Showing 213001 words to 216000 words out of 381117 words

Chapter 72 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2032

maka zakayi ba don Karan kanka zaka karbeta da hannu bibiyu, Ka sauke hakklinta dake kanka kuma Ka girmamata a matsayin matarka Ka kula da cinta shanta damuwarta da lafiyarta kai harma da Gurin kwanan ta,Ka aje wannan banzan tunanin naka Wai tayi maka kankanta karya ne wannan, Ka godema Allah ma ta karbeka hannu bibiyu kaida baka haihuwa, haka ta salwantar da Tata rayuwar ta karbe Ka ba tare da second thoughts ba hmm
Shuru yayi kamar ruwa yaci shi haka ammah ta silleshi tass ta mashi fada tare da nuna mashi inda baiyi daidai hade da shawarwari da nasiha don tunatar dashi ilimi da yake dashi, tunda ta fara magana harta gama kanshi a qasa idanunshi sunyi jaa sosai,  yanxu ka kai shekaru 35 wadannan abubuwan bai kamata ace ni Zan fada maka ba da ilimin Ka da tunanin ka ammah ta karashe tana kokarin gyara kwanciyanta, saurin mikewa yayi ya tallabota ta kwanta yace  Insha Allah za a gyara in Allah ya yarda
 Allah yasa ta bashi amsa tana rufe idanunta har barci ya kwasheta yana nan zaune ya dafe kanshi yana nazari daban daban, idan ya saka chan saiya warware nan, kwata kwata bai runtsa ba ko kadan maganganun ammah nayi mashi yawo akai,yanxu dole yayi abunda taa umarceshi ba tare da gardama ba.

Washe gari da safe shi da kanshi ya goge ma ammah hannunta da fuskanta da kafafunta don bata fara anfani da ruwa da kanta ba,saida ya gama, ya daura mata alwala ya zura mata hijab ta fada sallah anan zaune, fita yayi ya wuce kitchen ya basu orders abunda doctor yace zata dunga ci da sha Mara nauyi kafin ya dawo dawo dakin, lokaci daya dawo harta idar da sallah tana zaune, kallonshi tayi harya karaso tana lazimi kafin yadan duqa  good morning ammah na an Tashi lpy ya kwarin jiki
Dan sakin fuskanta tayi ba tare da ta kalleshi ba  morning, Ka Tashi lapia ta amsa shi
Shuru ya danyi baice komai ba don ya Lura da yanayinta Har lokacin tana fushi dashi kenan
Sallamar doctor ce tasa suka dago gaba daya, gaisawa sukayi ya duba ammah, kallon doctor sun tayi tace  yau zaku sallameni ko?
 Ah ah hajiya sai nan da kwana hudu haka
Yana kaiwa nan ya fuce, kallon Amar tayi tace  kaje kasan yanda zakayi su sallameni yau yau dinnan idan ma zasu hadani da home care taker ne su hadani da ita dan bazan zauna ba
Ta karashe tana kauda kanta gefe, sum sum ya juya ya fuce daga cikin dakin ya wuce office din doctor, nan ya buqaci a bata sallama, da farko doctor yaso qin amincewa sai daga baya Ganin ran shi a bace yake yasa ya bata sallama ya hada ta da home care taker nurse don ta dunga monitoring dinta,
Dakin ya koma nan ya tadda har an kawo mata tea tana kokarin sha hannunta na karkarwa, saurin karasowa yayi ya karba cup din don ya taimaka mata, bata hanashi ba ta bashi cup din, haka ya dunga bata tea sun harta shanye kafin ya aje ya janyo white carrot soup, kauda kanta gefe tayi  tea din ma ya isa
Bai kusa ba ya aje bowl din ya tura shi gefen, sallamar su salima ce ta sa suka juyo gaba dayansu daga shi Har ammah, salima ce ta fara shugowa hannunta rike da basket sai Salim a gefenta, kafin amra sai Aman dake biye da ita abaya yana latsa waya, gaba Dayan su matan sanye suke da abaya mai shegen kyau,
Kallonsu ammah tayi fuskanta dauke da murmushi idanunta kan amra tace  daughter maraba lale shugo,
Da fara a amra ta karaso hannunta rike da water flake babba, kallon food flakes din ammah tayi tace  yanxu babu wanda zai dauko flakes sun saike daughter? Ki bar masu su dauka mana karki wahalar da kanki
Salima ce ta turo baki tace  oh ammah wannan yar warayya da akeyi mana ni ban ganeba fah, nice na kinkimo garin basket fah amma ko kallona bakiyi ba
Dariya ce ta kufce ma amra  kedai Allah ya sawaqe maki wallahi
Murmusa wa ammah tayi tace  ahh dear harda fushi kuma, kema na ganki Wallahi, bismillanku ku shigo
Atare Duk suka karaso gabanta suka gaisheta cikin girmamawa, amsawa tayi tana jin dadin gani su kafin su zazzauna,  daughter zo daga nan naji lafiyanki
Takowa amra tayi feeling so shy yanda ammah ke nuna kulawa a gareta ta karaso, hannunta ammah ta rike tace  Ki ci abunci dai ko? Hope babu abunda ke damunki?
Girgiza mata kai amra tayi tace  babu komi ammah na, I m perfectly fine, yanxu burinmu kema allah ya Baki lafiya mu tafi gida atare
 Ay yanxu ma kuwa zamu tafi, Yan yakaddun sallama muke jira
Salim ne ya karaso wajen ammah ya rungumeta don murna tana Ganin haka itama ta rungumeshi tace  yaron kirki you can t wait mu koma gida ko?
Girgiza mata kai yayi yana fidda set of hakoranshi.

Suna nan zaune Madina ta shigo da sallama, kallonta duka sukayi gaba daya Harda ammah  lale maraba likitar mata, sannu da zuwa
Cikin fara a Madina ta karaso Har bakin gadon ta zauna tare da dan dukawa tace  Ina kwana hajiya? Ya jiki? Allah yasa kaffara ne
Gaba daya suka amsa da Ameen,
 Ay jiki yayi sauqi my dear, yau zasuyi min sallama ma Insha Allah
 Masha Allah Allah ya Kara sauqi Madina ta sake fada, bata wani dade ba tayi masu sallama don zata wuce office.

Karfe goma sha daya daidai doctor ya shugo da paper sallaman ammah,Ka karamin dadi duka suke jiba musamman salima da amra don sunyi missing dinta sosai gidan babu dadi kwata kwata, don itace farin ciki kowa gaba daya.

Akan keken marasa lafiya aka saka ammah while aka hadota da wata nurse da zata dunga dubata daga safe zuwa dare, atare Duk suka fito Amar ne ke tura keken ammah Har zuwa parking space, bayan motarshi aka bude ya sanya ta aciki kafin nurse din ta zagaye gefen ammah ta zauna, amra dai juyawa tayi zata shiga motar Aman inda su salima ke zaune, saurin tsaidata yayi  Aisha!!!!
Chak ta tsaya bata sake motsawa ba saida yace  get in
Juyowa tayi ta nufi gaban motar ta bude ta shige ciki ta zauna shima ya shige mazaunin driver ya kunna motar ya saka seat belt, kallonta yayi fuskanshi babu yabo ba fallasa yace  fasten your seat belt
Dan juyawa tayi ta kalleshi don this is the first time daya taba ce mata ta saka seat belt yawanci shike saka abunshi,dan tabe baki kawai tayi ta janyo seat belt din, haka ta fara kokawa da seat belt din saboda yayi stocking, waigowa yayi ya kalleta, kafin ya dan matso kusa da ita sosai ya janyo belt din ya saka mata, yana saka mata ya koma mazauninshi, Duk wannan abun nasu akan idanun ammah dake smiling tana sunnar dakai kasa, she s so happy seeing them like this fatanta Allah yasa ya dore a hakan&
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!!
Unedited&
Tunda ya kunna motar yayi reverse ya bar harabar compound din ya dau hanyar zuwa gida, motar tayi tsit sai karar ac, motar su salima na gaban tasu inda salima ke zaune agaban motar sai Salim a baya har suka karaso gida.
Tunda sukayi parking kowa ya fito ya nufi inda ammah ke zaune a bayan motar Amar na shirin fitowa da keken da za a sakata, da taimakon nurse Amar ya fito da ita, kafin su wuce cikin gidan gaba daya,babu wanda yakai su salima jin dadin dawowarta,suna biye da ita har suka shiga parlor, bin parlor ammah tayi da kallo kafin ta fara hamdala, salima ce Tayi saurin cewa  welcome back ammah, gidan was so empty bakya nan, yanxu ya zama complete Alhamdulillah!
Dariya Duk sukayi ammah dake zaune kan wheelchair ta fuskanceta tace  Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kaddarar hakan zai faru, Ina rokon Allah ya tsare mu daga Duk wani sharri na fili dana badi ni
Gaba daya suka amsa da Ameen, sama Amar ya wuce da ita tare da nurse, saida ya tabbatar she s comfortable kuma babu abunda zasu buqata ita da nurse din.
 Son kaje Ka huta, hidiman ya isa haka, tunda ga nurse nan zata taimaka min ammah ta fada tana kallonshi bayan ya taimaka mata ta zauna bakin gado, murmushi kawai yayi ya kalleta cikin kulawa  Akwai abunda zaki buqata a sayo?
Hannunshi ammah ta rike don yana tsaye bakin gadon  no son, kaje Ka huta you look stressed
Murmushi kawai yayi mata kafin yayi mata sallama ya futo daga dakin, da amra yaci karo dake shirin shugowa, batayi expecting mutun zai bude kofar ba don haka yana bude tayi baya saboda ta ciki aka budo, saurin rike hannunta yayi don yayi tunanin faduwa zatayi  careful!!!!
Ya fada ahankali kamar ba Amar ba, saurin cire hannunta tayi daga nashi tace  thank you , bai tsaya ba ya bar wajen, ya dauka kasa, yana wucewa ta shige cikin part din ammah, dakinta ta wuce direct ta bude kofar da sallama, kallonta sukayi gaba daya daga nurse din Har ammah fuskanta dauke da murmushi ta karaso bakin gadon ammah ta zauna tace  ammah kina buqatan wani abu? Me kikeso na daga maki?
Kallonta ammah takeyi tana murmushi fadin irin dadin da take ji idan ta kalli amra ma mai wuya ne, Nunfasawa ammah tayi fuskanta duaie da murmushin bata daina ba tace  daughter daga dawowa ko hutawa bakiyi ba, gashi alamu sun nuna jin fara nauyi, karki damu kinji, bana buqatar komai yanxu kije ki kwanta ki huta, Kisha barcinki kinji ko?
Sauke kai amra tayi dukda bata gane akalar zancen ammah ba sai kawai ta tsinci kanta da jin kunyar ammah lokaci guda, kallonsu nurse din tayi fuskanta dauke da murmushin tace  gaskia kam, barci nada amfani a wannan stage din da drinking lots of water
Shuru amra tayi don bata gane kan zancen ba,gaba daya sun gama confusing dinta, ammah na Ganin haka Tayi saurin cewa  kije ki huta daughter dake da son bansan waye yafi wani damuwa akaina ba, I will be fine
Mikewa amra tayi jiki a mace tace  Toh shikenan ammah, Zan dawo anjima
 Toh daughter Allah ya kaimu ammah ta fada tana godiya ga Allah a cikin zuciyarta
Futa amra tayi zuwa dakin ta don agajiye yake sosai dukda batayi wani abun gajiyan ba, abun yanxu ya daina bata mamaki kwata kwata, yawan barci, da mood swings ga changes da yake gani a jikinta, bata kawo komai aranta ba sai maybe stress din jigilar asibiti da suka dunga yi wanda tana tunanin idan ta samu ta tsaida natsuwarta guri daya komai zai daidata.

Tana shiga daki ta rage kayan jikinta ta shige bathroom ta watso ruwa mai dumi kafin ta fito daure da towel, gaban dresser ta tsaya tana son shafa mai saboda skin dinta dake zama dry sosai cikin kwanakin saidai kuma qiwar yin hakan na cinta sosai, lumshe idanunta tayi jin barcin na neman fuskaganta  wannan wani irin yawan barci ne haka nake yi
Ta fada tana Mirza idanunta da hannu, kallon kanta tayi a jikin mirror, yau kusan sati biyu kenan rabon da ta kalli kanta a mirror haka, ta dan kara qiba kadan don cukowar tafi futowa akan fuskanta fuskanta ma yadan kumbura kadan, shafa face din nata tayi kafin ta juya ta nufi kan gadon, zama ta fara yin tana tunanin abubuwa da dama, sauke idanunta tayi akan feet dinta Ganin kamar sun dan kumburo kadan, bata kawo komai aranta ba ta basar da komai tabi lafiyar gado cikin mintina kadan barci ya fusgeta.

Bayan futarta ammah ta kalli nurse fuskanta dauke da murmushi tace  is it obvious?
Kallonta nurse din tayi tana kokari balle magungunan da ya kamata ta sha yanxu kafin yamma tayi,  yea ma
Nurse ta amsa ta tana murmushi, murmusawa itama ammah tayi tana kara godiya ga Allah.

Tun bayan yabar dakin ammah dakinshi ya wuce direct, gaba daya agajiye yake don kana Ganin fuskanshi kasan he s stressed, gajiya ne sosai a tattare dashi, yana shugowa dakinshi ya wuce bakin gadonshi ya aje keys dinshi kafin ya fara kokari cire wrist watch din hannunshi, yana cire ya ajiye gefen gado tare da wayarshi kafin ya wuce closet room, cikin natsuwa ya bude kofar ya shige ciki ya soma rage kayan jikinshi saida ya rage daga shi Sai shorts dinshi kafun ya futo, yana fitowa toilet ya shige hannunshi sanye cikin gashinta yana hautsina Ganin nasa,cikin shower ya tsaya ya sauke shorts din nashi kasa ya kunna tab din ya rike kugunshi, ruwa na sauka akanshi yana tunanin maganganun ammah,bazai taba take zancen ta ba don haka dole yayi abunda yake so don ya faranta mata,na farko yanxu zai fara settling case din daddy ya cireshi daga hannunsa yabarma su asad don daman niyarshi ya tafi dashi chan dubai don ya hukunta shi achan don anan bazai iya hukuntashi ba saboda bashida wannan right din don ba Nigeria yake ma aiki, chan dubai kuwa babu wanda zai hanashi hukuntashi, shiyasa ya nemi asad ya karba mashi approval ko kuma ya karba da kanshi hannun president don abu ne mai sauki a wajen shi, kira daya zaiyi mr president zai sa abashi approval saidai baya son bin wannan hanyar don kamar ya karba ne ta inda dole abashi ba saida approval din military din Nigeria ba don case din na hannun su shiyasa asad ya dage akan ya bari ya karba mashi da kanshi idan sunyi approving.
Shampoo dinshi ya dauka ya latsa a hannunshi ya goga a gashinsa dake sheki, ya dauka kusan awa guda yana gida chan yana wanke chan,Har shaving gashin bakinsa saida yayi yana gamawa ya futo feeling refreshed, don kwata kwata tun bayan admitting ammah da akayi a asibiti bai samu time din yin komai ba musamman kula da kanshi daya saba yi koda yaushe, anatse ya fito qugunshi daure da towel harya karaso gaban dresser dinshi, Yan shafe shafen shi yayi ya feshe ko ina na jikinsa da body mist dinshi kafin ya wuce cikin closet room.

Cikin Yan mintuna kalilan sai gashi ya futo a shirye cikin kananun kaya da sukayi mashi kyau, Riga da wando, rigar ta kamashi sosai musamman wajen damtsen hannunshi gashi tabi lafiyar fatar jikinshi don six packs dinshi sun fito ta cikin rigar, agurguje ya janyon wrist watch dinshi ya saka kafin ya janyo wayarshi da car keys dinshi.

Anatse ya futo daga part dinshi ya tsaya ya karema gidan kallo, gidan is so big yanxu tunanin yanda zaiyi da help din da zata dunga taimakawa wajen Gyaran gidan yake don Yan matan gidan kadai bazasu iya ba,gashi dalilin abunda ya faru yasa baya jin zai iya trusting wata house help ayanxu, harma da professionals helps dukkansu baya jin zai iya yarda da kowannensu ayanxu.
Kauda kanshi gefe kawai yayi ya fuce daga cikin parlor zuwa motarshi, yana shiga motarshi ya kunnata yayi reversing kafin ya fuce daga gidan gaba daya.

Salima dake tsaye a kitchen tana kiciniyar dora lunch a kitchen ita kadai don kafin ta sauko saida ta Leqa dakin amra Ganin tana barci yasa ta sauko kasa kawai don bata son tashinta don alamu sun nuna agajiye take yanda take yin barcin a wahale,
Sanye take da simple doguwar riga mata nauyi hannun rigar ma karami ne sosai,gaba daya kana ganinta kasan tana cikin walwala saboda ammah, Bude freezer tayi ta fiddo Jan mama da kayan miya, naman ta fara sarrafawa kafin ta bude fridge ta fiddo veggies ta fara yankawa anatse cikin kwarewa, jin alamun shugowa mutun cikin kitchen din yasa ta dan juyo, idanun su ne ya sarke dana juna, kallon kallo suka fara na kusan minti biyu don Har wukar hannunta na neman gifcewa daga hannunta harta gives ya fadi kan kafarta,  ahhh wayyo Allah na 
Ta danyi Kara tana duban kafarta, da sauri ya karaso inda take tsaye tana kokarin dukawa, da sauri ya duka ya fara duban kafar nata yana dan fada  why are you careless sai jin jika kanki ciwo jin tsaya kina kallo na kamar zaki cinyeni
Saurin fusge kafarta tayi ta kalleshi  yaushe na kalleka?
Dagowa yayi tsaye ya mata kallon ko in kula yace  yanxu mana,
 Saidai in kaine ke kallo na ta bashi amsa tana kauda kanta gefe, matsawa baya shima yayi ya tabe baki yace  why are you denying bayan na kama ki?
 Hmm da wani idon kasan Ina kallonka in kaima ba kallo na kake ba ta bashi amsa tana kokarin dora carrot daya akan chopping board ta fara yankawa aqule, don maganar shi ta kona mata rai sosai, bai sake kulata ba ya bude fridge ya janyo hallandia yogurt, duban kitchen din ya soma yi yana neman glass cup don baisan inda suke ajiye wa, tana Lura dashi don jefi jefi take kallon side dinshi kafin ta kauda idanunta don karya kamata, ganin duban nashi yaqi karewa gashi cups din na drawer da yake tsaye, runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta ajiye knife din ta karaso gabanshi, yana Ganin yanda ta taho ya danyi baya ya jingina da gefen cupboard din drawers din, matsawa tayi daf dashi sosai don nunfashinsa na gogan juna ba tare da ta kalli fuskanshi ba ta zura hannayenta ttsakanin shi ta janyo drawer ta fidda glass cup kafin ta rufe drawer ta danyi baya, kallonshi tayi ta miqa mashi cup din ba tare da tace mashi qala ba, kallonta yayi kafin ya maida idanunshi kan cup din, karba yayi atsanake ya hada da hannunta, wani irin shock tayi saidai bata nuna hakan ba saima zame hannunta datayi ta danyi baya ta koma inda take tsaye tana yankan veggies don,  thank you! Ya fada ahankali yana kokarin bude


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login