Showing 342001 words to 345000 words out of 381117 words

Chapter 115 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2036

kirjinshi, barcinta takeyi peacefully kamar yar baby, fuskanta tayi fayau gwanin ban tausayi, lebenta yayi jaa sosai saboda yanda ta turo bakin nata,ya dauka kusan minti goma a tsaye yana kallonta, kwata kwata bai san ya shagalta ba,kauda kanshi yayi gefe tunawa da wani abu da yayi kafin ya maida kallonshi zuwa gareta,   ke! Kee! get up 
Afurgice ta bude idanunta tare da mikewa zaune don kwata kwata batasan lokacin da barci ya kawashe ta akan gadon nashi ba,
Adaburce ta sauke kanta kasa kamar mara gaskia, yana ganin haka yace   ke sai an tasheki sallah ne? 
Saurin girgiza kanta tayi ta miqe tsaye ta nufi hanyar futa daga dakin, tana futa ya danyi yar tsuqa ya rage kayan jikinshi ya kwanta.

Tana futa daga dakin ta wuce sama abunta, tana shiga dakin ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya, sai alokacin ta samu natsuwa, cire hijab din jikinta ta fara yi don dashi ta kwanta kafin ta wuce bathroom ta dauro alwala, cikin natsuwa ta fito ta hau kan sallaya ta tada kabarrar sallah, tana idarwa ta miqe tabi lafiyar gado don wani irin barci ne ke fusgarta sosai don sallar ma da kyar ta samu ta idar saboda jirin dake neman dibanta.

Zama ammah tayi bakin gado tana mamaki hali irin na amar, don lokacin da amra ta fito daga dakinshi akan idanun hakan ya tabbatar mata da korota yayi Kenan da asubar fari, daman saida tayi tunani zai korota don haka ta sauko kasan don ta tabbatar ko a cikin dakin ta kwana,futowan amra ya tabbatar mata da yayi halin nashi kenan, amra dai bata lura da itaba don a furgice ta fito harta haura sama zuwa daki.
Sauke nauyayyaiyar ajiyar zuciya ammah tayi tana mamakin hali irin na amar,yana da kafiya sosai, mamakin yanda ma kwata kwata amra bata gabanshi take, babu wanda zai kalli yarinyar ya kauda kai indai lafiyayye ne, dole saita sa idanu sosai akansu musamman amra data lura da yarinta sosai a tattare da ita.

Wayarta ta jawo ta yi dialing wata number datayi saving da madina marrage cousellor,   assalam alaikum likitar mata diyar arziki how are you 
  waalaikum salam hajiya ina wuni  matar ta fada daga chn bangare
  lafiya lau dear ya ayyuka da fama da mutane  ammah ta fada tana murmushi
  alhamdullah hajiya, kune da fama da mutane, yawan alkairin da kike mana saidai muyi fatan allah ya saka maki da alkahiri ya raya maki zuriyya  matar ta fada sounding very respectful daga chan
Murmushi ammah tayi kafin ta cigaba   haba yarinyar kirki ya kamata ki daina godemin, banyi maki komai ba ay 
  hajiya kinyi min komai wallahi dole nagode maki, kece sandiyar karatuna harna zama abunda na zama ayanxu, babu abunda zance sai godiya allah ya kara lafiya da tsawon rai 
Murmushi ammah tayi tana jin dadin yanda gaba daya shes surrounded with positive mutane, nunfasa ta danyi kafin tace   ina neman taimakon ki madina 
Da sauri wanda ammah ta kira da madina tace   babu abunda zaki nema a wajena da bazaki samu ba insha allah hajiya, 
  akwai diyata danake so ki koyama karatun ku na matan zamani, yarinya ce karama  ammah ta fada tana sauraron ta
  okay, tana da aure ne?  madina ta tambaya daga chan
  eh, inason ki koya mata duk wani abu daya kamata ta sani game da rayuwa da miji  ammah ta fada tana sauraron ta
  ba damuwa hajiya, zanyi kokari insha allah, zan duga zuwa ma har gida  goiya sosai ammah tayi mata kafin ta kashe wayar.


Bari mu leka katsina& ..
Rayuwa juyi juyi, yau idan kaga daddy da iyalanshi saika tausaya masu, abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda mutuwar inna wato mahaifiyarshi, tun bayan rasuwarta abubuwa sun dan raga masu sosai, don yanxu buga buga daddy yake yi yana dillanci, kaf anguwar nan babu wanda bai shede sa da damfanra ba, haj kareema dai itama taga sauyin rayuwa , ada chan itace da saka gwala gwala da manyan kaya, ayanxu kuwa komai ya juya masu baya, ya muhammd yana kokari sosai wajen taimaka masu da kudi duk wata, duk sanda yaso ya dawo Nigeria haka haj kareema zata hanashi saboda idan yazo ma karar dashi dasuyi kaff, khady dai taqi auruwa don yanda zance ke yawo kamar ruwa haka anguwar su ta dauka da tana dauke da cutar aids, asma kuwa tana nan tana fama da kafa daya, hajiya kareema data kallesu sai kuka don ko a mafarki bata taba kawo cewa zasu koma haka ba ita da iyalanta, zagi dai babu irin wanda dadi bayasha a wajenta, har takaiga zaman kananun yayanta kawai take a gidan, don badan sub a da tuni ta tattara ta kara gaba itama, ana cikin wannan zama allah ya hadata da wata hatsabibyar mata talatu mai gwajo uwar mata, a kasuwa suka hadu inda haj kareema taje sayan kayan miya, nan take kuwa suka hade, sai gashii allah ya hadasu anguwa dayaa ba tare da sanin su sai daga baya, haka talatu ta dunga shiga jikin haj kareema harta karanci rayuwar haj kareema da yanda take da kwadayin kudi da rayuwa don haka ta fara zugata kan shiga hanyar samun kudi irin yanda takeyi itama, da farko haj kareema bata fahimci talatu ba don duk a tunaninta sana ar gwanjo da talatun ke fakewa dashi a matsayin sana ar ta, shi take nufi, saidaga baya ta futo mata muraran ta mata bayanin yanda take samun kudi tana biyan buqatar kanta basai ta jira wani ya mata ba wato kawalci da bin manyan maza masu kudi dattijai a waje.
Da farko mummy batayi shaawar shiga harkar da talatu tayi mata introducing ba saidaga baya ta amince saboda wulaqancin da daddy yake mata, musammad idan muhammd ya tura masu kudi haka zai je ya akshesu abanza a sunan investing kudin yake, haka zasu wuni wani lokaci babu abuncin kirki a gidan, yaranma yanxu government school suke zuwa, khady ce kadai a gabanta wadda yanxu itama ta saduda ta koma yin sana ar sayarda sayarda takalma wanda jarin ma a wajen sabon saurayinta ta samu, shima dai saurayin dan jagaliya ne don ba auranta zaiyi ba. Change of environment yasa kananun yaranma suka koyi rashin kunya da zagi, idan kaji su jalal suna kuza ashariya saika rike baki, don babu wanda suke ragama har da iyayen nasu.
Hajiya kareema dai pressure din wahalar rayuwa yasa tayi diciding bin shawarar kawarta talatu wanda ayanxu ta kasance aminiyarta, tunda ta shiga harkar kuwa sauyi yazo masu a gidan, abunci baya yanke masu safe yamma da dare, alhaji mustpah dai bait aba tambayrta inda take samu ba don shima rakubewa yayi karkashin inuwarta ana ci dashi.
Akwana a tashi saiga hajiya kareema da ciki, aranar data gano tana da ciki hankalinta ya tashi sosai don haka ta fara laluben wayar talatu, rininging daya biyu talatu ta dauka   yar gari any aba batan hanya kikayi ba, tun ranar dana hadaki da wannan alhajin ban kara jin motsin ki  
Cikin furgici haj kareema ta mike tna zarya adakin tace   haba tlatu, inata kiranki tun jiya bakya dauka, kinsan irin damuwar danake ciki yanxu kuwa
  toh ay gashi nan na dauka ya ake ciki naga hankalinki ya tashi sosai meke faruwa?  talatu ta fada tana sauraronta
  talatu ciki, ciki ya shiga na shiga uku  kareema ta fada tana duban kofar shugowa dan dakin nasu
  shine kike wani tada hankali, amma dai kema wallahi kara wata karamar yarinya wallahi,  talatu ta fada tana dariya
A harzuke mummy tace   ke ba dole hanklai na ya tashi ba, ke kinsan wannan cikin shege ne, kuma yanxu da aurena da tsufana aka ganni da cikin shege akwai damuwa 
Da sauri talatu ta tari nunfashinta   waye zai gane? Nifa matsala dake wani lokacin kamar baki da kwakwalwa wallahi, ki gane mana 
Dan shuru haj kareema tayi kafin tace   ance maki banyi wannan tunanin bane,bazaiyuwu na barshi a matsayin na mijina ba saboda yau mun kusa wata rabonda mu kwanta tare 
Wata bazawarar dariya talatu tayi tace   and so what?, yanxu dai tukunna zubarwa zakiyi ko ajeshi zakiyi 
  zubarwa zanyi mana me zanyi dashi me zanyi da wani dan shege yanxu kuma  kareema ta fada
  ay shiknan, bari zan kira likita na saimuje kobe a cire shi  talatu ta fada
Sallama kareema tayi mata kafin ta kashe wayar.
Tana aje wayar khady ta shugo fuskanta dauke da takaicin abunda tajiyo ma kunnenta, a furgice mommy ta mike daga zaune ta dago ta kalleta, itama kallon nata tayi yanda take kallonta tace   chapp yanxu ke mummy cikin shege kika kwaso?,lallai ma, kullum kece meyi mana surutun kinyi asarar haihuwa, mu kasa mu kasa, munje munyi iskanci ashe kema shi kikeyi, koda yake wallahi alhakin marayun da kika&  
Afurgice mummy ta buge bakinta tace   a gidan ubanwa kikaji wannan batu 
Kallonta khady tayi tace   wanne daga ciki? Na cikin shegen kona su salima da kika sa azubar dasu saboda rashin imani 
Kwasheta kareema tayi ta mari tass, ta nuna ta da dan yatsa tace   dan ubanki ina matsayin uwarki kike fada min Magana haka  kallonta khady tayi babu kunyar idanu tace   hmm mummy Kenan, borin kunya ne ke damunki zanyi maki uzuri,amma wallahi allah saiya tambayeku keda dadi, duk halin da muka shiga ku kuka jawo mana, kuma bazan fasa fad aba wallahi alhakin marayun nan ne ke binmu mu duka shiyasa duk muka tsiyace,  ta kareshe tare da fucewa daga dakin tana hawaye, tana fita mummy ta dafe kirji tana innalillahi   wannan wace irin masifa ce na shiga uku ni kareema 
Washe gari haka mummy ta fuce daga gidan afurgice ba tare da sani kowa ba, direct asibitin da talatu ta bata address ta shige,a reception ta tadda talatu,saida suka gaisa kafin su wuce office din likitan, tunda suka zo talatu ta fada mashi buqatarsu, ba tare da bata lokaci bay ace   ayki kam in yanxu kukeso za ayi, saidai sai kun cika min hannu, bayan wannan dole sainayi mata scanning da yan gwaje gwaje saboda bana son asamu complications don wannan aikin kusan yana da risk sosai,  atake talatu tace   haba magaji baka da case 
Wata irin dariya ya kyakyace kafin yace   dillaliyar yan gwanjo ina yinki sosai 
Saida suka aje mashi kudinshi kafin ya buqaci mummy ta kwanta don yin scanning,anatse ya soma duba cikin nata, gama daya satinshi shida don haka yace   ayki zai yuwu don cikin baiyi gir&   dan shuru yayi yana gwalo idanu yana duban mahaifarta da kyau, ganin yayi shuru yasa takatu cewa ?adai 
Nunfasawa yayi ya dubesu duka yace   gaskia akwai matsala, cikin nan bazai zubu ba dole sai an haife shi,mahiafarta is weak, kuma kunsan cire ciki kamar forcing dinshi ne don ya futo bawai kamar bari bane don haka ayki bazai yuwu ba gaskia, idan kuwa akayi zata iya mutuwa 
Hankali atashe mummy tace   na shiga uku, yanxu babu yanda za ayi ya fit aba tare da wata matsala ba 
Dariya likitan yayi tace   haba hajiya lokacin da kike kwasar dadi bakiyi tunanin ciki ba sai yanxu, ai kawai kiyi hakuri ki haife shi don wallahi zaki iya mutuwa idan aka ce za ah cire shi don dole 
Mummy dai karamin hauka ne batayi bad n hankalinta ya tashi sosai, yanxu ya zatayi da wannan masifa data tunkarota, babu abunda yafi tayar mata da hankali sai tunawa da daddy, tabbas shizai fara tona mata asiri don sunfi wata hudu basu kwanta ba,tunda suka fito daga asibiti mummy ke kuka har suka shiga napep, ganin haka yasa talatu cewa   kewai kukan me kikeyi kamar tashin kiyama?, 
Cikin jin haushin talatu ta soma Magana   haba talatu, ay dole kice haka tunda ba kece a cikin situation din dana tsiinci kaina a ciki ba 
   toh ay naga kin tsaya kina bata ma kanki lokaci kina kuka ne, inma wanchan maholon mijin naki kike tsoron karya gane akwai yanda zamu toshe bakinshi, bazai taba cewa komai ba akan wannan  
Cikin jin dadi mum kareema tace   dan allah ki fada min,ya za ayi kenan 
Murmushi kawai talatu tayi tace   ki kwantar da hankalin ki indai kina da talatu bakida case 
Nan take ta fada ma mai napep inda zai kaisu, cikin yan muntina kadaan sai gasu cikin wata anguwa, saukesu mai napep yayi suka sallameshi suka wuce, saida suka danyi tafiya mai nisa har suka wuce wata maqabarta kafin su shige wani gida dake kallon maqabartar, da baya baya talatu ta shiga gidan, mummy na ganin haka itama ta shige,babu komai a cikin gidan sai katon fili dake sagaye da bishiyu, sao tsakiyan bishiyar wani tsoho zaune akan taburma, anatse suka karaso suka zauna gabanshi, talatu ce ta fara gaishesa kafin ta nuna kareema tace   malam na zango, wannan kawata ce, ga matsalolinta& ..  nan talatu ta fada mashi komai tare da buqatar da suke nema daga wajenshi, dago wa yayi ya karema karima kallo, kamar yanda itama take kallonshi, tsoho ne tukuf don har furfura ta gama cika fuskanshi, wata yar dariya yayi irin ta tsoffi yace   an gama, zaku niya tafiya 
Shuru mumy tayi tana mamaki, just like that an gama?, talatu ce ta kallshi ta aje mashi maqudan kudi tace   mun gode malam na zango 
Sallama sukayi mashi suka fito atare,kareema dai gaba daya hankalinta ba a jikinta yake ba, kallon takatu tayi tace   ban gane me tsohon nan ke nufi da an gama ba 
Kallonta talatu tayi kafin ta bude Jakarta ta janyo cingum ta wulla bakinta kafin tace   ayki ya tafi inda ya kamat yaje, ay an gama komai, da kanki zakizo ki bani labari 
Shuru dai mummy tayi bat ace komai ba har suka iso anguwarsu&


Abuja Nigeria& &
Yau sati guda Kenan, kullum madina ke zuwa wajen amra,da farko amra bata sake mata ba, ganin haka yasa madina ta fara janta da hira har suka shaku sosai cikin yan kwanakin, madina wayyaiyar yarinya ce, haifaffiyar garin sokoto ce aure ya kawota nan waje wajen Abuja har mujinta ya rasu, ya barta da yaya biyu,akwai wani program da akeyi na mata inda mata ke taimakon yan uwansu mata, ta hanyar basu jari da kudi da abubuwan da zasu dogara da kansu, ammah na cikin top member na cikin kungiyar inda take contributing sosai wajen taimakaw matan nan,anan ammah ta san madina,abunda yaja hankalin ammah ga madina shine,ta fita daban cikin sauran mutane, ita burunta kawai ayi sponsoring karatunta ba kamar sauran da suke neman aba su jariya ba, nan take ammah ta dauki nauyinta da karatunta, madina na ganin haka kuwa ta miqa yayanta wajen wan babansu don daman ba iya rikesu zatayi ba koda ta koma wajen iyayenta, cikin shekaru kalilian mdina ta gama karatunta na physiology harta fara aiki a cikin wani asibiti, inda ta samu wani bangare daban na sashen mata, har take yima mutane masu matsalolin aure counselling, duk wanna achievement din nata har yanxu she believe saboda ammah ne don kwata bata taba tunanin zata kai inda take ba ayanxu ba tare da taimakon ammah ba da suke kira da hajiya uwar marayu .

Yau Friday don haka sai wajen karfe hudu ta karso gidan don saida ta gama da office, lokacin data shugo ammah na zaune a parlor, cikin girmamawa madina ta karaso suka gaisa, nan ammah ke tambayarta any progree   ay hajiya daughter taki tana da wayewa sosai, tana daukan karatu ssoai  madina ta fada tana murmushi
  madallah, nasan bazaku bani kunya ba ay, haka nake so naji, allah ya taimaka yarinyar kirki  ammah ta fada tana murmuhsii
  ameen hajiya 
  kije saman yanxu ta haura  ammah ta fada tana kallon tv
Anatse madina ta mike ta hau saman, direct dakin amra ta wuce da sallama, amra dake sanye da riga da skirt tayi saurin juyowa jin muryarta   ?nty madinaaaa, sannu da zuwa 
Murmushi madina tayi ta karaso cikin dakin ta cire mayafinta tace   washh na gaji, yauwa student, ya zaman gida fatan ki fara bashi assaignment kema 
Shuru amra tayi tana jin kunya tace   anty madina its not easy oo, kinsan na maki bayanin komai 
Kama baki madina tayi tace   haba karki bani kunya mana mrs general 
Karasowa amra tayi har inda take zaune cikin nastuwa tace   hmmm anty madina Kenan wallahi bazaki gane bane, ahaka ma da nake zuwa dakin nashi bakiji kirjina ba 
Dariya madina tayi tace   banga laifinki ba wallahi, ni har yanxu mamaki nake ashe shine mujin naki?, dole kiji tsoro sister don wallahi jiya dana ganshi saida gabana ya fadi, yana da wani irin kwarjini sosai, saidai bari kiji na fada maki wani abu 
Madina ta fada tana kamo hannunta tace   kalleni kiga, sister ke macece, mace nada wani sirrin daraja, musamman irin ku, jibeki fah san kowa kin wanda ya rasa, wallahil azeem duk gigin kanshi zaki iya saukewa trust me and trust the process, 
Sauke ijiyar zuciya amra tayi tace   wallahi tsoronshi nake ji anty madina, kinga yanxu fah kamar ya kara tsanata, baya kallon inda nake kwata kwata, baya cemin komai har gaisuwata ya daina amsawa 
Shuru madina tayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login