Showing 72001 words to 75000 words out of 381117 words

Chapter 25 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2188

dr stefen, zama yayi bayan sun gaisa ya fara kora mashi bayani akan zazzabin da ya taho mashi gadan gadan wanda ya sanya shi ficewa daga hayyacin sa, saida ya gama sauraron shi kafin dr stefen ya soma Magana   mr amar, like a side last time, this is the side effect I m warning you about, this is about more than 3 month of frezzing your sperm and desires, I will advice you get it un-frezz or you ll experience worse  nunfasawa yayi kafin yadan shingida zamanshi ya kalli likitan   doc this is not the perfect for it, I need more time  , sanin ba hurumin shi bane bin diddigin patients sannan dole saiya aminta kafin ayi mashi wani aiki saidai ya nuna mashi risk din rashin yin abinda zai kawo mashi sauki hakan yasa ya rubuta mashi pain killers kawai sukayi sallama ya wuce pharmacy ya karbo, bai tsaya komai ba ya wuce office bayan ya kira m-5.
Yana isa office bai tsaya ko ina ba sai cikin office din shi, zama yayi kan kujeran shi ya kwantar da kanshi dake mashi wani irin zafi, saida ya dauka kusan awa guda kafin ya dago kanshi ya kunna desktop din gabanshi ya soma wasu ayyukan, kurama desktop din idanu yayi yana kallo, ganin yanda yake kallo yasa na dan leka dan naga me yake kallo, files ne burjik wanda saida yabi daya bayan daya yana duba date da time kafin ya danna file din da lokacin dayayi tafiya wato 25th march budewa yayi saiga recorded video na dakinshi wanda ke nuna alamun akwai cctv camera a cikin dakin nashi, dan relaxing kanshi kan kujera ya fara duba video din, ganin babu wani movement yasa ya dunga forwarding komai wanda aciki ma yawanci amra c eke movement dinta na zuwa bandaki, ganin babu wani important abu cikin file din yasa ya futa ya shiga next day da baya garin, shima dai bai samu wani abunba saida ya shiga next file wanda ya kasance third day da baya gari,tun daga lokacin data shugo dakin ya tsaida forwarding din da yake har zuwa lokacin data shigo dakin ta gyara mashi ko ina tare da saka mashi bahoor data saba koda yaushe, kanshi ya dauke wuta lokacin data gama komai ta soma tube kayan jikinta a tsakiyan dakin, da sauri yayi skipping wajen don bashida ra ayin kallon wajen harta futo da dan towel dinta a kugunta da brush and sponge bag dinta, ta fuce daga dakin,skipping ya dunga yi har aka kwankwasa kofar office dinshi kafin ya bada umarni aka shigo, saida m-5 ya sara mashi kafiin ya soma Magana   I have a very tight job for you, Ive sent some information to your mail, I want to know whos behind the contact, make sure you do a tough research okay? ?Da sauri yace   yes sir  Sara mashi yayi kafin ya juya ya fuce idanunshi ya maida kan cctv camera din ganin babu wani abu that is important yasa yadanyi tsaki yana tunanin wani tunani,   what im I even thinking, tsaki yayi harzai kashe desktop din sai kuma yadan tsaya ganinta shugo cikin dakin sanye da doguwar riga mai roba roba wanda tayi mata kyau sosai pink color, kanta da hula pink kalar rigar headphones ne sakale a kunnenta tana tikar rawarta gwanin burgewa, shagala yayi da activity dinda take har saida ta fuce ya dan kwantar da bayanshi akan kujerar ya furta   silly girl  rufe idanunshi yayi yana tunanin abunda likita ke fada mashi nay a zama dole ayi unfrezzing sperm dinshi idan akayi kuma dole immediately ya kusanci mace yanxu shi damuwarshi ta ina sai kusanci mace, bayajin zai iya yin zina don bayason ya haifi danda bana sunna ba, gashi ita wannan da sauri yace hell no nooo, wannan yar yarinyar ina bazaiyuwu ba, infact bazai ma taba bari ba tsaki yayi kafin ya bude shanyaynyun idanuwanshi da sukayi jaa ya mike ba tare daya kashe desktop dinba harya dan yi taku daya yadan jinkirta ya juya yana kallon screen din, ganin hammam kwatsam cikin dakinsa, da farko harya basar don yasan haka yake sometimes yana zuwa gidan harya kwana but kamar bazai kalla ba chan kuma ya kurama screen din idanu, da farko zagaye dakin ya fara kafin ya kunna tv ya zauna kan couch din daki, cikin yan dakiku kuma ya mike ya fuce, fitarshi dayan awanni amra ta shugo tayi alwala ta fuce, mamaki ne karara a fuskanshi ganinta da kayan dazun wani irin daci yaji da baisan daga ina ya faro ba, shifa matsalanshi da yan mata Kenan basu san ya kamat ba yanxu haka ta zauna namijin da ba muharraminta baya ganta, shi yana kishin yaya mata musammam marayu bayansan yaga zsunyi hanyi haryan da ba madaidaiciya ba hakan yasa ya danyi shuru kafin ya dauka wayan shi ya keys din ya fuce daga office din, direct penthouse dinshi ya wuce ya danyi abubuwan sa kafin ya wuto apartment dinshi koda ya shiga kamar kullum a zaune ya taddata tana shan smoothie hankalinta kwance sanye take da rabian gown ta shan iska mai karamin hannu purple color fuskanta faya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?u babu komai sai sheki takeyi alamu hutu da jin dadi ya zauna a jikinta, mikewa tayi da sauri ganinshi gadan gadan akanta, da sauri ta soma Magana   sannu da zuwa ina wuni  baima tsaya jin abinda take fada ba bare kuma amsa gaisuwar tata azafafe yace   daga yau kar ki kuma zama haka babu hijab koda kuwa ke kadai ce acikin apartment dinnan, bana son rashin hankali understood  kallonshi tayi da yanda fuskanshi tayi jaa baka taba tantance fushi yake ko ranshi ne yayi mugun baci saboda yanda fuskanshi take da wani sihirtaccen annuri saidai kuma kwarjini da yake dashi zaisa ka gane da wani abun alamu ranshi a mugun bace yake da yanayin fuskarshi da bazaka taba tantance taqamaiman matsalarshi ba ko abunda ke damunshi, fuu ya wuce daki kamar walkiya yabarta cike da mamakinsa, tabe baki don inda sabo ta saba da wannan halayen nashi shidai baka gane gabansa da bayansa dukda ba shiga alamuranshi take ba don sai suyi kwanaki da yawa basuyi Magana ba saidai gaisuwa itama idan ya fito ko idan ta shiga dakin nashi, komawa tayi ta zauna ta cigaba da shan smoothie dinta da latsa waya.
Shikuwa goga tunda ya shiga dakin kanshi bakhoor din da take sakawa ya mashi sallama, jingina yayi da jikin kofar yana furzar da numfashi kamar wanda yayi tsere, wani irin nauyi zuciyanshi ke mashi wanda ya kasa gane dalili saidai yana danganta komai da abubuwan dake faruwa daki cikin kwanakin wani irin zazzabi mai zafin ne ya fara zuwan mashi babu shiri, takowa yayi har gaban gadon nashi dake tsaf, kamar ba a kai ya kwanta ba donta gyareshi tsaf har an sauya bedsheets din an sanya wasu daban farare tass, zama yayi ya dafe kanshi dake sara mashi, wayanshi ya zaro daga aljihun wando ya danna ma m5 kira, ringing biyu ya dauka, yace   yes sir 
Cikin zafi ya soma Magana   when did you stop updating me on anything when I travel? Ya fada a zafafe, yanda yake Magana kadai ya tabbatar ma da m5 yana cikin fushi sosai, saidai abin mamaki ya kasa fadan takamaiman dalilin fadan nashi dukda koda yaushe koda kuwa tafiya yayi kuma a ranar zai dawo sai anyi updating nashi akan komai don shi mutunne mai lura da taka tsantsan sosai akan abubwan da suka shafe shi duk wani abu da m5 yasan zaiso ya sani yana fada mashi bare idan har wani abu ya faru saidai this time around babu wani abu da ya faru saidai zuwan abokin nashi daya dunga yi cikin kwanakin shikuma wannan ya saba zuwa don an san tsakaninsu, babu abinda m5 yace tunda ya fara Magana harya gama yace   im sorry sir  , ?shuru amar yayi yana nazari, why is he doing all this, sbd hammam yazo ne or what, ay bai kamata ace yana fada akan hakan ba sbd ay hammam ya saba zuwa gidan nashi koda kuwa baya nan, but why, shuru ya dan yana dogon nazari saida m5 yayi gyaran murya kafin ya dawo hayyacinci ya kashe wayan diff ya kwanta baima tsaya cire takalmin nashi ba.
Amra kuwa ganin biyar saura yasa ta kira haifa,   hey babe ya kike kwana biyu, bakizo office baya jikin abu?
Gyara zama haifa tayi akan kujeran patients guest wadda ke fuskanta gadon marasa lapiya nunfasawa tayi kafin ta soma magana   hey babe ina nan lpy jikin abu ne yadan motsa amma da sauki munaa asibiti an kwantar dashi  shiru ne yadan biyo baya kafin amra tace   subhanallah yaushe aka kwantar Dashi baki fada min ba please ki tura min address zanzo anjima kadan ki gaishe da ummi please allah ya bashi lpy&   nunfasawa haifata tayi kfin tace   thank you babe zan tura maki yanxu zan aje waya don inda likitoci sunce yana buqatan hutu banda hayaniya see youu saikinzo 
?
Kurama wayan ido haifa tayi ta kalli ummi dake zaune kan sallaya tana azkar, kafin ta maida hankalinta kan wayan ta kara dialing number hamman yau kusan kwana uku Kenan rabon da suyi waya shida ita, hankalinta ba karamin tashi yayi ba don yawaci yana fada mata idan zaiyi tafiya gashi wayan nashi a kunne yake bawai ya kashe bane kuma tana rininging duk sanda ta kira, kamar koda yaushe message ta tura mashi kamar haka   habibi ma bi, laqad atasalt bik iinak la tastajib (habibi whats wrong ive been calling you, you re not responding) please reply me ass soon as possible, abu has been admitted.  .. tana tura mashi message din ta mike da sauri ganin abu ya bude idanunshi da yadan fada kadan, da sauri ta matso gabanshi ta rike hannunshi tana mashi sannu, murmushi kawai ya iyayi mata kafin ya lumshe idanunshi, da sauri ummi ta danna emergency bell ganin yanda ya lumshe idanun tsoro kar seizure din ne ya sake zuwan mashi, da sauri doctor ya shigo da nurse suka farad an dudubashi, saida doctor y agama kafin ya masu bayanin alluran da akayi mashi ne bai sake shi ba don jininshi daya dan hau ke sashi jikinshi mutuwa sosai.
Bangaren hammam kuwa wani abu ne ya faru,wanda ya sashi daina daukan wayan haifa, wato akwai ranar da yakai wani proposal na wani business ?company din abuh wanda da farko abuh ya karbe shi da hannu bibiyu saboda yanda yaga da soyayya tsakanin shi da yarsa, saidai dan binciken da yayi ya gano kamshin rashin gaskia a tattare da hammam din da proposal din, saidaga baya ya gane daga inda proposal din ya fito wanda hammam yayi badda kama a zuwan da yayi ma abuh wanda hakan yasashi neman shi har office dinshi yazo, koda yaje abuh yayi kokarin bashi chance akan ya fada mashi gaskia daga karshe dai yace mashi yayi cancelling proposal din nashi, dukda bai fada mashi ko nuna mashi ya gano komai ba don lauje ne akayi shi cikin nadin, karshe ma dai abuh dariya kawai yayi mashi kafin sukayi sallama, koda hammam ya koma ma mahaifinshi da rejected proposal din yaji zafi sosai don dalilin wannan proposal dinne ma hammam ya tunkari haifa da soyayya duk dan ya samu shiga wajen mahaifinta sai abun yazo da sauki ba tare da neman taimakon nata ba da sukayi planning tun farko wannan dalilin yasa mahaifinshi ya sashi yanke alakarshi da ita don amfaninta ya kare sai kuma next plan.
?
Hammam s res
Kallon wayan nashi yayi dake ta ringing harta katse message ya sake shugowa, dubawa yayi ganin message din haifa yasa, ya aje glass cup din hannunshi ya bude message din yadan jima yana karanta message din kafin ya dago jin gyaran muryan da akayi mashi kura mashi idanu tayi sosai babu kaya jikinshi sai gajeran wando, dagowa yayi ya kalleta kafin ta karaso gabanshi sanye take da farar riga har gwaiwanta da alamu kayanshi ne ma cikin rausaya ta zauna kan laps dinshi,   young man are you affected if you are then call her up don t be a bastard?  ta daga mashi gira daya, dagowa yayi ya kalleta kafin ya soma Magana   no need, I don t need her anymore 
Ahankali ta fara shafoshi hartazo kan nippy dinshi tadan murza kafin ta matso da fuskanta daidai kunnenshi ?kallonshi take tabbas shima wannan zata iya rage zafi dashi saidai inaaa general ya wuce shi nesa ba kusa ba, kishirwarta ta general ce sosai takawa tayi tace  so whats the next plan now?  ganin ya soma shiga yanayi yasa tadan matsa mashi nipple din da karfi tare da furzar da numfashi cikin kunnenshi ahankali tace   I need your friend so badly, not only I want him to suffer I want him so badlyyy to my coreee  , wani ririn gauran nunfashi ya furzar kafin yadan tunkudeta gefen kujera ya mike yace   get ready, for office tomorrow, kinsan yanda muka tsara komai bana son kuskuren, keep your hunger aside first  yana kaiwa nan ya wuce cikin dakinshi yana sauke nunfashi, zama yayi kan lafiyayen gadonshi ya higa tunani, anya wannan hanya madaidaiciya ce, lallai ya cika butulu, saidai baya jin yanda ya faro komai zai iya tsayawa, tsaki kawai yayi ya kashe wayanshi baki daya ya shiga tunanin irin rayuwar da yayi achan baya.
Hammam haifanfan dan Iraq ne, mahifinshi asalinshi dan kasar Iraq ne mahaifiyarshi kuwa anan uae aka haifeta, tun tasowarshi ya taso yana ganin irin ukubar da mahaifiyarshi ta shiga sanadiyan mahaifinsa, iyayenta masu kudi ne sun mutu sun bar mata dukiya wanda sanadiyan mahaifinsa ta salwanta sbd shaye shaye da yakeyi da chacha, tun suna gidansu na kansu har suka yawo kan titinan da gidaje da akayi abandoning suna kwana, mahaifinshi kuwa acikin shaye shayen nashi ya mutu dalilin zuciyarshi data buga don giya tayi mashi illa sosai a wulaqance ya mutu, shida mahaifiyarshi basu wani damu ba don dama chan babu abunda yake tsinana masu saiya zamana mutuwar tashi ma sauki tazo masu dashi don dukan da yake ma mahaifiyarshi idan ya bugu yanzu an rufe shafin wannan, ya taso babu ilimi kwata kwata saidai bara, bashi da burin da daya wuce ya kula da mahaifiyarshi sosai, lokacin da yanada shekaru goma sha shida shiff a duniya cikin wannan rayuwa dai ta rashin gata ta cikin kasakanci allah ya kawo masu alif bin shuraim, babu zato babu tsammani, alif yana daya daga cikin manyan dake diban yara irinsu irinsu mabarata yana basu aiki a cikin business din da yake wau yana turasu wata kasar wasu kuma anan uae yae basu aikinda babu wanda yasan wani irin aiki ne saidai, shima hammam ya ganshi ne lokacin da aka kawo record din beggers, ganin yanda yaron keda wayo da hazaka yasa ya karbeshi shida kanshi amimakon ya bashi aiki koya tura shi wani wajen, saidai yayi alwakawri zai maidashi weapon din da zaiyi amfani dashi idan lokaci yayi, ba karamin dadi mahaifiyar hammam taji ba ganin rayuwar hammam na chanzawa, don bashi kadai alif ya dauka nauyi ba harda ita kanta mahaifiyar tashi, akwana a tashi alif ya sanya hammam a makaranta yayi dogon karatu inda ya hadu da amar suka shaqu sosai har alif ?ya saka shi cikin uae armed force wanda shima tare sukayi shi, akwai lokacin da hammam yayi dogon training wanda wannan ne training din dayayi wanda dawowan shi ya tadda mummunan labarin mutuwar uwarshi haka kawai kwatsam, ko lokacin daya zo din alokacin alif ke shaida mashi tayi wata hudu da rasuwa, hammam yayi kuka kukan baqin ciki sosai, yayi alqawarin bama mahaifiyarshi gata, gatanda bazaima kanshi ba don tasha wahala dashi sosai, she protected him, yana rayuwa ne sbd ita saidai mutuwa tayi masu Katanga shida ita, kokadan baiji haushin alif ba naqin fada mashi mutuwar mahaifiyarshi sbd yana daya daga cikin mutanen da yake girmamawa sosai, kuma shine wanda ya maidashi mutun kuma yayi alqawarin zaiyi duk abunda alif keso zai kasan ce mai halacci don abunda mahaifiyarshi ta raineshi dashi Kenan, duk wanda ya dago ka ya maidakai mutun ka dage kayi mashi halacci karkayi butulci.
Hammam bai fara karantar alif ba saida y agama makaranta tsaf ya karanci alif da kudururrukansa, wato alif babban mutunne mai connection, yana dealing da illegal jobs a uae, aiki na farko da alif ya saka hammam shine akan babba ogan su wato general ashraf wanda shine babban ?general mai hazaqa a shkarar 2014, lokacin suna officers shida amar, da farko aikin yaso bashi wahala don yana officer ne a lokacin saidai abun mamaki shine wanda ya daure ma shi kanshi hammam din kai shine, da yawa cikin manya manyan armed force dake cikin headquater mutanen alif ne, tun daga lokacin duk wani wahallaen aiki ko wani aikin da zai kawo mashi fargaba sai yazo mashi da sauqi, dukda shima dan sako ne, instruction kawai ake bashi saiya gudanar da komai, wanda duk aikin da yake yima alif din cikin kulli yake don shi kanshi ya kasa fayyace komai, duk sanya akayi sauyin manyan headquarters shike zuwa ya da mutanen baban kodai sukawo karshen lokacin generals din ko kuma ayi masu kulle kulle da zaisa subar aikin gaba daya shima idan basu amince da abinda suke tafe dashi ba, lokacin da suka fara tasowa shida amar, sun taso cikin kwarewa cikin aikinsu sosai, wanda amar ya wuce hammam a kwazo sosai da komai ma, amar yana aiki cikin ilimi da zurfin tunani, duk sanda zasuje operation amra ke dawo wa da rank, don da haka ake promoting dinshi, sannan duk wani important operation yana ciki domin he is very tough, ganin halayyansu ya banbanta yasa hammam tsorata sosai da amar saidai bai barshi ba don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login