Showing 219001 words to 222000 words out of 381117 words

Chapter 74 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2054

futo daga ciki main entrance hannunta rike da flasks  baba bismillah ga abunci
Da sauri baba mai gadi ya ajiye tiyo din ya taho da gudu ya karbi Kumar yace  Nagode karantar hajiya Allah ya Baki miji na gari
Murmushi kawai tayi mashi ta Mika mashi ta juya zuwa ciki.

Malam labaran dayaji muryarta Har tsaki Yan kanshi yayi saurin tsayawa, kanshi ne ya soma juyawa yana falshing wasu memories da bai gane daga inda suke ba, saurin juyowa yayi don Ganin koma wacece, bin bayanta yayi da kallon don harta shige cikin gida, dafe kanshi yayi dake Sara mashi yayi yana jin kamata rawar tasu tsaye akanshi, saida ya dauki kusan minti biyu a tsaye kafin komai ya kafa mashi ya fuce daga gidan.


Katsina& ..
Yau kusan wata biyu kenan hankalin hajiya kareema atashe, ga ciki nan sai girma yake dukda bata laulayi saidai kumburi, kana ganinta kasan ciki gareta don yana da girma sosai, komai yanxu ya tabarbare mata, hanyar samun kudinta Duk ya toshe saboda ciki da yayi mata cikas rabonta da talatu tun bayan dawowarsu daga wajen malami , ta daina daukan wayarta koda ta kirata, ga talauci daya fara masu katutu don yanxu makarantar government dinma ta gagari yaran gaba dayansu, khadi dai bata fasa Sana a ba don harda saida gwanjo yanzu takeyi, ta zama wata bugaggiyar Yan matan tasha babu mutunci, saboda da dan abunda yake samu suke samu au daura sanwa, yanxu muhammad ya rage tura masu kudi sosai saboda yabar Jordan ya koma France, nan kuma yanda zai tura masu kudi ya zama wahala saboda idan ya tura kudin saiya dauki watanni kafin yazo masu wanda ko yazo ma a banza yake tafiya don daddy ke cinyeshi tass ah harkar chacha daya koma da bariki, don yabar harabar dillanci don babu cigaba kwata kwata,daure baki kam anyi mashi don yaga ciki a jikin Haj kareema saidai baice komai ba game da ciki, haka ta dunga rainin cikin nata yau lafiya gobe jinya khady ce kadai tasan cikin shege ne a jikin mummy, tun tana damuwa itama harta watsar ta daina damun kanta akan abun kunyar uwartata ta cigaba da harkokinta na Sana a, asma is useless batada wani amfani kwata kwata, kullum tana fama da kafa daya a tsakar gida don ko shafa bata iyayi, akan haka kuwa babu irin zagin da bata sha wajen Haj kareema ita da ko dukansu bata yi ada chan baya balle akaiga zagi.

Zaune suke akan tabarma a tsakar gida gaba dayansu, khady na arranging gwajunan data saro while haj kareema na zaune tana jefa gyada a baki asma na yi mata tausa a kafa, su jalal ma na gefenta suna cin gyada, sallama akayi daga waje, kallon jalal hajiya kareema tayi  kai jeka ga da wa ake sallama
Mikewa yayi tsaye ya fuce, da gudu ya dawo yana haki,  daddy ne daddy ne
Mikewa haj kareema tayi ta janyo mayafinta khady ma mikewa tayi don Ganin yau wace irin masifar ya kwaso, futa sukayi gaba daya kafin su tsaya chak a bakin soro, daddy ne kwance jini na bin jikinshi yana wayyo Allah na Zan mutu, hannu aka kareema ta dora tana kallon yanda kafarshi ta karkace ta juya baya, kallon dandazon mutanen dake bakin kofar shugowa tayi da waenda ke gabanshi hankali atashe  na shiga uku meya sameshi yau wace irin masifa ce wannan Ka kwaso mana
Kallonta mutanen sukayi suna Allah wa dai da halin mata irin wannan, wani daga cikin mazan ne yace  accident yayi a bakin titin, munyi munyi yabari akaishi asibiti shine yace akawo shi gida shine muka kawoshi nan
Cije yatsa hajiya kareema tayi don yasan dalilin dayasa yace akawo gida saboda baya son fidda kudi,  Toh Ay shikenan kuje ku barshi anan tunda hakan ya tsaba
Mikew Duk sukayi suka barshi anan kwance, alamajirai biyu manya tasa suka shigo dashi cikin gida suka kwantar shi anan kan tabarma, zagaye shi duka sukayi yaran harma da kareema  Yanxu kai fisabillilahi kayi mana adalci kenan? Kullum cikin masifa muke daga wannan sai wannan ni Wallahi ba gaji
Yana jin azaba haka ya dunga surfa mata masifa yana kwashe mata albarka,  kinsan Allah kareema ki fita a idona, nine Ruffin asirinki don haka mu taru mu rufama juna asiri kawai
Yana kaiwa nan ya kwala uwar kara, wani irin murmushin takaici kareema tayi ta kalli khady  ki tashi kije gidan malam mai Gyaran hannu ki rokesa kozaizo ya duba
Tsaki khady tayi ta kalleta  nifa kinga Wallahi yau ban fita siyarda gwanjon nan ba saboda jin rikeni Saina yi shara da wanke wanke, ko tura wannan mara amfanin taje ta kirashi
Tana kaiwa nan ta mike ta kwashi kullin gwanjonta ta fuce daga gidan, shuru kareema tayi tana debe mata albarka a zuciya don bata tankwabarta ko musa mata saboda ita kadai tasan sirrin ta, kallon asma kareema tayi tace  Toh mara amfani ay gaskiar ta ne bazaki zauna ba bakya amfanuwa, mike kije gidan malam ki kirawoshi
Sauke kanta kasa tayi tana hawayen cin mutuncin da ake mata kafin ta zari mayafi ta fuce tana dogara sandarta.

After like 20 mins saigata da mai Gyaran targade, da sallama suka shugo nan kareema ta bashi waje don ya duba daddy, kallon hannunshi yayi da kafarta daya yace  karayar hannu ce sai targade a kafa
Tun kafin ya kaiga fara wa kareema tace  kuma Nawa za a baka
 Dubu daya ya amsata
 Haba malam ina laifin dari uku kareema ta fada,
Mikewa yayi yace  ku nemi wani yayi maku
Da sauri daddy yace  kutmaa kareema Allah ya tsine maki yanxu dari biyar ce bazaki iya badawa ba don jaraba ayi min gyara
Gyaran murya mai Gyaran yayi yace  dubu daya nace ba Dari biyar ba
Wani irin banzan kallo tayi ma daddy, yana Ganin haka yace  toh ki bada Dari biyar Zan bada Dari biyar nima
 Ay Wallahi baka isa ba, dari uku nayi niyar bayarwa idan bazaiyi ahaka ba Ka zauna Ka rube ma
 Ke wai wace irin Mara imani ce daddy ya fada yana hawayen azaba
 Akwai nada imani sama dakai azzalumi kareema itama ta maida mashi martani, tsaye a mai Gyaran yayi yana kallon ikon Allah yanda suke zagin juna agaban yayan su, tsaki kawai yayi yace  ni kunga tafiya ta
Da sauri dady ya tsaidashi  ki bada Dari ikon Zan cika sauran
Zama mai Gyaran yayi ya gyara mashi hannu da kafa kafin ya daure ko Ina  a dunga gasashi da ruwan zafi kullum sannan Zan dawo jibi na duba hannun mai Gyaran ya fada yana mikewa
Karema ce ta katse shi  Ay basai Ka dawo ba don sisi na bazan sake bayarwa ba
Maida kallonta tayi ga dady tana kokarin zaro dari uku daga gashinta datake kullewa tace
 Aikin banza asararre ashe da kudin Ka ajikinka amma bazaka fidda sai na bada a nawa  ta fada tana kallonshi bayan ta mika ma mai gyara dari uku, saida ya tabbatar ta bada kudin ya zaro nashi daga aljihu da hannu daya kafun ya kalleta yace  Ay babu asarriya kamar ke, keda y kikayi cikin shege da auranki Ay kece asarrariya
Idanun mummy ne sukayi jaa sosai, batayi expecting hakan ba daga wajen shi, ashe yasan komai, shiko mai Gyaran hannu saida ya taaya ya sake kare masu kallo yaqi fucewa don jin abunda zata ce
 An fada maki ban sani bane? An fada maki bansan ta yanda kike samun kudin da kike kashewa a cikin gidan nan bane? Tun Ranar da kuke maganar da diyarki na san komai? Saboda haka ki kama kanki wallahi

Tsit kareema tayi bata Kara ce mashi Kala ba karshe ma dai daki ta wuce tana hawayen bakin ciki da dana sani.

Abuja Nigeria& ..
Yau kwanan ammah goma da dawowa daga asibiti, taji sauqi sosai don tana takowa Har kasa tana saukowa, Duk bayan kwana biyu Amar ke kaita asibiti Ana mata general checkup, gaba daya yanxu health dinta shine damuwanshi, baya zaman hour guda koda baya gidan bai kirata a waya ba yaji yanayin jikinta, tun tana hanashi Har tazo ta saba ta hakura don gaba daya yanxu ya zama very strict akan komai, Har yau kuwa baiyi gigin kawo masu house help ba, salima da amra keyin komai dukda salima ce karfin aiki sosai don amra na kwance kullum bata da aiki sai barci sai cin abunci kamar kasa, ammah na kura da ita sosai don yanxu tafi damuwa da ita agidan akan kowa, kowa mamakin hakan yake Harda Amar saidai babu wanda ya taba tambayarta dalilin da yasa take damuwa akan amra da bata so much attention dinta gaba daya don Kowa yanaa Ganin hakan ne a matsayin saboda ta bata jininta ne alokacin da yake buqata, bangaren ammah kuwa ita kadai tasan komai haka zalika bata fada ma kowa ba tayi shuru abunta Harda amra ma.
Bangaren Amar yanxu babu laifi yana dan nuna kulawa ma amra don tun bayan da sukayi wannan maganar da ammah yake dan shiga sabgar amra, haka Duk Safiya idan yaje gaisheda ammah in ya fito zai wuce dakin ta don ya duba lafiyar yanda ta tashi, Duk sanda yake zuwa tana barci don haka yana shiga yake futowa baya zama ko na minti daya, ammah na Lura da hakan da yakeyi kullum kuma ta nuna mashi jin dadinta akan hakan sosai.

Tskanin Aman da salima kuwa yanxu sai fada kamar kaji haka zai biye mata suyi ta fada,Akwai ranar da tana shara a kitchen ya shugo, yana shugowa ya zubarda banana daya ci anan kasa inda ta share, ranar tayi masifa kamar menene haka nan ya tsaya yana kallonta ta rike kugu idanunta a rufe tana masifa  kaje Ka kira budurwar kanta share maka ni ba yar aikin ka bace
Kallon cute face dinta yayi, ba karamin burgeshi takeyi ba da yanda take masifa abun yana kunnashi sosai  Ay baby na bata shara, yar hutu ce shiyasa nake sonta sosai
Ya fada yana sake kunnota,
Wullata da tsintsiyar tayi ta wuce sama tana kuka. Tana futa kuwa ya tuntsireda dariya abunshi don ya gama gano ta, ko ba a fada mashi ba shi da kanshi ya shaida irin mahaukacin son da take mashi, shima dai daman ba wani giving up da yayi kawai dai yana son ya tabbatar tana sonshi.

Ammah ne ta fito daga part dinta ta wuce dakin amra, a kwance ta taddata wujiga wujiga daure da towel, da sallama ammmah ta shigo dakin  daughter barcin ne Har yanxu kusan sha biyu ko breakfast bakiyi ba
Da kyar amra ta dan gyara zaman towel dinta gaba dayanta kana ganinta kasan she s weak don ta dan zabge sosai tace  barka da rana ammah bismillah
Karasowa Ind a take ammah tayi ta kalleshi tana murmushi  ya jikinki daughter? Hope baby baya baki wahala sosai?
Da mamaki amra ta dago ta kalleta tana neman Karin bayani, hannunta ammah ta kama duka biyu tana murmushi tace  nasan baki sani ba,shiyasa nayi deciding na fada maki

Nunfasawa ammah tayi ta sake kallonta ya cigaba da magana  wannan barcin baby ne ke sakaki daughter ta karashe tana dariya,

da mamaki amra ke kallonta gaba daya kanta ya kulle Bakinta na karkarwa tace  ammah wani baby kuma? Ina baby yake?
 Listen to me daughter, kin kusa zama uwa, Allah ya amsa addua ta, you re pregnant a furgice amra ta daga ta kalli ammah da mamaki, gaba daga kana ganinta kasan she s shocked,  yes dear you re pregnant, tun daga ranar da kika shigo gidanan naga hakan a tare dake saidai ban tabbatar ba na barma Allah komai,

Kasa motsawa amra tayi sai binta take da idanu haka zalika ta kasa cewa komai, riko hannunta ammah ta sakeyi tace  listen to me dear, karkiji komai kinji ko, wannan kyauta ce daga Allah nasan zaki shiga rudu,Akwai wani abu daban fada maki ba acahn baya, tabbas Muhammad baya haihuwa kamar yanda na fada maki abaya don dalilin aurenki da yayi was his last chance of having his own blood line, nasan kunje asibiti ko? Kuma an gwadaki babu, wannan jarabawa ce daga Allah kuma hakan na Kara tabbatar mana da allah baya barci kuma mai yanda yaso ne kuma yana bayarwa a lokacin daya ga dama kuma ya hana a lokacin daya ga dama, zamuje asibiti gobe don muga how far you ve gone don naga baby bump din namu mai boye wa ne,saidai bana son Muhammad yasan da wannan zancen kinji ko sai mun Kara tabbatarwa kema dole ne yasa na fada maki don ya kamata ki sani.

Girgiza mata kai amra tayi kamar wata doluwa, ta kasa daina kallon bakin ammah dake furta mata tana da ciki cikinma na ya muhammad don sai yanxu kwakwalwarta ta fara processing.
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited

Mikewa ammah tayi fuskanta dauke da lausansan murmushi dake nuna tana cikin farin ciki sosai  Akwai abunda kikeson ci?
Sauke kanta tayi qasa tana mai jin kunyar ammah ayanxu sosai,  ah ah
 Daughter ki ajiye kunyan nan fah, yanxu ba lokacin kunya bane ba kinji ko, ba abun jin kunya bane abun farin ciki ne
Da kyar ta iya bude Bakinta ta amsa ammah  tohm ammah
 Bari na barki ki shirya saiki sauko qasan ko
Ammah na kaiwa nan ta fuce daga cikin dakin fuskanta dauke da murmushi, tana gab sauka qasa saiga Amar ya fito daga part dinta Ganin bata ciki, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi da fara a,  son Har ka Tashi
 Yes ammah na shiga naga bakya nan ya amsata anatse yana me karasowa inda take  naje wajen daughter ne ta amsashi kai tsaye tana murmushin jin dadi

 Good Morning, ya karfin jiki ya fada fuskanshi asaka yana kokarin maida wayar hannunshi cikin aljihun gajeran wandon jikinshi don daga gym yake.,  morning son, jiki kam Ay ya gama sauqi Alhamdulillah, muje ciki daman inason muyi wata magana ,
Cikin part dinta suka wuce Har zuwa sitting room dinta, zama tayi akan doguwar 3 seater kafin tayi mashi nuni da gefenta akan yazo ya zauna, takowa yayi ya zauna gefenta ya tattara duka natsuwarshi gareta,  yaushe zaka koma uae?
Dan shuru yayi yana nazari kafin ya soma magana  Duk ayyukan da zanyi na gama yinsu, anytime from now za a iya nemana a office don na rigada na gama tura duka report din ayyukan danayi anan so anytime from now Zan koma
Nunfasawa ammah tayi, jikinta yayi sanyi sosai, harga Allah tafison ya hakura da aykin na chan don ya samu ya kuka da dukiyarsa, saidai bazata taba hanashi yin abunda yafi so ba don wannan burin shi tun yana karami na zama babban soja, don haka ta dan nunfasa tace  matar Ka fah?
Sunkuyar da kanshi yayi yama rasa abunda zai ce,  ya zakayi da ita? Zaka tafi da ita ne?
Ammah ta sake tambayarshi
 Zan barta anan, Zan dunga zuwa every month
Shuru ammah tayi kafin tace  okay!
Da mamaki ya dago din baiyi tsammanin zata amince ba cikin sauqi don yanda yaga gana ji da ita cikin kwanakin nan ko shi bata bashi attention kamar haka,
 Inason Ka gyara gidan Ka na larrics, a refurnishing din gidan
Ba tare da ya tambayi dalili ba yace  Insha Allah!! Dukda yasan dalilin hakan.
 Allah yayi albarka ya Kara arziki da lafiya, ammah ta sake fada tana murmushi
 Ameen ya amsa ta anatse cikin kamewa, mikewa yayi tsaye ya nufi hanyar futa  Zan dan futa Zan kai dare
 Allah ya kiyaye, yauwa kaje Ka duba daughter bata jin dadi
Anatse ya amsa ta  Okay
Yana futa ammah ta mike tana hamdala ta wuce bathroom.


Tun bayan fitan ammah amra ta kasa mikewa tana nan zaune, lost in her thoughts completely, tunanin abun takeyi kamar a mafarki, maganganun ammah sun tsaya mata sosai,  I m pregnant??? Ta tambayi kanta in a confusing way, samun kanta tayi da taba tummy dinta dake a shafe kamar babu komi, dan matsawa tayi kadan taji tauri, sai alokacin ta tabbatar da wannan ma yana cikin changes din datake gani a tattare da ita cikin kwanaki,dan matsawan nan da tayi taji abu nayin zillo a cikinta, a rude ta miqe tsaye cikin firgici, is not like bata san komai
Game da ciki ba saidai Har Yanxu ta kasa yarda da abunda ammah ta fada mata, tabbas sunje asibiti kuma doctor ya tabbatar bata da ciki, Toh ya haka kenan? Boye wa cikin yayi komenene? Gaba daya ta gama daburcewa she s so confused, tana nan tsaye tana kallon cikinta Amar yayi knocking harya shugo dakin kai tsaye bata sani ba, tundaga bakin kofa ya tsaya ya kura mata idanu, towel ne kawai a jikinta sai gashi ta data baza a kafadarta, kallonta yayi daga sama zuwa kasa, ta dan rame kadan a fuskanta zuwa wuyanta, saidai kwata kwata ranar batayi affecting structure dinta ba da dirinta, idanunshi ne ya sauka akan inda yake kallo, bai gane dalilinta na kallon cikin nata ba don haka ya soma takowa Har inda take, ahankali ta soma jin daddadan turarenshi na shiga hancinta, da sauri ta dago idanunta ta sauke a cikin nashi dake yi kyalli, zuba mashi idanu tayi ta kasa daukewa don yau kusan sati guda kenan rabonta dashi, ya dan chanza ba kamar lokacin da suke jigilar zuwa asibiti ba, ya Kara kyau da kwarjini, bata ankare ba ganshi a gabanta ya zuba hannayenshi cikin aljihun wandonshi, Gyaran murya yayi ya dan kauda kanshi gefe  meke damunki?
Ba zato ba tsammani taji tambayar nashi, gabanta ne yadan fadi Tayi saurin kauda zancen ta hanyar cewa  Ina kwana
 Morning how are you


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login