Showing 102001 words to 105000 words out of 381117 words

Chapter 35 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2007

ma na neman gazawa, da sauri ya dauke nashi idanun daga kanta ya gyara tsayuwanshi kafun yace  me kika futo yi
Da sauri kamar wadda ke jiran tambayar ta bashi amsa  ruwa nazo dauka
Dan tabe baki yayi kafin ya raba ta gefenta ya fuce daga kitchen din cikin kamewa.
Yana futa kuwa ta sauke nauyyayiyar ijiyar zuciya wadda saida ya jiyota kafin ya bar kitchen din gaba daya.
Saida ta dauka kusan minti biyu kafin ta daidata natsuwarta ta wuce wajen da ake ajiye mugs, ruwan zafi ta deba daga diapenser dake jikin fridge din kafin ta fito ahankali jin yanda murdawan keyin gaba sosai, bata tsaya duban sitting room din kasan ba don ko ina a kashe yake babu haske Saina wajen entrance dake hasko parlor kadan, stair ta fara takawa atsanake, taku daya biyu tayi bata kaiga taku na uku ba taji ciki ta ya Kara murdawa, cikin hanzari ta dafe handrail din stair din tare da da yin yar Kara don yanda ta razana dajin zafin ya sa ruwan mug din ya dan fantsala akan skin din hannunta duqawa tayi ta dafe mararta tana jin wani irin azaba,
Amar dake tsaye nesa da ita don yana zaune a sitting room din harta fito yana hangota saidai ita bata ganinshi, harta hau stairs da tsayuwan datayi Duk akan idanunshi Har zuwa lokacin da tayi yar karar, tare da dan duqawa kadan.
Har inda take ya tako ya tsaya dan nesa kadan kafin yace  get up
Adan furgice ta jiyo ta ganshi tsaye don batayi tsammanin ganinshi ba don Duk a tunanin ta ya wuce sama, miqewa ta soma yi ahankali kafin ta daga kafa daya ta kwala yar kara, tabe baki yayi don ganin kamar Ma abun nata da raki da shagwaba baiyi wata wata ba ya sungumeta gaba daya, Sai jinta tayi a sama, tsoron daukan da yayi mata a bazata ya sata saurin kankameshi sosai wanda hakan saida ya sashi dan tsayawa for a moment jin lafiyarshi ta dan motsa, daidai ta natsuwarshi yayi kafin ya haura saman da ita, Har bakin gadon ta ya sauketa bai tsaya kallonta ba ya juya ya fuce daga dakin, yana futa kuwa ta sauke ijjiyar zuciyar don tunda ya dauketa gabanta ke faduwa, bayan Yan mintuna kadan Sai gashi da wani mug daban a hannunshi, karasowa yayi gabanta ya miqa mata, bai ce mata komai ba ita ma tana ganin yana miqa mata ta karba tare da cewa  thank you!
Ganin ya tsaya bai motsa ba Sai nannade hannayenshi dayayi a kirjinshi gashi ya zuba mayun idanunshi dake sata jin wani iri ya sata kauda kai gefe ta soma kwankwadar ruwan ba tama jin zafin ruwan harta shanye tass ta sauke nunfashi still hannunta nakan kirjinta tana kokarin rufe kirjin, shi mamaki Ma yake tana da kananun shekaru take da jiki haka, tsaki yayi ganin yanda take kare kare kafin yace  what are you hiding?, ya fada yana hade rai tamau
Saurin dagowa tayi ta zuba mashi idanu chan kuma ta sauke still hannunta na kan wajen,  babu komi ta bashi amsa kai tsaye
Wani irin kallo ya zagba mata mai wuyar fassara wanda ya sata daburcewa ganin yanda ya bata rai sosai.
Kamar wata munafuka haka ta sauke hannun ta kadan ta kare wajen yanda bazai gani ba.
Oga dai gyara tsayuwanshi yayi ya kura mata idanu ya cigaba da tambayarta  Ina kike jin ciwon
 Kasan mara ne ta bashi amsa Adan shagwabe don tama manta dawa take magana, abunka da mara lafiya da neman attention
Kamar ya karanenceta kuwa ya sake tambayan  wajen Ina ne let me see
Kamar doluwa haka ta mike tama manta da kare Karen kirji da take ta tako gabanshi tana turo baki a shagwabe ta daura hannunta kasan shafaffen cikinta wajen mararta ta sunkwi da kai tace  nan kasan
Tunda ta mike ta dunfaro gabanshi kamshinta ya bugeshi sosai Har cikin hancinshi, Dukda da yar tazara tsakanin su saida ya tako gab da ita sosai, itako da kanta ke Kasa tana kokarin nuna mashi Sai jin nunfashinsa tayi daidai fuskanta yadan duko gabanta sosai ya sauke mata lafiyayyen nunfashinsa mai zafi akan fuskanta, abunda yafi tada mata hankali shine jin saukan lausansan tafun hannun shi akan mararta dake cikin yaloluwar rigar da ita da babu Duk daya, da sauri ta daga idanunta tare da sauke wa kanshi, nan take tayi arba da tashi fuskar daidai tata Har hancinsa na neman gogar nata, tuni nunfashinta ya tafi wucun gadi, don kamewa tayi kyam ta Kasa motsi, hannunshi kam yana nan kan mararta shima ya Kasa daukewa don wani irin shock yaji ya durar mashi take ya gane cewa lafiyar ta dawo inma bata gama dawowa ba kiris ya rage, shafa wajen daya danyi ne ya maidota hayyacinta da kuma muryarshi dake dauke da kamshin mint daga bakinshi
 Daidai nan ne?
Kamar wawuya ta bude baki tace  uhm
Kara dan matsa wajen yayi yace  uhmmmm
Jikinta ne ya soma kyarma
Da sauri ta danyi Kara tace  zafi tare da saurin yin baya ta koma ta tsaya tana sauraron yanda zuciya ta ke racing sosai, tabe baki yayi Harda yar guntun tsuka yace  go back to sleep
Batayi wata wata ba ta hau kan gado ya bita da idanu harta janyo duvet ta rufa, jin alamun bai motsa ba yasata bude kanta tace  good night yaya
Bai tsaya amsata ba ya juya tare da janyo kofar ya rufe mata
Yana futa ta sauke ijjiyar zuciya sosai tana mamakin yanda ya sauko yau, saidai bata sama kanta hope din haka zasu dinga tafiya ba don baka gane mashi kwata kwata.
Dakyar barci barawo ya kwasheta dukda idan ciwon ya nuqurquso ta farkawa take yi idan ya lafa kuma ta koma.

Shima gogan yana shiga daki ya hau kan gadonshi ba tare da tunanin komai ba yayi kwanciyarshi saidai barcin baizo mashi ba Sai gab da sallar asuba tunani iri iri na yawo a kwakwalwarshi saidai yanda yake da dakewa yasashi kawar da komai kamar ba komai ba.

Washe gari Monday da sassafe ya fuce daga gidan saboda wani urgent investigation da zasuyi shida lieutenant asad, koda ya fuce Nadine ma bata fito ba,

Ahankali amra soma bude idanunta da sukayi mata nauyi sakamakon baccin data samu gab da sallah asuba, Mika tayi tare da adduar tashi daga bacci, ayanxu ciwon cikin nata ya dan ragu don sama sama take jinshi, gashi maganin datasha ya sata jin kwarin jikinta, kafafunta ta sauke kasa ta wuce toilet, bata tsaya komai ba ta fara watsa ma jikinta hot bath?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? , tana gamawa a gurgurguje tayi brush ta fito don yunwa take ji sosai, Riga mara nauyi ta zaro doguwa daga cikin kayanta tare da set din bra da pant kafin ta fara shirywa ,saida ta feshe jikinta da turarenta,bata tsaya shafa mai ba ta nannade gashinta ta tura cikin hula ta fuce daga dakin, Kasa ta sauka ganin Nadine bata parlor yasata wucewa kitchen direct, tana shiga kuwa ta hangota tsaye tana goge gogen gas da alamu bata dade da gama amfani dashi ba, cikin girmamawa suka gaisa kafin ta tambaya jikin ta.
 how are feeling now ma? Nadine ta tambaye ta fuskanta dauke da murmushi
 Alhamdulillah Nadine naji sauki amra ta bata amsa
 Na gama breakfast yana dining, daman na bari na gama ayyuka ne Saina duba ko kin Tashi don dazu wajen 7 bayan sir ya futa na leko don naga ko jin Tashi sainaga baki Tashi ba
Nunfasa amra tayi kamar bazatace komai ba chan kuma tace  uhm shi ya karya ne?
 No bai karya ba, lokacin daya futa ma ban dade da futowa ba, nima ban sameshi ba don saida naje kaima security da driver abunci naji sun futa shida driver da sassafe.

 Oh okay,Yau me kika dafa mana nadine amra ta tambayeta fuskanta dauke da murmushi
Murmushi itama Nadine tayi tace  ma, as asual dai chips ne Sai egg sauce da chicken pepper soup
Shuru amra tayi kafin tace  Bari naje dining din, sannu da aiki
Tana kaiwa nan tasa kai ta fuce nadine ta bita da ido tana murmushi tace  wannan yarinya badai kyauba ga fara a saidai shi yayan nata baida fara a kamar ita

Zama tayi a dining ta zuba chicken pepper soup a bowl daidai cikinta kafin ta hada tea mai zafi, ba laifi taci da dan yawa, kafin ta sha tea din don shi tafi buqata, tana gamawa tayi handala ta goge bakinta ta wuce sama, magungunan da doctor ya bata ta ballo tasha kafin ta zauna gefen gado ta janyo wayanta, line din haifa ta soma kira, baya shiga tun last time da sukayi waya ta daina samunta, haka zata dinga kira amma baya tafiya kwata kwata.

Amar&
Tunda ya karaso Nigerian army headquarters ya wuce direct office din lieutenant asad, tundaga gate kowa yasan anyi babban baqo,Duk zuwan da zaiyi Sai an zuba manyan securities wanda baya son haka sbd ba official zuwa yyi ba don cikin sirri suke yin aiki da taimakon asad saidai in Har zai shiga headquarters na sojoji dole Sai Ansan da zuwan shi, shiyasa yawanci idan zasuyi meeting akan investigation da sukeyi yake saka lieutenant asad ya nema masu waje mai sirri, wannan zuwan Ma da yayi zuwan gaggawa ne kuma dole ya shigo cikin headquarters don abun ya shafesu.
Yana iso wa ya wuce direct office din asad, yana shiga kuwa ya miqe suka gaisa cikin girmamawa kamar yanda suka saba, shima asad office dinshi babba ne kamar ko wani office saidai kuma bazai taba Kamo na general gabaki daya ba lols.

Tunda ya fara ma asad bayani, baiyi wani mamaki ba don abunda yafi haka Ma za a samu anan nigeria, gashi sunada report dayawa akan human trafficking da akeyi da yawan futar haramtarciyar kwaya wanda an Kasa gano daga inda take, gashi tana kisa musamman wa kauyuka sbd yawanci waste din drugs din rafi ake kaiwa ayi dumping inda baza ayi tsammanin ,mutanen kauye kuwa basu damu ba shan ruwan rafin su sukeyi wanda daga karshe su dinga cututukan da ba a gano ta yanda suka samu.

Nunfasawa asad bayan ya gama sauraron bayanin shi hannun shi nade a kirjinshi yace
 Oga nifa bazanyi mamaki ba,we have thousands of report akan human trafficking, yanxu haka da nake maka magana Akwai badge of yaranda went missing, Mun Kasa gano komai, amma yanxu ka kirashi muji idan zai samu turo mana evidence koda hoton yaranda aka tafi dasu tunda yace maka ya tabbatar Yan nigeria ne Sai muyi comparing mu gani daga nan zamu samu damar tracking ta inda yaran suka bace
Shuru Amar yayi kafin ya dauka wayanshi ya soma dialing number hammam..
Ringing daya biyu ya dauka
 hey dude amar ya fada yana relaxing a kan kujeran da yake zaune da take facing asad
 I m so surprised ka kira, bansan da wani baki zan baka hakuri ba, I m so sorry dude hammam ya fada daga chan bangaren
Nunfasawa Amar yayi kafin ya saka wayan a speaker
 It s okay dude, naji dadi da kayi uniting da mahaifiyarka
Murmushi hammam yayi yace  all thanks to you, ta dalilinka na gano komai and I promise you yanda na fada maka I will make sure Mun kawo karshe azaluman nan

 Insha Allah Amar yayi saurin fada mashi kafin ya cigaba
 Now I need your help, naga email din da kayimin akan abubuwan daka gano

 Oh yes, jiya an kawo yara wajen alif, ban tambaye shi ba don normally idan naga an kawo mutane gidanshi bana magana,don baya son yawan tambayoyi, saidai bayan an aje su ah gidan I sense something very fishy, I had to dress like one of the workers dake gidan, na shiga inda ake aje mutane a nan gidanshi kafin a kwashesu zuwa wata Kasa, dude I was so surprised with what I saw, yaranda na gansu an shigo dasu lafiya kalau Saina gansu sun zama mahaukata, Akwai mutun daya da naga yanata kuka, yaron is about 17 years i rush to him na tambayeshi, nan ya shaida min an shigo an basu wata kwaya, shi dai yaji tsoro bai sha ba yace zaije toilet bayan an bashi bai hadiye ba, yana zuwa toilet ya boye a wandonshi, I quickly ask him su sunsha, nan ya shaida min sunsha suka haukace after few hours don gaba daya daga zuwansu bayan an aje su a daki aka basu,
Da sauri Amar yace
 Zaka iya tuna lokacin da aka kawo su da lokacin da aka bama yaran kwayar

Shuru Hammam yayi kafin yace  yea about 5hours
 Damnnnn Amar ya bugi table da yasa asad saurin dagowa, ganin yanda idanunshi sukayi jaaa Har jiniyoyin wuyanshi na futowa yasa asad bude fridge din gefenshi ya zaro ruwa ya bashi, yana karba ya balle murfin ya kafa a baki ya mashi kwankwada daya ya shanye tasa kafin ya wurga bottle din ya cigaba ta cewa
 Dude send me the picture of the drug,I just need to confirm it, and also I need the picture of the boy, and some of his information tunda kace dan nigeria ne
 Okay dude hamman ya bashi amsa daga chan bangaren
Cikin qanqanin lokaci kuwa saiga hoton drugs din harda hoton yaron ta email, yana budewa ya bugi table din yace  ka gani ko, those bastards,I will Make sure they pay all they have been doing
Da kyar asad ya tausasa shi don ran maza yayi mugun baci saida yadan dawo daidai kafin ya sake Kiran hammam don wayan ya yanke, yana dagawa kuwa ya fara bashi command don gaba daya ya rikide ya juye ya koma asalin general. Babu fara a a kausashe ya soma magana da karfi
 officer Hammam shuraim
Jin haka yasa Hammam saurin cewa  yes sir, officer Hammam on the line waiting for your Command!!!!!!!
 I command you, with your power to investigate throughly on alif shuraim, don t leave even his finger tip during this investigation,most importantly I need his private account, that will be the link of his business, I want to crush every single one of them
 Yes sir!!!!!
Kashe wayan yayi Yana fudda nunfashi mai zafi,
 Calm down oga asad ya fada yana kallonshi
Mugun kallo ya zabgawa asad  how can I calm down Ana wannan ta addancin huh, yanxu dai tunda Mun gano link din kwayar da trafficking da akeyi, abu na gaba inason kayi min bincike akan wannan mutumin ya karashe yana nunama asad wayarshi dagowa asad yayi ya kalli hoton da yake nuna mashi,  wannan ne Alhaji Mustapha, inason na tabbatar idan yana cikinsu, cos yaronshi na hannunmu yanxu kusan sati biyu kenan, he s under investigation, yaso fita da kwayar daga Nigeria zuwaga Egypt saidai kasan saiyayi transit a dubai so anan aka kamashi, dalilin dayasa na gano Akwai hannun Nigeria a cikin case din kenan.
 Okay ba damuwa ka turamin hotonshi gobe zakaji bayani, asad ya fada fuskanshi seriously

Runtse idanu Amar yayi kafin ya bude idanunshi yace  Akwai wani dan Iskan danshi wahab, ko me zakayi kayi inason na ganshi anan nigeria, I have to deal with him for trying to touch what doesn t belong to him, I will make sure he never use what he tries to use to rap& .
Shuru ya danyi ganin yanda asad ya kura mashi idanu yanason Karin bayani, fuzgewa yayi yace  I will forward hoton wannan 17 year old yaron, check his profile a cikin data base dinku zuwa ga gobe Sai muje wajen iyayen shi don muji when last suka ganshi
Bai samu futowa daga wajen asad ba Sai wajen karfe goma na dare, gaba daya ya gama chanzawa rana daya ya dauko zafi sosai, don mutun ne shi mai kishin kasar sa da defending kasarsa akoda yaushe, yawanci akan ce masu zuwa suna serving wata kasar basa kishin tasu, shi dai yana cikin masu protecting kasarshi da kuma ganin ta samu cigaba.


Hammam& .
Tun bayan wayanshi da Amar ya cigaba da harkokinshi kamar koda yaushe, don shima yasan aikinda zaiyi Akwai risk a ciki don yana tare da mugayen ne baki daya, kullum yakan zuwa wajen mahaifiyarshi wadda ke Kara karfafa mashi akan ya kasance me adalci da yin aikin daya dace, yawanci da safe yake zuwa ganinta kafin ya wuce aiki saidaga baya ya sauya akalar zuwan nashi sbd Akwai ranar da alif ya zo don dubata ko tana cikin haukan don kwayar tana iya sakin mutane after few years,Allah ya taimaka yana fitowa daga cikin old age house din ya boye don Shiya fara ganin alif din yana shirin shugo wa saura kiris alif ya ganshi ya kubce mashi, tun daga wannan lokaci ya rage zuwa da safe, Sai idan dare yayi yake samun zuwa ganinta,magungunanta kuwa gudun Kar alif yayi bribing wasu daga cikin ma aikata don a dunga bata kwayar ba tare da saninta ba yasa ya hanata shan ko wane irin magani tunda lafiyar ta garau.

Aiki hammam ya soma yi underground yanda babu wanda zai ganoshi musamman mutanen alif dake tare dashi, bayan wannan Ma yana samun nasarar samun abunda yake bincike akai sbd idan ya nema dalilin saninshi da akayi a matsayin alif babu wanda ke kawo komai ko tunanin zai ci amanar alif, yasha wahala sosai wajen shawo kan daya daga cikin masu managing secret account din alif, wanda saida yayi abusing power dinshi ya samu gayen zai bashi duk information da transaction dake gudana a cikin account din alif wanda babu wanda yasan da account din Sai top management na bank din, shima gayen yana daya daga cikin maaikata dake karkashin tops din, da farko gayen ya buqaci maqudan kudade don yasan idan gaskia ta fito za a koreshi don haka Hammam yayi sorting dinshi don shima yana da kudade da yawa wanda yake samu daga babanshi dalilin ayyukan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login