Showing 30001 words to 33000 words out of 381117 words

Chapter 11 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1963

idar sannan ta zauna tayi azkhar, anan zaune bacci ya kwasheta mai dadin gaske.
Sai wajen 10 suka farka kusan atare, wanka haifa ta fara shiga bayan ta futo itama amra ta shiga yin wankan, tana futowa ta wuce gaban dresser ta shafe jikinta ta mayukan haifa masu saka laushin fata, saida ta gama sannan ta feshe jikinta da turare, tana gama wa haifa ta shigo hannunta dauke da breakfast, ajewa tayi sannan tace   babe baki shirya ba har yanxu, ga kayan dana fito maki dasu, ya kamata muyi sauri mu gama sbd hammam ya kusa zuwa, jin haka yasa amra cewa   yau kuma ina zamuje?, nifa na gaji gaskia  ..kallonta haifa tayi bayan ta miqa mata wata brown English gown tace   lallai ma, keda ya kamata ace baki manta ba kece zaki manta haka, to yau zamuje for application,mudai yan rakiya ne  & jin abinda haifa tace yasata saurin cewa   uhm ni harna manta ma  ..kayan ta saka ajikinta, ay kuwa kamar daman don ita akayi kayan sai yayi mata kyau sosai, zama sukayi sukaci breakfast sannan suka zauna jiran hammam.
?
Har akayi sallan asr bai zo ba, hakan yasa amra cire rai kawai na fita, haka yasa tayi kwanciyan ta bayan tayi sallah, sai wajen magrib haifa ta tasheta sanna??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n tayi sallah taci abinci ta koshi, abin zaqi haifa ta kawo mata mai suna kunafa ta kara ci ta koshi bam bam, mintuna kadan saiga ummi ta shigo dakin hannunta dauke da wasu packaging mai kyau, lokacin haifa ta shiga toilet don tayi wanka, kallonta ummi tayi sannan tace   taso kizo nan  .. miqewa amra tayi sannan suka zauna gefen gadon haifa sannan ummi ta soma Magana   abnati  awadu  an  ansahak (my daughter I will like to advice you)  nunfasa ummi tayi sannan ta cigaba   shi aure da kike gani ba abin wasa bane, idan anyi yishi anyi Kenan ba a fatan rabuwa, ki zauna ki natsu sosai, ki kula da mijinki, karki sake ki nuna mashi bacin ranki akan komai, sannan komai zai faru kiyi kokari kiga auren ku yayi working out, karki bari misunderstanding yasa kiyi abinda zaisa kizo kina dana sani, at the end ina maki fatan alkairi da zuria dayyab  kissing din goshinta ummi tayi sannan tayi mata kyakyawan runguma fuskanta dauke da smilying, anatse ta jawo wani park acikin kwali wanda ta shigo tare dashi da package din paper bags din, ta bude kwalin tayi ta zaro wani abu kamar chocolate sannan ta bata tace   ungo kici wannan, ga sauran nan zan hada da kayanki, make sure you eat one pack everyday,  sannan ta zaro wani pack din wani abun daban daga cikin packaging din tace   make-sure every single night you take a shower,with this  ta bude package din ta zaro wani abu da akayi rubutun larabci a roba mai kyau, sannan ta miqa mata wani turare tace   this should be one of your scent collection habibty  & nan ummi ta bata komi wanda amra na ganin haka tasan aikin da uwa ya kamata tayi ma diyarta da zarar zata aurar ummi tayi mata, wani irin dadi ne ya lullubeta sosai, anatse ta dago ta kalli ummi tace   shukran jazilan laki ya ummi  .. saida haifa ta futo daga toilet tukun kafin ummi tace   haifa ga delivery ya karaso, naga sunanki ne ajiki, bari na sauka qasa nasan abuh ya dawo yanxu daga masjid  ..fucewa ummi tayi sannan haifa ta kalli amra tace   ki shiga kiyi wanka mana, zamuje mu gaida abuh zai maki nasiha ne  ..tashi tayi kamar wanda aka zarema laka ta wuce toilet, wanka tayi sannan ta dauro alwala ta fito da brown towel din haifa mai laushi, anatse ta gyara curly gashinta wanda ya nannade sosai, cikanshi yasa dakyar take parking don tunda akayi mata wannan special treatment a spa da haifa ta kaita yasa gashin ya kara habaka sosai.
Anatse ta wuce dresser tadan feshe jikinta da turaren haifa masu kamshi sannan ta juyo ta kalli haifa wadda tasa wata doguwar riga orange ta haskata sosai, rigar tayi`matuqar amsar ta,   haifa kinga saida nace maki muje apartment dina na dauka kayan sawa kika qi, kika ce sabbin zan sa  ..kallonta haifa tayi sannan ta jawo package din ta bude ta zaro wata milky doguwan riga, wadda tasha stones red, rigar har taso ta fi wadda tasaka jiya tsabar kyau, gashi sai wani kamshi bakhoor take, karasowa haifa tayi gabanta sannan tace,   yanxu dai mubar maganar kayan nan ungo wannan kisa, kina matsayin amarya zaki saka tsoffin kaya, no noo& bazai yuwu ba   & kallon rigar amra tayi sannan tace   toh yanxu wannan rigar kikeso na saka muna shirin bacci  & kallonta haifa tayi sannan tace ?  gurin abu zamuje kin manta na fada maki zai maki nasiha  ..jin haka yasa amra ta amshe rigar, da taimakon haifa ta saka rigar& .wooo masha allah, dakyar haifa ta dauke idonta akan amra tace   masha Allah habibty, you look so stunning  ..murmushi kawai amra tayi don tasan haifa akwai zuzuta abu, amma itama kanta data kalli kanta ajikin mirror tasan tayi wani irin kyau sosai, da taimako haifa ta saka sarkan kayan shima mai ratsin red, da dankunne sannan haifa ta nadaa mata mayafin sai ta fito kamar black Arabian, batayi kwaliyya ba amma fuskanta wani annuri yake sosai.wani dan flat shoe haifa ta bata ta sanya a kafafunta da suka sha dan red wine henna kadan.
Kamo hannunta haifa tayi suka sauka qasa har main parlor na abuh, suna isa gabanshi suka zauna, basu ma lura da hammam dake zaune gefen shi ba don zuwanshi Kenan ko kiran haifa baiyi ba suka hadu da abuh ya dawo daga masjid,nan suka gaisheda da abu sannan ta dago suka gaisa da hamman, ita amra gashe sa tayi kafin abu ya soma Magana   Alhamdullah, I m so happy for you amra, may this beautiful knot last longer that we expect,  ..godiya amra t tayi mashi sosai akan karamci da yayi mata sannan yace  kudin sadakin ki yana wajen mijinki don mu anamu aladar miji ne zai bama matarshi da hannunshi ranar farko data kwana a gidanshi godiya sosai amra tayi mashi Harda yar kwallarta kafin suyi mashi sallama.

Futowa sukayi atare hammam ma yayi sallama da abuh sannan suka wuce, ganin ba hanyar stair zasuyi ba yasa amra kallon haifa tace   ina kuma zamuje yanxu  ..kallonta haifa tayi fuskarta dauke da murmushi tace   hammam zai kaimu shan ice cream na fadi ma abu karki damu  ..jin haka yasa amra bata bi ta kanta ba suka sa kai suka fuce, saida suka jira maids suka sauko da boxes din da haifa ta shirya kayan da suka sayo aka saka a boot din hammam kafin suka wuce, wanda duk wannan hayaniyan amra bata sani ba don ddanna wayanta take don trying number da salima ta kirata dashi wanda har lokacin a kashe yake, addua kawai ta soma yi don wani irin fargaba ta dunga ji sosai har suka kama hanya maidan nisa, tuni bacci ya kwasheta don ita ma abociyar son bacci ce sosai. 71-72
Suna isowa haifa ta zagaya bayan seat ta bude don ta tasheta, anatse ta soma bude cute idanunta ashagwabe tace   haif..gaskia wurin ice cream dinnan da nisa, mu koma gida inajin bacci sosai  & kallonta haifa tayi tace   stop doing this cute face of yours and come down  ..babu musu ta fito da kafafunta, wani irin sanyi ne ya buge ta, kallon building din ta soma yi, wajene babba sosai ga tsayi, ko ina na compound din flowers ne, ga wajen babu ko digon datti, sai tsirarrun mutane dake tafiya suna komowa harda masu yin jogging da running, wurin is so peaceful babu hayaniya. hammam ne ya futo daga cikin motar ya yi masu jagora, anatse ta fara takawa har suka shiga cikin building din apartment din, ko ina tsaftsaf, shuru amra tayi tana kallon wurin don ya burgeta don kwata kwata bai kai apartment din da take ba ko kadan, wannan daga gani upgraded apartment ne wanda yaci uwar nata, anatse suka hau lift su uku sannan hammam ya danna 7th floor,, suna isowa suka suka fito gaba dayan su, tafiya suka danyi mai nisa kafin tsaya gaban kofan da aka rubuta house number 55, anatse hammam ya soma dannan wasu pins jikin kofar sannan ya bude, tsayawa amra tayi tana muzurai, saida haifa ta jawo hannunta suka shiga, ko ina haske wal wal, acikin apartment din, saida suka wuce walk way sannan suka karasa cikin sitting room din da kal kal yake, zama sukayi akan L shape chair din sannan hammam ya juya ya wuce ciki,cikin master bedroom din ya shige kai tsaye ko ina dim babu haske hakan ya tabbatar mashi da yayi bacci already, baiyi kokarin tashinsa ba ya rufo mashi kofan sannan ya fito, yana fitowa yaji karar bell, anatse ya wuce ya bude kofan, nan helper din apartment din ya shugo da boxes din, nuna mashi wajen gaban sitting room yayi ya aje sannan ya rufe kofan bayan ya fuce, anatse ya kalli haifa sannan yace   we ve done our job so let s get going ko  & jin haka yasa ta miqe amra ta miqe itama, kallonta haifa tayi sannan tace   habibty ya naga kin miqe, koma ki zauna, ay gidan mijinki muka kawo ki, kin manta dole ku zauna gida daya, so mu munyi namu, yanxu kune zakuyi abinda ya kamata, please amra karmuyi wani jayayya kinfa san komai so please just get back to your seat mu zamu wuce   ..bude baki amra tayi galala tana kallonta, abinma ya daure mata kai, ta kasa gane me taqa mai mai haifa ke nufi, har suka saka kai suka fice ta kasa koda motsawa, anatse tabi kofar da suka rufe da ido sannan ta fara bin apartment din da kallo, yanxu Kenan dole ta zauna da wannan mutumin da bata san waye shi ba, bata san halinshi ba,anatse ta koma ta zauna kan couch din ta doka uban tagumi, tunanin kanneta ta fara, chan siraren hawaye suka fara zarya a fuskarta, tausayi kanta take da kannenta, tunanin shin yaushe wannan matsalar tasu zata kare take, kodai basu da rabo ne agidan duniya, da wannan tunani bacci barawo ya kwasheta anan kan couch din.
?
Wajen karfe hudu na dare ta farka afurgice, wani irin ciwon mara ne ya taho mata gadan gadan, afurgice ta sakko kasan kujeran, runtse ido tayi hawayen wahala suna zubo mata, ahankali bayanta ya fara riqewa kamar zata zauce tunawa da maganinta yana chan apartment dinta yasa ta fashewa da wani matsanancin kuka mai ban tausayi, da sauri ta daddage ta miqe da kyar ta fara laluben hanyan kitchen dake hade da sitting room daga gefen corner row, kitchen ne tsaf harda kitchen island daya raba tsakanin parlor da kitchen din, anatse ta matsa gaban smart dispenser kusa da fridge freezer,neman cup ta fara yi, juyawa tayi ta hango glass cup da glass jug akan island, anatse ta jawo cup din ta fara deban ruwan zafi daga dispenser din, ahankali ta soma sha dukda yana kona mata baki, haka tasha wajen cup uku na ruwan zafi tana hawaye, ahankali ta soma jin relief din ciwon, saida ta dan ji maranta ya gasu da ruwan zafi ta samu ta lallabo ta karaso har can L shape chair din parlor, ganin zufa ya tsatsafo mata dukda ac dake aiki acikin parlor yasa ta saurin zame veil din data yafa, ahankali tayi rub da cikin kan kujeran tana furzar da nunfashi mai wahala, saida ta dauka kusan awa guda tana juyi kafin ta samu bacci ya dauketa.
Lokacin sallan asuba nayi ya bude idanunshi, ahankali ya lumshe idanun nashi wanda sukayi lum lum kamar wanda bayason budesu, anatse ya fara karanto adduoi kafin ya yaye lallausan blanket din daya rufe jikin shi dashi, black and white pajama s ne ajikinshi masu santsi, anatse ya sauko da fararen kafafunshi masu kyan gani sannan yayi yar miqa, ya wuce toilet, wanka yayi don shi ma abocin wanka ne sosai, sannan ya futo daure da farin towel dinshi, a gaggauce ya sanya jellabiya fara sannan ya shimfida karamin Turkish carpet din sallah, ya fara raka a tainul fajr, kafin ya tada sallah fajr,anatse yake ibada ya dauka wajen awa yana azkar kafin ya miqe ya cire jallabiyan ya kwanta da shorts dinshi fari kal.
?
Karfe 9 daidai ya tashi bakinshi dauke da salati sannan ya wuce toilet, saida yayi wanka yayi brush sannan ya futo daure da wani towel din white, wanda ya dan wuce mazaunan shi, hannunshi kuma rike da dan karami, wanda ya kaishi fuskanshi yana goge sajen shi wanda yasha mayuwan gyara.
Karasawa yayi gaban katon mirror dresser din ya bude gaban dresser din ya fara futo da mayukan shafawan shi, anatse ya soma shafawa har yazo kan body sprays dinshi masu sanyin kamshi, budo kafar dakin da akayi ne ya sashi tsayawa daga shafa wani oil mai kamshi da walki a sajenshi, dan juyowa yayi yana kallonta, amra wadda ciwon maran ne ya kara farkar da ita daga wahallen baccin data samu ya dauke ta ne, ta rasa yanda zatayi gashi tana son zuwa toilet don wani irin futsari ne ya matsota sosai, gashi tana jin yanda ta fara staining dukda bai fito a riganta ba, afurgice ta fara duban parlor ko zata samu toilet ganin babu guest toilet yasa ta saurin bude dakin data gani daga gefe kawai ta fada ba tare da tunanin wani abun ba.
Ganin mutun atsaye ya bata baya sanye da towel, iya gwiwa wadda iyakacin towel din kasan kwankwaso, ga faffadan bayanshi a bayyane da gashi lub lub a kwance kamar na jariri ya sata sauri komawa da baya tana gwalo ido harta rufe kofar bata ankare ba juyowa yayi yana fuskantarta, da sauri ta kawar da kanta, jikinta sai faman kyarma yake yi kamar wadda aka kama tayi laifi, da sauri ta soma tattaro kalaman bakinta tace   I m sooooo& .so..rry wallahi bansan da mutun acikin dakin ba  ..tana kaiwa nan ta juya har fuskanta na buguwa da kofan sannan ta saka hannu da sauri ta bude kofan ta fuce kamar iska, don tsayuwan nan datayi da yanda yake kallonta qiris ya rage batayi futsari a tsayen nan ba. Shiko amar mamaki ne yagama cikashi, yaushe tazo,me takeyi a cikin gidan shi, don shi bashida masaniya akan zuwanta, sanin babu wanda zai bude mata kofa koya bata pin sai hammam yasashi saurin wuce wa gaban bedside ya lalubo wayan shi ya soma budewa, ganin message din hammam ya sa yayi saurin budewa ya fara karantawa   dude we came to your house last night naga kayi bacci, mun kawo maka bride dinka ne so enjoy your honey moon and remember yarjejeniyar nan, dole ta zauna tare dakai.  Yana gama karantawa ya wullar da wayan yana furzar da huci mai zafi, shifa wannan takura ne awajen shi, ya za ayi ya zauna gida daya da mace, macen ma wannan yar abar salon ta gama rainashi, gashi shifa baya son sharing komai, dole ma kawai ya bar mata gidan ya koma penthouse dinshi, saida yagama tunane tunanen shi kafin ya wuce wajen glasswardrob dinshi na dakin ya bude ya fiddo kayansa riga da wando ash, rigar mai buttons ce, wandon kuma daga kasa wajen kafanshi mai kamawa, kayan kana gani kasan designer ne basai an fadaba, anatse ya shirya tsaf ya feshe jikinshi da turaren shi mai kamshi sannan ya zari wayanshi ya futo daga bedroom din, koda ya futo kallo daya ya mata don bedroom din yana facing sitting room, tana nan araqube kamar wadda tayi sata aka kamata, motsin kirki ta kasa tunda ya futo, kamshinsa ne ma ya fara kai mata ziyara, da sauri ta rumtse idanunta ta tamke throw pillows dake gefen kujeran, bai ma bi ta kanta ba ya wuce wajen kitchen island, anatse ya jawo glass jug din wajen da glass cup din ya deba ruwa daidai ya kai bakinshi anatse yaji muryan ta a dodon kunneshi  Good morning saida yagama shan ruwan sannan ya juyo ya mata kallo daya suka hada ido tayi saurin sauke nata, tabe baki yayi sannan ya aje cup din ya wuce hanyar fita baiko bi takanta ba balle tasa ran zai amsa mata gaisuwan nata.
Saida ya futa ta samu ta sauke wata nauyayyiyan ajiyar zuciya da numfashi, har tana shafa kirjinta dake bugawa pat pat, tashin hankali, wannan wani irin tsoro take ma mutumin nan, lokacin daya futo har cikin zuciyarta take jin takunshi har ya wuce wajen kitchen island, anatse ta sauke kanta wasu siraran hawaye na zubo mata, sai yanxu ma take tunawa dalilin shigarta dakin, wani irin zabura tayi, nan take futsarin ya taho gadan gadan, da gudu ta mike ta kama hanyar dakin, saida tazo daidai kofar kirjinta ya fara bugawa, har yanxu wajen kamshin sa yake kamar yana wajen, runtse ido kawai tayi ta fada cikin bedroom, bata ma tsaya kallon dakin ba idonta ya sauka akan wata kofa daga gefe, da sauri take takowa kafanta har hardewa yake, ga murdawa da cikinta keyi, da sauri ta bude kofan ta shiga ciki, bata ma tsaya duban dakin ba saboda yanda futsarin ya matsota sosai,tana shiga ciki ta soma tube kayan jikinta, saida tayi futsarin tukunna ta samu sauqi, ahankli idonta ya sauka kan wc din, duk jini ya bata hankali atashe ta karasa sabule kayanta, saida ta fara wanka a shower din, ahankali ta dunga bin gaban shower nashi da kallo, wasu hadaddun shower gels ne ajere kusan guda goma,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login