Showing 60001 words to 63000 words out of 381117 words

Chapter 21 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1977

har wajen karfe takwas tana gaban sallaya ta kasa mikewa don gani take idan ta mike kamar zata rasa su ne gaba daya, tana nan kishingide har bacci ya kwashe ta mai nauyi sosai, daidai karfe tara ya futo daga dakinshi sanye da riga da wando na gyming, yana isowa parlor ya zuba mata idanuwanshi takowa yayi gabanta, tausayinta ne ya darsu a cikin zuciyarshi, baice komi bay a fuce daga gidan gaba daya, yana sauka ya wuce wajen parking ya dauki motanshi ya wuce penthouse din, don kwana biyu baijeba yayi motsa jiki shiyasa ya tashi da wuri. 89-90
Rayuwa juyi juyi wasu najin dadi wasu na cikin wuya, rayuwa dai ta gama juyawa su salima, don cikin wata uku abubuwa da dama sun samesu ciki kuwa shine azabtuwar da suka sha wajen rita, wadda ta gano wayan ta da salima ta dauka watannin baya da suka shude, yanda ta ganota kuwa akwai ranarda cutar salim tayi tsananin kamar zai mutu hakan yasa ta burkicewa ta zaro wayar hankalinta baya kanta ta nufi dakin rita arikice, tana zuwa ta fara dube duben charger ko zata samu, rita wadda futowanta kenan daga toilet din cikin dakinsu na masu aiki, idanunta ne suka sauka akan salima dake barbaza maka kayanta ganin yanda salima ta burkita mata katifarta kayyaakin data sato da yawa daga dakunan yan gidan duk sun zuba a kasa yasa ta dago kallonta ga salima, ganin tsohuwar wayrta a hannun salima yasa ta tako gadan gadan ta kwashe ta da maruka wajen hudu ajere, salima kuwa wadda yunwa ta gama busar da ita ta dago ta kalli rita, ganin yanda take kallonta yasa rita cewa   ke dan uwarki barauniyace ke dama, kece kika sace min waya, to yau kuwa saina nuna maki ni cikakkiyar yar bariki ce mai lasisi, fadowa tayi kan salima saida ta mata dukan tsiya kafin ta kwace wayar ta hankadata gefe, dakyar salima ta rarrafa zuwa kofar dakinsu dukda bakinta bai mutu ba babu abin take cewa sai Allah ya isa, tun daga ranar rita ta dunga gana masu azaba, yanxu takaiga har line din wutar dakinsu gaba daya tasa mai gyaran wutar gidan wanda suke soyayya dashi ya kashe ta bangaren su salima, haka zasu kwana cikin zafi ga duhu, abinci kuwa yanxu kamar dabbobi haka take basu, wani sa in zata zuba masu shinkafa banda miya ko mai haka zasu ci suna kuka, wani sa in kuwa abincin da take diga masu ko salim baya koshi balle ita ta samu taci,duk wannan wahalar da suke sha basu taba attempting guduwa ba, to ko sun gudu ma ina zasuje? Duk wannan rayuwar da suke babu wanda ke lekensu daga yan gida gaba daya dukda yanxu suma abubuwa sun fara juya masu, don akwai wani tashin hankali da gaba daya gidan suka shiga wandalabarin kamawar ya Ibrahim ya riskesu na safarar mugayen kwaya da yake yi daga manyan kasashe daban daban, wanda haka ya mugun tayarma da dai hankali, ya kashe maqudan kudi sosai akan belin Ibrahim har ta kaiga ya sayarda gidan su salima don sunanshi ne akan takardun gidan as their guardian dukda sune masu gadon gidan, saida ya dauke wata uku a kulle duk ya jeme ya lalace yaci uwar wahala kafin alhaji Mustapha yayi yan cuku cuku aka samu aka fito dashi don da kyar aka samu aka danne zancen don case din yaje har gomnati kasar nageria don abin ya shafi sauran kasashe da taimakon wani abokin alhaji Mustapha babban general of police aka samu zancen ya kwanta don o su manyan government din bazasu so zancen ya fitaba don zai zame masu babbar matsala tsakanin kasashe da akeyin safarar don ayanda report din yazo daga Nigeria ake futar da kwayoyin meaning daga nan ake hadata da wasu sinadarai da anan Nigeria kawai ake samu haka zalika idan gomnatin kasashen suka gane zai iya jawo matsala sosai wanda gomnatin Nigeria bazata so haka ba kwata kwata.
Tunda aka fito da ya Ibrahim aka fito da Ibrahim babu wanda yasan inda yake, hajiya kareema tayi kuka tayi magiya akan dadi ya fada mata inda danta yake amma fir yaki fada mata, karshe ma yace ta cire dan da ya jawo mashi bal in da bazai iya saukewa ba daga duk kudin shi daga jerin yayansa, don ya sallama shi.
?
Akwai wata ranar asabar tana zaune kusa da salim wanda ya jeme ya rame kamar wanda yayi shekaru yana jinya,saboda ciwon zuciya dayake fama dashi tun bayan rasuwar iyayenshi don yanxu har ta kaiga baya iya Magana sannan abu kadan ke furgitashi koda kuwa karar kofa ne sai ya zabura ya kankameta ya fara kuka, ayanxu kam ta fawwalama allah kawai don rayuwar su ta gama tagayyara, babu makaranta, babu gata, babu walwala, babu cima mai kyau sai rama da rayuwar kunci,itama kanta ciwon cikin da take ya gama maidata kamar mahaukaciya don duk dare saitayi shi, kallon salim tayi wanda ya maqalqaleta sosai a jikinta yana futar da wani i???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?rin nunfashi dakyar, tun safe yake wannan nunfashin wanda daga jiya zuwa yau ya chanza daga nunfashin da yakeyi, shafa kanshi tayi ahankali tace   Allah ya baka lpy salim, allah yana tare damu, nasan yana kallonmu kuma yana jinmu kuma zai kawo mana dauki insha allah  , haka ta dunga surutanta ita kadai don baya iya Magana shi, ganin lokacin sallah yayi yasa ta kwantar dashi gefenta kan carpet ta miqe ta wuce toilet dinsu, gaba daya toilet din ya fita hankalinshi yayi wani irin dauda saboda baya samu gyara daya kamat da omo don rita ta daina basu koda sabulun wanka ne, fanfon toilet din ta bude wanda shima tsatsa tasa kan famfon ya balle saidai ruwa yana bulalowa idan aka kunna ta gefen wajenda bai balle ba, alwala ta dauro sannan ta fito ta jawo hijabinta wanda dauda tasa ya kode don kayansu ma ba samun wankin arziki yake ba saidai ta dauraye masu da ruwa zalla idan dattin yayi yawa sosai, tana idar da sallah ta miqe ganin yanda salim ya takure yana rawar sanyi da sauri ta arsa gabanshi ta tallabo shi sosai izuwa jikinta ta daura shi kan gado wani irin tari ya soma yi kamar ranshi zai futa, zama tayi gefenshi tana mashi sannun, ganin tarin yadan lafa yasa ta gyara mashi fuskarshi daya toge da gadon, tana zare hannunta idanunta ya sauka akan jinin dake Malala daga tafin hannunta, kallonshi tayi da sauri, jikinta na bari ta soma furta   innalillahi wa inna ilaihi rajiun  , kai salim tashi mene, wannan jinin na mene  ..afurgice ta janyoshi sosai don ganin daga inda jinin ke futa, kurama fuskarshi ido tayi bakinta na karkarwa    na shiga uku salim, me nake gani innalillahi wa inna ilaihi rajiun  , jijigashi ta soma yi ammam ina kamar nunfashinsa ya tsaya, da sauri ta miqe ko ganin gabanta batayi wani irin juyawa da kanta keyi yasa ta kwala ihu ta fice aguje, har tsakiyar parlor rabonda ta fito harabar wajen harta manta, kallon ta daya bayan daya waenda ke zaune a parlor sukeyi, ya Muhammad wanda daga ya Ibrahim saishi wanda saukarshi Kenan kowa yazo tarbarshi don tafiya yayi ma tsayi sosai don ya shafe shekara kusan bakwai rbonshi da gida, su hajiya kareema da yayanta, khady dasu amina da jabir da jalal kananun duk suna zazzaune suka juya jin wani irin wari na doso parlorn, kallonta ibrahim yayi wanda shima warin jikin nata ne ya mashi iso zuwa hancinci anatse ya soma Magana cikin kamewa da nutsuwa sannan   mummy ina kuka samu masu tabin hankali a ckin gidan nan, kudai da kwashe kwashen yan aiki  , tabe baki haj kareema tayi tace   yar badaru ce fah  , gwalo idanu yayi yace   wani badarun?  , bata bashi amsa ba ta miqe ta haye sama abinta bayan ta tattara kananun yayanta suka wuce sama,don kar warin salima ya cutar mata da yaya.
Kallonta muhammad yayi da kyau sai a lokacin shima ya wani tuna da yayan kawun su daya rasu, hankali atashe ta dora hannu aka a fara sambatu, kallonta yayi lokaci guda ya fuskaci bata da lafiya don karatun likitanci da yayi,   keee ki nutsu  ya dan fada da karfi, juyawa tayi idanunta na dishi dishi ta kalleshi don bata shaida fuskarshi da sauri ta karasa gabanshi har yana dan matsawa gefe ta durkusa tace   dan allah ka taimaki dan uwana zai mutu na shiga uku  , saida tayi Magana ya tabbatar ba mahaukaciya bace da yayi tsammani ?  ina kanin naki  , da sauri ta miqe tace   yana daki hancinci da bakinshi suna fito da jini, da sauri ya miqe tayi gaba ya bita abya suka shige dakin, wani rin kura da datti asa shi toshe hancinsa, da sauri ta yaye labulensu wanda yaji jiki sannan ta nuna mashi salim dake kwance kamar gawa har jinin ya fara bushewa akan gado, da sauri ya karasa gaban gadon ya taba wuyanshi don neman pulse dinshi, jin yanda pulse dinshi yayi weak sosai ya sashi tsayawa akanshi sosai cikin yan mintuna pulse din ya tsaya, shuru ya mhammad yayi yace   I thik hes gone  , salima na jin haka wani irin hajijiya tahau kanta, atakae a wajen ta anke jiki ta fadi itama wanwas, akidime Muhammad ya mike yana kallonta da kanin nata, da sauri ya karasa gabanta jin pulse dinta yayi weak hankalinshi ya tashi da sauri ya mike ya fuce daga dakin, yana zuwa daidai hanyar futa ya kwala ma masu gadin gidan kira da driver daya daukoshi daga airport da gudu suka karasa cikin yayi masu jagorar cikin dakin tare da masu nuni da yaran yace, ku futo dasu akaisu asibiti, mai gadin baba dan ladi wanda shima rabon da ganin yaran kusa shekar biyu Kenan, don tun yana tunanin suna gidan har yazo ya yarda da zancen hajiya kareema na cewa duk wanda ya nemesu ace basa nan, da sauri suka sungume su, Muhammad na biye dasu aka saka su cikin motar daga salim din har salima, da sauri driver ya shiga gaba shima Muhammad ?ya shige baya gaban owner coner suka ja motar suka fuce daga gida, duk wannan akan idon hajiya kareem wadda tun daga window dakinta take hangensu, karshe ta tabe baki tace   zaka dawo ka sameni ne, sometimes I wonder ko nina haifeka, don jinina bazai tsaya bata lokaci akan walqantattun yayan nan ba,  & .
Cikin wani babban private hospital suka tsaya inda nan ne muhammd sai fara aiki, yana karasawa ciki ya miqa id card dinshi a chan kasar daya baro as professional health personel receptionalist din na ganin sunanshi ta kira nurse da babban likitan dake duty aka dauko gado suka wuce waje, yanda aka kwasosu daga gida haka nan suke kwance babu chanji, da sauri nurses din da taimakon driver aka fito dasu aka kwantar akan gadon aka shiga dasu cikin emergency, Muhammad kuwa office dinshi ya wuce wanda aka tanadar mashi tun kafin a iso kasar don part time job zaiyi a cikin asibitin kafin wasu yan watanni ya koma jordan don achan yake aiki, agajiye yake ga gajiyar tafiya ga wanda ya tarar a gida, mamaki ne ya cikaci sosai, nazari ya fara ya akayi yarannan suka wulqanta haka, bayan lokacin daya tafi ma suna kananu sosai cikin gata, kuma lokacin iyayen sun a raye, do mutuwar kawun nashi ma bai sani ba sai bayan yan shekaru cikin Magana daddy ke fada mashi, runse idanunshi yayi tausayinsu na ratsa shi.
Dakyar likitoci suka samu nunfsashi salima ya dawo, kafin suka fara bata treatment sosai, karshe dai harda operation aka kare ayi mata don hantarta guda daya ta lalace saida aka cire, salim kuwa sun dauka kusa awa shida ana fama, dank iris ya rage zuciyarshi ta buga wanda hakan yasa komai ya tsaya chak ajikinshi, wannan dalilin yasa Muhammad yayi tunanin yam utu don baisan yana da ciwon zuciya ba, shima dai saida aka kare da operation an samu komai ya daidaita saidai kuma ya fada coma.
Hankalin ya Muhammad ba karamin tashi yayi ba lokacin da manya manyan likitocin da sukayi operating dinsu suka mashi bayanin matsalolin yaran, wato bayan ciwon zuciya da ya salim ya kamu dashi wanda yanda tayi mashi mugun kamu don gab take da bugawa a kananun shekarunshi da ciwon kidney da salima take dashi wanda itama badan an cire wanda ta lalace dinba zai jawo dayan da ya rage mata yayi affecting, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, wani irin tausayi suka bashi kamar ya masu kuka don duk gidan bayan ishaq saishi waenda suke da tausayi da jin qan marayu duk yaya alhaji Mustapha.
Daga asibiti ya barsu cikin kulawar likitoci da nurses din dake da duty din daren ranar, sai wajen karfe takwas yabar asibitin ya wuce gida direct, yana isowa bai tsaya ko ina ba sai bangaren sun a samarin gidan, dakinsa ya wuce wanda yake kusa dana wahab, shiga yayi ciki ko ina fess fess, kayan jikinshi ya rage ya wuce toilet don yin wanka, saida ya tsaftace jikinshi kafin ya futo ya wuce bakin gadon sa, saida ya kira asibitin yaji yanayin lafiyar su kafin ya aje wayan, sallolinshi da ake biyanshi ya rama, yana idarwa ko abinci bai nema ba don baya jin zai iyaci don wani irin bacci yakeji sosai.
Haka hajiya kareema tayi zaman jiranshi har kusan karfe goma bai leko bangarenta ba ganin haka ta yanke shawarar neman shi washe gari, damuwa tayi mata yawa, business dinta yana neman yin kasa sbd itama saida ta fitar daga cikin savings dinta wajen fitar da Ibrahim.
?


Washe gari karfe goma ya ibrahim ya shirya fess cikin manyan kaya jumper skyblue, yana gama shirinsa yafuce daga gidan don da alamu yawanci babu wanda ya tashi sai rita dake kai kawo na abinci tana leken shi kamar munafuka aranta tace   chineke, this guy fine dieee, ahhhh  , baima san da mutun a wajen ba ya futo wajen garage din motocin gidan ya kira haladu driver daya kaishi asibiti jiya, suna gab da juya kan motar zasu fice motar haj labiba ta danno kai, yana ganin haka yasa ya tsaida driver ya sauka, domin su gaisa, tana ganinshi cikin fara a ta futo daga bayan mota, takowa yayi har gabanta yace   good morning mummy, na sameku lpy  , cikin fara ar ta ta amsa mashi tare da yabon shi don duk gidan babu wanda ya kaishi daraja na gaba dashi ba kamar sauran ba, wucewa tayi daman tafiya ce ta taso mata zuwa niger don abbanta dake jinya tsawan wata Kenan sai ayanxu kannenta suke fada mata ganin kamar yana gab da rasa ranshi kuma yana nemanta, bayan tace airport dinne jirginsu yayi delay har ta kaiga akayi cancelling flight din saina karfe biyar shiyasa ta dawo gida kawai, tana hawa sama ta wuce dakin hilma don ganin kota tashi don da safe ta shiga dakinta taga tana barcinta hankali kwance, ganin baccin take hankali kwance yasa ta wuce dakinta tana mamakin yawan baccin da hilma takeyi yanxu, gashi yanxu sun shiga 100 level amma kota kota taqi maida hnaklinta wajen yin karatu yanda ya kamata, Ibrahim kuwa bayan wucewar haj labiba ya wuce cikin mota haladu ya danna horn driver ya wangale masu gate suka wuce da gudu, malam audu na rufe gate ya koma kan bencinsa da yake zama a bakin gate a waje yana shan iska, nan yan abokanan sa suke zuwa susha hira suna tsaida masu talle suna sayan gyada da rake, malam audu irin masu gadin nan ne da tsegumi baya wuce bakinsu, yana nan zaune abokinshi iliya ya karaso kamar kullum hannunshi rike da ledar shayi da burodi harda soyayyan kwai da yake sayo musu suna ci, ganin shi yasa mlm audu wangame baki yace   ah ah abokina iliya, yauma ganimar zamu kwasa, kaidai baka gajiya da hira, kullum saikazo hira,  dariya wanda aka kira da iliya yayi ya zauna gefen bencin suka gaisa kafin audu ya dakko masu kofi suka rama shayin suka kora da burodi da kwai saida sukaci sukayi nak kafin audu ya soma Magana   kai abokina wallahi mutanen gidan nan basu da Imani ko kadan  , da sauri iliya ya soma maganar irin ta mutanen da sukayi zaman legas don kwata kwata ba bahaushe bane amma zama da yan arewa yasa hausa ta zauna radau a bakinshi, kallonshi iliya yayi kamar wanda yake jiran zancen yace   mazaa ya akayi bani labara maisa kace haka don ni ina ganin masu gidan nan kamar sunada mutunci  ..tsaki kawai audu yayi yace   wallahi a fuska ne amma waennnan da kake gani mugaye ne na karshe wallahi, nan ya fara bashi labarin yanda suka shiga dakinsu saluma suka gansu kamar gwawawwaki da irin bakar wahalar rayuwa da suke ciki, kai karshe harda rayuwar da su amra sukayi tun farkon zuwan su har zuwa lokacin da ta tafi karatun har labarin fyade itama da wahab ya mata da yanda itama salima Ibrahim yaso yi mata amma allah ya kubutar dasu da yanda alhaji ke wulaqantar da rayuwar su kamar ba yayan qaninshi ba, sannan ya kora mashi da hakkin yaran bazai bar alhaji mustapha ba da iyalanshi don tun a gidan duniya shima iyalanshi sun fara shiga cikin babbar matsala gashi yanxu an kama danshi dake safarar miyagun kwayoyi zuwa manya manyan kasashe daban daban har kawo yanxu babu wanda yasan inda yaran yake yana kaiwa karshe iliya ya karbe da   kai amma mutanen nan anyi azzalumai, allah ya saka masu, dana dam babu tabbas, duk wannan abun ace yayan dan uwanka jininka don kasa ta rufe mashi ido shikenan sai jinisa da ya kamata a basu kyakyawar kulawa su ake walaqantarwa, yana kaiwa nan ya zaro wayarshi ya danyi yan latse latsen shi kafin ya miqe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login