Showing 366001 words to 369000 words out of 381117 words

Chapter 123 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1978

amra tayi alamun gamasuwa kafin ta juya wajen Hamad ta fara mashi wasa& &

Yamma nayi wajen karfe shida saiga abbansu yazo, tarba ta mutunci ammah tayi mashi sosai anan sitting room don Har abunci saida salima ta ajiye mashi da lemuka agabanshi bayan sun gaisa da ammah.

In kunga babansu amra kamar bashi ba yayi qiba sosai kamar ba labaran ba, sai yanxu nake Ganin girmanshi ya fito sosai, kudi sun zauna mashi, Har lokacin idan zai gaisa da ammah saiya dan dukar da kanshi koyaya ne.

Gaba daya saukowa sukayi suka gaisa dashi Banda amra dake kwance a daki saboda ciwon kai data wuni dashi, bata ma san yazo ba,

A parlor kuwa gaba daya suna zaune a sitting room Harda Aman wanda yanxu ya daina biye kanshi, don bayan sunyi magana da salima haka ya fada courage dinshi yaje Har gidan gona ya nemi Afuwan Abban su akan abubuwan da yayi mashi, tashun farko labaran ya nuna mashi Ay komai ya wuce daman bai rikeshi da komai, Aman yaji dadin haka sosai don baiyi tunanin haka abban nasu keda sauqin kai ba.
Gyaran murya Abban nasu tayi yace  muhammd baya nan ne? Banga sirikinsa Nawa ba?
Ammah ce ta dan murmusa tace  Ay yau tun safe ya futa bai wuni a gidan bama

Sallamar salima ce ta katse su, hannunta rike da Hamad da Hamid, tana karasowa ta mikama Abban su, fuskanshi duake da murmushi ya karbe yace  Masha Allah Yan dugul dugul an fara girma Allah ya Raya
Gaba daya amsawa sukayi da Ameen.

Salim ne ya matso inda yake yace  abba yau Zan bika
Sunkuyar dakai labaran yayi yace  Ay bani zaka tambaya ba malam

Sallamar Amar ce ta katse su, anatse yake tafiya cikin kamewa har ya karaso parlorn, yana karasowa ya duka ya gaishe da malam labaran,
Cikin fara a ya amsa shi inda yake tambayarshi ya aiki da hidimar iyali.

Basu wani jima ba aka kira sallar magrib don haka suka wuce masjid gaba dayansu achan ma sukayi alwala sukayi sallar isha i

Ammah ma sama ta wuce zuwa nata bedroom din tayi sallar kafin ta futo sanye da hijab ta wuce dakin amra, da sallama ta bude dakin ta shige hannunta rike da wata katuwar paper bag.
A zaune ta taddata kan sallaya tana lazimi, karasowa ammah tayi bakin gado saida ta idar kafin ta nannade sallaya ta mike jiki a mace ta karaso bakin gado ta dan duka tace  barka da dare ammah
 Barka dai my dear,zauna
Zama amra tayi tana fuskantarta,  daughter naga Duk kinyi sanyi yau dinnan Akwai abund ake damunki ne? Ko baki son komawa chan ne?
Saurin girgiza kai amra tayi kanta a kasa  ah ah ba haka bake kaina ne kawai ke min ciwo
 Toh Allah ya sawaqa,
Kanta a kasa ta amsa ammah da  Ameen
Shuru ne ya biyo baya kafin ammah ta janyo paper bag din ta bude, wani box ta fara fiddowa ta ajiye akan cinyar amra  daughter ga wannan, kyauta ce dana so na baki tun watannin baya da suka wuce,
Kallon box din amra tayi kafin ta dago kanta murya ta chan ciki tace  ammah& .
 Karki ce komai daughter kyauta ce kawai nayi maki okay?
Girgiza mata kai amra tayi kafin ta sauke kanta kasa  thank you so much ammah Allah ya Kara arziki da budi
Ammah bata amsa ta ba ta fidda wani hadadden laffaya orange color wanda yasha stones sosai, kana Ganin lafayan kasan ba anan akayi shi ba, designer ne mai Kyan gaske,

Ajiye mata shi ammah ta gafenta tace  ki shiga ki wanka saiki saka wannan ki sauko Abban ku yazo yana jiranki
Ammah na kaiwa nan ta mike tsaye,  ki hanzarta
 Tohm ammah amra ta fada jiki a mace, ammah na fita tabi lafa yuan da kallo, hannunta dayasha red henna ta daura akan lafayyan, kafin ta maida hannun nata kan box din, kamar wadda ke jin tsoro haka ta soma bude box din, idanunta ne ya sauka akan tapkekiyar sarkar gold da dan kunne awarwaro Harda zobe dake ta faman sheki, wato idanu tayi waje taba kallon sarkar, wani irin dadi ne ya ziyarceta, babu abunda take a cikin zuciyarta sai godiyar Allah daya azurtata da sury Ka ta gari mai so da kaunarta ada ita ba kowan kowa bace sai gashi lokaci guda Allah ya sauya mata rayuwa.

Jiki a mace ta mike ta wuce bathroom tayi wanka a gaggauce Har ta fito daga wankan jikinta a mace yake kamar Ana tura ta,
Bata tsaya wani kyale kyale ba ta bude wardrob dinta ta janyo wata atamfar super wax Riga da skirt sai set of bra da pants da under skirt,
tana daukowa ta ajiye akan gado ta wuce gaban dresser ta dan goga mai kadan a jikinta, tana gogawa ta wuce gaban gadonta ta soma shirya wa, cikin Yan mintuna qalilan ta gama shirya wa ta Dora lafayan akan atamfar nata, gashinta dake a kwance lub ta kwance ta tattare shi baya kafin ta daura dankwalin atamfar, tana gamawa ta bude box din sarkar da ammah ta bata ta saka sarkar da dan kunnen,
Tana gamawa ta rufe box din ta Adana shi cikin bedside drawer kafin ta wuce gaban dresser ta kurama kanta kallo, tayi masifar kyau sosai dukda batayi wani kwalliya ba a fuskanta ba don ko kohl babu a idanu ta, ko a jikinta tana jin rana irin ta yau ta fita daban, sai a yanxu take jin wani iri, Anya zata bishi kuwa? Maysa ma zata bishi?, she s happy zamanta haka nan daga ita sai yaran ta da ammah babu wnai stress dinshi saidai bazatayi jayyya da maganar ammah ba don haka ta dan fesa ma kanta turare mai sanyin kamshi, tana nan tsaye Salim ya shugo dakin  adda abba yace kizo
 Gani nan ta amsa shi tana ajiye kohl din data dauka ta dan goga a fuskanta, kafin ta juya ta zura bedroom slippers dinta ta nufi hanyar futa daga dakin nata,

Anatse take saukowa kasan harta karaso sitting room, babu kowa a parlorn sai abbansu don haka tana karasowa ta dan duka domin gaishesa, fuskanshi duake da murmushi ya kalleta ya mata nuni da gefen da yake zaune kan kujera, hankali ta tako tazo ta zauna nan gefen nashi kanta a kasa don lokaci guda taji wani irin sauyi a tattare da ita,  Alhamdulillah!!! Godiya ta tabbata ga Allah daya kaddara mana yanda rayuwar mu zata kasance, Aisha!! Ya kirata anatse,
Dan dagowa amra tayi idanu ta Har ya dan fara jaa tace  naam abba!
 Aisha kiji tsoron Allah kina da ilimin addini dana Boko daidai gwargwado, Ina jin takaicin shekarun da akayi mana iyaka dashi, wanda yasa banga tasowarku ba ammah Ina alfahari dake da macen da kika zama, ayanxu ke uwace ga yara har uku wanda suka zama kamar kyautar allah, aisha kiji taoron allah kiyi ma mijinki biyayya karki bani kunya, aljannar ki na kafarshi Wallahi aisha idan kika kuntata mashi bazan iya yafe maki ba, wannan bawan Allahu da mahaifiyarshi sun gama yi mana komai a duniya, maganar da kikayi min kwanaki ta girgiza ni don idan har kika tafi da wannan kudi don a ranki to tabbas kinyi butulci, allah ya rufa maki asiri ya Baki miji na gari ya Baki sirikarta ta gari da bakinki kince min yanda yake kula dake kamar ita ta tsugunna ta haifeki,don haka nake fatan ki faranta ma danta ki mashi biyayya, ki zama madafar da zata sanya mashi nutauwa ki kawo mashi kwanciyar hankali a rayuwarshi don da haka ne kawai zaki saka ma hajiya da abunda tayi mana, I trust you my daughter and I m proud of you, Ina fatan allah ya baku zaman lafiya ya kore maku Duk wata futina kinji ko?
Amra dake kuka shabe shabe don ba karamin dukan zuciyarta kalamanshi sukayi ba sosai,

Hannu abbansu yasa ya goge mata hawayen ya cigaba  kibi mijinki ki mashi biyayya sannan kiyi hkuri a Duk yanda kika tsinci kanki kiji?
Girgiza mai amra tayi tana hawaye Bakinta na karkarwa tama rasa me zata ce mashi,
Salima ce ta sauko kasan hannunta rike da hamad da Hamid, gefen ta salim ne shima rike da princess, zama sukayi gaba dayansu nan Abban su ya fara nuna masu girman halacci, waazi yayi masu sosai mai shiga jiki sosai dazai amfani rayuwarsu, amra dai na daga gefe tana hawaye Har lokacin,& ..

Bayan ammah ta futo daga bedroom din amra dakinta ta wuce direct ta soma dialing contact din Amar, yana daukan wayar tace  idan Ka gama Ka same ni a bedroom dina,
Daga chan ya amsa da tohm kafin ya kashe wayar,
Yana kashe wayar ammah ya gaggauta goge jikinshi da towel dinshi, yana gamawa ya tsaya gaban dresser yayi yan shafe shafenshi, yana gamawa ya tsaya baki gado yana kallon kayan dake gabanshi, wata bugaggiyar gezner ce fara tass sai kyalli takeyi, Daukan inners dinshi yayi ya zurasu
Cikin Yan mintuna qalilan ya gama shirinsa, Kyan da yayi na daban ne ma yau dinnan kamar wani Sabon ango, fuskanshi fayau, babu abundake kunshe a zuciyarshi sai fargaba Mara dalili,
Saida ya gama feshe jikinshi tass da turarukanshi kafin ya zari wayarshi da laptop dinshi ya wuce dakin ammah, lokacin daya futo babansu amra na zaune baima Lura da fitowan shi ba don haka ya wuce sama, alokacin da ya shige dakin ammah a lokacin amra ta sauko kasa wajen babansu.

Da sallama ya shige dakin ammah, tana zaune bakin gado har a lokacin sanye take da hijabi, saida ya gaisheta kafin ya zauna,
Fada sosai ammah tayi mashi inda ta nuna mashi mahimmacin amra a rayuwarshi da yayanshi, sun dade sosai tana mashi fada mai shiga jiki kafin su fito a tare,

Hannunta a cikin nashi suka sauko kasa, zuwa sitting room Har lokacin amra kanta a kasa yake tana hawaye, suna zama ammah ta Dora daga inda Abban amra ya tsaya, fada sosai sukayi masu a tare mai shiga zuciya kafin baban amra yayi masu sallama don kusan karfe Tara na dare.
Yana tafiya ammah tace  ya kamar ku wuce kuma don dare nayi sosai
Mikewa sukayi gaba dayansu inda ammah tayi masu sallama daga nan sitting room, saurin rungumeta amra tayi tana hawaye, dabbing bayanta ammah tayi tace  daughter kukan ya isa haka, zai dunga kawo ki ay, gasu salima nan zasu dunga zuwa Ay suma
Ta dade sosai a jikin ammah tana hawaye, Amar dai fucewa yayi ya barsu anan sitting room din,
Sallama ammah tayi mata ta wuce sama don itama jikinta yayi sanyi.
Ammah na wuce sama suka fito a tare dasu salima da triplets, gaban Ind akayi parking suka tsaya, daya bayan daya amra ta karbi yayanta tana kissing dinsu taba hugging dinsu, tana jin kamar karta tafi saidai bazata iya yi hakan ba, amar dai na daga zaune a cikin motar yana jiranta, ganin lokaci na tafiya ya futo daga motar shima ya karbi yayansa yayi kissing dinsu kafin ya bama su salima suka wuce dasu cikin gida don baya son Ana futa dasu da daddare.
Suna wucewa amra Har alokacin kuka takeyi shabe shabe , bai kualata ba ya shige cikin motar tana Ganin haka ta bude gaban motar itama ta shige kafin ya jaa motar suka bar compound din.
Tunda suka futa daga estate din babu abunda takeyi sai kuka ahankali, yana jinta Har lokacin baiyi kokarin lallashinba kwata kwata, Har suka karaso gidan shi larrics, yana parking ta bude motar bata ma taaya kiranshi ba ta wuce wajen entrance ta tsaya, saida ya rufe motarshi ya bi bayanta yana kallon yanda take qunquni,

Gefe ta matsa mashi ya bude kofar yana budewa ta shige ciki ta tsaya kikam a sitting room kamar wata soja, don haushinsa take ji sosai, ahanakli ya karaso inda take calmly ya soma mata magana  Aisha!!
Bata motsa ba kwata kwata daga inda take harya karaso inda take tana Ganin haka Tayi saurin jaa baya,
Murmushi kawai yayi don yasan halin nata zatayi shi kuma baya jin yana da lokacin wannan don haka baiyi wata wata ba ya sungumeta, babu zato ba tsammani ta jita a sama, wutsilniya ta fara yi tana san ya sauketa yaki, karshe ma dai fashe mashi tayi da kukan shagwaba, yana jinta babu abunda yakeyi sai murmushi, bai tsaya ko Ina ba kuwa sai bedroom dinshi tana nade a hannunshi, harya karaso bakin gadonshi ya ajiyeta akai,yana ajiyeta ya danyi baya yace  wait for me here karkiji ko ina
Wata yar harara ta Galla mashi kuka ya gani saidai kawai yayi dariya aranshi yace  Zaki I kaniyanki ne yau dinnan yana kaiwa nan ya fuce daga bedroom sun ya sauko kasa, kowani ango yana shugowa dakin Amarya ma da kaza shi kuwa general sai ganinshi nayi da flower, wata katuwar rose mai shegen kyau da tsada ya zaro daga bayan booth dinshi, yana daukowa ya rufe motarshi ya koma cikin gidan, yana shugowa ya rufe kofar mai entrance din ya wuce sama cikin izza da kamewa,
Bedroom dinshi ya wuce direct har alokacin fuskanshi dauke da murmushi yana bude kofar yaga wayam,& .
[7/11, 11:18 PM] +218 92-2035171: Last Update part 2
Shuru ya danyi son yasan zata iya guduwa don haka ya fuce daga bedroom din ya nufi nata dake next floor yana zuwa ya nufi hanyar bedroom din nata,
Hannunshi ya fara sanya akan handle din kofar, yana danna handle din kofar yaji a rufe, shuru ya danyi yasa kunnenshi jikin kofar nan ya soma jin kukanta na Tashi a hankali,
Gyara tsayuwar shi yayi kafin ya soma magana  Aisha open up let s talk
Banza tayi dashi kamar batasan yana yi ba saida ya sake maimaitawa,
A taqaice sai ya dauka kusan 30mins yana karanta taki bude kofar saima Kara saurin kukanta da tayi, ranshi ya sosu sosai saidai yana kokarin dannewa saboda ayanxu dole ya lallabata,  okay shikenan ki kwanta ku huta pls ki dina kukan nan
Yana kaiwa nan ya ajiye mata yar bunch of roses din a gaban dakin ya wuce sama zuwa bedroom dinshi, yana shiga bedroom dinshi ya soma rage kayan jikinshi zuwa pjs, kafin ya kwanta ranshi Duk a dagule, dukda yaji zafin abunda tayi mashi hakan baisa yayi gushi da ita ba don yanzu ya koyi yanda zai dunga controlling anger dinshi.

Washe gari da safe amma ta aiko driver da breakfast,
Haka ya sauko kasan da kanshi ya karba hasket din kafin ya wuce dining dashi, da kanshi ya koma sama zuwa bedroom dinta yayi mata knocking shuru bata bude ba, ya dauka kusan minti goma yana knocking Ganin bata da niyar budea Yasa ya kyale ta ya wuce bedroom dinshi, wanka yayi ya sauya kaya zuwa kamani kafin ya sauko kasan for the second time ya sake yi mata knocking,  Aisha!!! Shuru babu response at that Point hankalinshi ya gama Tashi don haka yace  dan Allah say something mana? Are you okay
Daga ciki ta amsa shi da  yes I m okay
Wata nauyyyay ijiyar zuciya ya sauke kafin ya sauka kasa yayi breakfast dinshi yana gamawa ya fuce daga gidan gaba daya don he s preparing for something.

Bai dawo gidan ba sai wajen karfe uku na rana, Yan shugowa part dinta ya wuce yana zuwa yayi knocking Har lokacin bata bude ba saima kukanta daya jiyo, at that point yakai maqura don haka yace  what s the meaning of this aisha? What is wrong with you? Nace Zan mai wani abu ne ko nayi maki wani abun ne? At least ki fito kici abunci karkiyi ma kanki illa
Shuru tayi banza dashi saima daga karshe yaji tace  ni bana jin yunwa
Shuru kawai yayi ranshi ya sosu sosai don haka ya kyaleta kawai tayi abunda yake so.

Bangaren amra kuwa ta zabi zaman dakin ne saboda bata son anything dazaiyi encountering dinta dashi, ga ciwon mara daya dan riketa ya hanata sukuni,

Duk wannan magiyar daya dunga yi mata bai sata ta bude kofar bedroom dinba tana zaune a bakin gado wani irin haushinsa takeji Har barci ya kwashe ta, washe gari haka ta lallaba tayi wanka ta sauya kaya zuwa wasu marasa nauyi dake Jere a cikin wardrobe dinta wanda tun last zuwanta suke cikin wardrobe din, tana gamawa tabi lafiyar gado abunta.
Tana daga kwance ya sake yi mata knocking lokacin da aka kawo breakfast, harga Allah yunwa take ji sosai saidai taurin kanta yasa taqi futo wan balle taci abuncin.
Sai wajen yamma bayan data gama galabaita ta bude kofar ta sauko ta diba abuncin ta koma daki ta sake kullle kofar.

After 2days&
Haka suka dunga wasan buya ita dashi inda ya kyaleta kawai don baya son takurata saidai Duk Safiya saiya leko bakin kofar dakin nata yayi knocking ya duba lafiyarta, wani sa in tana amsa shi wani sa in kuwa bata kulashi haka zai tsaya inya gaji yayi tafiyarshi.
A cikin kwanakin kullum amma ke aiko masu da abunci Duk Safiya da yamma.

Bayan sati guda zaman dakin ma ya gudureta da kanta ta soma futowa tana saukowa kasan tana shiga kitchen ta dafa ma kanta abunci, don yanxu saidai ya fita ya sayo takeaway ya aje mata nata don baya son ya dunga zuwa gida saboda Kar ammah tayi sensing wani abu dukda ya sayo komai na provisions da za a iya dafawa..

Bangaren su ammah, gidan is so lively, daman gida indai da yara bazai taba zama shuru ba, Salim ya koma school, salima kuwa yanxu itace kamar second mum din triplet, itace cin abuncinsu itace wankan su Dukda sometimes tare da ammah suke yi, don yawanci ma a dakin ammah suke wuni gaba daya, yara dai sai girma suke sai san barka kwata kwata basa koke koken neman uwarsu, daman inkaji yaro na kukan neman uwarshi to fah yunwa ce, su kuwa basa Shan komai sai madara da puddings.

Aranar labaran yazo gidan don amsa Kiran da ammah tayi mashi, bayan ammah ta sauko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login