Showing 249001 words to 252000 words out of 381117 words

Chapter 84 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2039

ta bude idanun nata, koda ya kalli cikin idanunta saida yaga yanda yayi jaa sosai kamar agwashi,   menayi maka meysa ka tsaneni?da kake kokarin forcing kanka a jikina,wallahi yaya bazan taba yafe maka ba idan kayi sanadiyar abunda ke tattare dani, ban taba tsammanin zaka gwada min how merciless you are ba sai yanxu 
Jikinshi ne yayi sanyi don sai a lokacin ya lura da abunda yaso yi, wanda bait aba tunanin zaiyi hakan ba a gareta dukda ita halas dinshi ce, bashida burin forcing kanshi a jikinta, ayanxun ma baisan mey ya hau kanshi ba,fushin da yayi yasa ya kasa controlling zuciyanshi, saurin mikewa yayi daga kanta jikia mace ya soma maida wandonhi, yana gamawa ya yi unbuttoning rigarshi, baima gama saka rigar ba ya kalleta   the next time kika sake yin abunda kikayi yau bazan daga maki kafa ba,and it will be worst than this 
Ya karashe yana juya mata baya yana runtse idanu, he can t belive abunda ya fada mata bayan kuskuren dayaso tafkawa, wani irin haushi da takaicin kanshi yake ji,azafafe ya nufi hanyar kofar ya bude, ya fuce yana jin haushin kansa, bai ma tsaya ya lura da ammah dake shugowa da ledojin shopping a hannunta ba, gaba daya baya cikin natsuwarshi harya shige daki ammah na kokarin cewa   son..mun.. 
Bata karasa ba ta dubi yanda jikinshi ke karkarwa da yanda buttons din rigarshi suke a bude ya sauko daga sama a harzike, gabanta ne ya dan fadi dukda bata kawo komai aranta ba saidai gabanta daya tsananta bugu saboda tasan shid a zuciya kamar kuturu.

Yana shigewa daki ya dafe kanshi tare da fisge rigar jikinshi,   inaliahi what was I thinking ya allah 
Wani irin zafi da haushin kanshi yakeji tunawa da yanda idanunta sukayi jaa da yanda ta soma mashi Magana a galabaice lokacin da yke kokarin forcing kanshi, runtse idanunshi yayi ya aksa gane dalilin da yasa yake treating dinta haa dukda deep down baya jin dadin hakan shima, saidai wannan banzanego din nashi bazai sashi ya zama remorseful ba, babu abunda yakeyi anan tsaye sai tsaki, ganin hakan da yakeyi bazai maidoda agogo bay aba yasa ya wuce bathroom.

Bayan shigewarshi part dinshii ammah ta bishi da idanu tana nazari kafin ta soma shigewa da abubuwan data sayo kitchen ta ajiye komai inda ya kamata na abubuwan datayi shoping dinsu kafin ta dawo parlor don daukar handbag dinta data ajiye anan parlor, su salima ne sukayi sallama ita da aman, salima ne ta fara shugowa sanye take da uniform a jikinta sai aman dake biye da ita da school bag dinta da books dinta a hannunshi tana mashi shagwaba yana bata hakuri kamar wani mijin hajiya, kallonsu ammah tayi, sun burgeta sosai yanxu ta sake tabbatar da idan aman ya auri salima zai kula da ita sosai saboda irin kaunar da yake nuna mata a fili sosai, jikinta ne ya danyi sanyi tunawa da yanda amar da amra suke zama, suda suke auren juna kwata kwata babu wani kusanci a tattare dasu ko kadan, shi miskili itama miskila, abun yana damun ammah ssoai dukda tasan amar nason amra ammah yana boyewa, bangaren amra ne ma bata tabbatar ba.
  ah ah yau kuma mai kayi mata haka ne take kunkuni 
Ammah ta fada tana kallonsu, matowa salima tayi inda ammah take ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????don sai a lokacin suka lura da ita   barka da yamma amah na ya zaman gida 
  alhamdullahi daughter na ya kike ya exam, an gama lafiya?
  alhamdullah ammah, im so excited jibi grads 
Juyowa aman yayi ya kallesu yana dan murmushi yace   barka da yamma ammah 
  barka dai son, ya hidima da mutuniyar tata, hala kayi mata laifi ne naga tana turo baki  ammah ta fada tana kallonta
  ammah wallahi shine wain ace zan sha icecream ya saya min wai bazai saya min ba haka kawai  salima ta fada tana galla mashi harara
Kallonshi ammah tayi,   haba son, meysa baka saya mata ba 
  ammah wallahi mura takeyi, da safe dana kaita school baki ganta ba she keeps on sneezing kamar hancinta zai fita  aman ya fada yana mata gwalo
  haba daughter yafiki gaskia anan, saboda lafiyanki, yanxu ki wuce sama kiyi wanka saiki sauko kuc abunci, gobe zamuje shopping din graduation 
Cikin zumudi da murna salima tace   yauwa ammah naa, love you so so much 
  love you more my dear 
Juyowa salima tayi ta warci Jakarta ta wuce sama abunta tana jin dadi.

Tana wucewa shima aman ya wuce dakinshi, suna tafiya ammah ta wuce sama itama don dubo amra data bari tana barci, da sallama ta bdue dakin nata, babu kowa a cikin dakin sai karar saukn ruwa, takowa ammah tyi bakin gadon ta dan tsaya tana jiran fitiwarta, idanunta ne ya sauka kan kayan amra dake a yage a kasa sai pant dinta shima da yayi gefe, maida idanunta tayi baking ado nan take idanunta ya suaka kan beddings din daya cukwikwiye kamar anyi dambe ga dan jini akan bedsheets din kadan, hankali ammah ne ya dan soma tashi, ahankali kunnuwanta ya soma jiyo mata kukan amra dake cikin toilet, matsowa tayi da sauri hanyar bathroom din t tsaya bakin kofar tayi knocking, kunnenta ta saka ajikin kofar tana jin yanada take yan surutai   na tsanake yaya, youre so mean, baka da Imani, I hate you 
Azafafe ammah ta donyi knocking kofar,   daugter are you okay? Is everythingwrong, 
Amra dake tsaye gaban shower jikinta a mace tayi zaman dirshan ta mike tsaye ahanakli tana share hawayenta   e..eh.. im fine ammah, wanka zanyi yanxu zan futo 
Komawa bakin gadon ammah tayi ta fara zarya tana son gano wani abu, don tabbas taga yanda ya sauko kasa a hargitse,   badai muhammd forcing kanshi yayi akan yarinyar nan ba  ta tambayi kanta, fadin irin tashi hankalin da ammah ta shiga bata lokaci ne har saida amra ta futo daga bathroom kanta a kasa, idanunta yayi jaa sosai, hannunta ammah taja suka zauna baking ado,   daughter meya sameki, meysa idanunki sukayi jaa?  shuru amra tayi ta sauke kanta kasa   kaina ke ciwo 
  karkiyi min karya daughter whats wrong? Muhammd yazo wajenki ne? meya maki? 
Kasa dagowa amra tayi haka zalika ta kasa cewa komai,   daugter speak up, baki dauki matsayin uwa bane da kike boye min? 
Hawaye ne suka fara zarya a fuskan amra ta kasa cewa komai,   baki dauke ni a matsayin uwa ba Kenan? 
  ah ah ammah ba haka bane  amra ta fada ahankali kanta a kasa tana hawaye,
  then menene? Whats wrong ki fada min komai mai ya maki? 
Cikin shehekar kuka amra ta soma Magana   ammah bansan meysa ya tsanani ba, bayason ganina, ni na gaji da abunda yakemin, nace mashi bana so ban.. 
Saurin toshe bakinta tayi ta kasa karasawa,   innalillahi wa inna ilaihi rajiun,  
Rungumeta ammah tayi zuwa jikinta tana lallashinta, kiyi hakuri kinji, zan dauka mataki akan wannan, bazai cigaba da wulaqantaki ba idan baya sanki gwara ya rabu dake daina kukan my dear 

Saida ammah ta lalasheta kafin ta umarceta datasa kayan ta kwanta ta huta, futa ammah tayi ta bata space, saida ta sauka kasa ta dumama mata tuwo da take so sosai kafin ta hauro saman, a zaune ta taddata ta doka uban tagumi a baking ado.
Kaarsowa aammah tayi ta ajiye mata abuncin a gefenta   daughter ki daina tagumi babu kyau kinji, kici abunci ki kwanta, ki kwantar da hankalinki zan amshi iyaka dake okay? 
Grigiza mata kai tayi tare da yi mata godiya kafin ammah ta fuce daga dakin.

Dakinta ta wuce direct, koda ta shigo dakin zarya ta soma yi a dakin tana tunanin yanda zatayi da amar, dole saita koya mashi hankali, yana neman rasa yarinyar nan ba tare da saninshi ba saboda wani banzan ego dinshi.

Karfe takwas kowa ya sauko kasa, inda mazan suka wuce masallaci, suna dawowa duk suka wuce dining banda amra dake kwance a daki har lokacin bata fut ba saboda zazzabi daya riketa, tunda ya karas dining din ya gaishe da ammah yaga sauyi a fuskanta, hankalinshi ne yadan tashi don duk tunanin ko yayi mata wani abun ne batare da saninshi ba.
Saida kowa ya gama cin abunci salima ta wuce da plates din kitchen, ammah ne ta miqe tsaye ta kalli inda amar yake zaune kanshi a kasa   ka sameni a sama  tana kaiwa nan ta wuce sama direct
Gabanshi ya fadi dam tunda ta soma Magana harta wuce sama, jiki a amce ya mike yabi bayanta zuwa dakinta, da sallama ya shiga dakin a zaune ya taddata baki gado, kaarsowa yayi anaste ya zauna bakin gadon nata gefen da take zaune,   barka da dare ammah 
Bata amsa shi ba ta soma Magana   muhammd bansan haka ka koma very rutheless ba, bansan yanxu ka sauya ba zuwa mara tausayi da tawakkali, bayan wannan ban taba tunanin zaka take maganata ba, amma bbu komai, tunda ka kafe baka jin shawara sai abunda kaga dama kuma kake so kake shikenan zan barka kayi, saidai wallahi ian fada maka saikayi regretting nan gama, now inason ka saki yarinyar nan, zan nema mata cikakkayan namiji wanda ya fika komai na aura mata shi, kai kuma inkaga dam aka mutu a haka ma bazan kara yi maka maganar mace ba, 
Dammm yaji gabanshi ya fadi da sauri ya dago kanshi ya kalli ammah,   ammah.. 
 shut up my dear, wallahi saika saketa tunda dama chan kace baka buqatarta baka sonta, I was so selfish dana bar yar mutane a hannun wanda baisan darajarta ba idanda nasan haka zaka wulaqantata wallahi da tun wuri na barka ka saketa taje ta auri wanda take sotunda ba sonta kake ba, yarinya son kowa qin wanda ya rasa, wallahil azeem idan yau ta fita saita dawo da namijin da ya fika komai, kyau dai allah ya bata, uwa uba halayya na gari,ga rufin asirin miji, don duk abunda kake mata bata taba futowa ta fada min ba, she cares so much for you, abuncin da zakaci inda zaka kwanta gyaran part dinka dukda batada lafiya bata tsallake duk wani abunda ya danganceka ba, ammah maita samu daga gareka? You keep on pushing her, making her feel miserable dukda na fada maka wallahi bazaka taba samun mace kamarta ba, wadda zata zauna dakai despite halin da kake ciki na rashin haihuwa, haka ta amince ta amshe ka da hannu bibiyu kai kuma baunda zaka saka mata dahsi Kenan right? Toh ka saketa kawai babu dole, allah ya hada kowa da rabonsa, kuma wallahi aurar da ita zanyi to a gentle man dazai kula da ita ya tarairayeta ya bata kulawar daka gaza bata saboda wani banzan ego naka  ammah takai karshe tana haki kamar tayi tseren gudu.
Hankali aatshe amar ke kallonta yama rasa mai zaice, kasnhi har wani juya mashi yake yi tsabar tashin hankali,   im sorr.. 
  noo o, don t be sorry ba komai ay, wannan ne zabinka ay, kuma abunda kake so Kenan so ka saketa kawai ba damuwa nagode da nunamin da kayi ban isa dakai ba 
  ammah dan allah kiyi hakuri wallahi ba haka bane, kin isa dani, banida kamarke a zuniyar nan, wallahi na karbeta as my wife, 
Nunfasawa ammah tayi idanunta ya rufe sosai   ay Magana ya kare, nabaka nan da sati guda ka sakar min yarinya, bata buqatar wanda zai dunga kunsa mata bakin ciki a zuciya, 
  ammah please&   amar ya fada idanunshi sunyi jaa bakinshi har karkarwa yake
  don t please me, wallahi kaya yanda nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba, kuma youll regret it na fada maka, and nan da 1week ka ajiye min takardar yarinyar nan simple, now fita min adaki, I don t want to sight you anan 
Tana kaiwa nan ta nuna mashi hanyar futa, jiki a amce ya mike, duk duniya bayan ranar da ammah ta fadi bait aba shiga tashin hankali ba sai yau, gaba daya yama rasa tunanin da zaiyi harya shige cikin bedroom dinshi yana furta innalillahi a zuciyarshi , yanda yake zaarya tsakanin dakinshi da parlon shi zaka dauka ya zaunce ne,   noo please ammah, wallahi bazan iyaba ba 

Aranar dai amar bai samu wani abu da ake kira da barci ba, don a zaune ya kwana, idanunshi yayi jaa kanshi sai sara mashi yake sosai, fadin irin tashin hankalin da yake ciki bata lokaci ne, gaba daya yama rasa irin tunanin da zaiyi game da lamarin daya bijuro mashi.

Washe gari very normal amra ta sauko kasa, don ammah da kanta tazo dakin ta ta tasota akan ta sauko kasa suyi breakfast, tana zuwa dining din ta taddasu zaune gaba dayansu, ammah na ganinta tayi mata nuni da kujerar gefenta   zoki zauna nan daughter 
Dagowa amar yayi ya kalli inda zata zauna din, kujeran da ammah ke nuna mata ta zauna dake kusa da ammah,sauke kanshi yayi yana jin wani iri, don sai a yanxu ya fara tabbataer da abunda ammah ke fada, don akusa dashi take zama koda ayushe idan zasuci abunci a dining saidai akasin yau da ammah ta sauya mata gurin zama.
Haka nan akaci abinci kowa da irin tunanin da yake, amar dai da amra baifi spoon biyu sukayi ba, shi abun duniya ya isheshi na abunda ya tunkarosa, ita kuwa shi dinne ma bata son gani kwata kata, don tana shigowa suka hada idanu nan take taji wani irin baqin ciki ya ziyarceta lokaci guda.
Karfe biyu daidai kowa ya sauko kasa, salima da amra sai salim da ammah, gaba dayansu sanye suke da doguwar riga ta abaya, sunyi kyau sosai, futowa sukayi daga sitting room zuwa inda aman yayi parking don dashi zasu fita, amar dake zaune ya hango saukowansu gaba daya, saida gabanshi ya fadi lokacin dayayi arba da amra, tayi wani masifaffan kyau abayra tayi mata kyau kamar balarabiya, shape dinta ya futo sosai kamar ka sace ta ka gudu, she has this attracting look da bazaka iya resisting ba, cikin sauri ya dauke kanshi daga kanta ya hadiye wani irin miyau mai daci,saboda wani irin kallo da ammah tayi mashi, basu tsaya bin takanshi ba suka fuce yana kallonsu shima baice masu qala ba.

Wani makeken shopping mall suka shiga suka fara sayya saida suka jido abubuwa kamar babu gobe, janta gefe ammah tayi tace   ki dunga duba wasu abubuwan na baby saboda da zarar kin shiga 8minth zamu fara sayyayn komai kinji daughter, akwai wasu ma danayi order daga dubai unisex masu kyau, sai next month zasu iso 
Sunkuyar dakai amra tayi tana murmushi, ganin haka yasa ammah cewa   gwara ki ajiye kunyan nan fah my dear   tana kaiwa nan ta wuce wajen da su salima suke tsaye.
Sai wajen karfe biyar takwas suka dawo gida don sunyi yawo sosai inda ammah tace yau ranar salima ne saboda itace graduante,don haka suka dunga zuwa wuraren shakatawa da ciye ciye har suka kai wannan lokacin kafun su dawo.

Lokacin da suka dawo baya gidan do haka kowa ya wuce sama da abunda ya sayo, aranar dai babu maganr girki don gaba dayan su a koshe suke.
Amar kuwa daya dawo yaga sauyi don ko dan coffee da amma ke ajiye mashi ranar batayi ba, gashi baiyi dinner ba, haka nan ya je kitchen ya dauka laban yasha ya koma daki ya kwanta.

Washe gari karfe takwas kowa ya futo cikin shiri, ammah sanye take da wani dakkaken lace mai shegen tsada wanda akallah zaikai dubu dari biyar, gefenta amra ce datasha atamfar super mai shegen tsada anyi mata dinkin doguwar riga A shape gown, rigar tasha stones daga sama har kasa wajen pattern din, sai salima data sha ladies suit blue, tayi masifar kyau sosai dukda batayi kwalliya ba, sai graduation gown dinta data rike a hannun tare da hular gown din, salim ma yasha riga da wando English wears yayi kyau sosai kamar bashi ba.
Kasa suka sauko gaba dayansu nan suka tadda mai gayya mai aiki, yasha manyan kaya shima,   general amar taura 
Wata dakkakkiyar shadda ya saka sky blue sai baqar hula data haskashi sosai yayi masifar kyau don koda suka hada idanu da amra saida ta sake kallonshi kafin ta tabe baki ta kauda kai, abun mamaki shine kayansu sai yazo kusan color daya, don atamfar data saka itama skyblue ce da dan ratsin black don haka ta yafa black veil, aman ne shima ya fito sanye da English wear blue kolor kayan amaryarshi suma sukayi anko, gaba daya suka futo, saida aka zo shiga motar ammah ta kallesu tace   yanxu ya zamuyi tafiyan, mota daya bzai ishemu ba 
Salima ce tayi sauarin cewa   ammah kizo mu shiga motar ya aman, kaima salim ka taho nan, adda ke ki shiga motar ya muhammd 
Hade rai ammah tayi har zatayi Magana aman y ace   yes ammah kizo nan mu tafi su sais u biyomu a baya 
Amra dai babu abunda take sai tabe baki tana jinsu, saidai bata da energy din wani argument, shuru kawai ammah tayi ta wuce motar aman, salim na biye da ita, atare suka shige aman ya fuce da motar while su amra na tsaye, shine ya fara wucewa wajen motarshi yayi reverse zuwa inda take tsaye, saida ta dauka kusan minti biyu tana nazarin kodai tayi zamanta ta fasa zuwa, don bata son su kebance dagashi sai ita ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login