Showing 93001 words to 96000 words out of 381117 words

Chapter 32 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2033

ya shirya plans dinshi ta bayan fage,
Lokacin da zancen wani dan nigeria daya shigo da kwaya kasar dubai daga nan zai wuce egypt, nan take binciken dayasa m5 yayi mashi akan background din mutumin yayi mamaki sosai take ya gane cewa wannan mutumin dai daga gidan da yaran nan daya taimaka yake wato qannen amra kuma ubanshi shine marikin su a lokacin daya kara tabbatar da komai shine lokacin da health report din Salim na kwayar da taso mashi illa tayi daidai da kwayar da aka kama wannan mutumin, lokacin ya sanyo manya manyan Nigerian army a cikin lamari cikin sirri, nan take aka gano ba dan kadai ke mingling da kwayoyinba harda ubanshi ma suke business din.

Maganar aurenshi da amra kuwa sanin dole za a zo lokacin da za ayi using auren don ayi threatening dinshi hakan yasa ya shirya nashi plans din, babu tsoro ko fargaba ya Tara evidence manya manya da shaidun aurensu tun a Nigeria tun kafin tazo kasar, ba a barin nigeria dai da curruption cikin qanqanin lokaci ya shirya komai dukda baiso yin hakan ba saidai wannan ce kawai Damar da yake dashi don cimma burinshi.

Lokacin da Hammam ya kira shi ya nuna mashi true color shi baiyi mamaki ba don daman ya tsammaci hakan, kamar yanda yace ya shirya Duk abunda zaije ya biyo baya idan ba amince masu ba na cire hannunshi daga investigation din dayake, washe gari kamar yanda yayi expecting kuwa Hammam yakai Duk wani evidence din illegal auren da yayi ciki kuwa Harda abunda baiyi expecting ba wato Har wasu papers akayi na health issues dinshi Duk don koreshi saidai kuma higest attained rank group din basu damu da wannan ba don bai shafi aikin su ba, saidai samun report din cewa the most smartest, strongest and hardworking general ne zai sanya hannu cikin illegal doings, lokacin da aka nemi gani shi na gaggawa Har akayi meeting yayi expecting hakan don sun rigada sunyi planning hakan, Alokacin da aka kaishi interrogation room hankali shi a ka ace yake don yasan abubuwan da zai biyo baya, amra kuwa yasa m5 yayi mata arrangement din tafiya zuwa Nigeria ne don ya Kara tabbatarwa da mutane cewa an gane anyi banning dinta daga shiga kasar don tabbas yasan idan Har aka gano yana da nashi plan din za a iya using dinta ko ayi hurting dinta. Hakan yasa m5 yayi mata arrangement na komawanta nigeria, da farko yaso yasa akaita gida saidai ganin bashida time din yima Ammah bayani daya dace yanda zata fahimta, hakan yasa akayi necessary arrangements a gidanshi dake karkashin company taura estate tare da nema mata house keeper da zata taya ta zama kafin ya karaso. Zuwan Shi nigeria da zaiyi shima yana cikin plans dinshi don ya gano cewa Duk yanda akayi Akwai members na empire anan kasar don empire din tana da connections ba mutun daya bane tunda safarar kwayoyi sukeyi da trafficking kuma dole ta hanyoyin da yaga abubuwan dake connecting da empire din ta hanyar zai gano kosu waye don haka ya dukufa akan binciken hammam, tashin farko bincikensa ya gano masa cewa Hammam yana yin komai ne bisa ga umarnin mahaifinshi da yayi badda kama don tantirin drug smuggler ne bayaga wannan ma yana illegal abubuwan da uae government ta haramta wanda mutanen da yake dashi ne da connections ke sashi zama so powerful da ba a taba tukararshi ko gano shi.
Abunda yafi bama Amar mamaki kuwa shine, ya gano cewa Hammam ba asalinsa dan alif shuraim bane, adopting dinshi yayi wanda da hakan yake manipulating dinshi yake sakashi yi mashi abubuwa saidai kwatakwata hammam bai san abubuwan da alif keyi ba ciki harda smuggling drugs.
Zurfafa bincike sosai Amar yayi nan take ya gano mahaifiyar hammam wanda akayi registering mutuwarta tana raye a wani gidan mahaukata, a iya sanin dayayi ma hammam tun farko ya gane mutunne mai qaunar mahaifiyarshi baya ga wannan bai taba ganin Hammam ya shiga wani hali ba Sai Lokacin daya riski mutuwar mahaifiyarshi. Saidai abunda yafi bashi mamaki meysa akayi declaring mutuwar mahaifiyar hammam din, waye ya Kaita gidan mahaukata shin dama Chan mahaikaciya ce?
Babu wanda zai bashi wannan amsoshi dole Sai shi hammam din wannan yasa ya kira hammam din.
Cigaba labari& .
Tun bayan daya lumshe idanunshi a cikin motar abubuwa da dama yawo suke mashi a kanshi kallon m5 Yyi kafin yace  my phone
Da sauri m5 ya zuria hannunshi cikin gefen dashboard ya zari wayoyin ya miqa mashi
Karba yayi ya Kun basu duka wayoyin Kafin ya kurama line din hammam idanu, babu wani bata lokacin ya dannan Kiran hammam lokacin da call din ya shigo wayan hammam yayi mamaki sosai saidai sanin cewa dole za a sakeshi don Duk inda akace general ya wuce gaban wasa baza ayi mashi komai ba saidai za ayi suspending dinshi silently ba tare da kowa ya sani ba
Dariya hammam ya kyalkyace kafin ya daga wayan yace
 ka fito kenan daga& . Hmm daman na fada maka ka cire hannunka baka saurareni ba karka ga laifina fah nayi warning dinka baka ji ba

Nunfasawa amar yayi yace
 Bazan ga laifi ka ba hammam tunda bakasan abinda kake ba, you re under manipulation, hammam can t you see, open your eyes, why are you doing this,? Why are you protecting the empires
Shuru Hammam yayi kafin yace  if protecting them means protecting my father then I m willing to sacrifice cos that s what I promised my mother, bazan taba zama butulu ba

Dariya amar yayi kafin yace  talking of father mana nufin mutumin da yayi adopting dinka?

Mamaki ne ya bayyana akan fuskan hammam yace  how did you& 
 You mean how did I find out? Don t worry there are more that I find out sannan kace sabd mamanka kake yin haka ko to inada tabbacin bazata taba alfahari dakai ba, ya kamata ka dawo tunanin ka tun kafin lokaci ya kure, Ina fatan abunda Zan tura maka zai saka dawowa daidai ka gane hanyar da kabi gurbatacciya ce

Yana kashewa ya tura mashi hoton video mamanshi wanda yasa m5 ya dauka a asibitin mahaukata tare address din wajen kasan kuma ya rubuta *Mandate house of old age go and see for your eyes.
Yana kaiwa nan ya aje wayan a gefen ya dafe kanshi dake Sara mashi sosai

Ba karamin furgici hammam ya shiga ba ganin video da amar ya tura mashi, jijiyoyin kanshi ne suka fifito sosai idanunshi yayi jaaa kamar wuta, zarar key dinshi yayi bayan ya karanta last message din ya fuce don tabbatar ma da idanunshi, direct mandate house of old age ya karasa, yanda yayi parking kadai zai tabbatar maka da ya gama zarewa, yana zuwa reception ya nuna masu video yace yana son ganin matar, nan take suka gane wa yake nema saidai gani yanda ya zare yasa suka tambayi waye shi nan take ya shaida masu danta ne shi abunda ya bashi mamaki shine nan take matar dake reception tace saita tabbatar da hakan ta hanyar kiran guardian din matar, ganin tana neman bata mashi lokaci ya sashi zaro if card dinshi ganin shi army officer ne yasa tayi saurin aje wayan da take shirin yi ta jagoranceshi zuwa dakin, turus ya tsaya hankali tashe ganin mahaifiyarshi abar qaunar shi, nan take hawaye ya soma zuba akan idanunshi daya zuba mata su,itama shi take kallo saida ta mutsuke idanunta sosai kafin ta uwar kara nan take aka taho da sauri aka ririke ta, da sauri ya karasa gabanta yana  umiy hu hadha ant (ammi is that you) cikin kuka ya cigaba  umiy , 'ant ealaa qayd alhaya (ummi you re alive) sosai ya rungumeta abun mamaki itama rungume shi tayi a jikin ta tace  dana,yarona kaine
Ta fada cikin larabci
Saida suka gama kokekoken su kowa mamaki yake yanda ta shafe shekaru yana hauka lokaci guda memory dinta ya dawo,
Nan take ya soma mata bayani  bayan na dawo daga training abbu ya shaida min mutuwarki na shiga damuwa, amma maysa na ganki annan dama baki mutu ba
 Ban mutu ba Hammam saidai zabin da aka bani yafi min na zauna a haka don bazan taba bari ka salwanta ba, Sai gashi allah ya kawo ranarda Zan hana ka shiga hadarin da tun farko aka yaudaremu batare da saninmu ba

 Bayan tafiyarka na gano manufar alif shuraim aka ka na amfani dakai don biyan buqatunshi, babu tsoro na tunkareshi kuma ya tabbatar min da haka saidai na nuna mashi bama buqatar taimakon nashi zamu bar bashi gidanshi, nan take yayi threatening dina akan dole na nisanceka inba haka ba zai kasheni, nan ya bani zabi biyu ta hanyar bani kwaya ko kuma ya kasheni a wajen ganin banida Mafuta na karbi kwayar tundaga lokacin bansamu kaina ba Sai yanxu, I m so sorry son na barka cikin wannan rayuwa Kara amfani
Wani irin zafi da daci zuciyar Hammam keyi, Sai yanxu komai ya warware mashi idanunshi sun bude sosai, nan take yayi alqawarin saiya kawo karshen alif kuma zai taimaki amar, abokinshi na arzki saidai yana jin kunga da takaicin rufewar idanunshi wajen taimakon mugaye.

Nan ya barta bayan ya shaida mata komai akan abunda ke faruwa
 ka tafi ka barni anan Allah yana tare daku hammam Addu a ta Ma tana tare daku, idan Har ya gane cewa ka gani gaskia zai iya lahantaka, ya kamata mu boye komai

Da wannan sukayi sallama kafin ya tabbatar da tana under care din nurses din wajen.
Amar kuwa Yana zuwa asibiti babu wani bata lokaci yanemi ganin likitanshi, nan take ya buqata likitansa da yayi unfreezing sperm dinshi, babu wani bata lokaci suka shiga operation room cikin Yan mintuna suka gama don ba wani dadewa akeyi ba wajen unfreezing din, magunguna doctor ya rubuta mashi kafin ya soma mashi bayani  thankfully kazo anyi unfreezing don daka Kara wasu kwanaki I m sorry to say za a samu matsala, anyway for now bazaka samu erection, don t worry Duk cikin side effect din freezing dinne, but kana samun hutu da kulawa sosai komai zai dawo daidai, normally wasu in just 2days komai yake dawowa normal wasu kuma it takes a month ma,I m sure you re ready by now ko?
Ya tambaya yana kallon amar
 Uhm kawai ya iya ce mashi kafin doc din ya cigaba
 One of the side effects also is for waenda basu taba sex ba it will be a long journey, don zai saka feelings sosai and idan ka samu mace for the first time especially virgin zaka wahala sosai don zaka Kasa controlling kanka, but anyways waennan magungunan will help out sosai

Tunda ya Lauda kanshi gege yana sauraron doc din bai kallo shi ba har saida ya gama mashi bayani sukayi sallama ya fito.
Direct apartment dinshi ya wuce don daukan laptop dinshi a hajiya yake sbd haka yana shiga bai tsaya komai ba ya dauka laptop dinshi juyawa yyi zai fita nan idanunshi suka sauka akan kayan data tube Harda bra dinga garin sauri gama manta dasu bata kwashe ba, tsungunnawa yayi ya kwashe mata su, gaban closet ya karasa zai saka a ciki, Chan kuma ya tsaya kallon bra don nata yayi yana ayyana girman albarkatun kirji da Allah ya bata, nan take yaji wani abu na taso mashi, da sauri ya aje bra don ya juya ya fuce zuwa sitting room, gaba daya sai apartment din ya mashi girma sbd rashin ta a ciki, tabe baki yayi kafin yace  fitina girl
Dan murmushi ne ya ku ce mashi kafin yasa kai ya fuce daga apartment.
Direct penthouse dinshi m5 ya sauke shi kafin ya wuce sama direct bayan Pablo ya gaishesa, wanka yayi kafin yayi sallah magrib da isha I ya sauko Kasa sanya da Riga da gajeran wando bakake na under armor, sunyi matukar amsarsa sosai, dining ya wuce bai wani ci abunci sosai ba ya koma sama wajen gaming dinshi don ya kwana biyu baiyi ba, Sai wajen karfe goma ya fito daga gym ya wuce daki ya watsa hot shower
A jikinshi don yana buqata kafin yabi lafiyan gado. 108-109
Update& &

Washe gari ya kusa makara sallan asuba don Sai wajen karfe bakwai ya tashi, toilet ya wuce direct ya watsa hot bath da body wash dinshi masu shegen tsada da kyau, cikin natsuwa da kamewa ya futo, bai tsaya wani shafe shafe ba ya shingida sallaya ya fada kabbarar sallah yana idarwa ya fara shirin tafiya, normally yana aje travel box dinshi da Duk abubuwan buqatanshi daya Tashi tafiya kaya kawai zai deba wanda zasu ishesa tsawon kwanakin da zaiyi, wani lokacin kuma pablo ke hada mashi sanin yawanci kayan daga jallabiya sai kananun kaya karasa nauyi wanda yawanci yafi buqatansu musamman idan zaiyi tafiya Kasashen da ake yawan zafi sosai, yana gama hada box din nashi ya fidda kayanda zai saka, farrar Riga ya jawo ta brand din Ralph Lauren wanda ke cikin manyan collection din kayansa, sanin yanayi weather na nigeria a lokaci yasa ya dauko dogon wandon army ya saka, kafin ya feshe jikinshi da hadaddun turarukanshi masu da yin kamshi da tsada, laptop bag dinshi kawai ya jawo da wayoyinshi kafin ya sauka kasa, bai tsaya ko Ina ba Sai dining area, bai wani tsaya cin abunci da yawa ba, coffee kawai ya buqaci pablo yayi serving dinshi da english breakfast, cikin natsuwa ya gama cin breakfast daidai nan m5 ya shigo, saida ya gaishesa ya shaida mashi komai is ready kafin su fito tare m5 na gaba ya bude mashi bayan katuwar jeep dinshi da tasha zanen army a jiki kana ganin motar kasan ta manya ce, Pablo ne ya fito dauke da baggage dinshi, da mugun speed suka fuce daga penthouse dinshi, tafiyan 20 mins sukayi suka iso uae international airport, lokacin da suka iso kusan sauran 30mins suyi taking off, yana zaune hakimce kamar bazai fito daga motar ba idanunshi a lumshe yana tunanin abubuwa da dama wanda suke mashi yawo, saida ya dauka kusan minti goma kafin m5 ya bude mashi kofar ya sanyo kyakyawar fatar kafafunshi waje, wayanshi kawai ya rike a hannunshi yayi gaba m5 ya rufe kofan tare da janyi baggage dinshi ya bi sahunsa, bai tsaya ko Ina ba sai first class lounge, ya hakimce tareda daura kafanshi daya kan daya, turarenshi ne yayi ma mutanen dake zazzaune akan kujerun wajen sallama,nan kallo ya koma kanshi, wayanshi ya soma latsa wa ba tare da ya kalli kowa dake wajen ba don basuda wani yawa Ma a wajen don Sai yayan wane da wane ne a wajen.

M5 ne ya mashi Duk wani necessary arrangements, ya karba boarding pass dinshi, kafin ya wuce lounge din, cikin girmamawa ya aje mashi laptop bag dinshi gefen shi tare da su boarding pass dinshi da passport dinshi kafin ya mashi sallama ya fuce daga cikin airport din.

 Meeda kinga wani Hadadden guy kuwa, ya Allah ya hadu harta gaji da haduwa
Wadda aka kira da meeda ce ta dago ta kalli inda ta gefenta ke nuna mata, wani irin maybe kallo ta Bishi dashi kamar zata hadu ya shi, nan take taji wata Kibiyar sonshi ta daki zuciyarta, da sauri ta hadiye wani irin Miyau ta juya tareda kallon kawar Tata tace  kam bala i, zabgi wallahil azeem gayen nan ya hadu, kura bata ganin nama ta kauce
Dariya wadda aka kira da baby akay kafin ta juya ganin inda kawar Tata take tunkarowa, gaban shi ta isa lokacin ya mike don lokacin tashin jirgi yayi, kamar an wullota ya hanya gabanshi, dago idanunshi yayi da suka kusan saka ta suman tsaye dukda babu alamun dariya ko annuri a fuskanshi hakan bai hanata hango
Sirrin kyau da yake dashi ba, gaba daya saida ta karaso gabanshi ya tafi da imanin ta, cikin yanga da iyayi irin na Yan mata da sukaji duniya, ta soma magana  assalam handsome
Tsayuwanta a gabanshiya bashi daman yi mata kallo daya don ya fita tsayi sosai, kananun kaya ne a jikinta wanda ya fidda surar ta sosai, batada wani kyawun jiki don komai ya gama yin lanqwasa nan take ya soma jin kyankyamin ta, kauda sexy eyes dinshi yayi gefe ba tareda ya sake mata kallo daya ba ta sake magana  sunana hameeda idan babu damuwa inason na san sunanka harma dakai din gaba daya ta karashe tare da juya idanuwanta wanda shi baida lura da hakan ba, wani irin disgusting kallo ya mata tare da giftawa gefenta ya wuce, kamshinsa ne ya daki hancinta nan take ta lumshe idanu ba tare da ta damu da dizgata da kallon da yayi mata ba, kawar ya kuwa dake zaune ne zatayi Banda dariya harta juyo ta dawo inda suke zaune,  ke meeda daman wannan Ay yafi karfinki nesa ba kusa ba, kidai lallaba da sugar daddies dinki dake baki kudi suna biya maki jirgi kina zuwa hutawa

 hmm baby bazaki gane ba, wallahil azeem ban taba ganin hadadden gaye wanda kina ganin shi kinsan ya juqu da kudi ba kamar wannan,

Kallonta baby tayi yanda ta lumshe idanu tana smiling hakan ya tabbatar mata da abunda ta hango a idanunwan kawar tata
 Toh mayya, kedai ako Ina Sai kin nuna zalama, irin wannan Mazan dai kinsan basa daukan raini,don mugun wulaqanci ne dasu,
Ganin kamar bata sauraronta yasa tace  malama saiki Tashi kamu tafi ay tunda kinaji an kira flight din namu

Kallonta meeda tayi tareda daukan wayanta tace  Toh tsaya muyi hotunan posting mana

Karban Wayar baby tayi tace  aikin banza, dama dai rayuwar karyarki da kika saba kika bawa himma da zalama ba irin wadannan Samarin ba
Hotuna zafafa suka dauka, kafin su wuce cikin jirgi, suna shiga kuwa direct first class area suka wuce, tattara idanuwa meeda ta soma yi ko zata ganshi saidai bata samu damar hakan ba akayi announcing take off, daman seat dinsu ba roll daya bane da baby don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login