Showing 189001 words to 192000 words out of 381117 words

Chapter 64 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2022

a cikin bathroom kafin ya futo, baimabi takan gadon ba ya fuce daga bedroom din gaba daya zuwa sitting room yana tunanin yanda zai raba kanshi da ita gaba daya ba tare da ammah tayi fushi ba.

A zaune ya kwana Har aka kira sallan asuba, wanda barci da yayi ma gaba daya baifi na awa daya ba a zaune, mikewa yayi jiki a mace ya wuce bedroom din, as he expected bata Tashi ba, bai tsaya kallon inda take ba don karya ganoma ma kanshi ya wuce bathroom kai tsaye ya dauro alwala, yana fitowa ya saka jallabiyan shi ya fuce daga dakin gaba daya zuwa masjid.

Koda ya dawo daga masallaci kaya kawai ya sauya zuwa gym wears,wayarshi ya janyo dake gefen bedside kanshi a gefe ya fuce daga dakin.

Anan cikin estate din ya wuce sashen gym da aka bude a cikin estate ga wanda ke shaawar workout, yana shiga ciki kuwa cikin girmamawa couch s din cikin gym din suka gaishesa sanin shi a matsayin me estate din gaba daya.
Don kowa yaga live broadcast announcementda yayi akan taura company, inda ya bayyanar da matsayinshi na da ga Alhaji Yunus Taura, kuma magajin tauraCom gaba daya.

Amra kuwa saida tasha barcin ta ta koshi kafin ta Tashi, ganin baya dakin yasa ta fuce daga dakin gaba daya zuwa nata, tana mamakin wannan yawan barci da take yi hartana mising sallah.

Shiko goga sai wajen karfe takwas ya shigo gida, anan kasa ya tadda ammah, anatse ya tako Har Ind a take ya gaisheta kafin ya wuce bedroom dinshi.
Karfe Tara kowa ya hallara a dining Banda amra, ammah na Ganin haka ta tura Salim ya dubota,a kwance ya taddata tana barcin ta hankali kwance don tayi wanka harta sauya kaya, tashinta ya soma yi suka sauko kasa atare.
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!
Unedited page
Doguwar rigace a jikinta ta atamfa free gown sai dankwalin atamfar dake rike a hannunta, gashinta duk ya bazo har kan kafadarta, fuskanta fayau tayi wani irin kyau sosai anatse ta karso har dining din ta gaisheda ammah kafin tabi kowa da kallo, aman ta fara gaishewar kafin ta maida dubanta ga amar daya hade rai tamm kamar zai fashe, kauda kanta tayi ta karaso gefen da yake zaune ta janyo kujera ta zauna, saida ta zauna ta dan dago suka hada idanu, wani irin kallo ya watsa mata mai wuyar fassara,saurin kauda kanta tayi daga wajenshi,jiki a mace tace   ina kwana  
  lafiya  ya amsa ta atakaice saboda ammah na zaune, tabe baki kawai amra tayi janyo plate zata diba abunci, dan dagowa yayi ya faki idanun ammah cikin sauri ya buge hannunta, dan dagowa tayi ta zuba mashi shanyayyun idanunta tana mamakin abunda yayi, rai adan bace ya soma maggana kasa kasa yanda babu wanda zai jisu,   cover your hair  tana jin haka tayi saurin taba gashinta, sai a lokacin ta lura kanta a bude yake, mamakin yanda ta manta bata daura dankwalin ba tayi, nan take taji kunya ta lullubeta don ahaka ta sauko kasan, cikin hanzari ta daura dankwalin ta rufe kanta dashi, samun kanta tayi da kasa motsawa saida ammah tace   daughter bazakici ba? Ko kina buqatan wani abun daban? 
Da hanzari ta dago ta kalli ammah cikin kunya tace   no ammah, zanci 
Har amma ta mike ta fuce daga dining din bata diba abuncinba, haka duk suka fara fucewa daga dining din daya bayan daya,ya rage daga ita shi a zaune, dukda shima y agama hakan baisa ya miqe ba haka zalika inda take zaune ma bi kalla ba saida kowa ya watse ya dago ya kalleta babu fara a afuskanshi yace   this should be the last time zaki dunga yawo babu cover, understood?  ya karashe yana kallonta, dan waigowa tayi ta zuba mashi idanun nan nata kafin ta dan murmusa ta sauke kanta kasa tace   in sha allah baza a sake ba, wannan ma tsautsayi ne bansan na futo haka dinba,  kallonta yayi ganin yanda ta sauke kanta da yanda take magana calmly in a respectful manner sai ya bashi mamaki chan kuma yaji wani iri, yar tsuka yayi ya miqe tsaye ya fuce daga dining din.
Yana fucewa tabi bayanshi da kallo, haka kawai yau ta tashi with emotional mood, yana fucewa ta afshe da kuka, ita kanta bazatace ga abunda ke damunta ba ko ga abunda akayi mata, kawai dai shes not feeling her self, abuncin ma bata kalli inda yake ba ta miqe ta wuce sama tana hawaye.
?
Ammah na komawa daki ta zauna bakin gado ta jawo wasu papers, kallon takardar ta farayi hawaye na zubuwa akan fuskanta,abunda ke kunshe cikin papers din yarjejeniya ce da tayi sighning da hannunta na transfer din property din amar zuwaga alhaji kabiru, tunani ta soma yi tana hawaye wannan ne first threat da manipulation da alhaji kabiru ya fara yi mata bayan mutuwar dada, inda aranar ne ta ga asalin intention dinshi na karbar company da yayi asunan zaija ragamar company din, duk sanda ta dauka papers dinnan saitayi hawaye,dukda yanxu ta samu kwanciyar hankali da aka kama daddy but hakan baisa hankalinta ya kwanta dashi ba kwata kwata don ita ta fara gano cewa shi ya kashe dada, dukda ta boye ma amar saboda tsoron abunda zaije ya biyo baya dalilin hakan tayi sighing yarjejeniyar saboda daddy yayi threatning dinta akan idan har bata bashi komai ba zai kashe amar ta hanyar daya kashe dada, tayi kuka sosai lokacin data gano dady nada sa hannu a kisan dada don tunwa da wannan kadai ma yakesa ta samun heart attack,bayan wannan tunanin aman ya fado mata, bazata taba manta lokacin da mahaifiyarshi ta bar mata wasika ba kafun allah ya dauki ranta inda take ce mata   maryama, akwai masifa da ukuba a cikin zuriar nan, wanda na kasa hana ta yin tasiri a cikin family nan, bazan ce maki komai ba don nasan mutuwa zanyi, saidai nasan koba yauba allah zai kawo ranar da allah zai bayyanar da komai, ga yayanmu nan ki kula dasu, sannan a karshe ina rokon alfarma a gurinki yar uwa, don allah ki kula min da aman, dan allah ki jashi a jikinki karki bari yabi sahun mahaifinshi, bazan iya fada maki komai ayanxu ba amma zaki gane komai nan da yan shekaru agaba, 
Tun bayan mutuwarta cikin ikon allah abubuwa suka fara bayyanar ma ammah cikin ruwan sanyi wanda daga karshe bata da option daya rage mata don tayi protecting yayanta sai auren dady,inda shi da kanshi ya buqaci hakan, da farko tayi mamakin sai daga baya ta fahimci kudirinshi nayi hakan don ya karbi company da duk dukiyar da dada yabar masu, da farko dataqi yarda saiya nuna mata asalin kudirinshi akan inhar bata yarda tayi sighimg wannan papers dinba zaiyi abunda zaisa properties din su dawo hannunshi cikin ruwan wanda hakan na nufin zai kashe amar.
Sanin yanada hannu a kisan dada yasa hankalinta ya tashi don tabbas zai iyayin komai don haka ta amunce da buqatarshi harta aureshi, a wannan lokacin tayi kuka sosai babu wanda take tausayama kamar Amar don jin wannan zancen zaiyi shattering dinshi idan yaji labarin cewa daddy nada da hannu a kisan dada, don haka Tayi alkwarin bazata taba bari ya sani ba don abun zaiyi breaking dinshi sosai wanda bazata so ta ganshi cikin damuwa ba.
?
Baiwar allah abunda bata sani ba shine wannan papers din forging dinsu daddy yayi ba sune asalin real document dinba don babu wanda yasan inda asalin paper record of the property s din yake ba harshima don koda yazo kashe dada saida yayi threating dinshi akan ya bashi real paper record din ko yanda zai kasheshi haka zai kashe amar, saidai allah bai bashi ikon samun hakan ba saboda atake dada ya mutu, alhaji kabiru kuwa yayi takaici sosai don saida ya aiwatar da kudirinsa na kashe dada saboda ya gano sirrinsa ya tuna da property record din.
Saurin share hawayen fuskanta tayi bayan ta gama tunanin, anatse ta janyo locker da take aje duk wani important document ta aje aciki ta rufe.
Anatse ta mike tsaye don dauro alwala, nan take taji jiri na dibanta, ahankali ta furta   ya salam 
Da sauri tayi baya ta zauna ta dafe kanta don gaba daya kanta juyawa ya soma yi, wasa wasa bayan jiri ta soma jin throat dinta Nayin zafi sosai, wanda hakan yasa ta danyi coughing next thing saiga gudan jini ,abunda yafi tayar mata da hankali shine abunda yabiyo tarin, kallon hannunta tayi hankali atashe ta furta   subhanallah jini kuma
Wasu irin hawaye ne ke zubowa a fuskanta babu dalili saidai tabbas tasan something is definitely going on, anaste ta soma karanto innalillahi ta yago tissue dake gefen bedside dinta ta dauki gudan jinin ta nade shi cikin tissues din, tunani ta soma yi yanda cikin kwanakin yake samun changes a jikinta wanda hakan ke bata mamaki dukda doctor ya shaida mata effect din magungunan ta ne, wanda for the mean time zata samu changes daga baya kuma zaizo ya bari idan maganin ya kare, gaba daya she s not convinced with maganar doctor don abun gaba yake yi don haka Tayi saurin janyo wayarta ta soma dialing number family doc din,yana picking suka gaisa.
Tun kafin ta soma mashi bayani ya soma magana  hajiya yau ma Akwai wani chances din ne?
Tayi mamaki dajin kalamanshi don abun sounds like kamar yasan dalilin kiranshi datayi kenan, bata kawo komai aranta ba don haka tace  oh doctor harkasan complain zanyi maka kenan, anyway gaskia inaga zanzo asibitin don nayi checkup, don naga abubuwan na Kara gaba sosai, anya baza a sauya wasu magungunan ba da alamu dai wannan basu karbeni ba ta karashe tana murmushi.

Dariya ya danyi yace  Akwai wasu chances dinne bayan wanda kika fada kwanaki hajiya?
 Eh yau na Tashi da jiri, sai kuma tari da jini
Shuru ya danyi kafin yace  okay bayan tari da jiri Akwai ciwon kirji?
Ya tambayeta kai tsaye
 No gaskia babu Ay rabon da nayi ciwon kirji harna manta likita ta bashi amsa
 wannan ma yana nuna alamun Akwai ci gaba kuma maganin yana aiki saidai Ina Ganin kamar yayi maki karfi ne shiyasa kike jin jiri, amma za a iya chanza maki wasu suma dai babu guaranteed don kowani magani yana da effect substance da yake chanza organism, don wannan da na baki shine mai sauki sosai wanda bashida side effect and Duk wannan symptoms din normal ne ga masu ciwon zuciya with time zai daina
Ammah najin haka tace  Toh shiknan doc ba damuwa Zan cigaba da wannan din, kasan girma idan yazo sai ah hankali ta karashe tana murmusa daga bisani kuma tayi mashi godiya ta kashe wayar.

Wunin ranar ammah a kwance tayishi don tana miqewa sai jiri, koda su amra sukazo dubata jin shuru nan ta shaida masu da ciwon kai ta wuni.
Amar ma koda ya hauro sama don ya dubata shima boye mashi tayi saboda tasan yanda zai tada hankalinshi don haka ta shaida mashi ciwon kai ne kawai ya dan rike ta, shima saida yayi mata sannu kafin ya wuce kasa zuwa part dinshi.

Tun bayan daya dawo daga dakin ammah wanka kawai yayi ya sauya kaya zuwa pjs dinshi ya zauna kan gado tare da jawo laptop dinshi ya soma yin wasu ayyukan, daman evidence ne yake tartarawa gaba daya akan mks empire da wanda dada ya tura mashi da wanda ya samu shima.
Tunda ya kafa ma screen din laptop dinshi idanu ya kasa daukewa yana kallon property report dinda dada ya tura mashi cikin encrypted portal, gaba daya properties din taura sunanshi ne a jiki as the heir, haryau mamakin date din da dada yayi handing over Duk properties din yakeyi don if he can recall alokacin yana makaranta ne ko university bai gama ba,  Toh kodai tun lokacin dada ya gano sirrin daddy ne? Ya tambayi kanshi.
Ganin babu mai bashi amsa yasa ya rufe laptop din ya dubi time da agogon na rolex, almost past twelve, dan waigawa ya soma yi yana mamakin rashin zuwan ta dakin, tabe baki kawai yayi don she hakan ma yayi mashi, don he needs break from her new behaviour wanda ke sakashi yin abubuwan da ya kasa gane kanshi.
Saida ya kwanta ya janyo duvet yayi addaua ya rufe idanunshi, forcefully yake son yin barci saidai tunanin da yake hana kanshi yi yagama shiga ranshi, he keeps thinking of her, tambayar kanshi kawai yake yi meysa bata zo ba? Kodai she s sick ne? Ya tambayi kanshi, da sauri ya miqe zaune zumbur ya zauna ya dafe kanshi,  goddd why do I care ya karashe yana yar tsuka kafin ya kwanta, ko second biyu baiyi ba ya sake Tashi gama daya he s anxious, haka nan ya Tashi ya saka bathroom sleeper dinshi ya fuce daga dakin, sama ya wuce direct kamar Ana ingiza shi Har zuwa dakinta, saida ya dan tsaya yana nazari kamar ya shiga kamar karya shiga, karshe dai haka ya batse ya tura kanshi cikin dakin ba tare da yayi knocking ba, a zaune ya tadda daga ita sai singlet da shorts akan gado, ta aje dry cereal a gabanta tana ci,dan waigawa tayi tana jin alamun bude kofa, da mamaki ta kura mashi idanu don kwata kwata batayi expecting dinshi ba, shima idanun ya zuba mata Har ya shigo dakin dan nesa da ita yana mamakin Anya wannan yarinyar kalau take kuwa?,
Kallonshi amra tayi Ganin yanda ya Tamke fuska kamar bai taba fara a ba don haka tace  laa
Bakayi barci ba yaaya
Shuru yayi yana mamakin yanda yanzu ko irin fargabar da take yi idan zatayi mashi magana batayi, ayanxu yanda yake magana dashi sshe s talking casually.
Haka ya dunga binta da idanu baice mata Kala ba Har saida ta mike tsaye ta karaso gabanshi ko kunyanshi bata jiba, tace  kana buqatan wani abu ne? ta karashe tana mashi Farr da idanu, da ido ya dunga bin ta da kallo tundaga tsakiyan kanta don gaba daya bata da wani tsayi sosai a gabanshi zuwa cinyoyinta, cikin sauri ya kauda kanshi gefe yace  bring me coffee
Yana kaiwa nan ya fuce cikin kamewa, da idanu tabi bayanshi da kallo har ya fuce mata daga gani.
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited page
Wani irin jiri ne ya soma dibanshi ganin yanda jini kebin fuskan ammah ta baki ta hanci, idanunshi sunyi jaa suna neman kawo ruwa, thie is the most painful day of his life, ammah is his life entirely, he cant take it idan abu ya sameta don shes his everything, itace rayuwar shi gaba daya.
Jikinshi na kyarma ya tallabo kanta, bakinsa na karkarwa ya kasa motsawa gaba daya, hannunshi na karkarwa ya soma jijjiga ta,   am..mah..ammahh& innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ammah please wake up, ammah karki tafi ki barni yanda dada ya tafiya, ammah plaes  gaba daya y agama rikidewa ya chanza kamar ba general ba, amra dake gefenshi dasu salima babu abunda sukeyi sai kuka, tun yana Magana ahankali harya soma ihu idanunshi yayi jaaa, kana ganinshi kasan an tabo weak point dinshi  somebody should fucking call the ambulance 
Cikin sauri aman ya miqe tsaye ya wuce cikin gida ya domin ya dauko car keys dinshi, yana gudu yana tuntube harya shige dakinsa agigice ya dauko car keys.
Yana futowa motar karar motar ambulance ta karade anguwar hade da motocin su asad, cikin sauri securities suka bude gate, nan take suka fara shigowa aguje, motar ambulance din na parking emergency health team suka fito da gadon marasa lafiya daga motar, shima asad sunayin parking suka sauko shida yaransa kowannen su hannunshi dauke da bindigu,
Aguje suka firfitowa gaba dayan su sukayo kan lantana dake ayashe kamar babu rai, haka suka dibeta kamar wulaqantattun kayan wanki suka watsa a cikin mota, ammah ma dakyar aka banbareta daga hannun amar don gaba daya ya susuce don gani yake kamar ana rabata da jikinshi mutuwa zatayi,dakyar aka samu asad ya dagashi suka samu akasa ammah a cikin mota.
Aman na ganin haka ya fiddo da tashi motar shima, janyo amar asad yayi ya turashi cikin motar aman din, baima lura dasu salima da amra ba da suke tsaye, saida suka shige motar amra tace   dan allah ku tafi damu ya aman 
Wata uwar kara amar ya yi ya kalli aman yace   give me the car keys  da kyar asad ya karaso inda yake yace   oga bazaka iya tuki a wannan condition dinba ka bari shi tuka.
Kallonsu amra asad yayi yace   ku shiga 
Shigewa sukayi gaba dayansu bayan motar cikin gaggawa kafin aman yabi bayan motar ambulance din da matsiyacin gudu har saida suka kamo motar ambulance din, har suka karaso cikin asibitin amar dai tunda ya zauna cikin motar ya dafe kanshi hankali atashe, suna isowa ko parking aman bai gama yiba amar ya futo daga motar acikin hanzari ya shige cikin asibitin don already an shiga da ammah, hankali atashe aman yayi parking ya bude motar duk suka fito duk hankalinsu atashe, bin bayanshi duk sukayi kowannen su hankali atashe.
Yana shiga cikin emergency ward din ya wuce wajen emergency room da gudu, yana zuwa daidai kofar ya tsaya saboda family doctor su daya fito daga cikin ward din a hargitse, amar na ganinshi yayi saurin karasowa gabanshi cikin fada yace   whats going on aciki? Hows ammah? 
Yanda ya zubama doctor idanu haka shima ya zuba mashi jiki na bari ya kasa cewa komai, kana ganinshi kaga mara gaskia, amar na ganin haka ya daka mashi tsawa   don t just fucking shut your mouth,Talk to me whats going on there meyya samu mahaifita 
Saurin tattara natsuwa doctor yayi ya kalleshi yace   we are trying our best don mu gano meke damunta, excuse me 
Yana fadin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login