Showing 195001 words to 198000 words out of 381117 words

Chapter 66 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2193

gefe ta na sallah tana idarwa ta mike zuwa gaban aman tace   ya jikin ammah? An gama operation din? Hope babu abunda zai sameta? Bazata mutu ba ko? 
Haka ta dunga jero mashi tambayoyi, samun kanshi yayi da janyota jikinshi ya rungumeta yace   calm down, the operation is succeccfull 
Jin haka yasa amra ta bude idanunta don kamar a mafarki taji Kalmar, fuskanta yayi fayau sosai tayi haske saboda jinin jikinta da aka jiba, sai jijiyoyi da suka firfito mata, kallonshi amra tayi muryanta na karkarwa tace   is she out of danger?tana lafiya? Is she okay now?  
Saurin sakin salima yayi ya kalleta yace   alhamdulillah, it s a successful operation, but shes still in coma, yanxu we have to wait har saita tashi. 
  alhamdulillah alhamdulillah  amra ta furta tana hawayen farin ciki.
Kallonshi salima tayi tace   yaya muje inason naga ammah pls 
Katse ta yayi yace   bazaki samu ganinta ba saidai ki leka 
Amra ce ta soma kokarin mikewa tace   please zan dubata nima, wallahi hankalina bazai taba kwanciya ba inbanganta ba 
Badan yaso ba ya jagorancesu suka fito, salima na rike da hannun amra don bata iya tsayuwa saboda jirin dake dibanta, anatse suka tako har gaban dakin inda amar ke tsaye ya zuba ma dakin idanu,kallonshi aman yayi yace   zasu dubata 
Dn waigowa yayi ganin amra a tsaye kanta a kasa, nan take yayi saurin kauda kanshi gefe, wani irin daraja da girmanta ne ya sauka a kanshi, bayan ammah babu mace a duniyannan da yake jin ta kamar amra ayanxu, ta samu wani matsayi a zuciyarshi wanda bazai taba hadata kowa ba bayan amma, yau yarinyar daya raina itace ta taimaki mahaifiyarsa, itace ta ceci mahiafiyart ayanxu da babu ita a cikin asibitin da saidai ammah ta mutu,
Samun kanshi yayi da yin baya ya tsaya daga bayanta salima ta taimaka mata suka tsaya bakin kofar, shafa kofar amra tayi tana hawaye babu abunda take fada sai   alhamdullah ya allah, allah mung ode maka, allah ya tashi kafadunki ammah, allah ya tausasa maki ya baki strength, muna buqatarki a cikin rayuwarmu gaba daya, allah ya baki lafiya  & .

Amar dai kasa tsayuwa yayi ya juya ya fuce daga wajen, don shi kadai aysan abunda yake ji a cikin zuciyarshi a wannan lokacin.
Sun dade sosai wajen kofar dakin ammah kafin su koma dakin amra atare.

Karfe goma aman ya kalli amar yace   ya kamat muje gida sai mu dawo gobe 
  no ka tattara yarannan ku koma gida kawai ni zan kwana anan, 
Aman najin haka yace   okay ita kuma.. 
  kuje kawai zan kula dasu  yana kaiwa nan ya koma gaban dakin ammah, aman kuma ya juya dakin amra don sanar dasu salima sa salim su fito don su wuce gida
  salima ce ta kasteshi ta hanyar cewa   yaya, adda fah? Ku koma kaida salim ni zan zauna da ita 
Janta gefe yayi don amra nab arci karta tashi yace   amar zai kula da ita shi yace na wuce daku gida ma 
Jiki amace salima tace   toh muje, 
Juyawa sukayi ganin amra nab arci basu tasheta ba suka fuce daga dakin.
Suna wucewa amar ya wuce dakin amra, a kwance ya taddata tana barci fukantsa ya zubama idanu, ta rame sosai lokaci guda ta zabge, wani irin tausayinta ne ya dabaibayeshi, shi kadai yasan me yake ji game da ita a wannan lokacin, ya dade sosai anan kafin ya koma wajen ammah itama ya kai kusan awa guda a wajenta kafin ya sake dawowa dakin amra, sai ya zamana kamar shifting yake yi, idan ya duba nan saiya duba chan, gaba daya tausayinsu yake ji sosai, duk wata gajiya ma baya jinta ko kadan, karfe sha biyu ya dawo dakin amra, bai dade da shigowa ba ta bude idanunta ta sauke akanshi, kasa dauke idanunshi yay akanta, yana nazari abubuwa da yawa na yawo a kwakwalwarshi akanta, saurin kauda kanta gefe tayi batace mashi qala ba haka zalika shima baice mata komai ba, chan kuma ya juya ya fuce daga dakin, abunci ya nemo mata don yasan zata buqata anan cikin kitchen din asibitin, atare da chef din ya taho suka shigo cikin daki, kallonta ya sakeyi muryanshi kamar bazai fitaba yace   aishaaa  dan waigowa tayi ta kalleshi jikinta duk ya zama weak,   seat up  ya fada kamar bashi ba, da kyar ta fara kokarin mikewa saidai kash jikinta y agama tsami don haka tana dagowa ta koma, yana ganin haka ya matso kusa da ita ya tallabota ya zauna gefenta ya kalli cheaf din yace   bring the food here 
Katseshi tayi saurn yi tace   bana jin yunwa 
& & ..
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Uneditedpage

Binshi da idanu amra tayi harya fuce daga cikin dakin, da cearal dinta a hannunta ta janyo hijab dinta ta zura ta bi bayanshi, tana sauka kasa kitchen ta wuce direct ta fara kiciniyar hada coffee, anatse ta gama hadawa ta daura mashi akan saucer ta fuce daga kitchen din cikin natsuwa, da sallama ta bude bedroom dinshi a zaune yake bakin gado ya nade hannayenshi akan kirjinshi, dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta karaso har gabanshi ta dan sunkuya gefen bedside ta aje mashi mug din,   bismillah 
Kallonta ya danyi kafin ya maida idanunshi kan mug din, cikin kamewa ya miqa hannunshi wajen bedside din ya dauka mug din kafin ya fara kaiwa bakinshi, tana ganin haka ta juya zata fuce daga dakin, hankalin shi gaba daya nakan coffee din yana kokarin cire mug din daga bakinshi bayan yayi sipping   na baki umarnin tafiya ne? 
Tana jin haka tadan tsagaita ta juyo ta mashi kallo daya kafin ta tako har inda yake zaune ta dan tsaya daga nesa, ta dauka kusan minti biyar a tsaye duk ta gama takurewa, dan leka mug din hannun nashi tayi ganin ko half baiyi ba ta dan tabe baki ta karaso gefen da yake zaune ta zare hijab din jikin nata ta zauna gefenshi ta tankwashe kafarta kan gadon ta bashi baya tare da bude pack din cereal din nata data boye a cikin hijab, da mamaki ya waigo ganin yanda gaba daya yanxu bata kunyar shi, samun kanshi yayi da gyara zama yanda zai hangota da kyau akan gado, tana jin motsin chanza position da yayi ta juyo bakinta cike da cereal, cikin sauri ya kauda kanshi ya hade rai tamm kamar ba kallonta yake ba, sake maida idanunshi yayi kanta karaf suka hada idanu tana ganin haka ta sauke mashi lausansan murmushi mai melting herat wanda yasa heart dinshi skipping lokaci guda, cikin shagwaba tace   yaya nifa barci nake ji wallahi, ka sallameni na tafi 
Banza yayi da it aba tare da ya sake kallonta ba, itama tana ganin haka ta juya mashi baya tana turo baki tana cin cereal din harta cinye tass, wasa wasa sun dauka kusan awa guda shi baice mata ta tafi itama bat ace mashi kala ba har barci ya soma fuzgarta, time to time yake dubanta har barci ya kwasheta ta lafe akan gadon, zuba mata idanu yayi yana kallon bayanta, hakannnan yaji hes relaxed harya gama shan coffee din, yana gamawa ya miqe ya fuce da mug din zuwa kitchen, yana dawowa ya taddata ta baje ko ina, tayi rub da ciki, bin bayanta yayi da kallo yana ayyana abubuwa sosai aranshi kafin yayai saurin kauda kanshi, anatse ya tako bakin gadon ya kwanta daga gefe ya janyo masu duvet, koda yazo lulluba mata saida yadan tsagaita yana wani tunani aranshi   why im I doing this?  ya tambayi kanshi, kallon innocent face dinta yayi haka kawai yaji yana tausayinta babu dalili, saurin kauda duk wani tunanin dayazo ranshi yayi ya rufa mata duvet din ya kwanta gefe yana facing ceiling tare da nade hannayenshi a kirjinshi yana tunani har barci ya fusgeshi.
Cikin dare yaji mutsu mutsu a jikinshi, ahankali ya soma bude rinannaun idanunshi harya sauke su akanta, ta nadeshi gaba daya ta rungumeshi, da mamaki ya ware idanunshi da kyau don tabbatar da abunda idanunshi ke ganar mashi, ta wani kanainayeshi tayi cuddling dinshi, he can feel her bare chest a jikinshi, saurin runste idanushi yayi ya fara kokarin janyeta daga jikinshi,bai kaiga zareta ba ta zake hade jikinta da nashi ta rike shi gam kamar ta samu pillow, shiko goga take komai ya fara chanza mashi don gaba daya jinshi yayi kamar an arura mashi wutar azaba a marar shi,   ya allah, yarinyar nan zata haukata ni  ya fada ahankali yana fidda nunfashin wahala, rasa abunyi yayi don gaba daya babu alamun zata bari ya janyeta daga jikinshi, gashi any wrong move yayi saita kara damkoshi wanda hakan ba karamin affecting dinshi yake ba, don haka ya hakura ma ya kyaleta saidai daren ranar dai barci kaurace mashi yayi gaba daya.
Akunnenshi aka kira sallar asuba, yana jin haka kuwa ya turata gefe, ganin tana shirin damkoshi ya sashi daka mata tsawa   kee bakida hankali ne, whats the meaning of this? 
Firgigi ta bude idanunta ta sauke akanshi, idanunta sunyi mici mici,gaba daya barcin bai isarta ba don haka ta maida idanunta ta rufe yana ganin haka kuwa ya wuce bathroom azafafe rai a bace, yana shiga ya fara yin wanka, ya dade sosai a tsakiyan shower yana rage ma kanshi wahalan da yake ji, saida yaji ana neman tada sallah yayi saurin dauro alwala ya fito ya zura jallabiyanshi ya fuce daga dakin.
Koda aka idar da sallah tare suka fito daga masjid shida aman da salim, idan ka gansu gwanin burgewa har suka shige cikin gida kowa ya wuce part dinsh.
Yana shiga bedroom dinshi ya tako har bakin gadon ganinta a kwance kamar aynda ya barta, ranshi ne yadan sosu haka kawai don haka ya soma Magana afadace   keee aisha!!! 
Anaste ta juyo ta bude idanunta ta suka danyi jaa ta kalleshi,   ke are you okay?what sort of rubbishness is this? Ke kafira ne ko sai ance tashi kiyi sallah 
Miqewa tayi zaune ta kura mashi idanu, saida y agama fadace fada cen shi kawai ta fashe da kuka, wiwi ta dunga kukan shagwaba, shide tsayuwa yayi yana kallon ikon allah, lallai yarinyar nan ta gama rainashi yana mata Magana tana kukan rainin hankali, ya fada aranshi, ay baisan lokacin daya daka mata tsawa ba   shut the fuck up, are you insane? 
Ay kamar ya kara tunzirata don haka ta miqe tsaye ta janyo hijab dinta ta karaso gabanshi tace   haba yaya, why are you treating me like this? Meysa ka tsane ni? Me nayi maka a duniyar nan,ina kokarin ganin na faranta maka kai kuma kullum cikin neman hanyar kuntata min kakeyi,why??? 
Yanda ta tsaya gabanshi babu tsor babu komai tana fada mashi maganganu ya hasalashi ya kalleta daga sama har kasa ya mata wani disgusting look yace   nace maki ina buqatar farantawar taki ne? nace maki ki shiishigemin ne? ke kika sama kanki, waye ya yama baki wannan shawarar, look idan kina tunanin wannan abubuwan da kikeyi zai chanza mind dina youre mistaken, gwara ki daina bata ma kanki lokaci, Magana daya nakeyi bana chanza Magana, so I will advice its better you stop&   
Takowa tayi gabanshi tana sheshekar kuka jikinta na rawa ta tsaya gabanshi dab dashi ta rike kugu harda dan dingilawa don ya ganta da kyau don ya fita tsayi sosai   nooo, nooo I will not stop, this is just the beginning ma yaya, ko mai zakace min wallahi bazan taba rabuwa dakai ba, kace ina shishigi ko ina cusa kai?, ay aynxu ma na fara, kuma kyautatawa ne ba chusa kai ba  ta karashe tana murguda mashi baki kafin ta juya mashi baya ta duka ta dauki hijab dinta data yar da gangan a kasa, saurin yin baya yayi don gab ass dinta ya gogi gabanshi, ganin abunda take shirin yi wanda idan har ya bari hakan ta faru zaiji kunya, ba karamin chaza mashi kai yarinyar nan take yi ba itako tana dukawa ta dauki hijab dinta ta mike ta zura abunta ta gifta ta gefenshi ta nufi hanya, tana gab da fita ta dan waigo tayi murmushi don taga lokacin dayayi baya data duka   sorry my yaya ban gaisheka ba, ina kwana?hope ka tashi lafiya  
Bata jira jin amsan shi ba ta fuce tana dariya ciki ciki,   ay yanxu wasan ya fara, wallahi zaka ga chusa kai, daman kunya nake ji shiyasa nake baya baya dakai ammah wallahi yanxu zan nuna maka cewa ba a yima mace haka 
Tana kaiwa nan ta shige daki ta dauro alwala ta tada kabbarar sallah tana idarwa tabi lafiyar gado hankali kwance.

Tun bayan fitar amra ya kasa motsawa, he s so stunned with her new attitude, ya kasa ganema kanshi shima yanda ya kasa taka mata burki, cije lower lip dinshi yayi yana takaicin yanda ya tsaya take fada mashi maganganu ba tare da yayi maganin ta, he s so madd, yanda she looked into his eyes har tana iya cewa she won t stop, shi abunda yafi bashi haushi ma is the fact that deep down yana son yanda take chusa kanta zuwa gareshi, dukda he s trying to distance himself from her saboda neman haukatashi da takeyi with her presence, duk motsinta akan idanunshi wanda yakeyi afake ba tare da sanin yana yi da kanshi ba, bayan wannan he started to notice he cared so for her dukda ya dauka wannan a matsayin saboda ita marainiya ne kuma yanxu reponsibity dinta da kannenshi ya dawo hannunshi saboda sanin yanda suka taso cikin wahala.


Dubai uae& .
Tun bayan tafiyar amra without notice hankali haifa da Nadine ya tashi sosai.
Washe gari m5 ya shaida ma Nadine saboda yasan zata damu, haifa cedai babu wanda ya shaida mata, don sunyi plans din haduwa the next day ita da amra saboda zasuyi pre graduation photoshoot, haka ta wuni tana kiran line din amra baya shiga karshe dai haka ta hakura, washe gari ma haka ta dunga kiran lne din throughout switch off, ganin haka yasa ta shirya ta wuce penthouse din amar.
Koda ta iso gidan nan Nadine ta shiada mata cewa ta koma Nigeria saboda wani abu daya taso urgently wanda haka m5 ya fada mata, hankalin haifa ya tashi sosai don tana jin haka babu abunda yazo ranta sai maybe ko amra ta gudu, ko kuma general ya sake maidata gidanshi saboda wani kudirin nashi daban, ganin babu wanda zai bata amsar tambayoyinta yasa ta koma gida hankali atashe.
Haka ta jera kwanaki tana zuwa gidan don neman yanda zatayi connecting da amra,gashi duk zuwan da zatayi sai sunyi sabani da m5 sabod yabar zuwa gidan, daman amfanin zuwanshi saboda ya kai amra aiki ne ko idan general yana nan, yawancin zuwan nashi sai jefi jefi yake yi don duban gidan saboda ya bama general report akan abubuwan da suke gudana a gidan wanda hakan qa  idarsa ce duk sanda baya kasar sai m5 ya bashi report ,agidan kuwa Nadine ce kawai sai dayar maid din, suke kula da gidan don sir general din bai sallamesu ba haka zalika wata na karewa zai tura masu kudin aikinsu.

After 1 month&
Haifa s resident&
Lokaci kamar ruwa haka yake gudu, yau wata daya Kenan rabonda haifa taji daga wajen amra, cikin kwanakin nan haifa tayi su ne cikin tashin hankali da damuwar aminiyarta, amra ta zame mata wani bangare na cikin rayuwarta da bazata taba neglecting dinta ba kota manta ta da ita, acikin kwanakin har tunanin zuwa Nigeria saida tayi saidai abuh ya hanata saboda na farko that will be the first da zata shiga kasar, gashi bata san kowa ba shima abu bashida wani connection da Nigeria don baitaba zuwa ba, don haka ya bata hakuri akan ta bari daga baya after engagement dinta da hamman wanda ake shirinyi a cikin month din.

Yau gidansu haifa a cike yake tam da dangi, both dangin abuh da dangin ummi, asalin larabawa kake gani kota ina, an kawata gidansu da decoration din flowers, daga hanyar shigowa gidan anyi hanging wedding banner (welcome to haifa and hammans engagement) gaba daya anguwar ta cike da hadaddun motoci, cikin gidan kuwa shima cike yake da mata dam, anata guda, ga kamshin turaren wuta daya bade ko ina, compound din gidan yasha lightings da decors kamar yau ne ranar bikin nasu, cikin sitting room kuwa manya manyan carpet ne shimfide da tuntu inda jiga jigan larabawa masu ji da dirhams suke zaune, duk sunsha gwala gwalai kamar competition gabansu shake da abunci kala kala, irin nasu na manya, su hammus falafel,taboule, fattoush, su mandi ne,gasassun rago da kaji a jibge, kawayen ummi da danginta da dangin abu duk kowa na zazzaune ana hira masu guda na guda masu takawa na, abun dai sai san barka,yau engagement din diya daya tilo a cikin familyn, chan na hango ummi, taci kwalliyansu na larabawa cikin traditional arab dressing na iyaye, tasha gwala gwala itama kamar babu gobe, tana saukowa daga stairs aka fara guda yiiiii yiii ko ina, kawayenta ne suka miqe suka tarbota har zuwa cikin sitting room din.
Karfe biyu daidai dangin ango suka karaso, maman hammam ce kawai sai yan uwanta na chan Iraq mutane biyar wanda duk distance relatives ne, suma sunyi kyau sosai, itama tasha gwal dinta babu laifi don shima ana gani ansan kudi ya zauna, hammam dai ya fito da mahaifiyarshi, suna karasowa aka fara guda ana gaggaiwasa, abunka da larabawa ba barsu abaya ba wajen tsegumi, dole saida aka samu waenda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login