Showing 78001 words to 81000 words out of 381117 words

Chapter 27 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2019

ko kuwa dai dama c han akwai muguwar kiyayya a bayan fage wanda babu wanda ya sani, kananun shekarunta basu hanata tuna lokacin da abban su ya rasu ba da jinyar da salim yayi a lokacin da irin kwayoyin da uncle ke kawo mashi yana sha kusan kullum, guda daya kuma a daidai karfe uku na dare haka ya umarcesu da su dunga tashi a bacci suna bashi yana sha, toh amma meysa?, whyyy? Wani irin kukan baqin ciki ne ya zubo mata akan fuskanta, muryar ya Muhammad ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da take   salima meysa kike kuka? Kinada masaniya akan wannan abin ne?  shuru ta danyi kafin ta share hawayenta tace   ba komi yaya kawai ina tausayinsa ne, nidai a iya sanina salim baya futa ko ina lokacin da muke zuwa school ma tare muke koda yaushe break ne ke raba mu  ..shuru ya danyi yana wani nazari kafin ya kalli doctor yace   doc yanxu wani mataki yake, I mean a wani stake yake yanxu,  kallon file din doctor yayi kafin ya soma Magana   well mr Muhammad all we have to do now is to thank allah, don yaron nan yana da kaifin zuciya, kasan zuciya ma saida kwakwalwa take aiki, ban taba ganin case irin wannan ba, yanxu zan bashi magunguna, yana buqatan hutu sosai, by tomorrow ma zamu iya sallaman su gaba daya  ,& godiya Muhammad ya mashi suka fuce tare, sai bayan magrib ya dawo cikin dakin nasu, akan sallaya ya tadda salima wanda tayi zuru zuru gaba daya bata cikin nutsuwa tunda taji za a sallame su yanxu haka zasu koma cikin wannan uqubar rayuwa qila ma mutuwa zasu, harya shugo ya zauna tana chan luntum cikin tunani saida yayi gyaran murya kafin ya kalleta yace   goe za a sallame ku, zan maidaku gida domin zan wuce Jordan a goben in sha allah, zan bai karaman waya duk abindakuke buqata zan dinga kiranku saiku fada min  ..shuru ta danyi kafin ta dago jajayen idanuwanta tace   yaya dan allah ina neman alfarma, ka kaimu katsina wajen kaka,inaga zaifi mana kwanciyan hankali  ..shuru ya danyi kafin ya nunfasa ya fuskanceta yace   kodai akwai wani abun ne daya kamata na nasani baki fada ba  ..da sauri ta girgiza mashi kanta tace   ah ah yaya babu komai kawai gwara muje chan muyi hutu saimu dawo  ..baya son takura masu hakan yasa yace okay ba damuwa ki tattara abubuwan amfaninku zansa driver ya kaiku gobe amma inason ku fara zuwa gida tukunna ku diba abubuwan buqatanku daganan driver saiya kaiku, shuru ta danyi kafin tace   tohh yaya allah ya kaimu  , bai wani jima ba sukayi sallama ya fuce daga dakin, sai ya tsaya reception domin clearing duk bill din nasu,   wait what did you say  kallon accountant manager din yayi kafin ya ssoma Magana   yes sir all the bills have been cleared since a month ago, shuru ya danyi kafin yace who make the payment    shuru mutumin yayi yana duba sunan kafin yace   its anonymous sir,  shuru Muhammad yayi don babban asibiti ne kuma yawanci manya na ziyartar asibitin har suyi abubuwan lada wato biyama marasa lpy magunguna da gado saidai wannan yafi bashi mamaki don harda operations din da akayi da kwanakin da sukayi da kuma magungunan da zasuyi amfani dashi har su warke aka saya, karban takardar sallamarsu kawai yayi ya wuce zuwa gida, goda ya iso lokacin wajen karfe tara da rabi duk gidan sun kwanta, yana shiga dakinsa ya wuce bathroom ya watsa ruwa kafin y futo ta saka jellabiya ya soma shirya box din kayanshi don anytime email din ticket dinshi zai shugo don ya nema any available flight a bashi don aikin gaggawa zaije yayi, saida ya tattara komai kafin ya wuce dakin maman nasu gaba daya, yana shiga ya taddata asual tana waya khady kwance a gefenta dukta rame ta qanjame, samun waje yayi ya zauna kafin ya soma tambayan lafiyanta kuwa   ke meysa kike rama sosai haka kamar mai cutar aids  ..bai kaiga karasawa ba hajiya kareema ta katse shi, kai kaji neman bala I qanwarka kake ma fatan tsiya da masifa, wani irin aids kuma, shedanu ne suka shigeta suke sakata ramarnar na saka malam shitu yazo yayi mata ruqiya zata samu sauqi, ni kaina bana son wannan ramara tata,  shuru awai Muhammad yayi don shi likita ne yasan abubuwa sosai daga ido ma zai gane idan mutun na buqatar taimakon gaggawa saidai bazaiyi jayyay da uwar tashi ba don tunda ya zo naija take fushi dashi mai tsanani don ya taimaka ma yaran badaru, cikin nutsuwa yace   mama zan koma Jordan gobe daman nazo na maki sallama ne don zan iya wucewa da safe, sannan akwai yarannan haladu driver zai kaisu katsina gobe, idan har na wuce da asiba nasashi ya wuce da karfe goma asibiti ya dauko su saisu wuce katsina  ..tabe baki kawai tayi tace   allah ya kiyaye hanya, sai kuma yaushe inka tafi  shuru ya danyi kafin yace   zan dauki kusan wata biyar, amma zanyi kokari nazo ko kwana biyu ne nayi don duba yaran nan  ..wani ririn mugun kallo ta mashi kafin tace   wallahi Muhammad ka rufama kanka asiri ka rabu dani lafiya, ance maka su nan ba a kula?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? dasu ne da har saika dawo, to ban amince ba, ka tsaya kayi aikinka da ya kamata  jinjina kai kawai yayi kafin ya mata sallama ya wuce daki, yana zuwa ya kwanta don a gajiye yake sosai.
Da asuba yana tashi yaci karo da email, flight dinshi in 1hr da sauri ya tashi yayi wanka ya shirya cikin gaggawa ya sauko da luggage din ya wuce parking lot, saida ya kira haladu kafin suka wuce zuwa airport don saura mashi 30mins kawai, suna isa kuwa wajen minti ashirin ta basu baya, cikin gaggawa ya zaro envelop ya bashi hade da waya,   wannan kaje asibiti ka bama yarannan wayannan da envelop din da misalign karfe 10, kana daukosu ka kaisu gida su diba abinda zasu buqata sannan ka wuce dasu katsina, ka tabbatar ka kaisu, yana kaiwa nan ya amshi lugaggae dinshi don saura minti 10 flight dinshi ya daga zuwa Jordan, yana wuce haladu ya koma mota ya aje sakon a gefe, yana isa gida gari harya washe sosai, komawa yayi dakin ma aikata ya kwanta sai wajen karfe takwas ya farka donda sabo ya saba, duk tashin da zaiyi da wuri sai sunyi latti, yana futa gaban school bus kuwa babu kowa duk basu fito ba sai bayan takwas da rabi suka fara fitowa daya bayan dayan suna shiga cikin buss din sai suna gama shigewa yaja zuwa makaranta, saida ya saukesu duka lokacin wajen karfe tara da rabi ganin babu idan ya koma gida goma zata gitta kafin ya wuce asibiti yasa ya wuce chan direct, baima kaiga karasawa bay a tuna da sakon da Muhammad ya bashi na yaranba daya manta a cikin dayar motar daya kaisu, ganin babu lokaci yasa ya yanke shawarar idan ya kaisu gida saiya basu daganan saisu wuce katsina, yana isa asibitin ya nemi dakinsu kafin yayi sallama ya shiga, a zaune ya tadda su gaba dayan su, gaishesa salima tayi kafin ya masu ya jiki ya taimaka masu da yan kayayyakin da Muhammad ya saya masu suka fito, har cikin buss din suka shige kafin suka kama hanyar gida, babu abin da gaban salima keyi sai faduwa, ayanxu kam ta gaba tabbatar da cewa mutanen gidan nan ba qaunarsu suke ba a doran kasa, hatta hanyar gidan bata kaunar zuwa, da da yanda zatayi data cewa haladu ya wuce dasu katsina kawai saidai bata da wannan damar don taimakon su za ayi dole tayi hkauru, suna cikin tafiya misalign karfe goma da rabi akan hanyar express rininging din wayar nokia haladu ta doka kara cikin azama ya tura hannunshi cikin aljiu ganin sunana hajiya babba yasa yayi sauri dagawa yace   barka da safitya hajiya  , bata tsaya jin gaisuwarsa bat ace   kana ina ne haladu  ina kan hanyar zuwa gida ne hajiya naje dauko marasa lafiya a asibit  cikin fada ta soma Magana   klai wani irin mahaukaci ne, na gida bai koshi ba zaka taimaki na waje, ka zubar dasu anan titi kayi maza ka wuce zaria yanxun nan, motar hajiyata ta samu matsala akan hanyar zaria zuwa kaduna, kayi maza kaje ka daukomin tsohuwa daga ita sai direba  cikin gaggawa yace  toh hajiya na kusa karasowa dasu yanxu & bata bari yakai karshe ba ta doka mai tsawa   don ubanka ni kakema aiki ko yaran da basuda galihu  , haladu idan baka zubar da yarannan akan hanya b aka wuce hanyar zaria b aka gama aiki har abada   jin haka yasa ya taka burki kiiii hade da sauri cewa   an gama hajiya  yana aje wayan ya juyo ya kalli salima da sukayi tsuru tsuru yace   ku sauka zanje zaria road zan dawo nanda awa daya zanyi kokari nayi sauri na dawo  yanda duk ya burkice yasa suma suka burkice suka fito daga motar ko kayansu basu samu damar dauka ba sukatsaya bakin titi harya wuce ma ganinsu, samun dan dakalin kan titi sukayi suka zauna rungume da juna motoci na wuce daya bayan daya, saida suka shafe awa biyu a zaune har salim yayi bacci ya farka ya soma kukan yinwa, hankali ta bai gama tashi ba saida sukayi zaman awa biyar babu labarin haladu driver, kukan baqin ciki ne ya zuwan mata babu zato babu tsammani, ganin zaman babu abinda zai tsinana masu yasa ta lallaba salim suka miqe hanyar express way din, doguwar tafiya sukayi cikinsu babu wanda yasan inda suka nufa, ga yunwa dake cinsu, gashi babu kudi jikinsu balle su saya koda ruwa ne, samun waje sukayi bakin wani masallacin kan titin suka raqube har aka tada sallara zuhur suna nan zaune bakin daqalin masalincin mutane suka fara wucewa cikin masallacin, ganin ana alwala a jikin wani fanfo yasa suka tsaya mutane suka gama alwala, kafin suka karasa bakin fanfon, da kanta ta taimaka ma salim yasha ta hanyar taro mashi da hannunta harya koshi itama tasha ta koshi kafin suka matsa gefen titi bakin wata bishiya sbd zafin rana, tini salim ya soma bacci akan jikinta don daman shi alluran shi basu gama sakinshi ba, tagumi ta doka don at this point tabarma allah komai don yanxu kam ta tabbatar rayuwar su ta gama lalace babu wani sauran taimako da zasu samu saidai ta allah kuma. 96-97
UAE Daren ranar amra bata samu baccin kirki ba dalilin abinda ya faru tsakaninta da general din nata, gashi washe gari Monday tana son futa da wuri don yanxu ayyuka suna mata yawa sosai a office duk da an kawo sabbin inters suma ita ke training dinsu don ita ta dade sosai anan asibitin headquarters din, karfe hudu daidai ta mike sadaf sadaf ta koma dakin bude kofar tayi kamar bazatayi ba, ganinshi baje kamar yanda ta barshi yasa tayi sauri shigewa cikin dakin, wuff ta shige cikin toilet din, shaf shaf tayi wanka ta zura hijab dinta ta futo, anan yashe taga towel dinta da hijab dinta, wani irin kunya da takaici ne ya zo mata, da hanzari ta tako ta kwashe su sauke idanunta tayi akan fuskanshi dake da annuri, tabe baki tayi tace   ba laifi yana da kyau saidai halayyan ka ne sai a slow, ganin alamun kamar zai farka yasa ta bama kafarta iska gudun karya tashi kar ya goga mata Magana don ya iya yaba Magana dukda a fuska kamar bazaiyi ba.
Tana komawa daki tayi skincare dinta ta fidda kayan da zata saka ta aje a gefe, jin alamun yunwa na nukurkusarta yasa ta wuce kitchen ta hada tea maid an kauri tasha, kwanciya ta danyi nay an awanni kafin ta mike, 7 bai gama cika bama ta shirya tsaf cikin abaya blue mai igiya tayi mata kyau sosai don ta kamata sosai shape dinta ya futo, takalmin vincci ta blue ta zura, saida tadan goga kohl kadan da lip gloss kadan wanda yayi shining cute reddish lips dinta, jakanta ta janyo da wayanta ta fuce abinta.
?
Sir general kuwa sai wajen karfe 8 ya tashi don bacci ne mai dan banzan dadi ya fuzge shi, Wanka yayi ya shirya cikin kakin sa wanda ke kara mashi kyau da kwarjini ya feshe jikinshi da turare masu sanyin kamshi fuskanshi fayau, wani irin annuri ne kunshe a kyakyawan fuskanshi tunda ya soma shiryawa yanayi jiya ya soma dawo mashi tsaki kawai yayi don baya son tunawa, yanxu sai raini ya shiga tsakaninsu wanda shi kuma baya fatan haka, briefcase dinshi ya dauka da wayanshi ya fuce daga dakin, gaban motar shi da m5 yayi parking ya tsaya ya shiga, babu bata lokaci suka wuce.
?
Headquaters& ..
Tunda suka iso bayan m5 yayi parking saida ya dauka mintuna sosai kafin ya sanyo kafafunshi ya futo daga cikin army green lambor dinshi, lokacin wajen karfe 11 saura yan mintuna, futowa yayi cikin isa da kasaita ya fara takawa har gaban wajen entrance dago idanunshi yayi karaf ya sauka akan ta tana sanye da abayan dazu, ta bashi baya, dukda baiga fuskanta ba amma ya gama fuskantan itace daga baya data juya mashi, kayan nata yanda akwai madauri ta bayan rigan ya sanya shape din ass dinta ya futo sosai, kau da kanshi kawai yayi ya wuce kamar bai ganta ba, tunda ya shigo kamar koda yaushe sara mashi aka dunga yi, masu gulma nayi masu surutu ma nayin nasu don larabawa ma ba abarsu a bay aba wajen tsegumi.
?
Tunda ya shiga office dinshi ya dukufa da ayyuka a gabanshi sosai, wani sabon alamari ne yazo mashi mai wuyar fassara gaba daya dogument da evidences ne agabanshi wanda baiyi tsammanin samun ?su cikin sauqi ba, wasu abubuwan ma baiyi mamakin ganinsu ba, jingina yayi da bayan shi kan kujeran da yake zaune a office dinshi, daya bayan daya ya dunga warware duk wani important document na farko ya gano akwai mai hannu a cikin secret empire din da yake bincike akansu a cikin manyan manyan kasar, wanda ta bayan fage suke yin komai, na biyu kuma a cikin headquarters ma akwai waennda ke zame masu idanun leke duk lokacin da aka shirya operation akan su, saidai abin mamaki har yanxu babu wanda za a tsinta a cikin manyan wanda za ace shine keda hannu a cikin wannan kungiya, murmushi kawai yayi yana shafa suman kanshi data taru sosai sai sheki da laushi take   getting there very soon 
Bude kofa m5 yaayi bayan ya sara mashi ya karaso gabanshi tare da aje mashi wasu file din, kamewa yayi kafin ya soma Magana   new update sir, yesterday night we found someone at the airport, airport officials sun kamashi da wasu kwayoyi bayan ya hadiye su don wucewa dasu african country, acikin passport dinshi mun gano dan asalin Nigeria ne sannan kuma visa shi ya nuna zai tsaya a egypt anan zai cire drugs din don tafiyar awa biyar zaiyi and drugs din idan ya wuce wannan awannin zai loosing memory dinshi gaba daya don maganin zai narke ne a jikinki after that hours, so after ya cire su zai wuce kasashen da zai kaisu ciki harda Nigeria saidai a yanda muka tuntubi government din Nigeria da officials sun nuna this is the first time akayi mingling da magungunan, nayi additional binike after na airport official ayanda na gano ?alamarin kamar this isn t the first time aka kai irin wannan drugs din Nigeria, saidai har yanxu mun kasa gano shi kan suspect din, don kafin mu gama binciken mu yagama losing memoring shi don drugs din yakai kusan guda goma a jikinshi and guda daya kawai aka samu a cikinshi wanda a yanda likitoci sukayi bayani su masu ta ammali dashi daya ya kamata su sha a shekara.
Shuru amar yayi bayan ya gama sauraron m5 sosai cikin hikima, kwakwalwarshi nason janyo mashi abubuwa amma ya kasa warwarewa
  keep a close eye on the suspect, make an arrangement, I need him here in headquarters, everyone might think hes useless, I will try and see if I can get something from him and make sure you do a background check on him and for the drug I want to have a look on it ka tabbatar ka karba daga wajen official dinshi and secure it don nasan yanxu duk yanda akayi manyansu nada labarin an kama daya daga cikinsu so zasuyi duk yanda zasuyi don kubutar dashi, infact I need hin now 
Shuru m5 yayi kafin ya danyi wani tunani, ganin shuru babu inda zai kaisu ya sashi cewa   sir I have a request, why don t we just stoop slow and wait, we can actually kill 2 birds with one stone, kamar yanda kace tabbas manyansu zasu san yanda zasuyi su kubutar da shi idanma shi suspect din is useless to them zasuyi duk yanda zasuyi wajen kawar dashi gudun tonan asirinsu dukda yayi losing memeory shi, and after that akwai drug din shima bazasu so ya shigo hannu ba don sunsan dole za ayi bincike akan drug din kuma za ah gano inda suke kaiwa don za ayi tracing din illegal drug din da ayyukan da sukeyi dashi.
  uhm that s a good idea good job m5, now lets stoop slow for now 
  okay sir  juyawa m5 yayi zai fita chan kuma ya dawo
  sir maganar private training for new freshers da za ayi next week komai is ready sannan anyi preparing komai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login