Showing 39001 words to 42000 words out of 381117 words

Chapter 14 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2189

sanin bayason ana shiga harkarshi yasa tayi kamar bata ganshi ba ta cigaba da latsa wayan ta harya fuce abinshi.
?
Zaman ta tayi ita kadai, karshe ta kira haifa suka sha hira koda ta tambaye ta any update akan amar, kamar kullum ta shaida mata yana nan babu sauyi ita tsoronta ma kar yazo ya jawo ta rasa abinda take nema ta dalilinshi wanda duk sun kasa ganewa, haka ta karaci weekend din nata kunshe ita kadai, daga wanka sai sallah sai cin abinci da latsa waya.
?
Yauma tunda ya fucewanshi bai dawo ba sai wajen karfe goma, har yazo ya wuceta tana zaune kan sallaya tana lazimi, batako kalli inda yake ba, shima baibi ta kanta ba ya wuce ciki, saida yayi wanka ya chanza zuwa kaya masu laushi marasa nauyi kafin ya futo sitting room din, direct kitchen ya wuce saida ya dauka ruwa ah fridge sannan ya zauna kan kujeran dake table din kitchen island din yana fuskantar parlor, amra kuwa batama san yana wajen ba don hankalinta yayi nisa wajen latsa waya tun bayan ta nade sallayan nata tayi shirin bacci, yanxu tunda ta fuskanci lokacin futanshi da dawowanshi ta daina bari suna hada hanya dashi don bata son yanda yake treating dinta. Anatse ta miqe tana dariya ta aje wayan nata sannan ta tashi ta tube hijab din jikinta, duk wannan abin da take akan idonshi, ganin tana shirin daga riganta yasashi sauri kau da kanshi yayi gyaran murya, afurgice ta juyo ta kalleshi, harta daga doguwan rigan nata, santala santalan cinyoyinta sun bayyana, da sauri ta sauke rigar adaburce, don batayi tsammanin ganinshi a wajen ba gashi ya bata tsoro sosai, ahankali ta sauke kanta kasa tana shirin zama kan couch tajiyo muryarnshi   ke come here  & kunkune ta fara tana turo baki wanda duk hakan akan idonshi tayi batama san tana yiba, ahankali ta furta   shi wai sai ya dunga cemin ke kamar mara suna  duk wannan abin da take akan idonshi kuma ya gani sarai azaffafe yace  kina Magana ne?  & da sauri tataho ta tsaya dan nesa dashi sanan tace   ina wuni  & kallo daya ya mata sannan yace   sake abinda kikayi yanxun nan  ..dagowa tayi idonta zuru zuru akanshi tace   wallahi banyi komai ba fah  ..tsaki yayi sannan yace   shekarunki nawa  , ahankli bakinta ya furta   21  .. tsaki ya danyi aranshi yace   how can I even& mteww wannan idanma nace zan abun nan ay raini zai janyo min, no it s like a child abuse ma  & hade rai yayi kamar bazaiyi Magana ba yace   be sure you get ready by 10am tomorrow morning,I hate delays idan kika bata lokacin zanyi fucewata kuma babu ubanda ya isa ya sani na koma wajen karban application na abinda kike buqata, so be warned ?I don t repeat my self, and when ever I call you make-sure you distance your self from me understood  ..anatse kamar marainiya ta girgiza mashi kai, juyawa tayi zata tafi yace   ke na baki izinin tafiya ne  juyowa tayi anatse idonta na kawo kwalla a shagwabe tace   kayi hakuri  & tashi yayi fuu ya wuce ta gefenta.
Yana shiga daki ta lallaba ta wuce ta tube kayan jikinta ta sauya zuwa doguwan riga mai dogon hannu, saida ta saka alarm na karfe biyar sannan ta kwanta abinta.
?
Karfe biyar daidai wayanta yayi alarm dinta yayi kara, tana jin karar alarm din ta miqe zumbur, da sauri ta fara laluben hanya dukda bacci bai saketa ba, ahankali ta karasa gaban kofar saidata leka taganshi kwanshe kamar bai tashi ba, ahankali ta shiga tayi wankanta sannan ta dauro alwala, saida ta tabbatar ta wanke mashi toilet kafin ta futo, tana fitowa ta ganshi a zaune dukda dakin is dim, tana iya hango yanda ya dafe kanshi yana runtse ido, ahanakli kamar wanda batason Magana tace   good morning  & bai amsa ta ba yanda tayi tsammanin hakan ya miqe ya wuce toilet din, anatse yabi toilet din, ganin ribbom dinta agefen sink, ya jawo ribbom din kamar tsumma, tunawa da wani abun yasa kawai ya aje, ya wuce gaban basin ya janyo brush dinshi yayi brush ya dauro alwala ya futo,cikin wajen closet dinshi ya shiga ya jawo jallabiyanshi fara wadda kamshi ke tashi daga jikinta, ya shirya, sai yayi wani irin kyau, gashin bakinsa da suka cuko sosai ya shafa kafin ya fito ya shimfida sallaya a tsakiyan dakin ya tada kabbara, anatse yake sallah saida ya idar ya zauna yana azkar, ya dade hannunshi a sama yana rokon allah da ya shiga alamuranshi, ya dade sosai sai wajen 7 ya tashi, cire jallabiyan nashi yayi ya bar shorts sannan ya kwanta, wani irin bacci ne mai dadi ya fusgeshi, bangaren amra kuwa batayi baccin safiya ba, tun wajen 8 ta gama shirin ta don tana tsoron bata mashi lokaci hakan yasa ta shirya tun wajen 8 dukda tasan sai 10 yace zasu fitan, shiryawa tayi cikin abaya baqa mai shegen kyau, kana ganin rigar kasan mai shegen tsada ce, don duk tasha stones, anatse ta dan goga kwalli a idonta, da dan lip glosss, shafa kanta tayi wanda ya nannade sosai sbd rashin gyara dabai samu ba, jin babu ribbom din kanta yasa ta tsaya nazarin inda ta aje shi, tunawa da lokacin da take wanke mashi toilet yasa tayi saurin miqewa kamar zata je daki chan kuma wata zuciyar ta gargadeta, ahankali ta koma ta zauna jiran futowanshi kafin ta sulale taje ta dauko, don gashin nata yayi buzu buzu sosai daman ga yawa ga tsayi ga cika gashi coily, wayan ta ta jawo tana duba Instagram, time to time take duba lokaci, har wajen 10:20 shuru bai fito ba yasa ta miqe tsaye ta fara zaryar tsakanin kitchen da parlor, jin ana kokarin bude kofar dakin yasata saurin zama waje daya ta natsu kamar mai karbar karatu, kallo daya yayi mata yana gyara agogon shi na diamond rolex a hannunshi yace   go and get that you thrash out of my bathroom, I thought I warn you, the next time na kara gani belongings dinky a toilet dina zaki daina shiga  ..yana kaiwa nan ya wuce kitchen ya deba ruwa yasha yace,   na baki 10mins ki sakko, I repeat 10mins idan kika wuce  & kwafa yayi yasa kai ya fucewan shi.
Da sauri ta wuce dakinshi, tana shiga ta fada toilet ta dauko ribbon dinta, yanda ta barshi haka ta dauko shi, da sauri ta futo gudun karta wuce lokacin daya bata, saida ta tsaya ta tamke gashin nata da kyar kafin ta daureshi tam ta yafa gyalan, tana gamawa ta jawo wayanta ta saka takalmin ta ta futo, ahankali ta dannan lift din apartment din, ganin yana 10th floor yasa taga bazata iya jira ba don kusan minti biyu ya rage mata, da sauri ta wuce stairs, haka ta sakko daga 7th floor zuwa last floor, ga haki ga gumi daya fara tsatsafo mata wanda ya kwantar da edges din gaban gashinta, tana futowa gaban compound din wajen ta daburce don motocine da yawa pake a wajen, karar horn da taji yasa tayi saurin kallon wajen da take jin sound din, da sauri ta karasa wajen hadaddiyar motar shi lambor, saida ta tsaya dab da motar ta fara nazarin yanda zatayi, shin ta shiga baya kota zauna agaba, jin ya kara danna horn yasa tayi saurin bude gaban motor kanta a kasa, ta shige ciki muryarta kasa kasa tace   salam alaykum  kamar yanda tayi tsammanin bazai kulata bahakan ce ta kasance, da sauri ta sunkuyar da kanta ta rufe kofar,   alayk salam  ya fada chan kasan makoshinsa, shima don sallamar musulunci ce shiyasa ya amsa sbd shi Magana ma bata cika damushi ba, fusgar motar yayi suka fuce daga compound din suka kama hanya, karatun alqurani da yake sauraro ya kunna muryar sudais ce kawai ke tashi sai sanyin ac, hankalinshi kuwa yana kan tuqin da yake, yayi wani irin kyau sosai kamar ka sace shi ka gudu, kallon shi tayi ta wutsiyar ido, tana son tambayar shi inda zasuje amma kuma tana jin tsoron sa sosai karya fada mata Magana ko kuma yayi banza da ita. Da sauri ta kame kanta ta kalli window tana appreciating view din kasar, don inda yake tafiar ma bata taba bin hanyar ba.
Adaidai wani babban building inda aka rubuta UAE NATIONALITY CITIZENSHIP suka tsaya saida yayi parking ya kashe moton kafin ya lumshe kyawawan idanunshi kamar bazaiyi Magana ba saida ya dauka wajen minti goma kafin ya soma Magana anatse   you know what to do, and mind you bana son kaudi, muna zuwa duk abinda na fada kice yes kawai, and behave banason shirirtar yara  ..yana kaiwa karshe ya mata kallo daya ya kauda kanshi& .amra kuwa wadda kamar ya watsa mata garwashi haka ta tsaya kyam, daurewa kawai tayi don har ta fara jin saukar hawaye masu dumi daga fuskarta, ganin ya bude kofa yasa tayi saurin budewa ta fara takowa anatse tazo dan nesa dashi, saida ya danyi gaba kafin ta buyo bayanshi anatse, yanda yake tafiya da yanda take binshi kamar bazasu taka kasa ba, jin alamun kamar ana binsu abaya kuma ana kallonsu yasa tayi saurin juyowa, ahankali idanunta ya sauka akan wata mota wadda ana ganin ta juyo aka zuge glass din motor,..jin sautin gyaran muryanshi yasa ta saurin juyowa, wani irin kallo ya mata tayi saurin kauda kanta ta biyo bayanshi, saida sukazo dab da shiga wajen ya dan tsaya wanda bata ma san ya tsaya ba tadan bugi bayanshi da kanta, juyowa yayi kadan kamar bazai motsaba chan kuma kawai ya sanya hannunshi anatse ya kamo nata, da sauri ta daga kai tana kallonshi daidai shikuma yasa kai ya shige cikin babban building din, sauke kanta tayi kasa don yanda takejin hannunshi cikin nata dumin hannunshi na ratsa ta, shima dai saida yaji wani abu don zai iya cewa wannan ne first time daya taba rike hannun mace da sanin shi bawai an sashi ba, anatse suka shiga wajen duk wanda ya gansu sai sun bashi sha awa gwanin burgewa, da an kallesu sai an sake don sun dace sosai.
Cikin wani office suka shiga, suna shiga kamar bashine mai daure fuska ba cikin faran faran ya gaisa da mutumin dake zauna kan kujera, wani farin balarabe ne sanye da jellabiya, waje ya nuna masu suka zauna, anatse amra ta gaishe da mutumin cikin harshe larabci, sannan ta sunkuyar da kanta.
Magana sukayi mai tsayi tsakanin amar da mutumin kafin mutumin ya futa. Juyowa yayi ya mata kallo daya sannan ya kauda kai ya fara latsa wayanshi ganin yanda ta rakube waje daya kamar bazaiyi Magana ba chan kuma yace   zai kawo application form yanxu zakiyi signing application  ..anatse ta dago kanta wanda yake sara mata sosai don duk wani motsinshi har cikin ranta takejin hakan gudun kar tayi wani laifin yasa tayi saurin cewa   tohm  ..mintuna kadan saiga balarabe ya dawo, kallon amar yayi sannan yace   kunyi shuru kaida matar taka kamar bakwason Magana, jin haka yasa amar tunawa da wani abun, murmushi kawai yayi baima bama mutumin ansa baya juyo ya kalleta yace   Haa..bib..ty.. are you still not feelin okay  ..da dabara yayi mata tambayan Yana kamo hannunta cikin sigar lallashi, yayi hakan ne don tunawa da inda suke, jin sautin muryarshi da lausassan hannunshi cikin nata yasata saurin dago kanta ta kalleshi fuskanta dauke da mamaki hannunta har yana karkarwa, shima kallonta yake, anatse ya sauke wani dan guntun murmushi yana mata alamu da ido akan tayi abinda yace tayi dazu a mota, tunawa da abinda ya fada akan duk abinda yace tace yes yasata saurin cewa   yess ha..bi..bi  in a slow and shagwaba tone din da batama san tayi ba.
Kallonsu mutumin yayi sannan yayi gyaran murya yace   lets begin with the application  ..har suka gama rubuce rubuce hannunshi na cikin nata, yana jin yanda hannunta ke fidda wani ni imantaccen zufa da dumi, suna gama application din mutumin ya mike shima ya miqe tsaye sukayi musabaha. Ganin ya miqe da hannunta yasa ta miqe itama kanta a kasa, ahankali yake takawa tana biye dashi har suka futo daga wajen, saida ya tsaya gaban motar shi kafin yayi saurin cire hannun shi daga daga, itama batayi gigin dagowa don kallonshi ba ta sauke kanta kasa tana wasa da yatsun ta, tsaki yayi sannan ya bude motar ya shiga, ganin haka yasa itama ta zagaya ta shiga ta zauna, anatse ya tada motar suka fice daga wajen, koda suka fito motar dazu ta kuma gani, da yanda aka zuge glass din motar, bata kawo komai a rantaba ta kawar da zancen.
?
Da sauri hafiza ta sauke glass din gaban motar sannan ta cire bakin glasses din data saka hade da facemask, dagowa tayi tabi motar su data wuceta da kallo tace   ni hafiza nayi ma kaina wannan alqawarin saina tarwatsa farin cikin ka, duk yanda za ayi saina kuntata maka, ta hanyar zama ni kadai acikin rayuwarka wannan alqawari ne na dauka ma kaina idan har ina nunfashi. Wayen ta ta jawo wadda ta aje gefen kujerar gaba tayi dialing wasu numbers sannan ta sanya wayan a kunnenta tace   black, I need you to do some research on someone for me, I need something very big to use against him, he s a powerful man I cant compate with him so I need hands please   , saida tayi doguwar waya da mutumin bayan ta bashi information data sani game da amar kafin ta kashe wayan ta fuce daga harabar wajen gaba daya. 77-78
A daidai penthouse dinshi ya tsaya, ahankali gate din ya fara budewa, kwalalo idanu amra tayi ganin ikon allah, don ita duk a tunaninta gida zasu wuce, har gaban compound din dake facing parking space ya tsaya inda motocinsa ke parke wajen kala bakwai, dukkansu sai sheki suke yi da alamu an dauko su daga car wash ne, yana kashe moton ya futo ya bude motan ya sa kai ya fuce, bai ko kalleta ba itama batayi yunkurin yi mashi Magana ba, anatse ta juyo ta kalli bayanshi har ya bace mata, ahankali ta sauke wata nauyayyi ajiyar zuciya, sai a lokacin ta dan samu sarara ta kunce rolling din datayi don ya dameta ,yafa gyalen tayi akanta kawai yanda bazai dameta ba.
Tunda ya shiga ciki ya jawo laptop dinshi don yana jiran message daga wani anonymous mutumin da ya saka yayi mashi thorough private investigation, inda shi mutumin ya shiga cikin mutanen da wata kungiya sukayi abducting dinshi bada sanin su kan cewa shi dan leken asiri ne ba, kusan shekara guda yana hannunsu, yau kusan kwana biyu tun bayan lokacin da aka kamashi sai yanxu Kenan suke communicating dukda cikin sirri ya samu ya sato wayan daya daga cikin masu aikin kula da abducted mutanen wajen kafin a sayar dasu, yasha wahala sosai kafin ya samu amar, shiko amar duk yanda zaiyi yayi tracing mutumin ya kasa, gashi mutumin ya nuna mashi he s in danger and ya rasa yanda zaiyi and yace mashi karya fadama kowa don acikin sojoji akwai head tip din mutanen da sukayi abducting dinsu, yanxu yana son sanin yanda zaiyi ya gano su waye sukayi abducting mutumin don ya samu ya taimake sa kuma tunda yaji cewa cikin manya manyan sojoji akwai wanda yake aiki dasu yasa ya kasa samun sukuni, duk wannan abun da yake babu wanda yasan yayi wannan research din don this time around kozai dauka shekara yana aiki saiya cin masu. Tsayawa yayi ya zubama message din mutumin da yayo mashiin reverse way kamar haka  ?pleh em sti skm eripme..ganin ya kasa gane me rubutun ke nufi kuma this is the first time ya mashi rubutu haka yasa shi tsayawa yana nazari, na farko dai abubuwan daya rubuta basuyi making sense ba. Aiki tukuru ya fara saida ya dauke kusan awa uku idanunshi nakan system, ganin komai ya hau kanshi ya sashi saurin cillar da laptop din allah yaso akan gado yake da a zaune yake kan couch da tabbas saidai ya saya sabuwar laptop, bugun kanshi ya soma yi azafafe yace   noooo noo I need to know, I have to get something out of this, ganin jinin ji na boiling ya sashi saurin fara karanto addu oi har ya samu komai ya fara lafawa zuciyar shi ta fara sassautawa anatse ya sake bude message din, ahankali yake bin daya bayan dayan words din kamar idanunshi zasu fado yake kallon message yana nazari, futa yayi gaba daya daga message din ya shiga cikin wani private portal da encrypted security, wani uban dogon step yabi da wasu code kafin ya shiga, anatse yake bin duk wani information dayake gathering, da duk wani hindering dirty work na manya manya na kasar,da saurin yayi inputing information din yaron nan da duk wani communication da yayi dashi, idanunshi ne ya sauka kan word din mks empire, cikin hanzari ya futa ya koma message din yana dubawa daya bayan daya, wani uban ihu ya doka yace   yesssssssss got it, its mks empire  ,..anatse yayi arranging words din harya gama rubutawa yace ?  wallahi I promise my self who ever is behind this wallah I will make sure they suffer  ..tunawa da dada shi yayi inda yake ce mashi   amar son, kasan irin zaman da zakayi da mutane don t use anyone for your benefit but gain power, open your eyes, I feel betrayed, I feel so sad, but I can t tell you about it  & da sauri ya runtse idanunshi yana komawa cikin private portal din, a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login