Showing 231001 words to 234000 words out of 381117 words

Chapter 78 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2015

bismillah  bin bakinta yayi da kallo don muryanta bai futo ba sai motsin bakinta,kafin ya sauke idanunshi zuwa hannun nata dake dauke da juice din, dagowa ya sakeyi for the second time ya daga mata gira daya alamun menene?, tana ganin haka ta sake motsa bakinta   juice 
Wayarshi ya cigaba da m5 don dashi yake wayan tun kafin ta shugo inda suke Magana akan ayyukan da suke kan desk dinshi idan ya koma sai kuma report din da yake bashi kullum akan abubwan dake gudana acahn.

Kallonta ya sakeyi har lokacin tana rike da juice din ta dago shi tana miqa mashi, gaba daya ta gama gajiya da tsayuwan dukda ko minti biyar batayi ba, kanta a kasa tana tunanin kodai ta ajiye mashi ne ta tafi, idan y agama wayan saiya dauka,
Da sauri ta dago idanunta jin hannunshi kan nata, ya dago hannun nata yakai cup din zuwa bakinshi, saida ya danyi sipping kafin ya ire cup din da hannun nata, zuba mashi idanunta tayi tana ganin sabon salo daga wajenshi, bata gama tunani ba ya sake daga hannun nata da cup din yakai bakinshi ya sake sha for the second time yana lumshe idanu at the same time yana amsa m5 cikin harshen turaenci, samun kanta tayi da kallonshi da bakinshi dan yanda yake Magana kamar wata mace a gayance babu hayani cikin kamewa, dan jefi jefi shima yake maido da idanunshi kanta har ya shanye juice din tass, dukda bayan y agama sha dinma bai saki hannunta ba ya rike gam har saida y agama wayar.

A wannan lokacin already ta gama galabaita da tsayuwar, kafarta tayi tsami sosai tadan kumburo, cute feet dinta yayi bul kamar ka bula jinni ya futo, sauke wayar yayi daga kunnenshi ya maido da kallonshi gareta, kamar bazaiyi Magana ba chan kuma yace   meysa kike yawo babu cover? 
Da mamaki ta dago tana kallonshi kafin ta shafa kanta da dayan hannunta don dayan har lokacin yana rike dashi hade da glass cup din.
Muryanta baya futa sosai ta soma Magana   na mantashi a parlor ne 
  dazu ban ganki dashi ba?  ya sake tambayrta
  na manta ne, kaina ke itching shiyasa   ta sake bashi amsa a natse kanta a kasa don kwata kwata bata son hayaniya yanxu.
  meysa yake itching  ya sake tambayarta yana matso da fuskanshi wajen gashinta don yana iya hango tsakiyan kanta, san sana gashin yayi, babu abunda gashin keyi sai kamshin haddadun oils dinta wanda yasashi saurin runtse idanunshi ya saki hannunta ya dora hannunshi kan gashin nata ya fara shafwa ahankali,   uhmmmmm? Meysa yake itching? 
Ya sake fada yana kokarin shige mata, da sauri ta danyi baya kadan har tana kaiwa dab da bangon dakin nashi   ya cika ne da yawa  tana kaiwa nan ta juya zata fuce daga dakin, cikin sauri ya riko hannunta   ay ban sallameki ba malama 
Juyowa ta danyi kamar zatayi kuka,   dan allah ka barni na tafi, kafana yana min ciwo kuma inajin jiri 
Duban kafar nata yayi ganin yanda ta dan kumburo kafin ya maida idanunshi kanta   meysa kafan naki ke ciwo? 
  ba komai, tsayuwan da nayi ne?  ta bashi amsa
  tsayuwa yana saka ciwon kafa ne harda kumburi?  ya sake jeho mata tambaya babu wasa a fuskanshi
Ganin tayi shuru ta daburce yasa ya saki hannunta ya koma baking ado ya ajiye wayanshi, ba tareda ya kalleta bay ace   wanke min bathroom dina 
Da sauri ta dan dago ta zuba mashi ido, kafin ta sauke, ta fara takowa zuwa bathroom din nashi, ta gabanshi ta wuce ciki ta rufo bathroom din, gaba daya bata da wani kuzarin wankin toilet ammah haka ta fara wanke mashi, tana yi tana zama tana hutawa, toilet dima baiyi komai ba babu datti ko digo amma don tsabar neman Magana ya sata wankewa, tana cikin wankewa bata dauraye ba ta zauna agefen bath tana hutawa.

Cikin daki kuwa bayan shiganta bathroom ya kasa sukuni, don baiso ya sata wani wanke toilet ba kawai bayason ta fita ne yanxu, he just feel like dama ya ta zauna yayi ta kallonta yaan teasing dinta, wani iri yake ji game da ita sosai wanda yana jin yanason kasancewa da ita koda yaushe, dukda tana ciikin dakin nashi kasa sukuni yayi yana mai jin haushin kansa yanda yake acting.

Cikin sauri ya mike ya daidaita natsuwarshi ya shige bathroom din, yana shiga ta dawo idanunta da suka danyi jaa sosai, tana ganinshi tsaye tayi saurin miqewa da kyar, kaffunta sun fi da kumbura,   sorry yanxu zan gama  ta fada tana janyo shower don ta dauraye bathroom din, taku daya biyu tayi kafarta tayi gaba dayar kuma tayi baya, saura kiris ta fadi don tama saddakar faduwa zatayi, da wani irin sauri yayi taku biyu ya cimmata gaba daya suka fadi ita ta fado jikinshi while shi kuma ya fadi a kasan,   washhh allah na ciki na 
Ta dan furta ahankali, damamaki ya dago ya kalli fuskata, shida ya fadi akan tiles din wajen baice wash ba sai ita data fadi akanshi, samun kanshi yayi da cewa   are you okay? Kin buge ne? 
Saida yayi Magana ta luar a ajikinshi ta fado don haka tayi saurin kokarin janye tana sauke ajiyar zuciya don gabanta faduwa ya dungayi sosai don inda ta fadi ba karamin muguwar faduwa zatayi ba, babu abunda ya fado mata aria lokacin sai cikinta, da sauri ta shafa cikin nata tana hamdala kan kace me sai hawaye sharr afuskanta, kallon mamaki yake mata, don duk a tunanin ko ta fadi taji ciwo ne kafin ya taro ta saida tunawa da a jikinsh ta fado ya tabbatar ma da kanshi cewa bata fadin ba,   heyy heyy whats wrong? Are you okay  ya fada adaburce, don lokaci guda yaji kukan nata ya sakar mashi da jiki tausayinta ya baibaye shi, ay tana jin haaka ta sake fashe mashi da kuka tana kankameshi donta tsorata sosai, saurin rungumeta yayi hankalinshi adan tashe har hannunshi na danyin karkarwa ya soma shafa bayanta, mai ciki dai da shagwaba haka nan taji kawai bari tayi ta yin kukan, don sun dauka kusan minti goma ana abu daya, dago da fuskanta yayi jin ta rage kukan ya sake tambayarta fuskanshi dauke da damuwa dukda baisan ma yanayi ba   are you okay?whats wrong with you 
Turo mashi bakinta tayi tace   babu komi, na dauka zan fadi ne kua ina tsoron kar bab&   saurin guntse maganar dataso yi tayi don saura kiris tace baby, shiko zuba mata idanu yayi yana sauraronta,.

Saurin zame jikinta tayi daga nashi ta mike da kyar   bari na kaarsa wankewa 
  no ki barshi  yayi saurin katseta
  ah ah bari nayi ay na kusa gamawa  .. sake katseta shima yayi bayan ya mike   I said noo, bana son gardama 
Yana kaiwa nan ya fuce daga bathroom din, yana fita itama ta futo ta dauki glass cup din data ajiye a gefe ta juya ta nufi hanyar futa ba tareda ta sake kallonshi ba.
Tana futa ya sauke wata nauyayya ajiyar zuciya, yana mamakin yanda heart dinshi ke racing sosai anan zaune don ba karamin tashin hankali ay shiga ba lokacin datakusa faduwa da yanda ta soma mashi kukan shagwaba don har cikin kwanyar kanshi yake jinta.

Tana futa ta wuce bedroom dinta ta dauro alwala don an kira sallar magrib.
Tana idar da sallah salima ta shugo dakin nata, daga chan nesa ta tsaya   adda ki sauko muyi dinner inji ammah 
Dagowa amra tayi ta kalleta don tana shirin futa daga dakin   salima!! 
Ta kirata, juyowa salima tayi ta tsaya daga nesan don tun ranar da tace mata ta daina matsowa kusa bata son turarenta ta daina zuwa inda take.
  zo mana ya kika tsaya daga bakin kofa 
Zaro idanu salima ta danyi   inzo? Adda keda kikace na daina zuwa kusa dake bakyason kamshina dukda na daina saka turaren? 
Wani iri amra taji don bata ma san ta koreta ba harga allah duk sharrin tsirfan ciki ne,   sorry sweet sis, yi hakuri ki karaso, wallahi tsokanarki nake 
Tabe baki salima ta danyi ta kaarso har inda take zaune bakin gadon   uhm, ay ni adda lamarinki tsoro yake bani, kuma wallahi nasan akwa abunda kike boyemin bakyason na sani 
Hannunt amra ta rike ta marairaice   haba baby sis, yada fushi haka?,  
  eh mana dole nayi fushi ay, ni sometime inajin kamar bakyasona yanda kike sona ada 
Saurin toseh bakinta amra tayi   haba salima ki daina fadin haka, bani da waddda ta wuceki a matsayin yar uwa ta jinni 
  toh ki fada min meke damunki?, meysa kika sauya ba kamar da ba  salima ta tambayeta tana kureta da idanu
  zan fada maki amma ba yanxu ba kinji but wallahi I promise zan fada maki soon 
Rankwafar dakai salima tayi kafin ta danyi mata murmushi   toh shiknan muje muyi dinner kowa na zaune banda mu 
Mikewa amra tayi ta janyo dankwalin atamfar jikinta ta daura akanta kafin su fuce daga dakin, salima nag aba tana biye da ita don ahankali take tafiya don ammah na nanata mata lura da steps dinta musamman idan zata hau ko zata sauko daga stairs,

Da sallama suka shigo dining din, kowa na zazzaune, ammah amar aman da salim, dukkansu harsun fara cin abunci,   sannu daughter bismillah, salima zuba mata tuwo taci 
Zama gefen shi tayi inda ammah tayi mata nuni da idanu tayi kafin salima ta soma zuba mata tuwo,   adda wani miyan zan saka maki? Kuka ko egusi? 
  kuka  ta amsata kai tsaye don bata jin zataci wani egusi, amar dai bai dagoba tun da ta shigo dining din hankalinshi na kan abuncin da yakeci, hes trying so had to control and maintain himself.

Anatse kowa kecin abunci sai karar cokali, amra dai tunda ta fara da cokali taga kamar baya shiga tayi saurin ajiyewa ta wuce kitchen ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara loma, duk motsinta akan idanunshi harta wuce kitchen ta dago, saidai bai yarda sun hada idanu ba sabod idonta na affecting dinshi sosai yanxu, dan wani duk yanda ta lumshe su sai tsikar jikinshi ta tashi.
Suna gama cin dinner suka dawo parlor kowa ya baje ana hira banda amra da amanr da sukayi tsit sua zaune opposite din juna ita hankalinta nakan tv ma tana shan agwaluma idan anyi Magana takan dan jefa bakinta a cikin hira while shi kuma idanunshi nakan wayarsa saidai duk hirar da sukeyi yanaji and time to time yakan dan dago ya kalleta.

Salima ce ta maido dashi daga tunanin daya fada   ya muhammd gobe zamu gama exam fa kuma ranar Tuesday zamuyi graduation
Dan dagowa yayi ya kalleta   masha allah allah yasa asamu result mai kyau, and congratulation, wani gift kikeso 
Gyara zama tayi don a kasa take zaune ta tankwashe kafa   ya Muhammad digital drawing book nake so 
Da sauri amra ta dago ta kalleta tana mamaki kafin ta jefa mata harara,   shine baki fada min graduation din ba?
  toh ay adda kullum kina daki, idan nazo dakinki ma korata kikeyi shiyasa ni nama manta ban fada maki ba 
  ay shikenan saikije grad din naki ke kadai  amra ta fada ranta adan baci

Kallonsu ammah tayi tace   ayi hakuri yaya babba, mantawa tayi 
Sauke kai amra tayi tace   toh shikenan ammah, 
Kallon salima ta sakeyi ta gallo mata wata hararar   saboda ammah kawai na hakura 
Amar ne yadanyi gyaran murya, salima najin haka tace   sorry yaya, adda ta kaste mu, digital drawing board nake so 
  okay  ya amsa ta kai tsaye yana latsa wayarshi
Cikin murna salima tace   ammah ki tayani godiya thank you yaya 
  allah ya saka da alkairi  ammah ta fada tana kallon, kowa amsawa yayi da ameen,
  toh yarinyar kirki ni me kikeso na baki?  ammah ta tambayeta tana kallonta,
Hannu salima ta saka akan habarta tana nazari, amra dai bat ace komai ba tana sauraronsu aranta tana cewa   oh su salima an samu waje 

  ammah, basai kin bani komai ba, kawai inason ki kasance a wajen idan akazo bani certificate dina  salima ta fada tana murmushi
  toh shikenan dear sai kuma me kikeso?  ammah ta sake tambayarta yayin da take shafa kan salim daya kwantar da kanshi kan cinyarta   babu komi ammah na, wannan ma ya wadatar 
Dariya duk suka danyi, kafin a kalli aman,   toh su yaya aman me bazama a tambayi me za a bani ba 
Hararar ta ya danyi kafin yace   anqi tambaya din, 
Dariya duk sukayi gaba daya harda amra don inkaga yanda suke kamar wasu tom and jerry kwata kwata girmanshi faduwa yake idan har suna magana da salima.
Karfe goma daidai kowa ya fara waste wa, amar ne yafara mikewa,   ammah ina son coffee  ya fada baima tsaya sauraron response dint aba ya wuce bedroom dinshi, bayan tafiyarshi aman yayi masu sallama shima ya wuce kafin amra ta mike itama tana hamma,   ammah saida safe na fara jin barci 
Kallonta ammah tayi kafin tace    ki fara kai mashi coffee din saiki kwanta daughte 
  tohm ammah  ta fada kanta a kasa don kwata kwata bataso zuwa part dinshi ba don wani irin barci takeji sosai.
Sama ta fara wucewa ta watsa ruwa a gaggauce ta sauya kaya zuwa doguwar rigar bacci cotton wadda ta dan sauko mata har kasa don ta gifta gwaiwarta, sai yar hula data saka same color da rigar.
Tana gama shiryawa ta sauko kasa direct zuwa kitchen.

Kitchen ta wuce ta hada mashi lafiyayyan instant coffee sai kamshi ke tashi ta zuba mashi a cup ta futo daga cikin kitchen din, lokacin data futo duk sun wauce sama har ammah ta rage hasken parlor don haka kai tsaye ta wuce part dinshi, da sallama ta shige cikin bedroom dinshi kai tsaye bayan tayi knocking daya.
Tana shiga ta rufo kofar kafin ta juyo, a zaune yake kan gado ya rufe kafafunshi da duvet sai laptop kan cinyanshi yana typing cikin kwarewa sanye yake da pjs dinshi milk color, takowa tayi ta karaso inda yake zaune ta ajiye mashi gefen bedside   ga coffee din 
Bai kalleta bay ace   thanks  yana typing.
Juyawa tayi zata fita ya katseta   come back here  
Ya fada in a commanding way babu wasa, wanda yasa gabanta dan faduwa ta dawo ta tsaya dan nesa dashi   gani 
Banza yayi mata ya cigaba da aikinshi, saida ya dauka kusan minti goma yana aiki, ganin haka yasa ta zamu waje gefen gado ta zauna kusa da kafashi, saboda kafanta da baya juran tsayuwa.
Saida ya shafe awa guda yana aiki yana shan coffee harya gama kafin ya rufe laptop din, sai a lokacin ma yaji nauyi akan kafafunshi ashe hartayi barci abunta ba tare da snainta ba, ajiye laptop din yayi ya janye kafafunshi ya sauke su kasa ya mike tsaye, bathroom ya shige cikin mintuna kalilan saigashi ya futo, direct gaban switch ya wuce ya rage haske kafin ya kaarso bakin gado ya rankwafo ya gyara mata kwanciyanta gefe kafin shima ya kwanta dayan gefen ya lulluba masu duvet bayan ya masu addua& .Update
Unedited
Ammah ne ta dago ta kalleta Ganin ta takure waje daya  daughter jeki huta
 Tohm ammah ta fada a tsanake, kallon inda asad yake tayi tace  saida safe mun gode da ziyara 
 Ba komai nike da godiya ya amsa ta Har lokaci idanunshi na kanta, Amar dai kasa dauke idanunshi yayi akanta, haka kawai yaji bayason ganinta tsaye a wajen saboda yanda Asad ke kallonta,ya kasa dauke idanunshi har ta wuce sama.
Tana hawa sama ya sauke wata ijiyar zuciya dayasa Ammah dake gefen shi ta kalleshi, murmushi kawai tayi ta kauda kanta gefe.
Mikewa asad yayi ya ajiye bundle din naira note guda biyu a kan kujeran daya tashi kafin ya kalli inda salima ke zaune yace  kanwata thanks for the drink,ga wannan ba yawa a saya eyeshadow
Ya karashe yana mata murmushi, kallonshi tayi itama fuskanta dauke da murmushi tace  thank you uncle
Sallama yayi ma ammah, kafin ya kalli inda Aman yake ya miqa mashi hannu, Amar na Ganin haka ya miqe tsaye suka fuce atare, Har gaban motarshi ya rakoshi, suna karasowa asad ya miqa mashi hannu yana murmushi  congratulations oga, ashe itace madam
Dan murmushin da bai kai zuci ba yayi tare da saurin basarwa cewa  thanks for the visit, Allah ya bar zumunci
 Ameen oga yana kaiwa nan ya mashi sallama ya shige motarshi.

Bayan fitarsu salima ta miqe ta kwashe juice da cups din da baqon yasha ta wuce kitchen dashi, tana wucewa Aman ya miqe ya bi bayanta.
A tsaye ya taddata tana kokarin wanke cup din, tana gama wa ta juyo  wayyo Allah na ya fada da dan karfi saboda bataji shugowanshi ba kwata kwata,  ka bani tsoro yaya
Hannunshi ya nade a kirjinshi ya matso kusa da ita  meysa kike ma wanchan gardin murmushi?, bakisan murmushinki nawa ne ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login