Showing 96001 words to 99000 words out of 381117 words

Chapter 33 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2009

haka bata damu da wanda ke gefenta ba da yake a rufe ba, baka ganin wanda ke ciki ta zauna, wayanta ta fidda ta soma zafafan hotuna Harda tsaida wata crew ta sakata yi mata hotuna, cikin qanqanin lokaci jirginsu ya daga.

Saida tafiyan tayi nisa har aka fara zuwa rabon wine da juice harda starter ga masu buqatan Ana zuwa wajensu kuwa matar ta tambayeta abunda yake buqata, ba tare da bata lokaci ba tace red wine, nan take matar ta zuba mata, kallon gefenshi matar tayi tare da zagayowa gefenshi tace  sir would you like to have anything, juice,water,wine
Cikin dakakkiyar muryarshi kamar na zaiyi magana ba yace  no thanks
Jin daddadar muryarshi yasa hameeda sako kanta don ganin mai maganar, nan take idanunta suka sauka akanshi, cikin sauri ta koma ta zauna tana wani murmushi mai ma anoni daban daban, kallon matar tayi tace  can I get something else please
Sauya wine din tayi zuwa juice, tunda ta tabbatar shine ta Kasa sukuni, fatan ganinshi kawai takeyi don gaba daya bangarenshi a rufe yake, goga kuwa bai Ma san tanayi ba don tunda tazo gabanshi dazu kallo daya ya mata yaji kyankyamin ta a gabanshi yasa manta da ita nan take, don bashi da time din irin wannan matan.
Saidai yayi mamakin jin bahaushiya dake kusa dashi wanda ta buqaci a bata giya saidai shiga hurumin da ba nashi ba baya cikin tsarinsa don bai fiye bama mutane attention ba.
Tana nan zaune aka soma kawo abunci nan take ya bada order abunda take so still tana fatan ya zuge nash bangarenshi saidai bata samu daman hakan ba, kofa suka tambayi abunda yake buqata, juice kawai yake su kawo mashi nan take kuwa aka kawo mashi hadadden juice tare da glass cup, matar na kokarin zuba mashi takalmin kafar ta yayi slippering ta zuba mashi juice din akan jacket din daya daura kan farar rigarshi, Allah ya taimaka bai zuba a jikin white Riganshi ba, hankalin matar ne ya Tashi ta soma bashi hakuri, kai kawai ya girgiza mata ya miqe zuwa toilet ba tare da kallon gefenshi ba, gyaran wajen data bata mashi crew din tayi karfin ta koma don kawo mashi sabon juice din,yana shiga toilet din ya Gyara jikinshi kafin ya futo, meeda kuwa da taga wucewanshi toilet cikin sauri ta bi bayanshi, yana bude kofar kuwa zai fito ta kame hanyar ta zuba mashi idanu kamar mayya tace  do you need any help?
This time around tsayawa yayi ya mata kallo tsab take ya gano itace ta buqaci wine, mamakin yanda yayan musulmai suka lalace yakeyi qira qira yasan tayin wani abun yake mashi daban saidai bata san cewa shi ba irin mazan nan bane ba, Karon farko ya bude bakinshi dake kamshin mint yace  you re so disgusting,get the hell out my way
Ya fada idanunshi sun nuna babu wasa a cikin zancen nasa, a burkice ta matsa mashi baya dinta tsorata da yanayinshi tana nan tsaye wata crew tazo wucewa yace  get me head of Crew staffs now!!!!
Wucewa yayi nan kuwa meeda ta tsaya kyam don Duk ihun nan dayayi akan idanun mutanen dake zaune kusa da toilet dinne, kunya yasa ta komawa cikin toilet din ta rufe kanta a ciki.
Goga kuwa ya shaka sosai, don haka head of staff na zuwa babu bata lokaci ya buqaci roll guda ba tare da kowa ba, Allah yaso kuwa Akwai roll din da babu passengers nan take ya sauya zuwa chan don baya buqatan hayaniya dukda Sai ya biya kudin roll din gaba daya wannan ba damuwa shi bane don kudi kam Akwai su.

Ganin zaman cikin toilet bazai amfane ta da komai ba sum sum ta fitowa wuce wajen mazauninta, baby kuwa da take Yan gaba gaba me zatayi Banda dariya don akan idanunta akayi drama din. Kwafa tayi tace  shegiya kai taurin kai da zalama, maganinki kenan, nan gaba bakya kara tunkarar irin wadannan yan girman kan ba

Meeda kuwa tana komawa seat dinta ta kame, ganin baya wajen yasa ta jin wani iri, saidai tayi alkawarin koma waye shi saita nemo shi kuma ta nema abunda take buqata.

Karfe takwas daidai jirgi su na emirate ya sauka ah Nnamdi azikiwe international airport abuja, saida kowa ya tsaya akayi clearing ko ina kafin ya sauko cikin isa da kasaita, nan fa kowa ya soma kallon isa da harkar manya cikin Yan kallo kuwa Harda meeda wadda yanxu kam ta cire rai don taga fin karfi nesa ba kusa ba, gaban jirgin motoci manya manya kusan guda biyar a jere hade da sojoji suka zo tarbanshi, dan wannan official zuwa ne ba normal zuwa da yake yi ba na visiting Ammahn shi,Sara mashi aka soma hi kafin a bude mashi katuwar lexus baqa tinted, sauko wa yayi hannunshi rike da jacket dinshi Dayan kuma ya zuba cikin aljihun wandonshi, direct gaban Lexus din mai plate number hade da sunan TAURA a kasan da manyan harufa ya tsaya sojojin suka soma Sara mashi irin gaisuwar su ta sojoji, kamewa yayi bayan motar kafin a rufe mashi suka juya harsuka fuce gaba daya da tawagar datazo tarbanshi.
Ranar kuwa abuja ta shaida babban sojan uae ya iso nigeria, wanda basu san da zaman shi bama su san da zamanshi ba sun sani saidai kuma babu wanda yasan fuskanshi.
Bude laptop bag dinshi yayi ya fidda da wallet dinshi da yake zuba Duk wasu sims dinshi na kasashe daban daban, Ciro din din Nigeria yayi na mtn ya bude wayanshi ya musansa ya aje na uae, yana kunna wayan ya soma dialing wata number ya kara kunanshi Ana dagawa daga chan akace  oga harka iso kenan
 Wannan mutanen fa daka hadoni dasu, kasan fa bana son hayaniya, infact bana son Adam na shigo kasar nan Ma sbd aiki ne zamuyi cikin sirri

 Toh ka fa dawo kenan, anyway na turo su ne sbd bazan samu zuwa tarbanka ba
 please call them, bana buqata su

 Okay, anyway gida zaka wuce yanxu? Zan shigo anjima daman nasan ni mai laifi rabona da Ammah tun bayan rasuwar dada,

 No karka damu ba gida Zan wuce ba, heading somewhere else, zamu hadu gobe kawai
 Yes ranka ya dade sir
Ya fada yana dariya kafin ya aje wayan.
General asad Abdullah kenan da ga abokin Alhaji taura kuma babban aminin sa tun tasowarsu, shima mahaifin sa ya rasu saidai zumuncinsu bai dauke ba tsakanin yayansu dukda ba wani kusanci suke dashi sosai ba, asad shima soja ne mai rike da babban mukami na chief of army staff anan Nigeria(lieutenant asad Abdullah) ya girmi Amar sosai saidai yanda Amar keda kwarjini zaka dauka zai ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?fishi ma.

Kallon sojan driver yayi bayan ya gama wayan yace  to larrics estate
 Yea sir yayi saurin amsawa
Maida kanshi yyi bayan kujeran ya lumshe idanunshi Har wani bacci baccin gajiya ne ke neman fuzganshi.
Horn din da driver yayi ne ya tabbatar mashi da sun iso, drivern yana parking yayi saurin bude mashi bayan motar futo cikin kamewar shi, tunda ya sanya kafafunshi kasa yake jin wani irin niima na saukar mashi, kamshin kasa da bushiyoyi tare da sanyin dake kadawa ne ya bade ko ina, lumshe idanunshi yayi kafin ya soma takawa gaban entrance din, cikin sauri driver ya karaso gabanshi ya Danna door bell din tare da janyi baggage dinshi, bude kofar da akayi ne ya sashi dago kanshi, Nadine data bude kofar saida tadanyi baya, sauke kanta Kasa tayi kafin tace  welcome sir
Don Duk kwarjininshiya cika ko ina, ba tare da ya kalleta ba ya raba gefenta ya wuce ciki, saida ya karema ko ina kallo kafin ya juya ya kalli Nadine data karaso da akwatinshi da laptop bag dinshi, sama ya wuce tabu baya shi da akwatinnashi,karema gidan kallo yayi tsab babu abunda ya sauya Sai furnitures da yasa aka sauya zuwa sabbi, gidan yana daya daga cikin properties dinshi daya gina da kudinsa saidai bai banbantashi da saura gidajenshi ba da yake hadawa da inkiyar sunan familynsu wato TAURA
First stair ma ya fara hawa saida ya tsaya ya karema ko ina kallo kafin ya hau sama da yake na master bedroom a ciki Sai tapkeken sitting area Harda dining, bude kofan bedroom din yayi direct ya saka kanshi ciki, yana nan yanda yake saidai kayan alatu shima da aka chanza, Nadine kuwa tana karasowa daidai gaban dakin ta aje akwatin tareda Rossi awara gaishesa, bai kalleta ba ya amsa da  uhm bai sake cewa komai ba saima kafama babban frame din dake gefen bedside dinshi idanu yayi, hotone shida dadan shi lokacin da yana school yazo mashi surprise visit, muryar Nadine ne ta katse shi don yana dauka ta fuce  sir do you need anything
 no thanks ya amsa
Yana son tambayarta inda yarinyar nan take saidai kuma ya basar yace  you are excuse
Tana shirin futa yace  just coffee in the next 1hr
 Yes sir tayi saurin amsawa 
Sauko wa tayi ta wuce dakin amra, wadda tunda ta zo kwana biyu kenan bata lekowa ko ina, abincin Ma daki Nadine ke kawo mata shi, bude dakin Nadine tayi ganin an rage hasken dakin Saina bedside yasa ta kallon fuskanta mamakin yanda ta dage da kuka kullum wanda ya sanya idanunta yin ciki ciki Nadine keyi saidai bata taba tambayarta dalilin hakan ba don ba huruminta bane, gani ko taba abuncin ta saya kawo mata batayi ba yasa ta jawo mata kofar ta rufe ahankali, Kasa ta sauka ta fara diban time gudu min karya wuce lokacin daya buqaci coffee.
Wanka ya farayi kafin ya futo daure da towel, closet dinshi ya bude ganin komai nashi yana nan yanda ya barshi yasaashi yabawa da company daya bama maintainance din gidan hatta sabulun shi da abubuwan buqatanshi Duk an zuba mashi a ciki, jallabiya ya zura ya tada kabbarar sallah, saida ya Rama Salomon da ake binshi kafin ya miqe ya sauya zuwa kayan baccinsa farare don kusan karfe 10 na dare kenan, knocking akayi ya bada umarnin shigo, aje mashi coffee din tayi kan table kafin tace  sir here s the coffee bai kalleta ba haka zalika bai amsa ba, ganin kamar bai Jita bane yasa ta maimaitawa
Gyaran murya kawai yayi yace  you re excuse
Sum sum ta fuce ganin yanayinshi na rashin magana,
Saida yasha coffee don ya janyi laptop dinshi ya soma wasu Yan ayyuka, Sai kusan karfe 1 ya aje laptop din ya rage hasken dakin ya kwanta.

Washe gari kuwa a kunnanshi aka kira sallah asuba, dadin gida kenan, muke wa yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa mai zafi kafin ya futo Sai zuba kamshi baths dinshi yake, gajeran wandonshi ya saka kamar koda yaushe kafin ya zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin, benne farko ya fara sauko wa ganin ko ina dim ya sashi sauka kasa, nanba dai dim dim babu hasken kirki saina censor light din daua tsaya a wajen, fucewa yayi daga gidan ya wuce massallacin dake cikin estate din, masllacinma haduwanshi ma yakai a fada, ko ina kamshi da sanyin ac ya gama bade cikin massalaci tsaf tsaf very clean, very few mutane ne a cikin masallacin hakan yasa Ana idar da sallah mutane suka soma ficewa, zama yayi saida yayi azkar Sai wajen karfe bakwai ya fito daga masallacin, direct gidanshi ya wuce Nadine dake goge goge tana gani shi ta rissina tace  good morning sir
Daga mata kai kawai yayi ya wuce sama direct dakinshi, jallabiya shi kawai ya tube ya fuce daga dakin, second floor ya sauka ya wuce Dayan dakin dake gefe inda yake gyming dinshi don baya sake da physical health dinshi, ya dauka kusan awa daya da rabi kusan karfe 8:30,futowa yayi ya wuce sama ba tareda kallo side din Dayan dakinba da yake kyautata satin anan take kwana, wanka ya shiga nan ma saida ya shafe kusan 30mins ya fito, shirinsa yayi kamar na jiya saidai na yau din yafi na jiya kyau, yauma wa don army ne a jiki shi hade da rigarsa saidai ya daura had dadi yar jacket dinshi a sama, briefcase dinshi ya jawo tare da wayanshi ya sauko Kasa Sai baza kamshi yake, yana sauko wa Nadine na futowa daga cikin kitchen, da sauri tace  breakfast is ready sir
Baibi ta kanta ba ya wuce dining tayi serving dinshi chips da beef sauce da soyayyan plantain, da coffee, kadan ya tsakura yaci kafin ya kira driver yazo, kika mashi briefcase dinshi yayi yace  get the car ready now
A Gurguje ya gama shan coffee din ya fuce daga gidan, gaba daya, Nadine na ganin fitar shi ta tattara dining din ta deba na amra ta wuce sama don kai mata nata.
Lokaci data shiga dakin babu kowa a ciki, jin alamun saukan ruwa ya tabbatar mata tana wanka, Ajiye tray din abunci tayi gefen ottoman din dake hade da gadon kafin juya ta rufe mata kofar dakin, futowa amra tayi daure da towel dinta, gaba daya fuskanta ya dan kumbura alamun damuwa da kukan da take,ganin tray agefe ya tabbatar mata da nadine ce ta aje mata, agurguje ta shirya cikin kayan zaman gida masu kyau, doguwan rigace mai Dan hannu,kayan ya amsheta sosai, zama tayi ta tsakuri abunci ta soma ci badon ranta naso ba saidan yunwa dake nuqurqusar ta, wayanta ta jawo ta soma kiran haifa saidai kwata kwata wayan baya shiga, gaba daya ta rasa abunyi, babu irin tunanin da batayi ba, da farko ta yanke shawarar gudu kano saidai kuma bata san daga inda zata fara ba ga tsoron abunda zata tarar achan, saidai kuma tunanin qannenta ya bata karfin gwaiwar komawa don sanin halin da suke ciki gashi ba wani kudin kirki yake dashi ba gashi batama kawo zancen ragowar kudinda yake dashi cikin account dinta na chan ba don indai anyi banning dinta daga shiga kasar account dinta shima dole za ayi banning.
Tagumi ta doka don gaba na daya abun duniya ya isheta.

Wunin ranar kamar kullum a daki tayi shi bata leko koda parlor ba haka zalika nadine ma batace mata komai ba akan zuwan shi.

Karfe goma sha daya ya shugo gidan, nadine ce ta bude mashi tare da mashi barka da zuwa, baibi ga kanta ba ya wuce sama, saida ta tabbatar ya huta kafin ta Kwankwasa mashi
Kofa, tana shugowa tace  what would you like to have sir
 just coffee
Ya amsa mata,
Futa tayi ta Hado mashi coffee din kafin ta fuce, coffee din yasha kafin ya wanke bakinshi kafin ya fito yabi lafiyan gado don yasha aiki sosai.

Washe gari Ma haka ya Tashi da wuri ya fuce bai Ma tsaya yin breakfast ba, don ya samu Kiran gaggawa daga wajen asad inda yake shaida mashi sun samu clue akan wani member na empire saidai tracing dinshi ne ya basu wahala sosai don sun Kasa samun hanyar da zasu Farke mashi, sunma Kasa gane waye saidai ta wani account da akayi transacting wasu kudade in dollars wanda yanda suka gano hakan shine sun bibiyi account din suspect din da aka kama achan uae tana suka gane inda yake transacting kudin,bai samu dawowa da wuri ba Sai wajen karfe sha daya.

Washe gari kam bai Tashi da wuri ba Sai wajen karfe sha daya, wanka kawai yayi don weekends ne bashida plans din futa, sitting room ya sauko ya zauna bayan ya gama karin kumallo, wayanshi ne rike hannunshi yana receiving wasu calls masu amfani, yana gamawa ya danyi jin yanason kiran ammah ya shaida mata yana Nigeria saidai kuma yasan zata fara expecting dinshi shikuma bayason zuwa gidan saiya gama Ayyukan da yake, bayaga wannan bayason taji ya na nigeria a wani wajen, dialing number yayi, tana picking kuwa suna gaisuwa ta soma tambayanshi yaushe zai zo Nigeria ta matsu ta ganshi,
 Ammah zanzo very soon Insha Allah
 babana, na Kasa gane dalilinka na qin zuwa kasarka inda aka haifeka,
 Ammah please calm down shikenan zanzo next week Insha Allah
Sanin baya mata magana biyu ya sata saurin cewa  da gaske son
 In sha Allah ammah
 Alhamdulillah Allah ya kawo ka lpy, yarannan ma are so excited to see you

 Uhm suna zuwa school din kuwa
 Sun fara zuwa fah, saidai Muhammad baka min bayani ba yanda Zan fahimta,

 Amma ki bari idan nazo Zan maki bayani dallah dallah
 Toh Allah ya kawo ka lpy
Sallama sukayi kafin ya kashe wayan ya fuskanci katuwar tv dake aiki babu sauti sosai

Bude kofar dakin tayi ta fito, sanye take da doguwar rigar abaya sky blue tasha stones,fuskanta fayau babu walwala, idanunta sunyi ciki ciki da alamu ta danyi kukan da ta saba ne,babu komai a kanta Sai ribbom data nade jelar gashinta dashi duban parlorn ta soma yi kafin ta wuce stairs cikin nutsuwa kanta a Kasa take takawa harta kai karshe stairs din, bata tsaya dube dube ba ta gifta parlor da yake zaune ta wuce kitchen direct,alamun saukowanta hade da takun ta cikin natsuwa ya ankarar dashi,zuba mata kyawawan idanunshi yayi har ta shige kitchen, yana nan zaune idanuwanshi kan hanyar kitchen din ta fito hannunta dauke da bottle water mai sanyi tasha kusan rabi hannunta dafe a goshinta,harta sanya kafarta kan stairs ta tsaya chak, wasi wasi ne ya shiga ranta na kamshin sa dataji lokaci guda ya shiga hancinta, kalle kallen hanyar shugowa ta soma yi har lokaci. Idanunta bai sauka ga sitting room din da yake zaune ba runtse idanunta tayi ta bude jin jira na neman Zubar da ita lokacin da idanunta suka Sarqe cikin nashi, kamar a mafarki take ganin komai, rufe idanunta tayi ta sake budewa akansu, Har lokacin shima idanunshi nakanta, kafin ya kauda kanshi gefe kamar bai ganta ba, kafafunta ne suka Gaza daukanta saida ta dafe handle din stairs din,miqewa yayi ya soma takowa, Duk takun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login