Showing 54001 words to 57000 words out of 381117 words

Chapter 19 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1990

ganin ta buge da kofa ya sashi tsayawa ya hade hannayenshi biyu a kirjinshi yana jinjina yarinta irin tata don babu babba mai hankali da zai dunga tafiya yana waige waige ba tare da kallon gabanshi ba ganin tayi tangal tangal zata fadi ya sashi saurin tahowa ?da sauri ya tarota zuwa jikinshi sosai, anatse ya lumshe idanunshi don jin yanda jikinta gaba daya ya sauka ajikinshi, yanayin ya bada wani irin sanyayyan alamari, ga sanyin dake kadawa, ganin idanuwa na dawowa kansu ya sashi dan janye hannuwansi wanda ya zagayo qugunta dasu duka biyun, kamar bazai cireba ya janyeta daga jikinshi sannan yace   mind your step, kidinga abu kamar mace mana  & amra wadda salati ya kama bakinta tun lokacin data saddakar da faduwar ta, jin muryarshi wadda ko acikin bacci taji take wani mummunan farkawa don tsoronshi da kwarjini da haibarsa yasata saurin karasa sanye jikinta daga nashi, sauke kanta qasa, giftawa yayi ta gefenta, ganin haka yasa tabi bayanshi har zuwa dakinta, saida ya bude kofan sannan ya mata kallo daya yace   get in  ..wuceshi tayi sannan ta samu waje ta zauna akan gadonta, jin alamun takowan shi wajenta yasata sauke kanta kasa ta runtse idanunta saida yazo dab da ita sannan ya tsaya kyam ya fito ainahin sojansa, hannunshi biyu ya sanya cikin aljihun jallabiayn jikinshi wanda tayi mashi kyau sosai, kallonta yayi daga yanda take zaunen sannan ya dan furta   get up  .. da sauri ta miqe har kirjinta na nemen bugawa da nashi, dan baya kadan yayi sannan yace   dago kanki  ..dagowa tayi anatse tayi mashi kallo daya, yanda idanunshi suka cika idanunta ya sata saurin sauke kanta qasa don bazata jure kallon cikin idanunshi ba   don t make me repeat my self  ..jin ya yi Magana adan zafafe ya sata dagowa da sauri amma bata hada ido dashi ba don bazata iyaba, anatse ya soma Magana   bakida tarbiya ne? baki iya gaisuwa bane ko sai nace ki gaisheni  jin yanda yake Magana adan fada fada ya sa jikinta fara rawa kaf kaf, anatse cikin sautin alamun kuka ya ciyo ta ya sata saurin cewa   dan Allah kayi ha..kuri.. sir..  ..
Kallonta yyi sosai saita dan bashi tausayi, anatse ya dan rankwafo don kwata kwata tsayinta a daidai kafadar shi ta tsaya,ganin yanda ya rankwafo sosai don har tana jin saukar nunfashinsa wanda ke kamshi mint ya sata saurin runtse ido, so take ta sauke kanta amma ta kasa don tsoron kar yace wani abun, don kwata kwata maganganunsh akanta basuyi mata dadi kwata kwata,
  didn t I warn you from calling me sir..  , da sauri ta kalleshi tadan tabe bakinta ashgwabe tace   yi hkuri manta wa nayi  & matsawa yayi ya taka har gaban couch din dakin cikin izza da kamewa sannan ya zauna anatse ya daura kafanshi daya akan daya kamar basarake, dauke idanunshi yayi daga kanta sannan yadan kwantar da kanshi jikin kujerar ya lumshe idanunshi, tunda ya zauna ya dauka wajen rabin awa a zaune bai motsa ba, ganin bashida niyar tashi ya sata kame kanta tadan kwanta har bacci ya dauke ta. Shima dai baccin ne yadan fusgeshi kadan daga bisani kuma ya farka.
?
Ganin tayi nisa a baccin yasa baibi ta kanta ba ya nufi hanyar futa, daidai bakin kofar ya juyo ya sake kallonta ganin kamar kwanciyar da tayi zai iya sawa ta fado don tana gab da jikin gadon a ringine, kamar bazai motsa ba daga inda yake ba Chan kuma ya juyo ya koma gaban gadon, tsayawa yayi daidai saitin fiskarta dake fuskantarshi,kallonta yake sosai wanda shine kallo daya taba mata na kurulla, kyakyawar cute baby face dinta ya zuba Ma ido wadda curly gaban gashinta ya soma rufe fiskar tata she look so innocent, Jan dan numfashi tayi kamar wadda a ka tsungula, ta dan turo redish lips dinta alamun kwanciyar bai mata dadi ba, juyi ta soma yi cikin bacci, aykuwa kamar yanda yayi tsammani yanda ta mirgino dinnan zata iya faduwa,bai gama tunanin ba ta gangaro da sauri ya dan rankwafa sosai ya tallabota jikinsa, gaba daya bata da wani nauyi amma yanayin yanda take da jiki da kayan alatu zaka dauka zatayi nauyi, wani irin sanyin niima ke shiga cikin kashinsa da jikinsa, tare da yanda take dan juyejuye acikin kirjinsa daya saqala ta Sai abin yayi mashi kamar tana goga mashi kirjinta ne, daurewa yayi ya miqe da ita a jikinshi ya kwantar da ita akan gadon asibitin yanda bazata fado ba saida ya gama ya juya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? zai fita kenan idanunshi suka sauka kan rigar jikinta da sauri ya gyara mata rigar donta yaye sama Santala santalan cikakkun lallausan fatar cinyoyonta da suka bayyana, yana gama wa ya fuce bai sake Waiwayon ta ba.( Wurin doctor dayayi operating dinta ya nufa inda ya shaida mashi nan da gobe za a sallameta don ta ji sauki saidai abinda baza a rasa ba saikuma dingishin da takeyi shima within 2days zata dawo normal, Sai kuma yanayin cin abincinta da Har yanxu ba komai mai nauyi zata ke ci ba, godiya yayi ma doctor ya fuce wajen da yayi parking motar shi, office ya wuce direct yayi wasu few ayyuka don Ana saka rai dawowa hutu very soon.( ( Hammam& ..( Kallon mahaifin sa yayi wanda ke zaune kan kujera da mamaki dauke a fiskar sa,yanayin yanda yake mashi magana kadai zai tabbatar maka this time around da gaske yake akan kudiriri kan sa, sauke idanunsa yayi wanda sukayi jaa suka rine sakamakon maganganun da yake fada mashi da kuma tunatar dashi tushen sa da asalinsa  karka manta, nine na maidakai mutun lokacin da kake ba kowan kowa ba, ni na suturta ka nina ilimantar dakai sannan na baka Duk wani kin dadi na rayuwa, so this should be the last time dazan umarce ka akan abu kamin gardama ( ( Dagowa Hammam yayi ya kalli mahaifin nashi wanda ya hade fuska babu imani ko kadan acikinta, anatse ya soma furta  in sha Allah bazan Kara maka gardama ba za ayi yanda kake so, sannan ka bani number Zan yi kokari akai,daman badan komai Nace a jinkirta ba saboda yanda yanayin abubuwan suka zo ne kuma ban boye maka da wata manufa ba saidan na bari Saina Tara Duk wani evidence da zaka ji dadin samu duk wannan zancen nasu cikin harshen larabci suke yi, saida suka gama magana kafin ya Tashi ya fuce daga gidan ma baki daya kamar zai Tashi sama,tuki yakeyi Amma idanunshi sunyi jaaa sosai,bai tsaya ko Ina ba Sai wani kebataccen waje saida yayi parking ya kutsa futo anatse ya shige ciki, maqabarta ce cike tam sosai wanda tasha tsafta ko ina tsaftsaf babu dogon datti anatse ya Taka Har gaban wajen da aka rubuta Fatima bint malawi, tsungunnawa yayi daidai wajen idanunshi na kawo qwalla, saida yayi mata addua sosai na samun yafiya wajen Allah sannan ya miqe  umm I m successful now, amma Duk bana ganin amfani komai saboda bakya raye, nayi maki alqawarin baki jindadin duniya saidai rai yayi halinsa,Allah ya jiqanki ya gafarta maki & yana kaiwa nan ya juya ya koma cikin motar shi, zaman kusan Rabin awa yayi idanunshi na kawo qwalla sosai, deep down yana jin abubuwa da dama dayake yi kamar ba daidai bane ba amma tunawa da kalaman mahaifiyar sa wadda ke tinasar dashi koda yaushe Duk wanda ya daraja rayuwarsa ya daga shi ya maidashi mutun kada ya sake yayi butulci sannan ya kasance mai hallaci agaresa. Kallon wayansa yayi yana wasu Yan danne danne kafin daga bisani ya Kurama number da mahaifinsa ya tura masa ido yayi kafin ya aje wayan, tsaki yayi duk haushi ya gama kamashi Duk shi yayi sakacin mantawa baiyi copy din evidence din ba gashi yanxu komai ya tabarbare mashi don mahaifinshi yayi tsananin fushi kuma yana ganin kamar yaqi fada masa ne don wani dalili daban wanda shi Sam ba haka bane ya bari ne komai yadan lafa sannan ya bullo ta bayan fage, tsaki yayi ya kunna motar ya fuce daga harabar wajen.( ( Abu Dhabi hospital& ( Sai wajen magrib ta farka, ahankali take lumshe idanunta wanda sukayi mici mici ta sauke su kan couch din dake facing gadon da take kwance, ganin baya wajen yasa tayi miqa bakinta dauke da salati sannan ta fara kokarin sauko da zara zaran kafafunta, ahankali hancinta ya fara jiyo mata kamshinsa, mamaki ne ya cikata don baya cikin dakin amma yanda take jin kamshin kamar yana kusa da ita, sannin yanda komai nashi kamshin yake hatta kujera Idan ya zauna ya Tashi kamshinsa na maye wajen yasa ta Kawar da tunanin ta miqe, harta wuce toilet ta dauro alwala ta fito jin kamshisa take sosai, ahankali ta jawo kasan rigar ta don goge don ruwa daya shiga mata ido, tsayawa tayi kyam ba tare da tayi abinda taso yi ba jin kamshinsa tarr ajikinta ahankali ta gangaro da hancinta zuwa gaban rigarta, mamaki ne ya cikata ta yanda akayi kamshinsa yazo jikinta, Kawar da tunanin tayi don Duk zatonta lokacin daya tallabeta ne data kusa faduwa kasa. Saida tayi salla ta idan kafin ta cire hijabin ta koma kan gadon ta doka uban tagumi wayan take so ayanxu don ta sake Kiran su salima ko za a dace amma babu hali, wasu siraren hawaye ne suke saukowa daga idanunta zuwa kan fuskarta tun bayan ta farfado Sai tayi kukan don babu abinda ke fado mata arai Sai tunanin yanxu da ta mutu fah shikenan kannen ta basu da wani basu da kowa ita kadai ta rage masu,lokaci guda taji karatun da komai ya fuce mata, hankalinta Duk ya koma gida don gani take kamar idan Har ta cigaba da zama ba tare da tasan halinda suke ciki ba wani abun zai iya samunsu koya cutar dasu,Amman sanin cewa babu wanda ke rayuwa kuma ya tsare Sai allah Hakan yasa ta fawalla Ma allah komai ta kai kukanta wajenshi don yanxu bata da kowa wanda zai tsaya mata saishi.( ( ( Washe gari wajen karfe biyar na yamma Amar ya iso asibitin, saida ya gama clearing Duk wani bills kafin ya wuce cikin dakin da aka kwantar da ita, lokacin daya shiga yayi mamaki ganin babu kowa a cikin dakin, jin alamun saukan ruwa acikin toilet yasa ya samu waje ya zauna kan couch din dake facing patient bed din, zaro wayanshi yayi yana diban time don yana sauri ne sbd Kiran da Hammam yayi mashi akan wani aiki da zasuyi urgently a office, bai jima da zama ba ya bude kofar toilet din ya futo, sanya take da kayan daya kawo ta asibitin dashi wanda tasa aka wanke mata a laundry din asibitin, batama lura da mutun a cikin dakin ba saida tazo tsakiyan dakin ta hango shi idanunshi kyam akanta, da sauri ta sauke nata ta soma magana a hankali  Ina wuni yaa..ya .. bai amsa ta ba daman tasan hakan ce zai biyo baya,saidai tsintar hard voice dinshi tayi yana cewa  I hate people wasting my time, na baki minti biyu ki sameni a waje  yana kaiwa nan ya sa kai ya fuce, da idanu ta bishi saida taga fucewar shi ta tabe baki, daman bata dade da Tashi ba tayi wanka ta shirya don already doctor dake ganin ta ya shaida mata sun sallameta, shiganta toilet kenan zatayi alwala don bata samu tayi sallan asr ba sakamakon baccin da tayi sosai tun bayan sallar dhur, hijab dinta ta zura sannan ta sanya takalmin asibitin don kwata kwata babu takalmi aka kawo ta, ficewa tayi daga dakin anatse don Har yanxu tana dan digisawa sakamakon gefen inda akayi mata aikin cikin data dafe don tundaga kan wajen aikin Har zuwa kafanta na daman tana jin kamar ba a jikinta suke ba.( Daidai gaban kofar shugowa cikin asibitin ta tsaya ganin mota guda a gaban wajen sannan ga horn dataji daga motar yasa tadan qara saurin kafar ta don tun fitowar ta ya hangota, cikin hanzari ta bude kofar gaba ta shiga da sauri wanda hakan yasa tadan fama cikin nata, rufe kofar tayi ta runtse idanunta sosai hawaye na zubo mata, baima tsaya bi ya kanta ba ya fizgi motar ya fice daga harabar asibitin, shuru ne ya biyo baya baka jin komai Sai ijjiyar zuciya da take sauke wa Sai kuma sanyin ac cikin motar tashi da kuma kamshin turarensa wanda yanzu kam itama ji take kamar kamshi ya fara bin jikinta, sanyin ac ne ya soma shiga cikin kasusuwanta, ganin yanda ta takure yasa yayi mata kallon daya ta wutsiyar ido yace  lafiya? Kallon sa tayi wanda idanunta suka sauka cikin nasa da sauri ta dauke nata  uhm..daman sanyin ne yayi yawa .. kamar bazai yi wani abu abun ba don saida ya dauka kusan minti biyar kafin ya rage gudun ac, ahankali ta sauke ijjiyar zuciya tana mamaki halayenshi, shi ba a isa a saka shi abu ba Sai yayi niyya idan kuwa zaiyi saiya jaa aji, lumshe idanunta tayi wanda suka rine sosai dalilin dan kukan da tayi da kuma yawan koke koke da take Duk dare akan qannenta.( Direct apartment dinshi ya wuce suna isa yayi parking, baiko kalle ta ba yace  kije jin haka yasa ta bude motar ta fuce abinta, shima yaja motar ya fuce daga cikin compound din, ahankali take tafiya harta karasa gaban lift ta danna floor din da zata sauka, tana karasawa gaban kofar ta tuna bata san pin key dinba gashi ya tafi, ga magrib na dosowa, komawa gefen jikin kofar ta tsaya don babu abinda zata iya, gashi babu waya a hannunta ganin tsayuwa bazai yiwu ba ga yanayinta yasa ta danyi gaba wajen lobby inda Aka aje wasu Yan kujeru a wajen ta zauna, Har kusan karfe Tara tana nan zaune, ga yunwa dake nukurkusarta ga cikinta dake neman kullewa ga shi wani irin bacci ke fusgarta ga ramuwar sallah don ko sallar asr bata samu tayi ba don lokacin data so yi ya iso asibitin ya dauketa, kuka ne ya kubce mata don ta galabaita sosai, runtse idanunta tayi gam ta dan yi relaxing bayanta akan kujeran Har wani irin wahalallen bacci ya kwasheta, kusan baccin awa biyu tayi a zaunen nan wanda Duk a wahale tayi shi, ga wani irin futsari daya matsota sosai wanda dalilinshi ya farkar da ita, miqewa tayi azabure ta koma gaban kofar apartments din, wasu irin hawayen wahala take,babu abinda take aranta sai rokon Allah ya kawo mata dauki,karshe dai a galabaice ta zauna anan kasa,tunanin yanda zatayi ne ya fado mata arai, yanxu idan tace zata tafi babu waya a hannunta bare tayi requesting taxi, bayan wannan Ma babu kudi hannunta kuma Duk wani transaction da wayanta Take yi.( ( 11pm na dare daidai ya iso cikin harabar compound din saida yayi parking kafin ya fito ,zagayawa bayan motar yayi ya bude ya kwaso ledoji guda biyu sannan ya rufe motar ya wuce ciki, anatse yake tafiya Har ya shiga cikin lift ya danna floor din da zai kai shi apartment dinshi, yana fitowa tun daga kan corner din da zai sadashi da nashi apartment din, daga nesa ya hango ta zaune a kasan, mamaki ne ya cikashi don baiyi tunanin ganin ta a wajen ba, anatse ya tako ya karaso gaban kofar ya kalleta, kamar bazai ce komai ba ya soma magana cikin nutsuwa  zaman me kike anan? Amra wanda tun dosowarsa wajen kamshinsa yayi mata sallama tare da maganar karshe da yayi yasa ta dan gumtse rinannun idanunta ta bude akan shi, Kawar da nashi idanun yayi don lokaci guda yaji bazai iya jurar kallon idanuun nata ba, babu abinda ya hango Sai wahala da galabaitar da tayi, wani irin tausayi ta ne ya ziyarce shi ba tare da dalili ba, saida yazo danna pin alamarin ya fado mashi, wato bata san pin din kofar bane ta zauna tun wajen 6 daya aje ta a wajen, runtse idanunshi yayi a zuciyar sa yace  why I m I causing her so much pain .. shigewa ciki yayi ya aje ledojin a kitchen, ganin ya bude kofar yasa ta fara kokarin miqewa Amman ina babu kuzarin yin haka, da sauri ta koma ta zauna ta fashe da wani irin matsanancin kuka ahankali gadan gadan zazzabi mai zafi ya tunkarota, jin shuru kusan minti biyar babu alamun shugowarta yasa ya Ankara da tunanin daya tsunduma,ahankali ya tako Har gaban kofar,ganin yanda take kukaa wiwi yasa ya karaso Har gabatan ya tsugunna ya daukota gaba dayanta, ya shugo ciki da ita ya rufe kofar, Duk wannan dramar akan idanun hafiza wadda tun lokacin daya sauke amra take bibiyarsu Har lokacin da amra ta karaso ta tsaya gaban kofar apartment din, lokacin data koma lobby yasa hafiza gane cewa bata san pin dinba wanda haka yasa taga dama ce mai girma a gareta, Duk wannan abubuwan da take bata ganin fuskarta don tana nesa da ita sosai,wayanta ta jawo ta fara video tun lokacin da amra ta galabaita Har lokacin daya iso ya shige ciki ya barta dukda yaga ta galabaita saida hafiza ta dauka daidai lokacin daya dawo ya zo daukanta zai shiga ciki da ita ne yasa tayi stopping video din don bata buqatan wannan scene din Iyakacin wanda ta dauka ya wadatar don wannan kadai zai tabbatar da babu so ko wani alamun auratayya a tsakaninsu, murmushin mugunta tayi don wannan Ma evidence ne mai karfi, wanda idan Har uae marriage consent group suka gani dole za a fara zarginsu, saidaga baya ta fara jin gajiyar tsayuwar da itama tayi dukdan samun biyan buqatarta, anatse ta tattara ta fuce daga apartments din gaba daya sannan ta tafi.( ( Bai sauketa ko ina ba Sai cikin bedroom dinshi, anatse ya kalleta yace  go and freshen up ya fuce zuwa parlor, ahankali ta fara bin bango


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login