Showing 282001 words to 285000 words out of 381117 words

Chapter 95 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2047

 muhammd kaii muhammd menene haka, dukan mace kakeyi? Kome tayi maka bai chanchanci kayi mata haka ba 
Ay muhammd fa ba sauraron ta yake ba, haka su amra sukabi bayan su suma aman ma da y agama gano komai yayi saurin bin bayansu don tabbas amar zai iya kasheta anan take, don haka yayi gaggawar janyo wayarshi ya soma kiran hukuma,
Ammah dake bin amar har suka fito tsakar gida yana ball da lantana tayi saurin kallon amra tace   aisha meke faruwa ne?, 
Kasa cewa komai amra tai don itama Karin bayani take nema, saida amar yayi mata lugu lugu idanunshi sunyi jaa sosai ya janyo wayarshi daga aljihunsa baya gani ma sosai yayi dialing number asad,yana picking azafafe yace  idan ka wuce 5 minutes baka zo nan gida b azan kashe wannan wicked soul din  yana kaiwa nan ya kashe wayar ya fara neman abunda zai dauka ya karasata, ganin wani karfe daga chan gefe yayi saurin juyawa ya dauko yayo kanta dashi, ammah na ganin haka ta dafe kirjinta tana innalillahi, Muhammad zaiyi kisa akan idanunta, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, bat agama tunani ba taji kwal ya bugama lantana a kafa daya saida kafar ta balle, daga hannu yayi zai sake buga mata amra tayi saurin tahowa inda yake ta rungumeshi ta baya   yayaa don allah calm down, karkayi abunda zakazo kayi dana sani 
Baya ji baya gani yace   sakeni, 
  wallahi bazan sakeka ba yaya, bazan taba bari kayi abunda zai jefa rayuwar ka a halaka ba, 
  aishaaaaaaaaa  ya daka mataa tsawa, dukda ta tsorata hakan baisa ta sakeshi ba, wani irin juyi yayi ya zubar da ita a kasa, nan take ta kwala uwar kara dayasa ammah ta kalleta, kankace me cikin kankanin lokacin ammah ta zube a kasa wanwas, jini na fita daga bakinta da hancinta hankali atashe salima ta kwala kara   ammahhhhhhhh!!!!! Wayyo allah na shiga uku 
Amra da bat agama dawowa daidai tana ganin ammah a yashe a kasa tayi saurin rarrafowa ta karaso wajen, ganin ammah a kwance hankali aatshe ta taba ammah tace   ammah ammah  jin shuru ya sata taba wajen zuciyar ammah, dipp komai ya tsaya chak, hankali atashe amra ta dago agigice ta kalli salima da aman da suka zagaye ammah tace   am& .mahhh..ta mutu.uu..  hannunta da bakinta duk karkarwa suke, da sauri ta miqe tsaye kamar mahaukaciya har veil dinta na faduwa ta kaarso inda amar ke bugun lantana da duk jini ya gaba malalewa a jikinta ga uban raunuka daya ji mata, amra na karasowa ta daka mashi tsawa daya sashi tsayawa babu shiri   amarrrrrrrrrr!!!!! idanunta sunyi jaa sosai sai sauke nunfashi takeyi
Da sauri ya waigo ya kalleta ya zuba mata idanunshi, tana ganin haka ta juya ta nuna mashi ammah   ammahhhh & ammahhh  
Ay baisan lokacin daya saki rodin ba taku biyu uku ya iso inda ammah ke kwance kamar gawa, salima a furgece ta dago tana kuka   ya aman wai ta mutu, ammah ta mutu, na shiga uku na wayyo allah na 
Amar daya tsaya kikam ya kasa yin komi, jikinshi na bari ya durkuso ina ammah ke kwance rai a hannun allah& & & [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!
Unedited page&
Wajen karfe uku na dare ya farka saboda wani irin zafi dayaji a jikinsa lokaci guda, bude rinannun idanunshi yayi ya sauke su akanta, ta maqalqaleshi gaba dayanta ta sauke mashi nauyin jikinta tana rawar sanyi, ga wani irin turirin zafi dake fita daga jikinta, saurin lumshe idanunshi ya sakeyi yi ya budesu tarr akanta sosai bakinta na gab da nashi lebanta na karkarwa sosai, saurin mikewa yayi zaune ya gyara zamanshi ya kalleta da kyau saboda akwai hasken bedside lamb dake a kunne, kyawawan ya zubama idanu inda wasu siraran hawaye ke zarya akan fuskan nata, saurin taba wuyanta yayi ganin yanda ta fara kafewa bakinta har lokacin yana karkarwa sosai, wani irin zafi yaji daya sashi saurin cire hannunshi   shes burning up  ya fada ahankali yana kallon fuskanta, saurin janyeta yayi daga jikinshi ya mike tsaye yama rasa abunda zaiyi don ya mata taimakon gaggawa, tunawa da yanda ammah ke mashi lokacin da yake karami yayi don haka ya wuce bathroom ya jiko hand towel kafin ya dawo gefen gadon ya zauna ya soma goga mata a fuskanta.
jikinta ne ya tsananta don har lokacin he can feel yanda take sauke nunfashi mai zafi sosai akan hannunshi, last option daya yake dashi wajen taimaka, kamar bazaiyi ba don yasan zaiyi affecting dinshi sosai, saidai ganin yanda take rawar sanyi ya sashi jin wani iri don haka ya mike tsaye ya kashe ac dakin ya wuce ciki closet ya dauko babban duvet mai nauyi sosai ya sauya da dayan, yanda yake yin komai a gaggauce zaka gane hankalinshi a tashe yake.
Yana nan tsaye yana nazari kamar ana fusganshi haka ya soma zame kayan jikinshi ya rage daga shi sai dogon wando pjs dinshi.
Ahankali ya hau kan gadon ya zauna kafin ya janyota jikinshi ya soma zame kayan jikinta, saida ya cire kayan barcin nata gaba daya kafin ya hade jikinshi waje daya ya rungumota, wani irin shock ya soma ji saboda yanda fatar jikinta ke gogar nashi don babu bra kwatkwata jikinta, runtse idanu kawai yakeyi jikinshi na vibrating saboda kusanci yayi yawa sosai, janyo duvet din yayi ya rufa masu gaba dayansu tundaga sama har kasa har lokacin tana cikin jikinshi tayi lamo.
Ahankali zafin jikin nata ke transferring zuwa jikinshi don shi temperation dinshi is normal, shida idanunshi suke a bude kuma yana cikin hayyacinshi shi kadai yasan irin connection din da zuciyoyinsu suka shiga, don heart beat dinsu kusan a tare suke bugawa, at the point ya tabbatar zuciyarshi is beating for her don kwata kwata ba haka zuciyarshi ke bugawa ba,
Bakinshi ya maotso saitin kunnenta ya soma karanto mata addu oin samun sauki harta daina rawar darin da takeyi nunfashinta na sauka ahankali akan kirjinshi da gashi ke kwance akai.

Har aka kira sallar asuba bai runtsa ba ko kadan yana maqale da ita, sallar ma bai samu yayi ba don sai a lokacin barci ya fusgeshi saboda wani matsanancin ciwon kai daya fara kawo mashi ziyara.

Amra dai bata san wainar da yake toyawa ba saidai daren ranar taji wani irin sanyi a zuciyarta, daman duk dare saitayi wannan zazzabin wanda ayanxu ya zaman mata jiki don duk dare saitayi.

Basu suka tash ba sai wajen karfe goma na safiya, amra ce ta fara bude idanunta saboda wata irin yunwa data nuqurqusota, saurin bude idanunta tayi ganin duhu duhu yasa tadan razana don bata ma lura da ajikinshi take bay a lullubesu da duvet, mutsu mutsun da ta soma yi ne ya farkar dashi daga barcin, bude kyawawan idanunshi yayi ya sauke akanta, sai alokacin itama ta kalli fuskansa da kyau, janyota yayi sosai a jikinshi ya lumshe idanunshi da suka danyi jaa yace   shiii go back to sleep 
Dauke idanunta tayi akanshi don yanda yayi mata maganar yasa ta soma jin wani abu chan kasan ta saboda whispering tone yayi using, dan turo bakinta tayi kafin ta soma Magana anatse   ni yunwa nake ji 
Bai bude idanun nashi ba ya sake cewa   baki isa ba fah, yanda kika hanani barci jiya sai kin koma 
Ashagwabe ta sake cewa   wallahil azeem yunwa nakeji, cikina yana ciwo 
Banza yayi da ita, idanunshi a rufe to his surprise sai jin kukanta yayi kamar wata baby ashgwabe tana kuka tana gunguni tana Magana   ni wallah yunwa nake ji  ,ta fada tana harba kafarta har wani zungurinshi takeyi da kafafun nata wanda ya sashi runtse idanunshi ya danyi yar tsuka ya bude idanun ya saukesu akanta   why are you so stubborn ne? ke ba a isa a fada maki abu kiji ba 
  toh nace maka inajin yunwa kaqi barina na tafi  ta sae fada tana kauda kanta daga gareshi.
Bai saketa ba haka zalika bai sake ce mata qala ba harta karaci kukan nata ta gaji ta rabu dashi, don kukan ma galabaitar da ita yakeyi sosai.
Saida suka dauki kusan minti atalatin a haka, har lokacin bai saketa daman dalilin qin sakinta nata da yayi was erection din data tado mashi wanda bayason ta ganshi a haka ta samu kofar sake rainashi shiyasa ya ki sakinta saida ya bari komai ya dan lafa mashi.

Sauke duvet din ya farayi kafin ya sassauta rikon da yayi mata ya sauke kafafunshi kasa ya wuce bathroom anatse ba tare da ya waigo inda take zaune ba don har lokacin engine dinshi na nan a tsaye bai sauka ba, ya shiga bathroom ya soma zame kayanshi ya fara wanka.

Tana ganin ya shige bathroom ta mike zumbur, sai alokacin ta lura da babu komi a jikinta said an pants dinta, wani irin takaici ta danji a ranta don yanzu kiriri ta gane buqatarta yake sosai, wanda tayi alqawarin bazata taba bari ya kusanceta ba sai ya karbeta a matsayin mace kamar kowacce mace a wajen mijinta.
Yar tsuka tayi ta zura rigar barcinta, bata ma staya saka hula ba ta fuce daga dakin aranta tana rokon allah yasa babu kowa a parlor, koda ta futo daga dakinshi ta karasa wajen kofar fita daga parlor nashi saida ta dan tsaya ta bude kofar ahankali ta zuro kanta, babu kowa a parlor kuma bataji wani hayaniya ba ko karar spoons don haka tayi maza ta bude kofar ta fuce fit tana dan sassarfa kamar munafuka.
Batayi landing a ko ina ba sai dakinta tana shiga ta sauke wata ajiyar zuciya tana haki, saida ta dan dawo daiidai kafun ta wuce cikin daki ta soma rage kayan jikinta ta wuce bathroom tayi wankanta.

Tana gama wanka ta fito daga bathroom tana tsane jikinta da hnd towel data ruko a hannunta, agurguje ta soma shiryawa ta saka wani doguwar riga wanda ta dan kamata kadan, tana gama shiryawa ta hau kan sallaya ta tada sallah, tana idarwa ta mike tsaye tana kokarin cire hijab din jikinta saiga sallamar ammah, cikin sauri ta sauke hijab din kasa ta wuce wajen dresser ta tsaya tana murmushin yaqe don bazata so ta ganta tana sallah yanxu ba don duk wand aya ga haka sai ya kawo wani abun, ammah dai ta kamata lokacin da ta bar wajen sallayar haka zalika taga fitowarta daga dakin nashi don tana tsaye tana shirin futowa daga kitchen ta hangota.
Fuskan ta dauke da murmushi ta tako cikin dakin tace   daughter yau kin Makara sosai 
Adaburce amra ta saukar da kanta kasa tana wasa da yatsunta tace   ina kwana ammah? 
  lafiya kalua daughter ya kwanan ki da na baby?,  ammah ta sake tambayarta
  alhamdullillah  ta amsata anatse muryanta baya futowa ma sosai.
  zo ga breakfast na kawo maki, na sanki da son dumame  ammah ta fada tana karasowa baking ado ta ajiye mata akan carpet   bismaillah, zoki zauna kici dear 
Cikin jin dadi amra ta karaso inda ammah ke tsaye kanta har lokacin a kasa fuskanta fayau said an murmushi da ya wanzu akan fuskanta   thank you ammah, daman dashi na tashi wallahi 
Murmushi kawai ammah tayi mata kafin ta juya hanyar futa tace   idan kin gama ki sauko kasa, yaudai kid an zagaya estate din, ga salim nan saiya rakaki 
  tohm ammah  amra ta bata amsa.

Ammah na fucewa ta zauna ta nadi tuwon nan sosai, saida taci ta koshi harda sude hannu kafin ta wuce bathroom ta wanke hannunta, tana wanke hannun ta fito ta dauki plate din ta fuce daga dakin.
Kasa ta fara saukowa babu kowa a kasan don haka ta wuce kitchen kai tsaye ta ajiye plates din, gaban fridge ta tako ta dauka bottle of ice water kafin ta fuce daga kitchen din.
Tunda ta gifta ta wuce kitchen ya dago ya kaleta harta futo daga kitchen din batama san yana wajenba, itako amra bata lura dashi ba kwata kwata kanta a kasa saida tazo daidai wuce hanyar dining din ta jiyo karar spoon, duk a tunaninta ma ammah ne a wajen don haka ta dan dago da idanunta, karaf idanun nata suka sauka akan nashi, hannunshi rike da toasted bread yana kokarin kaiwa baki, samun kanta tayi da galla mashi harara tayi wani farr da idanu tare da turo mashi baki kafin ta kauda kanta gefe tana kokarin amsa kiran da ammah dake zaune a sitting room takeyi mata   daughter daughter, kin sauko ne? 
  eh na sauko ammah, plate na ajiye ne a kitchen  tana kaiwa nan ta sake mashi kallo daya ta dauke kanta ta cigaba da catwalk tafiyanta kamar wata tarwada,mazaunanta yabi da kallo har saida ta gifta ma kallonshi kafin ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya   ya allah,  ya furta ahankali, tunani ya soma yi aranshi har lokacin bread din na hannunshi bai kai baki ba,   yarinyar nan na neman haukatani  ya fada aranshi kafin ya danyi wani murmushin da shi kadai yasan ma anar shi   zanyi maganinki ne 
Tura bread din yayi abakinshi, da farko kwata kwata bayajin cin komai saidai yanxu daya ganta da yanda tayi wannan abun da tayi mashi da fuskanta saiya tsinci kanshi da jin dadin cin abunci,.

Amra kuwa wani irin haushinsa takeji yanda yake kokarin maidata kamar wata toy dinshi, don sai ayanxu ta lura da take takenshi na neman coffee da daddare, saboda yasan ammah zata ce takai mashi, tun kafin ta karaso parlor ta soma Magana a zuciyarta   ay kuwa bazan kara kai maka ba wallahi, daman na lura da take taken ka 
Kaarsowa tayi parlor har lokacin tana tunani aranta,muryar ammah ne ta katseta   daughter kayannan baya damunki? 
Dan dagowa tayi kafin ta maida idanunta kan kayan   ah ah ammah, baya damuna 
  toh shikenan, ki dauko mayafi salim ya rakaki ku zagaya  ammah ta fada tana maida kallonta ga tv
  tohm   tana kaiwa nan itama ta wuce sama anatse, tana shiga daki ta dauka dankwalin doguwar rigar ta tsaya gaban mirror ta daura dankwali, ba karamin kyau daurin yayi mata ba dukda bata iya ba, tana gama daurawa ta dauka kohl ta sanya a idanunta da suka dan fada kadan, tana gamawa ta dan jaa baya ta karema kanta kallo, dan bumb dinta ya futo sosai don sai a lokacin ta lura dashi saboda yanayi rigar jikin nata daya fiddashi dan kiff, shafa cikin tayi tana murmushi,   yanxu da baby anan wajen  ta fada tana shafa cikin nata tana murmushi, ta dauka kusan minti biyu a tsaye tana shafen cikin nata kafin ta tuna da wani abu, take yanayinta ya sauya tana tausayin kanta, duk sanda ta tuna yanda ya Muhammad ke treating dinta tana jin rashin dadi aranta, ta rasa dalilin dayasa hes always cold to her, kowani aure tasan koda babu soyayya akwai mutuntawa da kulawa da juna saidai ita batayi sa a ba, don ko fara arshi baifi sau biyu ta taba gani ba, baya sake mata ko kadan, doguwar Magana ma bata shiga tsakaninsu saidai fada, har lokacin ta kasa gane wani irin mutunne shi, da farko bayan rashin lafiyar ammah har tana cewa ya chanza ashe ashe bai chanza, koda yake what did she expect? Baka taba chanza mutun daga yanda yake dlilin wannan yasa ta kasa tantance a wani matsayi ta sakashi a zuciyarta, bata jin zai taba sonta a duniya don haka bata daurama kanta bama saida ta kawo zancen soyayya aranta ta tuna da Haifa,ada chant un tana tunaninta sometimes harda kuka idan tayi missing dinta saidai yanxu komai ya chanza, but har lokacin tana ranta.
Nunfaswa tayi ta janyo mayafin ta ta nada shi kan kafadarta ta fito daga dakin har lokacin bottle of ice din data dauko yana hannunta, natse take tafiya harta sauko kasa, dan dagowa tayi daga nesa ta hangoshi zaune kusa da ammah ya daura kafa daya kan daya, wayarshi maqale a kunneshi yana responding calls,   har kin sauko?  ammah ta tambayeta tana kallonta
  eh,  ta amsa ta kai tsaye kanta a kasa
  toh tashi kuje salim, ku zagaya ko ina ki danyi exercise kafin ku dawo  ammah ta fada tana kallon salim dake zaune yana buga ball
Mikewa salim yayi ya zagayo inda take   ammah sai mun dawo  amra ta fada tana bin hanyar futa daga cikin parlor hannunta rike dana salim suna tafiya ahankali.
  toh daughter saikun dawo  ammah ta fada tana maida idanunta kan tv.
Saida y agama wayar ya dan kalli ammah ta gefen idanu, kamar bazaice komai ba chan kuma ya hade rai yace   ina zasuje da safen nan 
Yanda yayi maganar yana basarwa kamar bashi ba,ammah bata kalleshi ba ta bashi amsa kai tsaye   zasuje strolling 
Dan tabe baki yayi kmar bai damu ba, yna son mikewa saidai kuma yana ganin kamar amma zatayi tunanin wani abun don haka ya soma latse latsen wayarshi.
Tunda ta fuce yake kallon time din wayarshi don ya dauka suna fita zasu dawo saidai yaga akasin haka don kusan 30mins basu dawo ba, kasa sukuni yayi daga zaunen da yake dukda bazaka taba tantance hakan akan fuskanshi ba sai tsaki daya dunga jerowa har lokacin idanunshi nakan wayar, ganin tsukar tashi taki karewa yasa ammah juyowa ta kalleshi   is everything okay son? 


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login