Showing 75001 words to 78000 words out of 381117 words

Chapter 26 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2004

ance, makashinka na tre dakai, alif wato mahaifin hammam ya kwallafa rai akan hammam saidai ganin hazakar amar yasa yaji yana son yaron ya shugo hannu, saidai kashh amar yayi masu nisa sosai, tun alif na saka ran hammam ya zama shugaban armed form wato general har ya kawo yanxu bai kaiba, wanda amar ne ya amshe wannan rank din.
Ayanxu alif bashida wani buri daya rage ya kawar da amar daga mulkin da yake don sauran generals din yanda yake da power yana tunkarar su har ya samu yanda yake so saidai shi wannan tun kafin ya zama abunda ya zama ya kasa tunkarar shi, don uae militriy ke rike da kasar ba sarauta ba ko government saidai mu kami.
Sauke gauran nunfashi hammam yayi bayan y agama dogon tunanin kafin ya gyara kwanciyarshi har bacci ya daukeshi anan wajen.
?
KANO STATE.
Tun bayan ya Muhammad ya kaisu salima asibiti suke samun kyakyawar kulawa sosai, har salima ta farfado saidai salim da yake cikin coma, daki daya ya muhammada ya hadasu, wanda kullum salima tana gefen dan uwanta dukda itama da sauran waraka a jikinta hakan bai hanata kula da kanninta ba, ita ke sauya mashi kaya, ita ke wanke mashi wasu kanannun abubuwan buqatunsu anan asibitin, duk wannan zaman da sukayi da kusan wata guda babu wanda yazo duabasu daga nan gida sai Muhammad wanda shima yadan dauke kafa cikin kwanaki biyu da sukayi a asibitin saidai shi ayyuka ne suka mashi yawa don yana da aikin gaggawa akan Jordan da yake shirin komawa, daman aikin da yaxo yayi anan ba dadewa zaiyi sosai, bangren abinci suna samu cima mai kyau dukda salima ce kawai mai cin don shi salim saidai drip da Karin jini, gaba daya salima ta sauya tayi kyau sosai, ta murmure, dama chan cutar tata harda yunwa ma sosai a jikinta, rana daya tana zaune wajen karfe goma salim ya soma bude idanuwanshi har ya bude su tarr akanta, lokacin tana zaune gefenshi bacci nadan fusgarta,jin alamun motsawa yasa ta farkawa idanunta suka sauka akan kaninta da da ya raege mata a duniya, da sauri ta mike tana hamdala, kallonshi tayi sosai ta kamo hannunshi tace   salim ka tashi, wayyo allah nag ode maka alhamdullillah, bari na kira likita karka rufe idanunka salim gani nan zuwa kaji 
Futa tayi ta kira likta yazo da hanzari ya duba shi, jikinshi yayi kyau sosai saidai yan abubuwan da baza a a rasa ba, cire mashi drip akayi da jini kafin nurses suka taimaka aka kwantar dashi akan kujera, gaba daya ya dawo kamar wani dolo dolo don yanda jikinshi yayi tsami, saidai hawaye da yake yi, da sauri doctor ya kalleshi yace   meke damunka yanxu?  runtse idanunshi yayi yanason Magana amma ina ya kasa, da sauri doctor yace   calm down boy, its okay youre healing, now nod your head idan kana jin abinda nake fada  , gaba daya zuba mashi idanu sukayi har salima da nurses din wajen ahanakli ya soma juya kanshi, murmushi lilkitan yayi yace   hes perfectly fine now, the operation is successfully,  hamdala salima tayi kafin likta ya futa nurse ta tsaya ta zare mashi sauran drip din tare da bama salima daman kula dashi sosai, mikewa salima tayi ta debo ruba a rober da dan towel ta dawo gabanshi ta soma goge mashi jikinshi, murna take sosai, ganin dan uwanta daya rage mata a gabanta ya warke, saida ta gama tass kafin ta maida rubber toilet ta wanke towel din ta futa, yanda ta barshi haka ta same shi anan, zama tayi ta kura mashi idanu fuskarta dauke da murmushi shime kokarin maida mata yake saidai ya kasa don komai nashi yayi sanyi saida taimako, wunin ranar suna zaune ita da kaninta, salla kawai ke miqar da ita shi kuma saidai ya bita da idanuwa don har lokacin jikinshi bai saki ba, saida nurse ta dawo ta sanya mashi drip don bazai soma cin komai ba sai washe gari, ana saka mashi kuwa bacci ya daukeshi, sai a lokacin salima ta samu taci abinci tayi sallloli tare da godiya ga allah kafin ta kwanta a nata gadon gefen nashi, wani irin kuka ne yake ciyo ta, shikenan yanxu adda ta manta mu, wani ririn hawaye ne mai zafi ke sauka a fuskanta,   adda kina ina kika barmu cikin kunshi, adda baki kyauta mana ba kin saba alqawari, kece gatan mu allah allah gatanmu shi kadai ke sonmu, shima ya Muhammad ya tafi ya barmu, kuka ne sosai ke ciyota kafin babci ya kwasheta mai nauyi sosai. 94-95
Abuja Nigeria taura estate&
Alhaji kabiru dake zaune hannunshi rike da news paper ya kalli ammah yace..
 Kin tsaya min aka cirko cirko lafiya, kallonshi tayi daga sama har kasa kafin tace   kabiru what s the meaning of this, menene wannan nake gani?, over 200 million has gone missing? How, kana menene haka acikin wata hudu, amanar dana barmaka Kenan, yanxu idan magajin wannan dukiya ya tambaya me zance mashi?  innalillahi wa inna ilaihi rajiun& kallon ta yayi dakyau kafin ya soma Magana   maryam karki manta ni mijinki ne kuma wannan dukiya da kike Magana akai ta dan uwana ne qanina, me kike nufi Kenan,ke koda ninayi amfani da kudin duk ban a gyaran companying bane, kinada hankali kuwa ko kin manta ni mijinki ne?, da kike Magana magaji magajin dukiyar shi ya damu ne da dukiyar da uban nasa ya bar masa ne? ya tattara ya zabi aikin ma kasar da ba kasar data haifesa ba, gaskia bansan ke butulu bace ba sai yau, duk crises din da company ya shiga da nasarorin da company ya samu ta dalilina duk baki gani ba sai qalilancin miliyan dari biyu da suka bace cikin hidimar kamfanin, maryama ki fta min a cikin daki bana son sake maimata magana  & shuru Ammah tayi wani irin hawayen baqin ciki na zubo mata, juyawa tayi da sauri tabard akin nashi zuwa nata, koda ta shiga wayanta ta zaro ta soma kiran amar, yau kusan kwana biyar Kenan basuyi way aba kuam wayanshi baya shiga, hankalinta ne ya tashi kafin ta soma kiran account manager da lawyer company, cikin yan mintuna kadan ya dauka,  good afternoon madam ya gida ya iyali,  bata tsaya amsa gaisuwan sa ba kafin ta soma Magana   tun yaushe kudade suka fara bata daga cikin ccount din company ba tare da sanina ba, yanxu badan naje company ba bazan san ha;lin da ake ciki ba whats the meaning of all this, am I not the next kin of this company?  cikin tashi hankali lawyer ya soma Magana   im very sorry ma, wannan matsalar badaga mu bane daga cikin gida ne sanda abubuwan suke faruwa yallabai yace basai mun kai maki record ba sbd karki damu but komai is written akwai hard cop da soft copy of the slush fund, akwai waenda oga ne da kanshi ya buqa& .   bata tsaya sauraron sa bat ace send all the copies through my email, and let me warn you this should be tha last time, imform me on every transfersion don t leave a penny out of this, and don t do any transactionwithout my approval    yess maa& , kashe wayan tayi wani irin baqin ciki na tunkaro ta what going on, meke faruwane, cikin watannin nan komai tabarbarewa yake, aman y agama lalacewa, ya koma wata turba daban wanda ta kasa gane mashi kwata kwata, baya dawowa gida sai wajen karfe uku kamar yanda ubanshi yake yi wanda da farko bata damu ba don haka yakeyi tun farkon aurensu wanda ya nuna mata duk sbd aikin da yake ne na ganin cigabansu gaba daya, wannan abu baya damunta kwata kwata don ita kanta bata sha awan kadaicewa da shi balle suyi wata doguwar rayuwar aure,saidai lamarin aman ne ke tsorata ga shima amar ta kasa gane mashi duk sanda sukayi waya tanaji a jikinta yana cikin damuwa yaqi fada mata kwata kwata gashi duk yanda takeso tayi ta dawo dashi kasarshi ta haihuwa yaqi, daman abunda take gudu Kenan gashi yanxu abubuwa sun fara sauyawa, innalillahi kawai take maimatawa, yanxu miliyan 200 sun fice haka kawai an rasa ta yaya,da sauri ta bude wayan ta ta shiga email dinta, da sauri ta danna official email din daga accountant din company kasa tsaywa tayi kwata kwata, da farko ta soma ganin yanda ribar kampanin take sauka duk karshen shekara kafin farkon shekara ya dago, duk shekara kusan shekaru bakwai, sannan a wannn shekara maqudan kudade ke fita daga cikin account din company, hankali tashe ta soma lissafi cikin wannan shekarun anyi asarar kusan 48% din kudin kamfanin, hankali tashe ta wurga wayan gefe, whats going on ne, dama chan kamfanin baya gaba ne ko akwai wata a kasa ne, don ita tabbas bata shiga alamarin company don komai yana hannun kabiru wato kanin mahaifin amar wanda take aure yanxu, kuma ya nuna yana kula da company sosai saida yana ina akeyin duk wanna abubuwan, ganin duk wannan zulumin babu inda zai kaita yasa ta miqe ta wuce toilet ta dauro alwala tayi sallah, tana idarwa tayi adduoi sosai akan sallaya sai wajen karfe biyar ta sauko kasa ta soma shirya abincin dinner data saba koda yauseh don bata bari yan aikin suna yi mata idan har mai gidan yana nan dukda sun samu sabanin hakan baya sakata tauye mashi hakkinsa a matsainsa na mijinta, da taimakon lantana ta shirya komai akan dining, nan ta zauna a kan lumtsatsun kujerun sitting room din gidan tana dan lazimi akayi sallama, da fara arta ta tace   ah ah kodai anyi batan hanya ne mlm labaran,  murmushi yayi harya karaso gefen parlor ya tsugunna har kasa   hajiya ina wuni mun sameku lpy ya alamura,  lpy lau malam labaran, yau kusan wata rabon mu dakai, ya kasuwanci   & alhamdullahi hajiya ay akwai cigaba sosai, babu abinda zamuce saidai muyi maku godiya, allah ya kara daukaka ya kara arziki mai albarka    ameen malam labaran bari akawo maka abinci kaci, lantana  da sauri lantana ta fito sanye da riga da zanin ta wanke abinka ta daurin kallabinta irin nay an kauye ta kalli labaran kafin ta sauke kanta kasa cikin kunya tace   ina wuni  bai kalli inda take ba yace lpy sannu da aiki  yauwaa ta amsa mashi tare da kunshe murmushin dake subuce mata, kallonta Ammah tayi tsaf ta karanci lantana da yananyin da take shiga da zarar labaran yazo saidai shi kwata kwata babu wannan yanayi a tattarare dashi, murmushi kawai amma tayi kafin tace   kije ki zuboma mlm labaran abinci a kula ki hado mashi da ruwa dajuice mai sanyi  da sauri ta miqe tace   tohm hajiya  .. juyawa tayi tana dan satar kallonshi kafin ta wuce kitchen, juyowa hajiya tayi ta kalleshi kafin ta soma Magana   ya wajen noma kuwa? Ina ta so naje naga yanayi wajen? 
Ay hajiya noma tayi kyau, yau insha allah zan tsinkayi fruits din da suka nune sai a kawo nan, masarace dai bat agama tsura ba amma ana samu san harharda akai akawo sosai, ni ina ganin ma har kiwo idan babu damuwa za ah dungayi hajiya  .. murmushi tayi don labaran mutun ne mai qima da mutuntawa dasanin ya kamata sosai,   ay babu komai labaran zaka iya yin kiwo ma idan kana so ay babu damuwa, allah ya taimaka   ?meen hajiya allah ya kara karfin ido nagode sosai..
Shuru ne yadan biyo baya kafin ta kalleshi ta soma Magana cikin dabara   ni kuwa labaran baka sha awar yin aure ne, gashi dai ka manyanta, inma kana tunanin muhalli ne, bakada matsala da wanan, indai zakayi ay babu damuwa  dariya ya danyi kafin yace   ay hajiya, allah bai kawo wadda ta dace bane, bayan wannan ma ina tsoron irin rayuwar da nayi abaya don har yanxu bansan ni wanene bane, ina gudun matsalar rayuwa, a rayuwar yanxu ma babu wanda zata iya auran wanda baisan kanshi ba balle yan uwanshi ko dangin shi, hajiya banida kowa ayanxu sai ku, amma ina rokon allah ya kawo ranar da komai zai zo min da sauqi har na samu komai ya dawo min  .. dariya tayi irin ta manya kafin tace   toh allah ya akwo mana mafita  ameen yaa amsa, cikin yan mintuna kadan lanatan ta dawo rike da plates shake da abinci da ruwan sanyi da lemo shima mai sanyi, miqewa hajiya tayi kafin tace   zaka iya cin abincinka anan bari nace zama nadan huta  godiya ya mata sosai kafin ta hau sama, ganin ta wuce sama yasa lantana saurin dawowa gefenshi tace   malam labaran meysa kake tunanin babu wanda zai aureka,  kallonta yayi tsaf ya tsuke fuska kafin yace   ki koma wajen aikinki nagode da abincin  mikewa tayi jiki a sanyaye ta wuce kitchen, tausayinta yakeji sosai, don tana da hankali sosai saidai bazai bata fuska ba don harga allah idan har ba tunaninshi ne ya dawo ba baya tunanin kara wani aure ko soyayya don baisan irin rayuwar da yayi a bay aba, kila yana da yaya ko mata, ko masoyiya dake jiranshi achan, saida yaci ya koshi ya kora da ruwa, yana nan zaune aman ya shugo gidan cikin shigarshi ta ta kakken yan iska, bai tsaya kallo ko wanenen a wajen ba ya soma kiran lantana   ke yar aikin gidan zo  da sauroi lantana ta zo cikin sauri tace gani alaji, kallonta yayi cikin kaskanci yace tattara abubuwan wajen nan, nan ba wajen mabarata bane bana son karikicen mutane anan parlor, labaran naji haka ya miqe salin alin yana mai allah ya shirya da halayya irin da aman, to shi wannan Kenan da yake gaban iyayen nasu inaga dayan kuma da baya kasar ma Kenan shi nashi iskancin qila yafi na wannan saidai allah ya shirya kawai, wucewa yayi wajen mai gadi suka sha hira kafin yayi mashi sallama ya wuce wajen gidan gona chan gangare y agama duk wani abu da yake kafin ya wuce gida, gida ne dan karami mai daki daya da bandaki, wanka yayi ya sauya zuwa riga yar shara shara ta san iska lokacin an kira sallan magrib yana idar da salla aka kawo wuta, futa yyi ya sayo biredi ya dawo zama yayi bakin yar katifarshi,tunani ya shiga yi cikin yan kwanakin nan yana yawan mafarke mafarke ya kasa fuskantar komai, jawo buredinsa yayi ya ci ya kora ruwan pure water kafin ya mike jin an fara kiraye kirayen sallar isha I, janyo sallayan shi yayi kusada yar bakkwon kayanshi kafin ya tada kabbarar sallah, yana idarwa ya ninken sallayan, ya tura cikin bakkon kayan sa, ya shingida kan yar katifar janyo littafin da yake yawan zane zane yayi ya soma dubawa, yawanci zanen gida ne ya soma yi kafin yakai karshen zanen da yayi na mutane uku a zaune bakin bishiya sun juya baya hannunsu ruke da juna ta yanda ya zana sub aka tantance yanayin fuskansu don bayansu kawai yake iya zana wa, zanen ya tsaya mashi arai sosai, ya kasa gane komai game da zanen, yayi ne sanadiyan mafarke mafarken da yake yi kwanakin kusan kullum kuma mafarki daya ne akan ?hannaye da suke rike da junan shekara bakwai Kenan da loosing memory da yayi tun lokaci baya jin akwai abun daya rasa amma yanxu yana ji a jikinshi akwai abubuwan da yake missing sosai yana rike da littafin nashi har har bacci ya kwashe sa.
?
Bangarensu salima kuwa yau kwana biyar Kenan da farfadorawar salim yaji sauqi sosai saidai Magana dake mashi wuya sosai, wani lokacin kuma yakan burkice kamar mai ciwon kwalkwalwa ya soma Magana kamar mara hankali, dukda yawanci maganganun nashi akan abban su da ummasu da suka dade da mutuwa ne, yanda yake ambatonsu kamar wanda yayi shiwon mantuwa ya tuna abu daga baya, likitoci sunyi kokari sosai wajen ganin matsalar dake damunshi saidai abinda aka gano kawai shine lafiyar kalua, burgicewar da yake ne datayi yawa yasa suke bashi maganin baccin da zaisa kwakwalwarshi hutawa, karshe ma dai saida aka hada mashi da general test, lokacin da result din daya futo hankalin salima ya tashi sosai, a ranar kuma allah ya kawo Muhammad wanda yayi tafiya zuwa Abuja wanda yayi ta da gaggawa, lokacin da yaga result din salima yayi mamaki sosai, a yanda result din ya nuna, salim yana shan wata haramtacciyar kwaya wadda yawan shanta ke janyo juyewar kwakwalwa wanda kesa mutun ya manta abu lokaci guda idan har kuwa tayi tsamari yanda tayi mashi zai iya janyowa ya dawo kamar mahaukaci, a yanayin binciken likitoci ya nuna yasha maganin na akalla wajen shekara biyar ajere, wanda tayi mashi illa sosai saidai kuma allah yayi mashi baiwa sosai don abin aljabi shine wannan maganin yana healing a jikinshi yana sakinsa don kanshi ba tare da magance maganin ba ko therapy don maganin yana mugun karfin da saida therapy wanda suke ta ammali dashi suke buqata don dawowa daidai, kuka sosai salima ta dunga yi, ta kasa cin komai hankalinta ya tashi sosai, don idan harda saninta tabbas salim babu inda yake zuwa balle yayi ta ammali da wannan muyagun kwayoyin saidai kuma ina ya samu wannan kwayar har ya dauka waennan shekaryn yanasha har tayi mashi illa haka, shiyasa ya kasa warkewa daya samu ciwon zuciya Kenan innalillahi wa inna ilaihi rajiun  shuru ta danyi jimm ta soma wani dogon tunani, da sauri ta kau da shaidan din dake raya mata, tabbas wannan ba sharrin shedan bane gaskia ce to amma anya kuwa ba mugun hasashe take ba, anya kiyayyar uncle takai ga haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login