Showing 9001 words to 12000 words out of 381117 words

Chapter 4 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1955

mu, ciwon salim ya dawo, adda kizo ki daukemu ki dawo damu wajenki dan Allah  jin hakan yasa amra tsugunnawa anan mutane kuwa me zasuyi banda kallonta don duk ta furgice, cikin shesheka amra tace   salima meya faru daku, meya sameku innalillahi,  kittt wayan yamutu sakamakon chargi daya kare,
hankali atashe amra ta soma cewa   salima say something salima!!!!! Jin shuru yasa ta duba wayan taga call din yayi ending hakan yasa tayi sauri sake kira amma me switch off, hankali atashe ta daura hannu aka ta fashe da kuka, haifa wanda sai yanxu hankalinta ya dawo kan amra yasa tayi sauri zuwa gaban ta tace   amra what s wrong  innalillahi kawai amra ke furtawa dakyar haifa ta jawo ta suka wuce office suka zauna, saida ta bata ruwa sannan ta fara dawowa dai dai, anatse ta soma Magana   haifa siblings dina, suna cikin mawuyacin hali, ashe sune suketa kirana da wani line over a month now, I m so stupid for not recognising them, bazan taba yafema kaina ba idan qannena suka shiga cikin matsala, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, na shiga uku haifa & saida haifa ta kwantar mata da hankali tukunna ta dawo dan daidai, babu abinda kwakwalwarta ke tariyo mata sai maganan salima da take cewa   adda kixo ki taimake mu ki tafi damu, muna cikin matsala, ciwon salim ya dawo gadan gadan, runtse idonta kawai tayi don bazata iya jurewa ba kwata kwata.

Aikin da basuyiba a ranar Kenan ba, koda ta koma gida number ta dunga kira amma switch off, aranar dai amra batayi bacci ba kwata kwata.
Bangaren salima hakan ta kasance, tayi kuka harta godema Aallah, karshe dai alwala kawai tayi domin kai kukanta wajen Allah, salim kuwa da yanxu rabin rayuwar shi kamar mattace kullum sai barci yake ta kalla, tausayinsa duk yagama lullubeta.
?
Washe gari, kwata kwata amra ta susuce, bata cikin nutuswarta, koda taje aiki babu abinda ta iya yi kwata kwata, gashi ayyukan sunyi mata yawa don hafiza tunda ta tafi bata kara dawowa ba, haifa ce kwai ke taimakonta sosai wajen wasu abubuwan, yanxu kam ta yanke hukuncin duk yanda za ayi saita san yanda tayi ta kawo qannenta kusa da ita kuma zatabi ko wace irin hanya ce.

?Zama sukayi ah caf?, wanda kwata kwata amra ta kasa cin komi sai haifa ce take dan turawa itama bata cikin kwanciyar hankali ganin yar uwarta cikin damuwa, hakan yasa ta zuba mata ido kawai sannan tace   ?mra I have a solution but I don t know if its going to work,(inada shawara saidai bansan ko zata yiwu ba), kinga dai visa ki saura shekara biyu kuma kince baki gama tara bashin uncle ba ko?..girgiza mata kai amra tayi tana fuskantarta da nutsuwa .. anatse haifa ta cigaba   babe why not ki nemi katin kasar nan sbd ki kawo kannenki kusa dake  jin wannan batu yasa amra yin shuru chan tace   wannan ce kadai hanyar da zan iya kawo su kusa dani haifa??   girgiza mata kai haifa tayi sannan ta cigaba   but babe samun katin kasa ah uae shine abu mafi hatsari musamman ma ke mace yar Africa domin hanyoyin da akebi asamu are not legal, kuma akwai risk babba  ..kallonta amra tayi don a yanxu kam bata jin akwai abinda bazatayi ba akan qannenta, gyara zama tayi sannan tace   haifa all the risk are not important to me now, ni yanxu damuwa na qannena ne, so I can go to any extent don na taimaka masu, kuma wannan katin kasar shine kawai solution ayanda nayi tunani yanxu.

Nunfasawa haifa tayi sannan tace   okay idan har kinga zaki iya ni kuma zan taimaka maki, akwai wata secretary data tabaa aiki karkashin abu na, itama kusan issues dinku daya saidai ita iyayenta ne wanda suke cikin mawuyacin hali wanda hakan yasa tayi AUREN KATIN KASA&   jin haka yasa gaban amra faduwa ana wata ga wata, dakewa kawai tayi ta cigaba da sauraron haifa,   yanxu zan kira abu don ya bani number nasan yana dashi har yanxu, idan na sameta zan roki ganinta sai muyi fixing date between yau da gobe don mu ganta yanxu dai ki kwantar da hankalin ki komai zaizo da sauqi kinji 
Saida haifa ta gama tukunna tadanji sauqin zafin da ranta keyi mata sannan sukaci abinci suka koma office.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?
Paid book =???

Chapter 56-57

Amar kuwa satinshi guda a asibiti, tun bayan abinda ya faru tsakaninshi da hafiza likitanshi ya sashi on a bedrest.

Wato bayan fitarshin nan dakyar ya shiga motor sbd wani irin masifar dripping da ya dinga yi, gashi yana da low sperm count, hankali atashe ya shiga yace ma m5 ya wuce dashi asibiti, bayan sun isa likita yayi mashi scanning ba karamin asara ya samu ba don kwayayen haihuwanshi duk kusan masu amfanin sun zube, aranshi kamar yayi kuka, dama already doctor yace ya dinga lura sosai, yanxu gashi dan sakacin da yayi ya jawo mashi asarar mai yawan dai zai iya jawowa bazai taba haihuwa ba harya mutu, wanda haka ba karamin tashin hankali bane agareshi domin yana qaunar yara sosai ba kadan ba.

Ganin yanda result dinshi ya fito with bad news yasa likita ya bashi bed rest, wanda yau kwanan shi biyar cur kuma ayau za a bashi sallama.
Zaune yake gaban likitan nashi wanda ya soma bayani kamar haka   mr amar I m so sorry to say this, but this time around your condition is worse and I m afraid you may not be able to & but we did a second test after your bed rest so we  ll see how it turns out,..kwankwasa kofar akayi wata nurse ta shigo hannunta dauke ta file ta mikama doctor sannan ta fice, amar kuwa wanda tunda doctor ya fara bayani yayi resting kanshi wani irin azaban sara mashi yake ga wani sabon bad news ya sashi kasa cewa komai, saida yaji muryan doctor tukunna ya bude idanunshi ya kallesa..  ?ncredible, mr amar,nayi mamaki sosai, wannan bedrest ya taimaka yayi stabilizing jikinka sosai, and ina maka albishirin din cewa kana da 10% chance na samun da ko ya, so ina baka shawara yanxu ya kamata kasan yanda zakayi,because daga wannan bana tunanin zaka samu chance kamar haka, sanan akwai medication da zan baka ka dunga amfani dasu,  godiya kawai amar yayi mashi sanan ya wuce motor & tashin hankali, koda ya shiga motor kanshi ya kulle ya rasa tunanin da zaiyi, ya rasa mafita, dole yasan yanda zaiyi don bazai taba yarda yayi loosing wannan 10 percent dinba,ahankali ya zaro wayanshi yayi dialing hammam, yana picking ya soma Magana   hamman I need you now, please come to my pent, its urgent.  Yana kaiwa nan ya kashe yaja motor har penthouse dinshi. Yana parking motor hammam itama tana parking, saida suka yi musabaha sannan suka wuce cikin penthouse din atare.

Zama sukayi a kan daya daga cikin set of chairs din sitting room din suna facing juna, Pablo ne ya shigo cikin parlorn ya gaishesu atare sannan ya aje masu abubuwan sha masu sanyi, godiya hamman yayi mashi, shiko amar ko kallon wajen shi baiyi ba, saida Pablo ya fuce kafin hammam ya kalleshi yace   dude what s the problem, duk hankalina ya tashi, menene matsalar?  runtse idanu amar yayi yana jin zafin abin sosai aranshi sosai saida ya dauka almost 2mins kafin ya fara Magana cikin natuswa  I just came back from the hospital,akwai abinda ya faru last week, I don t even know where to start, but that s not important now,  kallonshi hammam yayi sbd ya qagu yaji mey ya faru sannan yace   dude just say it anyhow  & komawa amar yayi ya jingina da kujera sannan ya jawo file din daya aje gefenshi ya miqa ma hammam, da sauri hammama ya karba ya fara budewa, saida ya bude file din ya karanta tsaf sannan ya soma Magana   amar I don t understand, 10 percent kuma, explain it to me so that I can understand you better  & bude idanunshi yayi wanda sukayi jaa sosai, jijiyoyin kanshi duk sun fito sosai yace   yess hamman I have just 10 percent in me, and I can t have children if I loose those percentage,  & magana hammam ya soma da fada fada yace   what!! Oligospermia!!!!!kaga matsalarka Kenan, tun last year nace maka, we should find solution tun kafin abin ya zama worst, shin kasan male infertility yayi destroying mutane da yawa, naka da sauki ma tunda ance zaka iya haihuwan, amma yanxu with 10 percent chance idan kayi loosing komai fah, gashi kana da saurin feelings, waima tsaya how did dis happen? I thout last time da mukaje kaga doctor ya baka magani kuma naga dai kai ba neman mata kake  & & ..runtse ido yayi baya ma son tunanin abunda yayi causing duk wannan matsalar tashi, kallonshi hammamn ya kumayi yace   amar talk!!...dagowa amar ya sakeyi ya kalleshi yace,   dude I just don t want to talk about it, yanxu solution kawai nake nema, I don t even want Amma to know about this because she will be so disappointed, cos tun ba yanxu ba take so nayi aure ta samu jikoki but na hana hakan faruwa, hammam please tell me what to do, kaina duk ya kulle  & .shuru hammam yayi yana nazari sannan yace   solution daya ne kamar dai yanda na fada maka last time, you just have to get married tunda dai bazaka haihu ta hanyar zina ba,  shuru amar yayi yana nazari sannan ya kalleshi dakyau yace   but..but..  katseshi hammam yayi da cewa  but you don t want to get married outside your culture ko?, I knew that s what you want to say, well wannan kuma ya rage naka, solution dai daya ne, get married fine. 
Gyara zama amar yayi yana fuskantar hammam   kai maysa kake haka ne, kasan cewa niba kula mata nake ba  yatsine fuska yayi sannan ya cigaba   kuma kasan cewa bazan iya auran wadda ba culture na daya da nata ba, I mean ni bana son auren larabawa irin ku, kai kasan yanda auren culture ku yake, complications din akwai yawa, on top of that ma, kai kasan bakwa auren bare and bayan wannan ma,kuma karkayi tunanin Nigeria, don I don t know how on earth you expect me to find someone in just couple of days to bear child for me, bama wannan ba kasan yanda nake da kyankyanmi I cant just share bed with anyone  & kallonsa kawai hammam yake baki galala yana mamakin amar da yanda yake magan yana tabe baki kamar bayason maganar ma, girgiza kai kawai hammam yayi ya miqe yace   you are not serious dude, ni zan tafi duk sanda ka shirya then call me, ina nuna maka gabas kana yamma, inaga baka fuskanci me 10percent din nan ke nufi ba, inda ka gane tashin hankalin cikin haka da ko begger ka samu zaka aura ka dura mata sauran abinda ya rage maka  ..yana kaiwa nan ya sa kai ya fice, takaici ne ya turnike amar, tabbas abinda ya fada hakan ne ba karya yayi baa, saidai baya tunani zai iya yin haka, dakinsa kawai ya wuce ya watsa ruwa mai dumi sannan ya saka shorts da farar tight vest ya kwanta.

Tunda amra sukayi maganar katin kasa da haifa hankalinta yaqi kwanci, duk tunani ya dabaibayeta, abu daya ne ya tsaya mata rai, auren da taji haifa tace secretary din abu tayi, wanda batajin zata iya wannan.
Wunin ranar adaki tayi shi, babu abinda take sai zullumin jiran call din haifa.

Haifa kuwa tana komawa gida ta kwanta baccinta dukda damuwar amra ta saka ta a gaba , saida tayi baccin kafin ta yi wanka ta shirya cikin kayan shan iska sannan ta wuce wajen abu, nan ta sameshi yana zaune yana riqe da newspaper, gaishesa tayi sannan suka dan taba hira, daga bisani ta tambaye shi secretary dinshi, kallonta yayi da mamaki yace wace secretary din, bata boye mashi komi ba ta kwashe duk labarin amra ta fada mashi, jinjina kai yayi da tausayin amra sannan yace   gaskia na tausaya mata don qawar Kirkice a wajen ki haifa, but ina son ku sani nemen katin qasa is a long process and it takes years kafin mutun ya samu, but zan baki contact info na secretary jemima tunda itama tana daya daga cikin wanda sukayi applying kuma suka samu sai tayi maku bayi  ..godiya sosai haifa tayima abu kafin ya bata number.
Bayan ta koma dakinta ganin dare yayi yasa ta fasa kiran jemima a lokacin saita bari sai gobe da safe.

Washe gari kuwa Sunday, da matsanan cin ciwon kai haifa ta tashi, bayan tasha magani ta kwanta sai wajen asr ta tashi, koda ta tashi kan nata ya lafa, abinci kawai ta nema sannan ta lalubi wayanta domin kiran jemima,tana bude wayan taga missed calls birjik a wayan, daga wajen amra da hammam, saida ta fara kiran hamman tukunna suka sha hiransu ta masoya sannan sukayi sallama.
Amraa na ganin call din haifa wadda daman tunda ta tashi take zullumin kiranta yasa tayi sauri daga wa tace  haif, ina kika aje wayanki, inata kiranki baki dauka.  Da sauri haifa ta soma mata Magana   I m so sorry habibty, yau da ciwon kai na wuni,  shuru amra tayi tana sauraron bayani, jin hakan yasa haifa cewa   yauwa ban fada maki ba,na samu contact din secretary din abu jemima, yanxu haka ma muna gama waya dake zan kirata,  murna fal ciki amra tace   bari na kashe saiki kirata, please duk yanda kukayi ki kirani immediately  kit ta kashe.. murmushi haifa tayi don ta ji yanda amra taji dadin wannan batun samun contact din jemima.

Zama tayi gefen gadonta sannan tayi dialing contact din jemima, saida tayi mata kira biyu ana uku tayi picking   hello, this is jemima how may I help you  , jin haka yasa haifa saurin cewa   hii jemi this is haifa abdul-samad shuraim,  jin sunan haifa yasa jemi saurin cewa   ohh hy haifa, how are you?, how s sir abdulsamad, and family?  & & gaisawa sosai sukayi ta mutunci kafin haifa ta soma mata bayanin kiranta da tayi, jimm kadan jemi tayi sannan tace   I really don t want to ever talk about my own experience but I can t say no to abdulsamad family, so fix a lunch day and forward the details to my sms, lets meet up tomorrow by 4pm,  jin haka yasa haifa saurin cewa thank you so so much jemi, I will surely booked and send you the details, nagode sosai  .. sallama sukayi sannan ta kashe wayan, tana kashewa kiran amra na shigowa don duk ta kosa,dagawa haifa tayi cikin murna da farin ciki ta shaida mata komai sannan sukayi sallama.
?
Washe gari da safe da wani irin dadi da farin ciki amra ta shirya cikin shigarta ta kamala abaya ce kalar burnt orange har kasa, tayi rolling veil din fuskarta fa yau babu komi sannan ta fito domin zuwa wajen aiki.

Tana sauka daga motor direct cikin asibiti ta wuce lokacin haifa ma bata karaso ba, saida tayi round checkup kafin ta koma office din haifa don jiranta, batafi minti goma da zama ba haifa ta dira, tana shugowa suka rungume juna sannan suka fara aiki atare, lokacin sallah nayi suka wuce masallaci, suna idawa suka dawo asibiti don rounding up komai don yau da wuri zasu tafi sbd appointment dinsu da jemi.

Amar kam, abubuwa sunyi mashi yawa, don yanxu akwai sabon policy ta yake shirin budewa a cikin headquarters akan staff da dama, duk aiki yasha mashi kai, anatse yake komai cikin office dinshi, hankalinshi nakan system, jin knocking din kofa yasa shi dago kanshi, ganin hammam yasa ya tamke fuska, sai yanxu ya tuna da matsalar da yake ciki, don kwata kwata yama manta gaba daya, takowa hammam yayi ya samu waje ya zauna wajen da aka tanada don baqi sannan ya fuskanceci yace   dude whats up, daga fada maka gaskia sai shariya kuma, anyways hope yanxu ka samu naka solution din tunda wanda na baka which is the fact that I stated baiyi maka ba huh??   amar baiko kalleshi ba yace   muje muyi salla lokaci yayi  , atare suka sauka domin zuwa masjid,saida suka idar sannan aka kira hamman wani office don zaiyi wani aiki, nan sukayi parting ways shi kuma amar ya wuce office dinshi don ya kammala aikin nashi da wuri.
?
Karfe uku daidai suka fito, ko wannen su dauke da handbag dinshi maqale a hannun, direct moton haifa suka wuce, bayan sun shiga suka fuce daga premises din wajen.

Adaidai lushrose restaurant suka tsaya bayan haifa tayi parkin suka fito ajere, direct table din da haifa tayi reserving suka zauna, restaurant din is so peaceful, babu wani hayaniya sannan ko ina is private, zama sukayi a sit din mai dauke da kujeru uku, anatse haifa tayi masu ordern cool smoothie bayan an kawo masu suka fara sha kafin jemi ta karaso.

zaman minti talatin sukayi saiga wata ta karaso table din, tana zuwa tace   heyy girls, I m so sorry for being late  , murmushi ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?haifa tayi don ta santa sosai tace   hey jemi, welcome  zama jemi tayi ah empty kujeran gefensu wadda itace ke facing dinsu sosai, jemi black African ce, kana ganinta, batada wani qiba sosai doguwace kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login