Showing 90001 words to 93000 words out of 381117 words

Chapter 31 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2002

fito, ganin plate number motar yasa shi juyawa ya danna remote control din gate din ya zuge da kanshi, tunda suka shiga tsakiyan compound din ta wangale bakinta don saita rantse ma ba a Nigeria take ba, daga waje ashe gidan ba komi bane saida aka shigo, parking driver yayi daidai inda motoci kusan guda uku suke a jere an rufe su da car cover, fitowa driver yayi da sauri ya bude booth ya fiddo da akawatinta kafin yayi saurin zagayowa ya bude mata kofar bayan, rarraba idanunwata ta soma yi kafin yace   welcome ma, 
Idanuwa kawai take zuba mashi don ta zama kamar kurma, babu abunda take buqata sai bayanin ina ne nan aka kawota, jagora yayi mata zuwa main entrance din gidan kafin ya danna door bell din, babu wani bata lokaci wata mata ta bude kofar tare da saurin yin baya tace   sannu da zuwa ma 
Saurin mikawa wanda tayi Magana akwatin drivern yayi kafin ya juya ya kama gabanshi, murmushi yake kawai amra tayi don komai y agama kulle mata,
  bismillah!!  matar ta fada yayinda ta shige da akwatinta ciki, da bismillah amra ta sanya kafafunta cikin gidan, don tsoron shigama take, tunda kan walk way ta soma yaba irin tsarin gidan, gidan ya kawatu da luxurious kayan alatu, ganin inda matar ta bi ya sanya ita bin hanyar ta, duk inda ta taka sai haske wajen ya bayyanu da alamu wutar gidan ma censor ne, cikin parlor ta sanya kafafunta wanda tana shiga wani irin sanyi da kamshi ya buget lokaci guda, fadin tsaruwan parlor kanshi bata lokaci ne don ya hadu ba kadan bag aba daya tsarin kasar waje ne a cikin gida, nuna mata wajen zama matar tayi kafin a tsorace ta dake ta zauna kan hadaddun kujeran kafin matar tace   ina wuni ma ya hanya  fuskanta dauke da murmushi   lpy alhamdullah thank you 
Juyawa matar tayi kafin ta mike wata hanya ta shige kitchen, fitowa tayi hannunta dauke da katon tray na kayan marmari da juice mai sanyi, tunda matar ta fuce amra bata dago ba harta dawo, duk ta gama takurewa, so take taga mutanen gidan saidai bataga kowa sai wannan matar dake kiranta da ma
Aje tray din matar tayi a gabanta kafin tace   bismillah ma 
Kallonta amra tayi tace   no thanks, dan allah ina mutanen gidan 
Shuru matar tayi don itama mamaki take da tambayar amra din don gaba daya kwananta daya a cikin gidan don hiring dinta akayi daga wani company dake kawo house keeper koda aka daukota bayanin da aka mata shine zata dunga kula da gidan har madam dinta ta karaso daga kasar waje,
  ma, ni kadaice a gidan, an daukoni ne don nayi house keeping gidan 
Kasa tantance maganar matar amra tayi saidai tayi shuru kawai, maganar matar ne ya katse mata tunanin data tsunduma a ciki

  kina buqatan wani abu ne ko zaki fara hutawa? 
  please ko zaki nunamin bathroom 
  okay ma 
Mikewa amra tayi ta fara bin matar har suka bi hanyar da zai sadaka da stairs, staircase dinma kanshi abun kallo ne, har wani curvy yayi gashi yasha carpet mai kyau, gidan is so cozy, bin bayar matar tayi har suka hau benen farko wanda keda dakuna biyu manya manya da parlor hanyar parlor sukabi kafin matar ta bude dakin dake facing parlor, tunda suka shiga ta soma raba idanuwa, dakin yasha kayan alatu, gado ne royal Turkish bed mai kyau yasha gyara da zanin gado wanda daga gani kasan na masu kudi ne, an jere dakin da pillows masu kyau, sai tsakiyan an kawata shi da carpet mai laushi gefe guda kuma wardrop din gadonne shima babba wanda ya shanye gabada wall din wajen, matsawa gefe matar tayi kafin tace   ga toilet nan ma  ta fada tare da nuna mata wata kofa daga gefe chan, shigewa amra tayi ciki kafin matar ta rufo mata kofar ta fuce, takowa amra tayi ta aje jakanta da wayanta akan gadon kafin ta soma nannade mayafin abayan dake jikinta don ji take kamar shaketa yake, hanyar bathroom din da matar ta nuna mata tabi, koda ta shiga nanma toilet din ya gaji da haduwa, saida ta fara rage mararta kafin ta dauro alwala ta fito don sai a lokacin ta tuna da sallolin da ake binta, futowa tayi lokacin matar ta bude kofar itama ta shugo hannunta duke da box din data aje mata a parlor, kauda kai gefe amra tayi kafin tace   thank you, please ina buqatan sallaya 
Da sauri matar tace   okay ma 
Takowa tayi ta bude slide wardrop din ta fiddo da sallaya katuwa ta ta shimfida mata, godiya amra tayi mata kafin ta fuce, mayafin abayrta ta dauka ta nade wuyanta dashi kafin ta tada sallah, koda ta idar ta dade sosai kan sallaya tana addua akan lamuranta, ciki kuwa harda general da bata san a wani hali yake ciki ba saidai tana jin zafi don duk wani hali yake ciki a yanxu itace ta jefashi, wannan kadai idan ta tuna yake sata kuka sosai, ta dade akan sallaya kafin ta miqe ta raqube a gefe guda ta zauna ta doka uban tagumi.
Tana nan ta janyo wayarta, tama rasa me zatayi sai hawaye, tana nan zaune akayi knocking kofar, dagowa tayi ta bada izini aka shigo, matar dazun ce sanye da uniform din aiki, ktakowa tayi kafin tadan rissina tace   me food is ready, ko akawo maki nan 
Shuru amra tayi don yanda matar dai a grime ta girmeta amma sai rissina mata take yasa taji babu dadi tace   nagode zan sauko naci 
Juyawa matar tayi ta rufe mata kofa kafar.
Koda ta kasa kanta ne ya rabu gida biyu don bata gane inane hanyar dining dinba, saida matar ta fito ta jagorance ta har dining din shima dai ba a Magana, zama tayi idanunta kan jerin warmers din, da sauri matar ta soma bude warmer din tace   wanne za ah saka ma 
Shuru amra tayi kafin ta dan dago fuskanta dauke da murmushi tace   zaki iya saka ko wane ma 
Murmushi itama matar tayi kafin ta zuba mata fried rice da tasha veggies da hanta sai shredded beef sauce a gefe, tana gama zuba mata ta aje mata spoon a gefe kafin ta janyo wani bowl din ta zuba mata green salad, tana gamawa ta janyo hadadden glass jug din da yasha apple juice ta zuba mata ta aje a gefe, kallon plate din amra tayi, abuncin yayi kya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????u a ido ga kamshin sa daya bade dining area din gaba daya saidai gaba daya damuwan dake cikin ranta yasa batada appetite gaba daya, dagowa tayi fuskanta dauke da murmushi tace   thank you so much 
Murmushi matar tayi matai tama don haka kawai taji amra ta shiga ranta sbd calmness dint aba kamar wasu madams din ba da kudi ke sasu jin kansu har suna wulaqanta wanda suke masu aiki,
  if you need anything ma, zaki iya kirana, sunana nadine 
Girgiza mata kai amra tayi kafin matar ta juya zuwa kitchen ita kuma ta maida chokalin cikin plate ta soma deba ahankali tana kaiwa bakinta,abuncin yayi dadi sosai saidai gaba daya tunda tayi loma daya biyu taji ta koshi, juice din kawai ta samu tasha don kishirwan da takeji sosai, tana gamawa ta dauki plate din tayi hanyar da matar tabi, tundaga bakin kofar shugowa kitchen din matar ta hangota, da sauri ta sakko daga kan kujeran da take zaune ta karaso gaban amra tace   ma dakin barshi zan kwashe 
  haba ba komai ay, nagode sosai 
Karba matar tayi kafin tace   ma kije ki hut azan kula da wannan, its my job 
Godiya amra ta sake mata kafin ta juya, sama ta wuce saida ta karema parlor kallo sosai, kafin ta wuce direct dakin nan, gefen gadon ta samu ta zauna ta doka uban tagumi, hawaye ne ya soma sulalewa a fuskanta, gaba daya hankalinta a tashe yake, tana nan zaune har barci ya kwashe ta akan gadon.
Bata farka ba sai wajen laasar, toilet din ta wuce tayi wanka kafn ta fito ta bude box dinta, wasu kayan ta chanza kafin ta shimfida sallaya ta soma sallah, anan zaune tana azkar aka turo kofan, karasowa Nadine tayi gabanta kafin tace   ga sako driver ya kawo 
Karban ledar amra tayi kafin ta mata godiya ta fita, mikewa tayi ta koma gefen gadon ta bude ledar, katin sim ne na mtn, da sauri ta bude ta janyo wayarta ta cire nata na saka sabon na mtn din dama tana tunanin yanda za ayi ta samu sim card don ta manta nata achan apartment dinta, tana kunnawa kuwa taga an loda kati da yawa a ciki na kusan 20k, rasa abinyi tayi, cikin call log dinta ta shiga last call din shi ne a logs dinta cikin wasi wasin rai ta rasa me zatayi runtse idanunta tayi Ta budesu kan special contact dinshi na Chan dubai, don last call dinta dashi ne, Saina haifa dake kasa, ba tare da tunanin komi ba ta danna call din, kwata kwata wayan ma baya shiga, ba karamin tashin hankali ta shiga ba don komai ya tsaya mata Chak, ganin contact din baya shiga yasa ta danna na haifa, saida tayi kusan ringing uku kafin a dauka, haifa kuwa tana zaune hankali a tashe tana neman line din amra don gaba daya headquarters ta burkice da zancenta da general, gashi taje Har apartment dinsu bata sameta ba shima kanshi general ba asan inda yake ba, Har haifa ta dawo gida hankalinta a tashe yake don rashin sanin inda kawar ta take ba karamin tada mata hankali yayi ba don ko wani irin hali ta shiga Harda ita don ita ta kawo mata shawaran yin AUREN KATIN KASA, tana zaune a daki babu irin lallabawan da ummi batayi mata ba akan ta kwantar da hankali ta saidai fur ko abinci ta kasa ci, ringing din wayanta ne ya sata janyo wayan dake gefenta ganin number da ba ta kasar ba yasa ta aje wayan gefe,Chan kuma dai jin ringing din yaqi karewa yasa ta janyo wayan tayi picking, murya amra ne ya daki kunnnenta  haiffff& it s me amra
Da sauri haifa ta mike zaune jikinta Har tawa yake tsabar murna da furgici a tare,
 Babe Ina kika shiga, kina lpy? Ina kike where are you calling from
Fashe wa da kuka amra tayi kafin ta soma magana cikin shesheka  haif na dawo Nigeria,ban samu damar kiranki ba sbd gaba daya jiya hankali na a tashe yake, babe please tell me what s going on over there

Shuru haifa tayi don tama rasa ta inda zata fara mata bayani,wayancewa ta soma yi
 Thank god tunda kin koma,gaskia I can t say taqamaiman abubuwan dake nan,
Saurin Tarar nunfashin ta amra tayi tace  haif just tell me, please, what s going on over there, an gano gaskia? How about him, how s he?,Haifa bazan taba yafe Ma kaina ba idan wani abu ya sameshi because of me
Tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka, mamaki ne karara a Fuskan haifa cikin taushi murya hade da lallami tace

 Calm down babu abinda zai faru, yanxu kome zai faru a cikin headquarters za ayi don ko government baza ta iya karban wannan case dinba balle kuma wasu officials din, yanxu abunda ya kamata ki fara damuwa dashi shine karatun ki,
Dakyar haifa ta lallabata kafin ta kwantar mata da hankalinta. Sukayi sallama ba tareda ta samu abunda take son ji ba daga wajen haifa din


Tana nan zaune international call ya shigo cikin wayanta cikin, da sauri ta dauka wayan ta kai kunnenta  hello ma am
Da farko bata dago wanda yake maganar ba Sai dataji yace  m5 speaking
Bata Ma tsaya amsa gaisuwanshi tace  dan Allah kamin bayanin meke faruwa, cikin harshen turanci ya soma mata bayani

 Ma am you need to calm down, you re safe now,
Shuru tayi jin ya taqaita maganar sa ta cewa  how about sir? Is he okay
 Yea ma am he s fine, he will join you shortly
Nunfasawa tayi kafin tace  can I speak with him please

Kamar bazai ce komai bai Chan kuma yace  he s not in a state of speaking
Hankalinta ne ya Tashi lokaci guda hawaye ya soma mata ambaliya a fuskanta tace  dan Allah ka fadamin meke faruwa, Ina ne nan aka kawoni

 Ma am zaki samu Ansan da kike buqata nan gaba, if you need anything you can call this line directly
Yana kaiwa na Ya kashe wayan, wani kukan ne ya sake kubce mata saida taji kanta na Sarawa kafin ta tsagaita kukan nata.
Kwanan ranar tayi shi ne a wahalce.

Bari mu leka bangaren general&
Kwanan sa biyu chiff anan interrogation room kafin Ana ukun aka bashi damar futowa, tunda ya fito aka wuce meeting room inda ka ganshi bazaka ce daga interrogation room ya fito ba don kamar ma hutu aka kaishi yayi ya fito, dogon zama akayi inda kamar yanda akayi zaman farko aka sake wani zaman,saida ya Sara masu kafin ya samu waje ya zauna kallon shi sukayi kafin suka soma magana  general Muhammad taura
 yes sir yayi saurin amsawa
 Ah binciken da mukayi mun gano auren da kayi is not illegal, aurenka is legal,your suspension has been called off you can now go back to your rank seat

Murmushi yayi da gefen bakin sa kafin ya dago ya kallensu yace  thank you sir

Mika mashi rigar rank dinshi akayi kafin ya fuce daga wajen meeting din, Kasa ya sauka kowa na harkar gabanshi Saidai bbu wanda ya sara mashi kamar yanda akeyi a da Saima Yan kuskus da akeyi, fucewa inda m5 ya yi parking yayi kafin ya bude mashi bayan motor ya shiga suka fuce daga cikin headquarters.

Dagowa yyi ya kalli m5 yace  weldone m5, you did a great job
 Thank you sir yayi saurin amsawa
 So what s the next plan now,

 Daga nan Zan wuce dakai gida gobe flight dinka zai Tashi by 10 na safe, kamar yanda mukayi planing yanxu kowa yana tunanin anyi suspending rank dinka, and I believe daman hakan sukeso, na Har hada duk wani arrangements tare da Nigerian army, sauran binciken daya rage saika je chan, anan kuma saika bada go ahead yanda za ayi.

Shuru yayi ya lumshe idanunshi yana son ya tambayi yanda take saidai kuma ya rasa ta yanda zai fara
 How s everything going over ther in Nigeria
Sanin abunda yake nufi yasa m5 cewa  everything is going according to our plan, madam is also safe sauke nauyayyan numfashi yyi tare da lumshe idanunshi yace
 Take me to the hospital..

Maida kanshi yyi kan kujran kamar mai yin bacci. Tunanin komai ya soma dawo mashi

Asalin abunda ke faruwa& ..
Akwai lokacin da yaje asibiti ganin likitan shi Har yayi clashing da hafiza dake bibiyarshi harta tura mashi anonymous message,da farko bai dauka abun serious ba saidai yasa m5 yayi bunciken su na sojoji. Tashin farko M5 ya nemo mashi Duk information din unknown number da farko dayagane itace Sai ya yanke shawarar ganin me zatayi, lokacin da ya gano tana da wanda suke aiki tare suna bibiyarshi shine lokacin da suka je mall shida amra wanda yayi hakan ne shima don Ya tabbatar da abunda yake zargi, nan take kuwa ya tabbatar da hakan, hafiza na aiki da Hammam wanda abun bai bashi mamaki ba kwatakwata saidai bai nuna alamun ya gane komai ba, lokacin daya fara suspecting Hammam kuwa shine tun bayan general din daya sauka wanda daga shi aka bama Amar, a lokacin ya fara bincike akan yanda Duk yawanci masu qwazon aiki anan headquarters suke barin aiki Ko kuma a sallamesu akan wani abu da sukayi achan baya su kuwa threatening dinsu da akeyi da weakness dinsu wanda suke da kawa zuci kuwa amincewa sukeyi da buqatun waenda an Kasa gano suwaye, yana kan gabar yin wannan bunciken Hammam ya kawo mashi batun yarjejeniyar auren amra wanda ya amince da hakan ne dukda aure baya cikin tsarinshi a wannan lokacin don yayi amfani da damarshi, abunda ya Kara tabbatar mashi da
cewa Hammam da hafiza suna aiki tare kuwa shine Akwai ranar da Hammam ya tambayi ko Pablo ya bashi takardar yarjejeniyar auren da sukayi, amar yayi mamakin tambayar da ya mashi saidai ya shaida mashi bazai iya tunawa ba koya bashi ko bai bashi ba, hakan yasa Hammam neman pablo don jin koya bama oganshi takardun, nan ya shaida mashi ya bashi su, tundaga lokacin Amar ya cigaba da kallo shi, daga lokacin amar ya tabbatar da abunda yake zargi na neman weakness dinshi da akeyi Ko kuma abunda zaisa ayi suspending dinshi idan yaqi amincewa da buqatun su.bayan wannan ma Akwai lokacin da yayi tafiya inda yayi kusan sati guda, da taimakon cctv Amar ya gane zuwan da Hammam ya dungayi a apartment dinshi harda abubuwan da Hammam ya yi a cikin bedroom dinshi wanda bai san da Akwai cctv a cikin bedroom dinba, na farko binciken laptop dinshi ya fara da yake yawan aje wa a daki, ganin ya Kasa samun komai don strong encrypted password ne a laptop din wanda yasan a headquarters ne kawai ake amfani da portal din kuma Duk yanda zaiyi bazai taba budewa ba hakan yasa ya soma duben duben takardun da yake aje wa cikin briefcase dinshi, nan ya samu copy din takardar yarjejeniyar aure.
Lokacin da Amar yaga recorded moments din daga files din cctv camera din baiyi mamaki ba saidai ya fara nashi plans din.
Kamar Amar yasan da ranar threatening dinshi zaizo hakan yasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login