Showing 33001 words to 36000 words out of 381117 words

Chapter 12 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1965

kowanne brand daban daban janyo wani lavender gel tayi ta fara murzawa ajikinta, ahankli ta lallaba ta gama wankan sannan ta wanke mashi wajen data bata tass,neman abun da zata daura ta farayi kafin idanunta suka sauka kan towels dinshi wanda suke ajere jikin hanger kusan guda biyar, kawar da idanunta tayi daga wajen ta maida rigar ta sannan ta futo, fucewa tayi daga dakin gudun karma tayi wani abun da zai jawo mata Magana.
Ahankali ta koma parlor ta bude kayan da haifa ta hado mata wanda suka sayo,budde box din tayi ta samu wata decent English gown mai kyau ta saka sannan ta samu waje ta zauna ta rabka uban tagumi, wayarta dake gefe ta jawo charging ma ya kusa sauka, duba location din da take tayi sannan ta shiga 24 hour online shop tayi ordern pads da sabbin toothbrush harda maganin pain killer, zaman kusan awa guda tayi kafin ordern ya iso,kafin ta tashi ta bude kofan don ganin house number na gidan kafin ta fada ma delivery man din, bayan yan mintuna kadan sakonta ya iso, koda ta bude kofan anan gaban kofanta taga delivery din, anatse ta jawo box din ta bude, ta fiddo komai ta koma dakin nashi, toilet din ta koma sannan ta sauya pants dinta wanda yagama baci sosai, tana gama kimtsawa ta gyara mashi toilet din ta fito, zama tayi a parlor ta sha maganin, nan take bacci yayi awon gaba da ita.
Amar kuwa yana fita ya wuce penthouse dinshi, yana sauka ya wuce cikin main entrance din, kamar kullum gidan yana nan fess fes sanin shi ma abocin tsafta ne yasa Pablo ke qoqari sosai wajen gyara ko ina,wajen dining ya wuce don wata yunwa ce ta ciyo shi sosai,kujera ya ja ta luxury dining set chairs din ya zauna, fitowa Pablo yayi hannunshi dauke da wasu tsadaddun warmers masu kyan gaske, ganin oganshi yasa ya sara mashi sannan ya fara serving dinshi abinci, saida ya gama tsaf ya zuba mashi coconut drink mai sanyi sannan ya koma wajen aikin sa, anatse ya soma cin abinci, kusan rabi yaci don bai samu yayi dinner ba ya kwanta kwanan jiya, anatse yake cin abinci kamar wanda baison ci, saida ya gama ya jawo savage ya goge bakinshi kafin ya miqe ya wuce lift, yana shiga yayi resting kanshi ya danna floor din part dinshi, sama ya wuce bedroom dinshi, yana shiga nanma fessfess sai kamshin freshners mai dadi,gaban light switch ya karasa ya maida light din dakin zuwa dim, kwata kwata kwanakin ya rasa mey zaiyi tunda suka samu hutu karshen shekaran nan, anatse ya wuce closet ya chanza kayanshi zuwa masu sauqi, dan short ne da farar armless top,yana gamawa ya dawo ya zauna gefen gadonshi ya dafe kanshi, duk wannan abin auren yana tariyowa akanshi, yanxu shi aure yayi bada sanin Ammah ba dukda auren ba wai auren dindin din bane, amma dai still aure baa bin wasa bane don yana da ilimi, amma bayajin zai iya fada ma ammah dalilin yin haka, sbd bazata taba jin dadin yin aurenshi ta wannan hanyar ba. Dafe kanshi yayi wanda ya soma mashi zafi, sai yau tunanin dada yake dawo mashi kanshi   amar ka kula min da Amman ka, komai ka gani arayuwar nan yana da dalili, ciki kuwa harda mu gaba daya, duk wandaka ganshi haka, ba haka allah ya barshi ba, kayi kokari ka zama mutun na gari, mai tausayin alumma, ka zama gatan marayu karka bari ayi rashin adalci agaban idonka.  & dago kanshi yayi yana kallon sama, idanunshi sunyi jaa sosai, ahankali ya kwanta bacci yayi awon gaba dashi.
Amra kuwa bacci ne sosai ya dauke ta sai wajen asr ta farka, shima wata masifaffiyar yunwa ce ta farkar da ita, ahankali ta tashi ta koma dakin ta sake wani wankan ta futo, sai alokacin tayi ma toilet din kallo mai kyau, komai fes fess kamar ba a taba amfani da wajen ba,kana ganin designer towels dinshi zaka san yana da bala in tsafta da gayu, futowa tayi sannan ta tsaya tsakiyan dakin, dagakan gadon zuwa couch din dakin zuwa ga bedings din tabi da kallo, ahankali ta furta   masha Allah  ..murmushi ne ya kubuce mata, arayuwar ta tana kaunar taga komai organise kuma mai kyau, haka yasa ta shagala sosai wajen kallon ko in ganin kamar gadonshi yana buqatar gyara yasa ta karaso gaban gadon, ta gyara shimfidar, wani irin kamshi ne ke tashi mai sanyaya zuciya, saida ta gama tukunna ta futo ta koma parlor, kayanta ta kuma sauyawa zuwa masu sauqi, zama tayi ta lalubo wayanta ta soma yin ordern abinci, pasta tayi order aka kawo mata taci sannan ta kwanta tana tunanin rayuwa da su salima.
?
Dare nayi wani irin tsoro ya dirara mata, kwanan gidan da bata tabayi ba babu mutane, afurgice ta miqe ta fara zarya, jawo wayarta tayi ganin charging ya sauka sosai yasa wasu siraran hawaye suka fara yi mata zarya, tama rasa yanda zatayi, tunanin kodai ta koma gida ne ya fado mata, ganin har wajen karfe goma yasa ta yanke shawarar tafiya kawai, ahankali ta jawo wayanta ta soma requesting mota, bata kaiga gamawa ba wayan yamutu dipp, kuka ne kawai ya kubce mata, yanxu dai bata jin yinwa amma ya zatayi idan wani abu ya faru da ita, ahankali ta koma ta zauna, har wajen karfe sha biyu idonta kwal babu mai gidan babu motsi ko kadan, tsoro ne ya dirar mata, tabbas lokacin da take apartment dinta ita kadaice amma yanxu ta rasa dalilin da yasa take jin tsoron nan, ko motsin mutane ba a ji, ganin babu sarki sai allah yasa kawai ta samu waje ta kwanta nan kan couch din har bacci ya kwasheta.
Amar kuwa bai tashi ba shima sai gab da sallar magrib, yana tashi ya wuce toulet ya dauro alwala sannan yayi sallah yana idarwa ya jawo laptop dinshi ya fara aiki, bashine ya aje laptop dinshi ba sai wajen karfe daya, anatse ya tashi ya aje laptop din ya jawo landline din dakisnhi yayi dialing wasu numbers, Pablo yana daga wa yace yes sir, lumshe kyawawan idonshi yayi wanda lashes din sukayi zara zara sannan yace   bring me coffee  ..aje landline din yayi, bayan yan mintuna pablo yayi knocking, kamar bazaiyi magana ba yace   come in  & anatse Pablo ya shugo ya aje mashi gaban side stools dake kusa da couch din bedroom din parlorsannan ya fuce.
?
Ahankali ya sauko ya ya zauna kan couch din, tunani iri iri aranshi, yanxu damuwan shi daya yanda zaiyi ya kawo karshen wannan empire din, sannan abinciken da yake akwai mutane da dama dake son ganin bayanshi dukda shi wannan ba matsalar shi bace he has ways of saving him self amma mutane fa da yayi swearing saiyayi protecting dinsu, sipping coffee din yayi, gaba daya ranshi adagule yake, ajewa kawai yayi ya wuce toilet don ya watsa ruwa, bayan ya futa pjs dinshi ya sauya sannan ya kwanta. 73-74
The next morning&
Amra kuwa bata tashi ba sai wajen karfe goma, anatse ta tashi tana bude kyawawan idanunta kafin tayi adduar Tashi daga barci ta mike gaba daya ta wuce cikin bedroom din,sadaf sadaf ta bude kofan don duk a tunaninta ya dawo tana bacci, batayi gangancin kunna light din dakin ba ta wuce bathroom, agaggauceta fara yin brush, kafin ta zame kayan jikinta ta fara wanka, anatse ta fito daga shower sannan ta jawo rigarta ta maida tsayawa tayi ta soma bin bathroom din da kallo, very clean fess fess kamar ka zuba abinci akasan kaci, ga wajen wc din ma abin kallo ne, da wash hand basin din, yanda ya jera kayan wankanshi gwanin burgewa, yauma bata taba komai nashi ba in banda shower gels dinshi, anatse ta futo sannan ta sulale ta bude kofan dakin ta fuce, tana karasowa sitting room ta janyo boxes dinta tare da budewa, wajen bras da pants ta bude ta zaro wata hadadden cup bra da pant masu shegen kyau ga laushi, kana gani kasan masu quality ne da kudi sosai, ajewa tayi agefe sannan ta bude wajen mayuka ta dauko wanda zata fara amfani dashi dasu perfumes da body sprays, anatse ta fara shafawa tana karema sauran kayan kallo, saida ta gama sannan ta bude na kaya, wata abaya ta jawo mai kyau sosai hade da veil dinta purple color,cikin natsuwa ta shirya ta rufe boxes din ta janye su gefe, zama tayi don tunanin yanda zatayi gashi yunwa ya fara damunta, ga wayanta ya mutu bare tayi order, anatse ta tashi ta taka Har wajen kitchen, ko ina tsaf tsaf kamar ba a taba amfani dashi ba, karema wajen kallo tayi sosai , dan kitchen ne daidai mutun daya, babu wani girma sosai, babban gas plate ne awajen sai dishes washer sai microwave da oven a hade cikin yar cupboard sai fridge freezer a hade shima babba sosai wanda har yaso ya wuce tsayinta, daga gefe kuwa wani sako ne da manya manyan shelves na pantries, anatse ta shiga, babu wani kayan girki na kirki,rasa abunyi tayi ta fara duba ko ina ganin madara da hot chocolate da cereal yasa tayi saurin jawosu, harda zuma, kitchen ta koma ta fara duban cups, bude upper drawer ta fara yi ta dakko katon bowl da spoon, saida ta wanke kafin ta aje akan island sannan ta zuba madara yanda zai isheta da zuma da dan ruwa, gaba daya pack din cereal din ta kinkimo ta dawo kujera ta zauna ta fara hadawa, hannu baka hannu kwarya ta dunga turawa dake yunwa ta ciyota dayawa sai ya mata dadi sosai, dakyar ta shanye donta hada da yawa sosai, anatse ta miqe ta wanke bowl da spoon din sannan ta maida sauran ceareal din da madaran kafin ta dawo parlor ta rabka uban tagumi, gashi babu cash ajikinta da saita tafi gida kawai, ganin kuma hakan bai daceba idan tabar mashi gida abude yasa kawai ta zauna tana tunani kala kala har wani baccin wahala ya dauketa anan zaune.
?
Dai dai karfe uku na rana karar bell ya tada ta daga bacci, afurgice ta miqe don duk tunaninta mai gidan ne ya dawo, ahankali ta karasa gaban door din ta fara kokarin budewa, dake kofar is smart ajikin screen din gaban holder din taga wanda yake knocking, da sauri ta bude taja da baya kadan, da sauri haifa ta gifta gaban hammam ta shugo tana rungume amra tace   babeeee nayi missing dinky, amarya how are you my dear?  rungumeta tsaf amra tayi tana murnar ganinta, hammam kuwa kallo daya ya musu ya wuce ciki zuwa bedroom, bude kofar dakin yayi ganin wayam yasa ya tsaya ko zaiji saukan ruwa jin shuru yasa yayi saurin futowa yace   baya gidan ne?  sai alokacin amra ta kalleshi tace   good afternoon   ..jin haka ya sashi yi mata murmushi ya sake tambayan dazu , shuru ta danyi tana nazari kafin tace,   yau 2days baya gidan  ..jin haka yasa hammam saurin cewa   whatt ke kadai kike kwana anan?, abinci fah?  duk atare ya jero mata tambayoyin, batako kalleshi ba tace   inashan cereal ay, and besides badan wayana yamutu ba da dashi nake order,  & shuru kawai yayi sannan ya kalli haifa yace   babezz bari na danje wani wuri zan dawo bada jimawa ba na dauke ki, yana kaiwa nan ya barsu zaune kan couch ya fuce.
Juyowa haifa tayi sannan tace   kai wallahi wannan mutumin anyi baudadden mutun, wai maima yake nufi kamar ba taimake ni in taimakeka bane wannan yarjejeniyar, I just hate mutun mai yawan ego,  ..tana kaiwa nan ta miqe tace   bari naga gidan naku best girl  ..zagayawa sukayi ko ina kafin su dan gyagyara ko ina, daman gidan ba wani datti yayi ba.
Kallon haifa amra tayi sannan tace,  babe muje gidana mana kafin hammam din naki ya dawo, inason daukan abubuwan buqatu na  ..jin haka yasa haifa cewa to muje saidai kinsan bansan password din gidan ba but I will text hammam yanxu sai muje mu dawo kafin ya dawo. Atare suka futo daga gidan, sai yanxu amra ke ganin kyan wajen, wato apartment ne duk yawanku zai iya occupying dinku, don akwai apartment din room biyar, da mai room uku, daidai yanda kake so, anatse suka sauka ride din da haifa tayi requesting ya karaso, saida sukaje gidan amra suka kwaso kayan amfaninta sosai, wanda daga charger sai yan mayukanta da wasu kayan sawa sannan suka fito saida suka tsaya suka saya pizza da burger da Oreo smothies sannan suka kama hanyan dawowa wajen karfe 7 na dare.
?
Hammam kuwa Yana futowa ya wuce penthouse din Amar yana zuwa gidan ya wuce dakinsa direct, nan ya tadda amar kwance ,tashinsa ya soma yi yace   dude wake up tashi akwai wani aiki da zamuyi a headquarters yanxu
Tsaki kawai Amar yayi don Hammam ne kawai ke iya yi mashi hakan don baya son Ana interrupting barcin sa, baice mashi komai ba ya mike zuwa bathroom saida amar yayi wanka ya shirya hammam na zauna na jiranshi kafin suka fito atare, nan yasa m-5 ya buyoshi da motorn shi don zasuyi partings ways da hammam idan sun gama da headquarters, ajere motocin suka tsaya acikin parking space na headquater, anatse suka futo gwanin burgewa, amar na sanye da jellabiya white kundura shima dai hammam casual dressing dinne jikinshi, ciki suka shiga wanda yawancin mutanen wajen yan apartment din dake cikin hedquaters ne wanda suke zaune da iyalansu ko su kadai, ciki suka shige inda ake private meeting na manya manyan seniors officers, zama amar yayi suka fara introduction akan private meeting din wanda is professionally private kusan awa uku suna cikin meeting sai wajen karfe biyar suka fito suna fitowa hammam yace   inason magana dakai amar, ko zamuje office dinka  anatse amar yayi leading hanya har suka isa office din amar, zama suka yi a kujerun guest kafin hammam yayi gyaran murya yace   amar I thought you re matured enough but as for now I don t see that anymore, what s wrong with you ne dude?, munyi maganar nan ba sau daya ba, duk a tunanin na you understand what s going on here, Amma da alamu baka gane ba  & shuru yayi yana kallon amar dake kallonshi kamar yaga tv, yama rasa ina zancen hammam ya dosa, lumshe idanunsa yayi ya bude alamun bashida energy yin jayyay da hammam hakan yasa yayi saurin cewa   you have to talk fah, bazakayi shuru ba, inason nasan dalilinka na acting this way,idan har bazaka taimaki yarinyar nan ba, ay da baka bari munkai har iyanxu ba,.   & & ..nunfasawa hammam yayi sannan ya cigaba,   waima tsaya, ka manta mai nace maka ranar ko, kai baka san kai zata taimaka ba, because taimakon da zatayi maka dukda nasan bata sani ba don wayon da muka masu na qin fada masu, yarinyar nan yarinya ce, marainiya ce, bata uwa bata da uba sai wan mahaifinta wanda he s wicked, bari kaji na fada maka, wannan abun da yarinyar nan take na neman citizenship wato katin kasa bawai don son zuciyarta zatayi hakan ba kodan ta zauna anan, no its because tana son taimakon kannenta wanda suke zaune wajen wan mahaifin nasu, rayuwar wulankanci ta fuskanta achan gidan har allah ya kawo nan, basu da kowa, itama kanta scholarship ta samu tazo nan din, ko kasan cewa upkeep dinta da uncle din nata ke bata saita biyashi don yace saitayi hakan inba haka ba cikin will dinsu zai dauka wanda shi kadai mahaifinta ya bar masu ita da kannaneta, &   ?a karashe da dan fada, lumshe ido amar yayi ya kwantar da kanshi jikin seat din zuciyan shin a mashi wani iri, anatse hammam ya cigaba,   this girl needs katin kasar nan don ta kawo kannenta nan kusa da ita, which gaba dayan su ma basu cikin issashiyar lafiya, haba amar be matured mana  & jin haka yasa amar saurin bude idanunshi kan hammam yace   do I look like I care about problems dinta, please I don t have time for this  ..yana kaiwa nan ya miqe, da sauri hammam ya tsaidashi wajen cewa   shin baka jini da kyau ba Kenan, YARINYAR NAN MARAINIYA CE, na dauka kafi kowa sanin rayuwar marayu yanda take kasan cewa dan you re one of them  ..tsayawa chak amar yayi tunanin maganganun dada ya fara dawo mashi cikin brain dinshi   my dear son duk inda kaga marayu ka taimaka masu please, guide them and protect them  & .runtse idanunshi yayi wanda sukayi jaaa, jijyoyin kanshi duk sun fifito alamun ranshi abace yake, da sauri ya mike yasa kai ya fuce gaba daya daga building din, gaban motor shi ya tsaya sannan ya umarci m5 daya bashi key din motor shi, yana karba ya fuce bai tsaya ko na ba sai bar din da ya saba zuwa, kamar kullum tsaftaccen private loung aka bashi ya zauna yana jin kanshi na sauka, zaman kusan minti talatin yayi kafin ya jawo wayanshi ya fara dialing Ammah, anatse tayi picking da sallama abakinta   hey son, ya kake ya aiki?  anatse ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciyaa yace   Ammah na I missed you so so much  ,& jin hakan yasa ta tabbatar yana cikin damuwa, anatse ta soma yi mashi nasiha, kan ya rage sama kanshi damuwa sannan ta tambaye shi matsalan shi   Amma babu wani matsala kawai na tuna da dada ne  ya bata amsa& jin haka yasa tace   idan ka tuna da mahaifinka addua zakayi mashi bawai kasa damuwa aranka ba, kasan he s up there and he s


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login