Showing 264001 words to 267000 words out of 381117 words

Chapter 89 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1972

 an gama, zaku niya tafiya 
Shuru mumy tayi tana mamaki, just like that an gama?, talatu ce ta kallshi ta aje mashi maqudan kudi tace   mun gode malam na zango 
Sallama sukayi mashi suka fito atare,kareema dai gaba daya hankalinta ba a jikinta yake ba, kallon takatu tayi tace   ban gane me tsohon nan ke nufi da an gama ba 
Kallonta talatu tayi kafin ta bude Jakarta ta janyo cingum ta wulla bakinta kafin tace   ayki ya tafi inda ya kamat yaje, ay an gama komai, da kanki zakizo ki bani labari 
Shuru dai mummy tayi bat ace komai ba har suka iso anguwarsu&


Abuja Nigeria& &
Yau sati guda Kenan, kullum madina ke zuwa wajen amra,da farko amra bata sake mata ba, ganin haka yasa madina ta fara janta da hira har suka shaku sosai cikin yan kwanakin, madina wayyaiyar yarinya ce, haifaffiyar garin sokoto ce aure ya kawota nan waje wajen Abuja har mujinta ya rasu, ya barta da yaya biyu,akwai wani program da akeyi na mata inda mata ke taimakon yan uwansu mata, ta hanyar basu jari da kudi da abubuwan da zasu dogara da kansu, ammah na cikin top member na cikin kungiyar inda take contributing sosai wajen taimakaw matan nan,anan ammah ta san madina,abunda yaja hankalin ammah ga madina shine,ta fita daban cikin sauran mutane, ita burunta kawai ayi sponsoring karatunta ba kamar sauran da suke neman aba su jariya ba, nan take ammah ta dauki nauyinta da karatunta, madina na ganin haka kuwa ta miqa yayanta wajen wan babansu don daman ba iya rikesu zatayi ba koda ta koma wajen iyayenta, cikin shekaru kalilian mdina ta gama karatunta na physiology harta fara aiki a cikin wani asibiti, inda ta samu wani bangare daban na sashen mata, har take yima mutane masu matsalolin aure counselling, duk wanna achievement din nata har yanxu she believe saboda ammah ne don kwata bata taba tunanin zata kai inda take ba ayanxu ba tare da taimakon ammah ba da suke kira da hajiya uwar marayu .

Yau Friday don haka sai wajen karfe hudu ta karso gidan don saida ta gama da office, lokacin data shugo ammah na zaune a parlor, cikin girmamawa madina ta karaso suka gaisa, nan ammah ke tambayarta any progree   ay hajiya daughter taki tana da wayewa sosai, tana daukan karatu ssoai  madina ta fada tana murmushi
  madallah, nasan bazaku bani kunya ba ay, haka nake so naji, allah ya taimaka yarinyar kirki  ammah ta fada tana murmuhsii
  ameen hajiya 
  kije saman yanxu ta haura  ammah ta fada tana kallon tv
Anatse madina ta mike ta hau saman, direct dakin amra ta wuce da sallama, amra dake sanye da riga da skirt tayi saurin juyowa jin muryarta   ?nty madinaaaa, sannu da zuwa 
Murmushi madina tayi ta karaso cikin dakin ta cire mayafinta tace   washh na gaji, yauwa student, ya zaman gida fatan ki fara bashi assaignment kema 
Shuru amra tayi tana jin kunya tace   anty madina its not easy oo, kinsan na maki bayanin komai 
Kama baki madina tayi tace   haba karki bani kunya mana mrs general 
Karasowa amra tayi har inda take zaune cikin nastuwa tace   hmmm anty madina Kenan wallahi bazaki gane bane, ahaka ma da nake zuwa dakin nashi bakiji kirjina ba 
Dariya madina tayi tace   banga laifinki ba wallahi, ni har yanxu mamaki nake ashe shine mujin naki?, dole kiji tsoro sister don wallahi jiya dana ganshi saida gabana ya fadi, yana da wani irin kwarjini sosai, saidai bari kiji na fada maki wani abu 
Madina ta fada tana kamo hannunta tace   kalleni kiga, sister ke macece, mace nada wani sirrin daraja, musamman irin ku, jibeki fah san kowa kin wanda ya rasa, wallahil azeem duk gigin kanshi zaki iya saukewa trust me and trust the process, 
Sauke ijiyar zuciya amra tayi tace   wallahi tsoronshi nake ji anty madina, kinga yanxu fah kamar ya kara tsanata, baya kallon inda nake kwata kwata, baya cemin komai har gaisuwata ya daina amsawa 
Shuru madina tayi tana sauraron ta kafin tace   wace irin gaisuwa kikayi mashi? Kinyi irin wadda na koya maki ko yaya? 
Sunkuyar dakai amra tayi tana dan murmurshi   gaskia anty madina nidai bazan iyaba wallahi  amra ta fada tana sunnar dakai
  kinji matsalarki Kenan wallahi, menene abun kunya adan hugging,kinga wallahi in baki cire kunya da tsoronshi ba wallahi zaki wahala 
Kallonta madina ta sakeyi tace   dear in tambayeki mana? Bakyason kiga kuna sakewa kedashi?, 
  ina& so  amra ta amsa ta jiki a mace
  then you have to make him know your existence, you have everything da namiji mai lafiya dai bazai iya kauda kai daga ganinki ba,kuma wallahi yanxu kiyi min alkawarin zaki cire duk wani tsoronsa daga ranki, ki saki jiki kiyi abunda ya kamata inba haka ba wallahi haka zaiyi ta maki kallon hadarin kaji, don yarigada ya dandana ki, inason ya haukace akanki ta yanda bazaiyi yan seconds b aba tare da yaji motsinki a kusa dashi ba 
  anty madina zan iya kuwa? Ni ina ganin kamar yafi karfina  amra ta fada ashagwabe
Dan buge mata bagi madina tayi tace   waya fada maki namiji yana fin karfin mace, musamman mace irinki, gaki da kayan alatu allah ya baki diri da komai, ga kyawun fuska gana hali duk kin hada ke kadai 
Dariya amra tayi ta kalleta   kai anty madina da zuzuta, yanxu me zaki buqata akawo maki? 
Dan dagiwa sukayi jin an bude kofa, daga nesa salima na hangosu tace   yanxu nasan zaku koreni, waima anty madina me kike koya mata ne? nima akoya min 
Hararata amra tayi tace   toh mara kunya, futa anan 
Dariya madina tayi tana kallonsu har salima ta fita tana cewa   ina wuni anty madina,  
Amsata madina tayi harta fuce tana kunkuni, maido da kallonta ga amra tayi tace   yauwa as I was saying,wallahi saikin dage damtse ki cire wannan tsoron naki fah, yanxu dai daga ina muka tsaya jiya?  ta fada tana kallonta& ..
Sun dade sosai inda madina ta tsatsarata akan yanda zata dunga tarairayarshi, itadai kawai tana jinta ne saidai tasan cewa shidai duk wannan ba lallai yayi aiki a wajenshi ba.
Sai wajen karfe shida na yamma madina tayi masu sallama ta wuce gidanta.

Yau amra da kanta ta sauko kasan ta dora dinner, nan salima ta sauko ta tayata tare da talatu, sai wajen gab da sallar magrib suka gama, da taimakon salima suka jera komai a dining, suna gamawa suka wuce sama atre gaba dayansu.
Wani sabon wanka amra ta sake ta sauya kaya zuwa doguwar riga a shape gown data fidda shape dinta sosai, atamfa ce Holland mai zanen flowers mai kyau, anyi mata dinkin stones tundaga sama har kasa yayi mata kyau sosai, feshe jikinta tayi da turaren ta masu sanyin kamshi kafin ta tada sallah, tana nan zaune aka kira sallah isha I tana idarwa ta danyi yan addu oi ta dan dade sosai a zaune kafin ta miqe ta zare hijab din nata ta wuce gaban gado ta janyo wayarta, ammah tasa an mata sabon sim card saidai bata da number dayawa a ciki daga na ammah saina haifa da Nadine ,suma duk numbers din nasu basa shuga, gashi tayi trying tura masu message shima baya tafiya, har social media din haifa saida ta shiga ta tura mata message thrug Instagram, shima shuru babu response, haka nan ta hakura saidai kullum saita duba Instagram dinta,
Yanxu ma zaman datayi duban Instagram din ta soma yi, ganin babu response yasa ta hakura kawai ta soma duban timline dinta,da sabbin followers dinta, tana cikin yan dube dubenta ta shiga wajen suggested followers, taga handle din amar, bata dauka shi bane ba don sunan dayayi using as   A..mar, kallon profile din ta soma yi ba tare da ta shiga ba don tabbatar da ko shi dinne, ginin picture din baya fita sosai yasa ta shiga cikin account din, nan take pictures dinshi sukayi appearing guda hudu ajere, samun kanta tayi da shiga cikin hoton don tabbatar da shi dinshi, first picture din a tsaye yake a safari da kundura a saka wani bakin glass gefenshi wani tattabara ne dayayi landing a kafadarshi ya juya yana kallon tattabar, yayi masifar kyau sosai a hoton don ita kanta saida ta shagala da kallon shi, hes looking so so cute and charming, haka ta sakankance wajen kallon hotunan nashi kaf har tayi liking day aba tare da saninta ba, saida salima ta shigo dakin tace   adda dinner  kafin ta danyi firgigi ta waigo tace   gani nan 
Atare suka sauko kasan , ammah ne kawai zaune kan dining gefenta salim, zama duk sukayi atare, cikin yan mintuna kalilina ammah tace   salima jeki kira yayanku  sanin wa take nufi yasa ta miqe a tsanake ta wuce dakin nasa, da sallama ta shiga har cikin dakinsa, azaune ta hangoshi ya doka tagumi abun tausayi, kallonshi tayi kafin ta karaso har inda yake kanta a kasa tace   dinner is ready ammah tace ka fito  dan dagowa da jajayen idanunshi yayi ya kalleta yace   ina zuwa 
Wani iri taji ganin yanda yanayinshi yake gashi yanda ya bata amsa ma yasa taji babu dadi harta juyata dawo tace   is everything okay with you 
Ay kamar jira yake ya juyo ya kalleta yace   youre asking me if everything is okay?i thought kince you don t care anymore, so why are you asig huh?  ya fada yana kafeta da idanu, wani irin rashi dadi taji saidai hakan baisa ta ji zata sauke kudurinta akanshi ba don haka tace   I just ask bawai don na damu bane 
Ataqaice ya bata amsa da   okay good 
Yana kaiwa nan ya juya mata bata, rike kugu tayi tana mamakin shi kafin tace   me yake nufi da hakan Kenan?daman nasan ba sona yake ba 
Yana gab da shiga bathroom ta dago murya a hasale tace   hmm namiji Kenan daman nasan ba sona kake ba fada kawai kake abaki 
Juyowa yayi gadan gadan jin abunda ta fada yazo gab da ita yace   are you kidding me?bayan kinyi neglecting dina yanxu kuma kina questioning son da nake maki?anyways laifina ne dana kasa moving on da rayuwata dama chan nike sonki ba sona kike ba so nima zanyi kokari na cireki araina  yana kaiwa nan ya fuce daga dakin ya barta tsaye hawaye na zarya a fuskanta, rai abace ya wuce dining din ya zauna, itama saida ta daidaita natsuwarta kafin ta fito daga dakin ta zauna
Abunci suka fara ci atsanake babu wanda yace tak sai karar cokula dake tashi,
  barka da dare ammah 
Da sauri duk suka dago don gaba dayansu babu wanda ya lura da karsowarsa har ya wuce mazauninsa, kallonshi da gefen idanu amra tayi kafin ta sauke kana
  yaushe ka dawo son, na dauka zaka kai dare yau ay  ammah ta fada tana sauke spoon din hannunta kan plate
  dazun na shigo  ya fada yana jan kujera ya zauna fuknshi na nan yanda take babu wasa
Duk gaishesa sukayi banda amra data tsaya dacin abunci nata saida ya zauna ta dan dago da fuskta dake kyallin hutu tace   barka da dawowa, ina wuni 
Atakaice ba atre daya kalleta bay ace   alhamdulillah 
Mikewa tayi ta tako har inda yake dab dashi sosai don yana jin kamshinta a hancinsa tace   what sould you like  yanda ta fada saida ya sashi dagowa ya mata kallon second biyar kafin ya sauke yace   any thing  & anatse ta soma juya mashi baya ta koma wajen warmers ta bude, tunda ta juya mashi baya ta soma takawa gabanshi ya fadi dammm, bayanta ya zuba ma idanu, ya kasa kaudawa, ammah dai tunda ta dago ta kallesu tayi saurin sauke idanunta ta cigaba da cin abuncinta, su salima kuwa daman su hankalinsu ba akansu yake ba, salim kam shi harya mike yabar dining din,
Saida ta zuba mashi yanda zai isheshi, white rice da kidney and liver sauce kafin ta tako har inda yake ta aje mashi tace   bismillah  bin bakinta ya danyi da kallo kafin yayi saurin kauda kanshi, daman juice yana daga dayan bangarenshi don haka daga gefe ta rankwafo ta zagayo da hannunta ta janyo glass jug din, ay tunda tayi hakan ya saki spoon din hannunshi kan plate din, saida ta janyo glass din ta matsa ya samu yajaa dogon nunfashi yana mamakin abubuwan da takeyi, da sauyin data yi cikin kwanaki, haka ta zuba mashi juice din ta tura gabanshi kafin ta koma mazauninta hankali kwance.

Anatse kowa yaci abunci har suka miqe su duka don daman sun kusa gamawa ya shugo dining din, ammah ce ta fara tafiya kafin salima follow by aman, amra dai bata dagaba haka zalika bata dago ta kalleshi ba shima bai kalleta ba saidai yana mamakin qin tashi datayi don ya lura da ta gama cin abuncin.
Saida y agama tsaf ya janyo tissue ya goge bakinsa kafin ya jayo glass cup din juice, tana ganin haka ta mike tsaye ta fara tattare kwanukan, saida ta kwashe duka harta dawo dining din yana zaune juice a hannunshi, takowa ta soma yi cikin takunta mai daga hankali ta karaso har inda yake tace   kana buqatan wani abun ne?  ta karashe tana kafeshi da idanu yanda ya kafeta itama, mamakin yanda take kallon cikin idanunshi yasa ya kasa cewa komi, at the same time bai dauke idanunshi akanta ba, saida tace   yaayaa?, do you need anything? 
Samun kanshi yayi da girgiza mata kai, tana ganin haka kuwa ta juya ta soma taku daidai kamar mujiya, yanda take tafiya kamar bazata taka kasa ba harta nufi stairs,ta haura saman abunta, baki asake ya dunga kallonta harta wuce saida ta fuce mashi daga gani yadan yi tsaki ya miqe yabar dining din.

Kamar kullum saida tayi wanka ta goge jikinta da turaren da ammah kafin ta janyo nighties dinta da ammah ta saya mata kwanaki wanda ta jingine su saboda kunyar sasu da take yi, yanxu kuwa maganr anty madina da karfin gwiwa da take bata yasa take jin zatayi kokarin rage kunyar da takeyi,
Janyo wata milk night gown tayi,rigar straight ce kamar ta sirara, hannun rigar sirri, gaban rigar anyi v neck don cleavages dinta ya fito sosai,koda tasa rigar saida ta tsaya ta karema kanta kallo, she looks so breath taking, tayi masifar kyau sosai ba kadan ba, murmushi kawai tayi gabanta nadan faduwa tunawa da maganr da madina tayi mata akn cewa ta rage kunya idan tana tare dashi ta saki jikinta ta daina jin tsoronshi kwata kwata, da kyar ta tattaro kuzanrinta ta kalli kanta tace   an y azan iya kuwa 
Chan kuma ta kara kallon kanta   why not, kefa macece, dole ki tsaya tsaye akanshi inba haka ba haka zaki kare rayuwarki cikin kunci 
Saida ta jaddama kanta tare da hana kanta tsoron komai kafin ta janyo hijab dinta da wayrta ta tare da sleeping mask dinta ta fuce anatse, tana fitowa taci karo da salima tana haurowa hannunta rike da cereal, kallonta amra tayi tace   kedai da ciye ciyen dare 
Tabe baki salima tayi tace   ina zuwa adda  ta fada cikin zolaya don tasan duk nuqu nuqun da takeyi tare da madina harma da ammah, banza amra tayi mata tace   ruwan da zan dauko ma saina fada maki 
Dariya kawai salima tayi tace   mu kwana lafiya addan mu 
Da harara amra ta bita harta shige dakinsu, amra na ganin ta shige ta sauka kasan cikin nastuwa, bata tsaya knocking ba ta shige part din nashi, saida tasan tsaya a sitting room ta karema ko  ina kallo kafin ta wuce bedroom din kai tsaye, da sallama ta bude kofar bedroom din, zaune yake baking ado ya dafe kanshi dake mashi wani irin masifaffan ciwo, takowa tayi gefen gadon inda take kwanciya ba tare da ta kalleshi ba, tunda ta shigo kuwa yaji kamshinta daga zaunen da yake, tana ganin haka kuwa ta kauda kanta gefe ta cire hijab dinta ta ta aje kusa da ita don dashi take luluba, tunanin ko me yasameshi ya dafe kanshi takeyi tan nan zaune tajiyo muryanshi ahankali   bude side drawer ko miqa min magani 
Anatse ta miqe tsaye ta janyo drawer dake gefenta ganin magunguna da yawa yasa tace   wanne za a dauko 
  panadol  ya bata amsa, tana jin haka ta gane kanshi ke mashi ciwo, don haka ta dauko Panadol din ta tako inda yake ta mika mashi,   gashi 
Dan dagowa yayi ya soma kallonta tundaga kan yatsun kafunta zuwa fuskanta, saurin runtse idanunshi yayi don baiyi tunanin ganinta a haka ba, itako daman da gayya tayi haka dukda tsoron daya cikata,ganin yaqi karban maganin ya kafa mata idanu yasa tace   ga maganin 
Kauda idanunshi yayi ya miqa hannu don karban maganin, nan take ya hade hannunta da maganin, wani irin shock yaji da sauri ya dago ya kalleta tare da karban maganin, tana ganin haka ta wuce gefen bedside ta dauka bottle water ta mika mashi, karba yayi ba tare da ya kalleta ba haka zalika baisha


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login