Showing 162001 words to 165000 words out of 381117 words

Chapter 55 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2017

zumm sosai, nunfashinta ma kanshi da zafi yake futa daga bakinta, ganin haka yasa ammah tace   wannan wani irin zazzabi ne oh ni Maryam, yarinya daga dawowa  kallon lanata ammah tayi tace   ke rage min ac nan 
Mikewa lanatana tayi don itama a furgice take ta kashe ac, suna nan zaune after like 20mins saiga doctor, amar ne ya shigo dashi har cikin dakin, ammah na ganin haka ta bashi waje ya fara dubata, futa lanatana tayi don ta basu waje shima gogan bai tsaya bay a fuce ganin irin kallon da ammah take jefanshi.
Cikin gaggawa doctor ya dubata harda drip ya saka mata ganin ta zama weak, kafin ya mata allurai da zai saukar da zazzabin, saida ya tabbatar shes stable kafin ya kalli ammah yace   hajiya bamu gaisa bama ina wuni 
Murmushi ammah tayi don tana zaune daga bakin gadon tace   lafiya kalua doctor, ya jikin nata? 
  alhamdullah its just a fever, nayi mata allurai da zai saukar dashi sannan ga drip nan na saka mata zuwa anjima idan yak are sai a cire mata 
Godiya sosai ammah tayi mashi kafin ya ta rakoshi har kasa, doctor na tafiya ta wuce dakin amar kai tsaye, tana knocking kofar tace   muhammd 
Amar dake kwance daga shi sai shorts yayi saurin miqewa ya janyo jallabiyanshi ya saka ya bude kofar bedroom din, ganin ammah tsaye fuskanta babu walwala yasa ya sauke kanshi kasa, kallonshi tayi cikin fada tace   muhammad lafiyanka kuwa?matarka na chan kwance babu lafiya kai kana nan zaune hankalinka kwance? Waye zai kula maka da ita ni?  
  im sorry ammah ba haka bane  ya fada kanshi a kasa
  okay menene then? Don t tell me kana kan bakar ka saika saki yarinyar nan? Look bari kaji, Muhammad baka isa ka saki yarinyar nan ba saina baka umarnin haka, don sainaji daga bakinta idan tana raayin haka  ta karashe rai abace
Dan dagowa yayi ya kalli ammah zuciyanshi na mashi zafi sosai yace   but ammah& . 
Katse shi tayi ta hanyar cewa   but what? 
Sunkuyar dakanshi yayi don bazai iya kallon cikin idanunta a wannan yanayi ba, ganin haka yasa ammah fucewa daga bedroom din nashi gaba daya, tana fucewa ya cije lower lips dinshi, saida wajen yayi jaa sosai amar zai fashe, dakin ya koma ya zauna bakin gadonshi ya dafe kanshi, ahanakli ya soma Magana   ya allah, ammah please karki hanani abunda nayi niya, babu wani amfani aje mace arayuwana, bana buqata 
Ranshi a dagule haka ya kwanta, abubuwa sunyi mashi yawa.
?
Ammah na fitowa daga bedroom dinshi ta nufi hanyar stairs, salima dake zaune a dining tana cin abunci ta hango ta, da sauri ta karasa cin abuncin don daman kadan ya rage a plate din,kafin ta miqe zuwa wajen ammah   ammah naaa tun daxu nake zuwa dakinki ban ganki ba 
Murmushi ammah tayi mata tace   ina dakin daughter ne bata jin dadi 
Shuru salima tayi kafin ta dan tabe baki, kallonta ammah tayi tana karantar ta, kafin tace   ina salim?yayi dinner? 
  eh yayi tun daxu, har yayi bacci mah,  ta bata amsa fuskanta dauke da murmushi
  ammah kinci abunci?  salima ta tambaye ta cikin kulawa
Murmushi amma tayi mata kafin tace   nayi dinner tun daxu, kune dai da kuke son cin dinner late 
Dariya salima tayi suka hau sama atare har daki salima ta rakata kafin tayi mata sallama ta fito, tunda ta fito daga part din ammah ta kafa ma kofar dake chan gefen dakin su kallo, tunani kala kala na yawo aranta, tana son shiga saidai wata zuciyar na hana ta yunqurin shiga.
Jiki a mace ta taka zuwa bedroom din tayi knocking, jin shuru babu response yasa ta dan bude kofar ta shiga, a kwance ta tadda amra hannunta da drip, kasa daga kafa salima tayi, hawaye ne ya soma bin kuncinta take tausayin amra ya fara dabaibaye ta, takowa tayi har bakin gadon ta tsaya ta kafe fuskar amra da kallo, ta chanza mata sosai, tayi kiba da cika, ta zama wat babbar mace a fuskanta, kallon yanda take barcin wahala salima tayi, tana jin qaunar yar uwar tata na ninkuwa hade da tausayinta lokaci guda, nan take ta fara tunanin da bata son yi,ganin amra na kokarin juyi da hannunta dake dauke da canula zata danne hannun yasa tayi saurin rike hannun nata don har yadan kumbura kadan, ahankali salima ta taimaka mata ta gyara mata kwanciyar kafin ta janyo mata duvet ta lulluba mata ta juya gaban switch ta rage mata haske kafin ta fuce..
?
?
The next morning&
Wajen karfe takwas amra ta bude idanunta da sukayi mata nauyi sosai,kallon dakin ta fara yi daga kwance, kafin ta miqe zaune dakyar, cije lebenta tayi jin yanda bayanta ya rike,tace   arshhh  da muryarta da baya fita sosai,kallon rail din dake dauke da drip tayi kafin ta maida kallonta ga hannnuta dake mata zugi dauke da canula,anatse ta cire canula din ta kafin ta sauke kafafunta kasa ta wuce bathroom, wanka ta farayi da ruwa mai dumi sosai don jikinta yayi tsami sosai kafin ta wanke bakinta ta dauro alwala, dakin ta dawo ta maida kayan data cire kafin ta shimfida sallaya don gabatar da sallolin da ake binta, tana idarwa ta jingine da bangaon dakin tana tunani, da sallama ammah ta shigo dakin, da sauri amra ta miqe muryarta chan ciki ciki tace   ina kwana 
Takowa har inda take ammah tayi ta riko hannunta zuwa gefen gadon ta zaunar da iat kfin ta zauna gefenta tace   morning daughter kin tashi lafiya? Ya jikin ki? 
Anatse amra ta sunkuyar da kanta tace   alhamdullah da sauqi, 
Murmushi amma tayi mata tace   bari akawo maki breakfast ko akwai abunda kike so adafa maki 
kasa cewa amra tayi kanta a kasa jiki a mace tace   ah ah!! 
nunfasawa ammah tayi ganin har yanxu taqi sakewa yasa tace   toh bari akawo maki saiki samu ki karya,babu abunda ke maki ciwo ko? 
  ah ah babu nagode ammah  amra ta fada tana dan murmusawa
Wani irin dadi ammah taji kafin ta fuce daga bedroom din, cikin yan mintuna kalilan lanatana ta shigo da lafiyayyan breakfast ta aje mata bayan sun gaisa, lanatana na fita ta tako har inda ta aje mata breakfast din, zama tayi ta deba yanda zai zauna a cikin ta.
Nan zaune lantana ta sake dawowa hannunta dauke da kaya doguwar riga mai mayafi mai kyau cuttons,gabanta ta karaso tace   gashi hajiya tace akawo 
Karba amra tayi tare da yin godiya, kafin ta juya.
Anatse ta gama cin abuncin ta mikew ta sauya kaya, rigar ta zauna mata ciff ciff don bubu ce, mai hade da mayafi, tana gama shiri ta dan fesa turaren dake kan dresser, cikin nastsuwa ta kwashe plates din data gama cin abunci da tray din ta futo daga dakin, waige ta fara yi don parts din dake saman suna na da yawa, chan gefe ta hango stairs, cikin natsuwa ta bi hanyar ta fara saukowa, babu kowa a kasan don haka ta fara waigen hanyar kitchen, gashi bata san ko  ina a gidan ba, tana cikin waige waige ta hango hango wani dan sako da sautin cokula, takowa ta farayi don duk tunaninta nan ne hanyar kitchen din, shiga wajen tayi kai tsaye bakinta dauke da sallama, duk atare suka waigo suka zuba mata idanu banda amar dake facing hanyar shugowa dining din, dago tayi idanunta ya suaka akanshi, nan take hannunta ya soma karkarwa don kirish ya rage plate din ya fadi, saurin sauke kanta kasa tayi, kallonta amma tayi tace   daughter kin sauko?kina buqatan wani abun ne?  tayi tambayar fuskanta dauke da murumshi, anatse amra ta dubi bangarenta don tana daga gefen amar tace   daman kitchen nake nema zan aje wannn 
  ay da kin barshi kin kwanta kin huta lanatana zata kwashe,lantana lantana  ammah ta fada tana kallon hanyar kitchen, daga chan kitchen lantana ta amsa
Aman dai kasa tauna abuncin dake bakinshi yayi don yana ganinta yaga kammaninta da su salima sosai,don badan yaga tana da kiba bama zaice wannan ay salima ce, amar kuwa ta wutsiyar ido ya kalli inda take tsaye kafin ya kauda kanshi gefe, maida hankali da yayi wajen cin abuncin sa cikin kamewa, ba tare da yace tak ba, amra dai kamar ruwa ya cita ta kasa cewa komai saida lanatana ta karaso ta karbi plate din kafin ammah tace   daughter kije ki huta ko 
Sunkuyar dakai amra tayi kafin ta juya, har zata tafi ta dawo tace   ina kwanan ku  Aman ne kawai ya amsa ta fuskanshi dauke da surpise,
Batare da ta tsaya sanin wanda ya amsa ba ta juya ta wuce sama gabanta na faduwa don wani irin kunyar amar take ji sosai.
?
Tana fucewa aman ya kalli amma yace   ammah whos she? 
Murmushi amma tayi ta cigaba da cin abuncinta tace   your sister inlaw ga mijinta nan a gefenka 
Da sauri amar ya dago ya kalli ammah, itama shi take kallo don ganin reaction dinshi, saurin kauda kanshi gefe yayi ya miqe yabar dinin din, aman kuwa da tambayoyi suka mashi yawa ya sake cewa   itace matar shi da yayi aure? 
  yes itace  ammah ta bashi amsa kai tsaye, jinjina kai kawai yayi
?
?
Amra na wucewa sama ta shige daki ta z?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
auna gefen gado ta doka wani uban tagumi, gaba daya jikinta yayi sanyi, tunawa da yanda ko kallon inda take baiyi ba, ahankali wani hawaye mai dumi ke xubowa a fuskanta, tana regretting abubuwa sosai akan shi, yayi mata abunda duk duniya bazata taba ganin laifinshi ba, takaicin kanta takeyi akan yanda ta dunga judding dinshi, ashe gata yake mata, she can clearly recall lokacin data gudu daga gidanshi, ashe all this while shike protecting kannenta shine ya taimake su shine ya inganta rayuwarsu, saurin runtse idanunta tayi tana jin takaicin kanta da yanda ta dunga behaving.
?
Yana shiga daki bathroom ya shige after few minutes ya fito daure da towel,agaggauce y agama shiryawa cikin kananun kaya, saida ya feshe jikinshi da turarukanshi masu sanyin kamshi kafin ya fuce daga dakin, yana fitowa sama ya wuce zuwa dakin ammah, yana shiga bai jima ba ya fito ya sauka kasa ya fuce daga gidan gaba daya.
?
Haka amra ta wuni a daki ita kadai, time to time ammah ke shigowa dakin tana dubata, su salima kuwa daman sun tafi school, karfe biyu daidai suka dawo ita da salim, daki suka wuce direct suka sauya kaya, salim ne ya fara fitowa yabar salima a daki, direct dakin amra ya wuce yayi knocking kafin ya bude kofar, amra na ganin shi tayi saurin miqewa tsaya, kallonshi ta soma yi tana mamakin yanda ya kara girma, miqewa tayi da saurin ganinshi tsaye shima ya kafa mata idanu, har gabanshi ta tsaya ta mashi murmushi tace   salim kaima kana fushi dani ko? 
Hannunshi ta janyo fuskanta gwanin ban tausayi tace   forgive me kaji salim, bazan taba abandoning dinku ba kaida salima 
Saurin rungumeshi tayi tana hawaye shima rungumeta yayi yana hawayen kewar ta, yanxu wannan addar su ce, yana jin abun kamar a mafarki, da kyar amra ta janye jikinta daga na salim, yana ganin haka ya soma goge mata hawyen fuskanta yana mata murmushi, itama murmushin take mashi, kallonshi tayi tana nazari don tunda ya shigo baice mata kala ba don haka tace   bazaka kulani ba ko salim? Kana fushi dani har yanxu?  ta fada tana marairaicewa , kallonta yayi ya girgiza mata kai alamun ah ah, daga chan bakin kofa salima data fito daga dakinsu ta hango su tayi saurin karasowa inda suke, kallon yanda amra ta kafe salim da idanu tayi, cikin sauri salima ta karaso dakin ta janyo hannunshi waje ranta a bace tace   meka tsaya yi anan, wuce mu sauka  juyawa tayi tare da salim, amra na ganin haka tayi saurin cewa   salima& 
Tsayawa salima tayi ba tare da ta waigo ba, amra na ganin haka tace   salima dan allah& .
Katseta salima tayi ta hanyar cewa   don allah ki rabu damu adda, na fada maki bama buqatar ki yanxu, alokacin da muka buqace ki ay baki waigo mu ba 
Tana kaiwa nan ta jaa hannun salim suka bar wajen,ammah dake jinsu daga kasa tayi mamakin yanda salima ke Magana da amra, tasan dole suji zafi saboda ta tafi ta dauka shekaru acahn wata kasa ba tare da ta waiwaye su ba saidai sanin cewa basu san halin data shiga sanadinsu bane yasa suke jin haushin ta,
Suna saukowa kasa salima ta kalli salim tace   duk sanda na kara ganinka a dakin nan saina mareka wallahi 
Kallonsu ammah dake zaune a sitting room tayi kafin tace   salima zo nan 
Karasowa salima tayi don bata lura da ita bama a sitting room, bin bayan salim yayi shima yana gunguni har suka karaso gaban ammah.
Zama salima tayi a gefen ammah kanta a kasa, kallonta ammah tayi in a calming tone tace   why zaki hanashi zuwa wajen yar uwarshi?, nasan kuna jin haushinta but that doesn t give you the audacity kiyi ma addan ki Magana haka,kin tsaya kin saurari dalilinta na qin dawowa da tayi? 
Jiki a mace salima ta girgiza kanta, nunfasawa ammah tayi ta shafa kanta cikin dabara ta manya tace   haba dearest, bai kamata kina mata Magana ahaka ba kinji ko, kamata yayi ki sameta kuyi Magana ta fahimta, babu yanda za ayi dan uwanka na jini yayi abandoning dinka, listen to her with open ears kinji ko? 
Hawaye ne ya zuboma salima tayi saurin sharewa tace   toh ammah 
  yauwa ko kefa, kuje kuci abunci kafin lokacin islamiyya yayi 
  tohm ammah  salima ta fada tare da miqewa, dining suka wuce ta zuba masu abunci ita da salim.
?
Bangaren amar direct headqauters ya wuce inda suka hadu hardasu m5 da sojojin da suka karso suka shiga helicopters kusan guda uku, tafiyar awa hudu ta fiddasu daga Nigeria, daidai inda bunciken su ya tabbatar da nan ne factory din alhaji kabiru suka tsaya, wajen gaba daya daji ne gaba da, suna landing duk suka fifito harda asad da mukarrabban shi,gaba daya kowannensu hannunsu dauke da bindigu, tun daga bakin gate suka fara harbi, agurgije suka shiga cikin factory din, nan take yaran alhaji kabiru suma suka fara don zuwan bazata sukayi masu, nan take wajen ya kacame da karar harbi, an kama kusan mutane talatin da suke cikin factory din, waenda sukayi yunkurin guduwa ma saida aka kamosu, daga bayan factory din kuwa katon gida ne da dakuna inda maaikatan ke kwana, nan take suka farabinciken ko ina, akallah sun samu kudi a cikin factory din akallah kusan billion goma, bayan wannan harda kwayoyin da sukayi sealing, abunda yafi bama su amar mamaki shine suna yin production din drugs din professionally harda batch number da seal din nafdac alamun shaidar drug din an tantance su, nan take suka fara fidda drugs din daya bayan daya, da chemicals din da suke amfani dasu wajen hadawa, harda waste din drugs din komais aida suka dauka saboda evidence, asad dai tsayawa yayi yana kallon yanda ake ainihin bincike, ba kmar yanda sukeyi baa nan Nigeria, don nan idan an kama mutun kotu kawai ake kaishi a yanke mashi hukunci, suko su amar da sauran sojojin dake karkashinsa daga uae aiki sukeyi tukuru wajen tattara komai babu abunda suka bari, saida suka gama komai suka tattara komai kafin su rufe wajen gaba daya.
?
Basu suka dawo ba sai wajen karfe sha biyu na dare, daga headquarters gida ya wuce direct, yana shugowa ya wuce dakinshi direct.
Washe gari da sasafe ma haka ya shirya ya fuce daga gidan tun kafin kowa ya tashi.
?
Bangaren Aman ya natsu sosai, ya daina shaye shaye ya zama natsatse sosai da taimakon salima, wanda yanxu sun fara jonewa dukda har yanxu bata karbi tayin soyayyar shi shiko kullum nuna mata yake yanda yake qaunarta, yanxu ya maida hankali sosi wajen aiki a company don gayara abunda mahaifin ya lalata, relationship dinshi da amar ya gyaru sosai don yanxu baya mashi irin kallon da yake mashi a baya, don ya gano da taimakon aman aka gano duk wani ayyukan da alhaji kabiru yayi.
?
Salima ma tun bayan Magana da ammah tayi mata akan amra, tayi kokarin danne abunda ke zuciyarta, saidai har yanxu ta kasa daina fushi da ita, don ko hanyar da take bata bi,salim dai kullum yana zuwa wajen amra don hanashi da salima keyi yanxu ta daina.
Bangare amra har yanxu ta kasa sakewa da gidan,yau kwanan ta hudu da suwa gidan kullum tana kunshe a daki,zuwan da salim keyi ne ke debe mata kewa, abunda yake tayar mata da hankali shine yanda kwata kwata salim baya Magana, gashi salima taki bata dama zuyi Magana don tsoron tambayarta ma take yi, haka zaizo idan tayi Magana yayi shuru sai ta fashe da kuka.
?
Saturday morning& .
Tunda ta tashi take fama da ciwon kai,tun bayan datayi wanka ta zauna bakin gado ta doka uban tagumi, tan nan zaune lanatana ta kawo mata breakfast, tana futa salim ya shugo, kallonshiamra tayi harya karaso inda take ya zauna agefenta,kallonshi amra tayi tace   salim ka tashi?  girgiza mata kai kawai yayi yana murmushi
Tana ganin haka tace   salim baka Magana ne? 
Nan ma girgiza mata kai yayi, jiknta ne yayi sanyi ta kara tambayrshi   meysa baka Magana? 


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login