga wannan mole din, irin na babansu ne sal hancinsu irin na mamansu skin dinsu irin na babansu, kai ni I m jealous ma, gaba daya mazajen Nawa basu dauko mamansu da yawa ba
Dariya sukayi gaba dayansu daga ammah Har amra dake dan cije lebe don Har lokacin tana dan jin zafi a wajen donma basu yi mata stitches ba.


Nnamdi ezikiwe international airport abuja& ..
Karfe biyar daidai na asuba sukayi landing a international airport din abuja,
Sir general Amar taura&
Ahankali ya fara saukowa daga cikin jet dinshi Sanye yake da kakin sa na sojoji, yana saukowa ya shakur iskan Allah, garin yayi dan duhu don gari bai gama wayewa ba, ahankali yake tafiya majestically Duk da agajiye yake, cikin motar da aka tanadar masa anan airport ya shige nan driver ya jaa shi sai gida.
Tunda yayi relaxing bayanshi a cikin motar ya lumshe idanunshi, as he promised ammah suna gama operation zai dawo gida, hakan kuwa ta kasan don suna gamawa baima koma uae ba ya taho airport ya shige jet dinshi.
Ya rame sosai wanda dalilin harbinshi da akayi a kafada wajen operation din.
Parking din da driver yayi ne yasa shi dawowa daga tunani daya tsunduma, bude idanunshi ya fara yi ahankli nan take gabanshi ya fadi babu dalili, ciwon dake cinshi a zuciya yana dannewa ya dawo sabo tunawa da yayi da ita, fadin irin kewarta da yayi cikin watannin nan bata lokaci ne, da ita yake kwana da ita yake Tashi kullum,

Driver ne ya bude mashi kofa don haka ya saqalo kafafunshi ya fito, yana fitowa yace  thanks tare da wucewa cikin gidan don gari ya soma haske, yana karasawa wajen entrance baima tsaya knocking ba ya Danna pins ya bude kofar ya shige ciki, futilun kasan Duk a kashe suke don haka ya tabbatar mashi da basu Tashi ba, daman abunda yake so kenan shiyasa he wanted to surprise them, yana nan tsaye yana karema parlor kallon maid ta fito daga kitchen hannunta rike da mopper, tana karasowa inda yake dukda bata sanshi ba tace  good morning sir
 Morning ya amsata kai tsaye kafun ya wuce bedroom dinshi, yana shiga ya watsar ruwa yayi salla yabi lafiyar gado.

Su salima Ana ta shaka barci wajen karfe goma tana Tashi bayan tayi wanka dakin ammah ta fara wucewa donta gaisheta tana zuwa taga wayam don haka ta futo ta wuce na amra nan ma wayam, hankalinta ne ya dan Tashi don haka ta sauko kasa, nan ta tadda maid tana shirya dining  cinty ammah bata nan ne?
 Yes ma,
???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Sir Aman fah?
 Shima bai fito ba sai dai wani daya shugo daxu da safe maid ta fada
 Wani kuma? Waye wani? Salima ta tambayeta
 Wannan part din ya shige maid ta fada tana mata nuni da part sun amar, tana Ganin haka ta gane amar take nufi, wani irin dadi ne ya ziyarceta don haka tace  laa ya amar ya dawo,Toh ina su ammah suka tafi kenan
Bata gama tunanin ba saiga horn din motar su aman, cikin sauri salima ta fuce zuwa tsakar gida, tana tsayuwar aman na parking, cikin sauri ta karaso  yaa& yaa
Saurin guntse bakinta tayi Ganin ammah ta fito hannunta rike da babies guda biyu, bata gama mamaki ba saiga amra ta fito da baby daya a hannunta, jikinta ne ya soma bari  ammah& .. baby???? Babyn adda???
Wata uwar kara salima ta buga ta rungume amra tare da karban babyn hannunta nan take ta soma hawaye, ganin amra zata gaji a tsaye yasa ammah cewa  yarinyar kirki muje ciki ta huta
 Ammah I m so happy ya Allah adda wannan babies dinki be wayyo Allah na

Cikin gidan suka wuce gaba dayansu inda ammah tace su taci sama gaba dayansu, wucewa sukayi nan aman ya wuce bedroom dinshi shima.

Suna hawa sama salima ta amshi sauran babiea din, fadin irin farin cikin da yake ciki bata lokaci ne  Alhamdulillah double celebration ammah, ya amar ma ya dawo
Da sauri ammah ta kalleta  yaushe ya dawo,
 Maid tace da asuba ya shugo yana bedroom dinshi
Murmushi ammah tayi tana hamdala kafin ta kalli amra data Sunkuyar da kanta, gaba daya mood dinta ya sauya  Alhamdulillah lallai we have double celebration kam, yanxu daughter ki kwnata ki huta ko,
 Tohm ammah
Kallon salima ammah tayi tace  yarinyar kirki daukan min baby wannan mijin Nawa ni bari na rike amaryar dada da Dayan mijin nawa, mu bata wuri ta samu ta dan runtsa 
Mikewa sukayi atare suka bar amra ta kwanta nan take barci ya kwashe ta.

Suna fitowa ammah ta kalli salima,  muje kasa,
Cikin zumudi salima tace  ya& Muhammad
 Shii ammah tayi amra nuni kan tayi shuru, ahankali suka fara saukowa kasa suna saukowa suka wuce bedroom dinshi direct, ko Ina a kashe sai karar ac daya kunna, dakinshi suka wuce direct inda salima taso yin sallama nan ammah ta ce mata tayi shuru har suka karasa bakin gadonsa yana nan kwance cikin duvet ya rufe jikinshi sai fuskansa dake a bayyane, wani irin dadi ne ya ziyarci ammah yau ga Muhammad ga yayan Muhammad, suna karasowa gaban gadon ammah ta zauna a gefenshi har lokacin baby no 1 da baby no 2 na hannunta while salima na rike da baby no 3.
Hannu ammah ta dan saka ta shafa fuskanshi tana murmushi, dan juyawa yayi kamar zai farka don barcin yayi nisa sosai,  son!!!
Kamar daga sama yaji voice din ammah. Ahankali ya soma bude idanunshi, da kyakyawar fuskar ammah yaci karo da yake hawayen farin ciki tana murmushi, saurin mikewa yayi yana kokarin goge idanunshi da sukayi jaa alamun barci bai sakeshi ba  son& . Ammah ta sake fada
Dan dagowa yayi don baima Lura da abubuwan dake hannunta ba sai fuskanta daya kafe da idanu yana Ganin hawayenta
Hannunta biyu ta daga ta Dora mashi su duka akan laps dinshi, da sauri ya waigo ya sauke idanunshi akan& & ..
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!!
Unedited page& .
Hankali atashe amra ta jita a sama babu zato babu tsammani ya dagata har lokacin bakinshi na cikin nata, yanda ya shige tsakankanin kafafunta yasata kankameshi hankali, tasan duk abunda zatayi bazata taba iya kwatan kanta ba daga hannushi ga tashin hankalin da take ciki na yanda ya yake kissing lips dinta kamar mayuwacin zaki,
Bangaren goga kuwa kasa controlling kanshi yayi don tunda ya matso kusa da ita yayi perceiving kamshin ta yaji gaba daya kamar ana connecting jikinshi da nata, kasa hana kanshi daga abunda yake yi yayi saima kara zurfafa abun da yayi, tunda yakai bakinshi cikin nata kuwa komai ya dauke mashi diff, hes so much enjoying it, ganin tsayuwa yana neman gagarar shi yasa ya riko ass dinta dakyau ya nufi gadonshi da ita, ahankali ya kwantar da ita tare da yi mata runfa, amra najinta a akan gadonshi da yanda yayi mata runfa yasa hankalinta tashi sosai don har yanxu memory din first haduwanshi da ita bai goge ba daga kwakwalwarta, she can vividly recal lokacin da yanda tasha wahala sosai a hannunshi, cikin tashin hankali da tsoro ta fara bugunshi, tana son yin kuka ya qi bata daman hakan don yayi gumming bakinshi da nata, bai damu da yanayin data shiga ba haka ya fara cukwikwiyata yanda yaga dama, kwata kwata baiyi gigin cire mata rigar jikinta ba saida yayi mai isarsa kafin ya kyale ganin yana neman jefa kanshi inda bazai iya fitowa ba indai ba samun abun yayi ba.
Adaddafe ya mike ya wuce bathroom ya sakarma kanshi ruwan sanyi, tunda ya tsaya gaban shower din ya runtse idanunshi shi kadai yasan irin wahalar da yake sha, ya dauka kusan awa guda a cikin shower din.

Tunda ta runtse idanunta bata budeba har ya shige bathroom, ta dauka kusan minti talatin tana hawaye akwance, he was never gentle ko kadan,mikewa zaune tayi da kyar ta lalubo hijabinta ta zura, haka ta zauna daga gefen gadon nashi ta raqube, saurin taba lips dinta tayi jin yanda yayi suntum.
Tana nan zaune ya fito daure da towel akugunshi, hannunshi rike da karamin towel yana goge wuyanshi, kallon ta yayi ganin yanda ta raqube a gefe kafin ya kauda kanshi gefe.
Cikin natsuwa ya shirya cikin pjs dinshi, anatse ya tako gaban switch ya rage lights din dakin kafin ya wuce gefen gadon yayi kwanciyarsa tare da janyo duvet dinshi.
Tunda ya fito harya shriya ya rage lights din dakin har ya kwanta bata dago kanta ba, gaba daya ta rasa me zatayi, shiko tunda ya juya mata baya bai sake waigowa ba, barcin ma kaurace mashi yayi gaba daya
Tana nan zaune har kusan karfe biyun dare, tsoron kwanciya kusa dashi y agama cika ta ga gyangyadin da takeyi.

Karfe biyar daidai ya bude rinannanun idanunshi alamun barci bai ishesa ba, mikewa yayi tsaye yayi miqa kafin ya janyo bedroom sleeper dinshi,ya nufi hanyar bathroom, cikin yan mintuna qalilan saigashi ya fito, agurguje ya zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin don an kusa tada sallah.
Bayan an idar saida ya tsaya yayi morning azkar kafin ya fito daga masjid, direct apartment dinsu ya wuce cikin kamewa, gaishesa baba mai gadi yayi bayan ya bude mashi kofa, yana amsawa ya wuce cikin gida, bai tsaya ko ina ba sai part dinshi.
Kai tsaye ya bude kofar yana hamma saboda baccin da bai ishesa ba don gaba daya baifi barcin awa biyu yayi ba aka kira sallah, yana karasowa tsakiyan dakin yayi turus ganinta kwance gefen gadonshi, gaba daya ta takure waje daya ta hade jikinta kamar mai tsoron wani abu zai sameta, karsowa yayi har bakin gadon ya zuba mata mayun idanunshi, kallon cute face dinta yayi hannunshi nade a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login