Showing 141001 words to 144000 words out of 381117 words

Chapter 48 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2023

that& ..
A harzuke tace  let me just end the call
Da sauri ya ce it s just a fake scandal,
 I don t understand, what do you mean by it s a fake scandal
 I can t tell you everything, but it s a fake scandal, no one Is banned,not even the general, it s just a plan

Shuru tayi tama rasa me zatayi murnar abunda ya fada mata ko haushinsa, you mean it s all a plan?, and you didn t even bother to&  da sauri taja Bakinta tayi shuru Tunawa da lokaci da abun ya faru basa tare,  hold on a sec
Tana fadin haka ta kashe wayanshi ta shiga Kiran amra ba qaqautawa stil baya shiga, burinta yanxu kawai ta samu amra ta daga wayanta ta bata wannan kyakyawanan albishir,saurin sake kiranshi tayi tace  do you know a way that I can reach some one that is in nigeria?
 I ve been trying to reach her out

Da sauri yace  kina da contact dinta na chan ne?
 eh ina dashi but it s useless , don ina kira baya shiga ta bashi ansa
Gyara zaman wayan yayi a kunnenshi don yana office nema
 What does the number start with
 It s start with zero
Da sauri yace  hold on a sec
Sauke wayanshi yayi ya shiga contact din Amar na nigeria.
Sake kiranta yayi yace  I don t know if this will work but you have to add 3 more digit before the first digit, let me send you an example through sms
Da sauri ta sauke ijiyar zuciya tace  thank you so much ta kashe wayan
Yana tura mata ta saka tare da saurin dialing, nan take wayar ya shiga Har ya fara ringing, da sauri ta miqe fuskanta dauke da murmushi farin ciki.
Amra dake zaune tun bayan sallar la asar bata motsa daga inda take ba tana tunani duniya da makomar rayuwar ta sanin cewa yanxu ita baza a saka kanta cikin jerin budurwa ba hawaye na saukowa daga fuskanta tayi saurin goge wa, tunani ta shiga yi da zuciyarta inda ta yanke samunshi don suyi magana akan rabuwar su don bazata tafi da auren wani ba gida koda wasa, bala in da zata tarar a gidan uncle na banning dinta da akayi babu karatun ma ya isheta.
Tana cikin wannan tunanin wayanta yayi ringing& & .
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!!!
13/05/2023
Da sauri ta dauka wayan ganin contact din haifa akan screen din, Har jikinta na bari
 Hello& .haifa, is that you
Cikin murna da farin cikin samun kawar Tata tayi saurin cewa  habibty Ina kika shiga,I m so sorry, bansan yanda Zan sameki ba saida hammam yam min bayanin yanda Zan kira ki cikin mamakin abunda haifa ta fada tayi saurin cewa  hammam? Are you guys back together?
Sauke nauyayyan numfashi haifa tayi tace  it s a long story,and what I will tell you now will shock you even more
Shuru amra tayi cikin damuwa da daurewar kai tace  haif, so much has been going on in my life recently, na shiga damuwa sosai na rashin samunki
cikin farin ciki da zumudin abunda zata fada mata tace  babe abunda Zan fada maki yanxu zai kawo karshen damuwarki I promise
 Haif na&  saurin katseta haifa tayi tace  babe you ve not been banned from uae Da sauri amra ta miqe tsaye idanunta tap da qwalla kanta ya gama qullewa da abunda haifa take fada mata  babe what, what are you talking about, ban gane ba kimin bayani yanda Zan gane
 Yea babe, abunda na fada maki gaskia ne, Duk abunda ya faru a lokacin it s just a plan made by general for some certain reasons,dazu hammam ya fada min,
 Then that means he used me?,haifa you mean all That has happened kwanakin Duk karya ne?innalillahi wa inna ilaihi rajiun, haif Im so stupid
Tana karashewa ta fashe da kuka, tsagaitawa haifa tayi hankali tashe jin kukan da amra keyi tace  babe what wrong, na dauka you ll Be happy with the good news

Cikin dacin rai da baqin ciki tace  no& noo haifa,
Ta sake fashewa da kukan, abunda take son fada mata ma ya maqale, sanin halin amra yasa haifa yin shuru, saida ta dauka kusan minti ashirin tanayi kafin ta tsagaita don kanta, hankalin haifa ya gama Tashi gaba daya saidai ta Kasa gane dalili kukan kawar tata
 Babe ta kira amra ahankali cikin natsuwa
 What s wrong? Why are you crying?
 Haifa he lied to me, he used me dan kukan data tsagaita ta cigaba
 Amra pleas explain to me yanda Zan fahimta, who used u?
 He played with my innocence, shine ya kawoni gidansa don ya samu cikar burinsa, yanxu ne Ma komai ya gama dawowa kaina
Da sauri haifa wadda ta gama kufuluwa da zancen tayi saurin cewa  kin saka ni a duhu, kimin bayani
Nan take amra ta fara zayyano mata bayanin tundaga lokacin da m5 ya dauko ta ya kaita airport zuwa lokacin da aka kawo ta gidan, shuru haifa tayi don itama kanta ya gama daurewa  you mean, kina zaune a gidanshi? And bai fada maki gaskia ba? What s his motive kenan, to protect you?
Cikin bacin rai amra tace  to protect me? He lied to me because all this while ya nuna min saboda ni da taimakon da yayi min akayi banning dinshi shima Har yayi affecting all his achievements,I was so stupid, I ve been blaming my self all this while, what did I do to deserve this?
Da sauri haifa ta tari nunfashinta tace

 Babe if that s the case then why would he do that?,maysa zaiyi haka
 Saboda yaga I m helpless, saboda yaga banida kowa, haifa he slept with me, forcefully tana kaiwa nan ta Kara fashe wa da kuka mai shiga rai

 Wahttttt!! Haifa ta fada da dan karfi tayi saurin gyara zaman wayar a kunenta ta cigaba  he slept with you? How did you let that happen
Nan take amra ta sake fashewa da wani kukan da zaka gane abun ya taba zuciyarta sosai tace  I don t want to stay for a second in this house haif,I m in pain
 Babe calm down, ki kwantar da hankalin, karki yi saurin yanke hukunci,mubi komai a hankali
Da kyar haifa ta tausasa ta tare da bata shawarwari, sun dauka kusan awa guda suna magana kafin suyi sallama.
Aje wayan tayi a gefenta ta wuce toilet ta dauro alwala,kafin ta fito ta tada sallah, ta dade sosai kan sallaya tana adduoi da neman taimko wajen Allah, babu abunda yakai tsayawa gaban Allah kakai kukanka, wannan zaman da tayi sai Tashi kashi 50 cikin damuwarta ya ragu, daman batada riko a ranta, saidai wannan ya tabbata sosai, mikewa tayi ta ninke sallayan ta zauna gefen gado, abincin da Nadine ma ta kawo mata bata kalleshi ba kwata kwata, tagumi ta tafka na tausayin rayuwar data tsinci kanta, tawakkali tayi tare da fawwala Ma Allah komai saidai tafiya kam Saitayi ta babu fasawa.
Shawarar da haifa ta bata ta dauka, cikin kwarin gwiwa ta mike shiga tattara kayanta tsaf babu abunda ta bari ta saka acikin akwatinta.

Karfe Tara na dare daidai ta sauko kasa, fuskanta a kubure idanunta yayi jaa sosai, samun waje tayi ta zauna akan kujeran sitting room ta rafka uban tagumi, zaman awa uku tayi anan zaune, idanunta kyam babu alamun barci tana zaman jiran dawowan shi, karfe sha biyu daidai da Yan mintuna taji karar horn hakan ya tabbatar mata ya dawo, gyara zamanta tayi tare da saurin cire tsoron daya durar mata lokaci guda don tayi alqawarin cire tsoronshi daga ranta.
Bude kofar yayi kai tsaye ba tare da tunanin komai ba ya iso Har sitting room din baima Lura da ita ba zaune, Har ya wuce sitting room din tayi saurin miqewa ta fuskanceshi tace  sannu da dawowa
Tsagaita tafiya yayi hannunshi duka na cikin aljihun wandonshi, fuskanshi na nan babu yabi ba fallasa Sai zallan gajiya shimfide a kan fuskar tashi, kamar bazai ce komai ba ya dan juyo kadan yace  yau..wa!
A rarrabe kafin ya juya yana shirin Taka stairs tayi saurin bin bayanshi ta tsaya dan nesa dashi tace  inason magana dakai
Dakatawa ya danyi bai juyo ba haka zalika bai ce mata komi ba, ganin haka ya sata saurin cewa  daman ina& . Bai bari ta karasa ba ya wuce sama  idan magana kike kiyi dani ki sameni a sama bin shi tayi da idanu harya kauce Ma ganin ta kafin ta sauke wata nauyayyan ajiyar zuciya, ba tare da tunanin komai ba ta dake tare da tattaro Duk wani kizarinta ta hau saman,tunda ta tsaya bakin kofar dazai sadaka da sitting room gabanta ya soma faduwa, tana jin yanda heart dinta ke racing, saurin danne wa tayi fuskanta babu alamun fara a ko murmushi Sai damuwa, saida ta fara knocking kafin ta bude kofar, a zaune ta taddashi ya daura kafa daya kan daya idanunshi na kan wayar yana dan latsawa, takowa tayi dan nesa dashi ta kauda kanta gefe don ko kallonshi bata son yi don abubuwa ne da yawa ke dawo mata a cikin zuciyarta data kalleshi ciki kuwa Harda tsiraicin shi data gani mura ran.
Kasa cewa komai tayi yanda shima baice mata Kala ba don kwata kwata bai dago ya kalleta ba tun bayan kallo daya daya mata saidan kallonta da yake ta gefen ido ganin yanda ta kauda kanta gefe idanunta sun dan kumbura sunyi jaa, ganin tana shirin dagowa ya sashi kauda nashi idanun gefe
 Zan tafi gida, Ina buqatar rabuwar auren mu
Dan dagowa yayi ya kalleta don yayi mamakin futowa daga zancen daga Bakinta saidai baice komai ba ya kura mata idanu yana son karantarta
 Da izinin za zaki tafi?
Rai Adan bace ta kalleshi ido cikin ido, kafin ta sauke nata don yayi mata mugun kwarjini tace  bana buqatar izinin kowa, zama na anan bashi amfani
 And who told you that? Yayi saurin tarar nunfashinta
Baki a sake ta dago ta kalleshi, wani irin abu na tsaya mata a makoshi, saurin runtse idanunta tayi ta bude su yar akanshi tana kokarin tattaro courage dinta tace  bana buqatar aure a kaina tunda anyi banning dina daga uae babu amfanin auren, daman anyi shi ne saboda yarjejeniya da mukayi, tunda ban samu abunda na nema ba Ina son ka sake ni
Yanda take fada adan fada fada ya bashi mamaki sosai, wannan yar yarinyar ce ke mashi magana haka lallai ya jama kanshi raini, saidai zai koya mata hankali, rai Adan bace ya kike gadan gadan yayo kanta, saurin jaa baya tayi har tana turgudewa gabanta na bugu fat fat don koshi daya karaso gabanta saida yaji bugun zuciyar, saurin runtse idanunshi yayi idanunshi sunyi jaa sosai yace  how dare you talk to me like that? Bakya bukatar auren? Babu macen data isa ta kalli cikin idanuna ta fada min abunda zanyi, now open your ears ki saurare ni, you are going no where, zaki bar gidan nan only if I say so, and I will only free you when I m pleased
Da sauri ta dago ta kare mashi kallo, kallon kama raina kin hankali, shima ita yake kallo kuma tsaf ya gane ma anar kallon, saurin hana kanta kukan da take shirin yi tayi, tana son bude Bakinta saidai mamakin shi ya hanata, kallonta yayi sama da Kasa kafin ya juya ya wuce dakinshi ya barta a sandare, wani irin haushi da takaicin shi yake ji, me yake nufi kenan? Ai kuwa zata nuna mashi ita ba yarinyar yake kallonta dashi ba.
A zafafe ta fuce daga dakin ranta ya mugun sosu sosai Kalaman shi sun mata zafi,koda ta karasa daki zarya ta fara yi acikin dakin  I will on free you when I m pleased!!!! Me yake nufi kenan, ta fada da dan karfi wannan kalaman sunyi mata zafi sosai.
Da kyar ta lallaba kanta taga Safiya ranar don hancin Ma qaurace mata tayi, kuka kam saida tayi shi don idan batayi ba bazata samu sassauci ba, Sai bayan sallar asuba barci ya kwasheta akan sallaya.

Karfe sha daya daidai ya fito cikin shirinsa kamar kullum na kananun kaya, sunyi mashi masifar kyau Sai kamshi yake, wayar shi ce kawai a hannunshi Sai laptop bag dinsa ,saukowa kasa yayi ya bi hanyar dazai kaishi zuwa bedroom dinta, hankali kwance ya danyi knocking ya bude kofar, a zaune ya taddata ta gefen gado ga akwatinta dake gefenta ta dafe kanta, ta dade da Tashi ta tayi wanka ta shirya tana tunanin yanda zatayi, gashi ta kira haifa yafi sau Nawa, idan ta kira baya shiga kwata kwata, knocking din da taji baisa ta dago ba don Duk tunaninta Nadine ce ta shigo dakin, ahankali kamshinsa ke shiga cikin hancinta wanda ke sa zuciyarta racing sosai, saurin dagowa tayi ta mashi kallo daya kafin ta kauda kanta gefe, takowa yayi dan nesa da ita kadan ya kura Mata idanu, saida ya dauke kusan minti biyar a tsaye baice mata qala ba itama bata ce mashi ci kanka ba,rai a bace ya fuce daga dakin ta bishi da kallo harya bace mata daga gani.
Breakfast kawai yayi ya fuce daga gidan, saida ya tsaya wajen masu gadi kafin yaja motar ya bar anguwan gaba daya.
Yana fita daga dakinta ta janyo mayafin abayar jikinta tayi rolling akanta tare da janyo wayarta, taba shirin fita saiga Nadine ta shigo hannunta dauke da tray na abinci data saba kawo mata, da ido Nadine ta bita ganin ta janyo akwati, bata shiga hurumin da ba nata ba shiyasa tayi saurin cewa  ma am ga breakfast
Ba tare da ta kalli Nadine dinba tace  thanks Nadine baba buqata I m okay
Tana kaiwa nan ta janyo akwatin nata ta fito daga dakin, tana shirin sauka dashi Nadine ta karaso tace  let me help you ma

Kasa suka sauko tare ta karbi akwatin tace  thank you Nadine ta fuce daga parlor, ahankli cikin natsuwa take tafiya Har tazo bakin gate, da sauri security ya futo daga dakinsa don ya hangota ta cctv camera da aka saka a kusa da gate,  good morning ma am
Morning tayi saurin amsa mashi, ganin baiyi yunkurin bude kofar ba kuka tasan smart gate ne yasa ta juyo ta kalleshi shima ita yake kallo tace  ka bude gate Zan fita ne
 I m sorry ma, but sir yace Kar abar kowa ya fita daga gidan nan
Kura mashi idanu tayi ta sake cewa  what do you mean?
 I m so sorry ma am I can t let you out
Rai abace ta sake kallonshi tace  lub yaushe yace maka Kar abar kowa ya fita
 Dazu ne ya bada umarni I m sorry ma
Rai abace kamar ta shakeshi take ji, wani irin kuka ne yake neman kufce mata, ta wuce cikin gidan rai abace, Nadine da taga shigo wants saitayi makakon ganinta sosai Har ta wuce sama, da sauri gate man ya janyo akwatin nata ya shige dashi Nadine ta karba ta wuce mata dashi sama, koda ta hau sama kuka ta fashe akan gado, ta rasa wani tunani satayi, mai yake nufi da ita kenan, wannan wani irin masifa ne,a dake ka a hanaka kuka, ranta a bace yake sosai, haushin sa ya ninku a zuciyarta.
Koda Nadine ta shigo mata da akwatinta ta tausaya mata ganin irin kukan da take yi
 I m sorry ma am bansan meke damunki ba but ba kuka ya kamar kiyi ba, try and fine d solution to your problem
Dago da jajayen idanunta tayi ta kalli Nadine tace  Nadine please help me out, Ina don barin gidan nan, bana son zama
Takowa Nadine tayi Har gabanta ya zauna gefenta tace  Bana son shiga hurumin da ba Nawa ba, kuka bazan tambayeki ba, but inaso kiyi hakuri ki daina kukan
 Nadine Wallahi bana son zama acikin gidan nan, ko Inuwa daya bana son hadawa dashi
Shuru Nadine tayi don kanta ya gama rikidewa tace  na taba shiga irin halin da kika shiga na tsabar wani abu lokaci guda lokacin ina kamar shekaru ki, saidai na tabbatar matsala ta da taki ba daya bace don bansan menene matsalarki ba
Nunfasawa tayi kafin tace  you need to be strong and believe in your self, kuka ba solution bane karshe Ma zai Kara maki ciwo ne don kuka ke tunzira mutun, ki gode ma Allah you have everything in life, baki rasa ci ba Baki rasa sha ba, you have a family you can turn to, kinada yayanki wanda ya dam& .
Da sauri amra data kura mata idanu bayan ta tsagaita kukan ta kalleta jin abunda ta fada, saurin kauda kanta tayi tace  how can I calm down bayan bana da kowa bana tare da family s nawa, banma san a wani hali suke ciki ba
Cikin mamakin kalamanta Nadine ta kalleta. Ta Kasa dago zancen amra din
 But ma am you have your brother, you can talk to him
Dago da jajayen idanunta tayi tace  he s not my brother, he s my& husband
Nan take Nadine ta dago zancen, tayi mamaki sosai, don bata taba tsammanin Akwai aure tsakaninsu ba, Toh indai mata da miji ne maisa babu alamun haka a tattare dasu ta tambayi kanta.
Nadine ta dade sosai a wajenta ba tare da ta tambayeta matsalarta ba ta bata shawarwari wanda ya sata jin sauqin zafi da ranta keyi mata harta samu tayi breakfast ta kwanta don kanta dake mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login