Showing 234001 words to 237000 words out of 381117 words

Chapter 79 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2003

ni kadai?
Da mamaki take kallonshi kafin ta kufce da dariya Ganin yanda yayi kicin kicin da fuska  yaya are you jealous?
 Yea I am ya bata amsa kai tsaye, tuntsirewa tayi da dariya kafin ta dan matso daf dashi fuskanta dauke da murmushi Har wani blushing takeyi,  ka kwnatar da hankalinka my yaya, babu wanda zai chanza gurbin da kake dashi a zuciyata
Hade rai ya danyi kafun ya kauda kanshi irin bai yarda dinnan ba tana Ganin haka ta dan shgwabe  yaya Wallahi da gaske nake , bakisan yanda nake jinka araina ba
Dan murmusawa yayi kafin ya kalli cikin idanunta in a naughty way yace  zaki aure ni?
Sunkuyar da kanta kasa tana mai rufe fuskanta cikin sassarfa ta gifta ta gefenshi Har takai bakin kofa tadan juyo  yes honey
Da sauri ya juyo ya kalleta harta fuce daga kitchen din aguje tana dariya.
Wani irin dadi ne ya ziyarceshi, soyayyar da yake mata ta dabance a cikin zuciyarsa.

Amar na shugowa gidan ya wuce bedroom dinshi, har lokacin yana jin wani irin zafin yanda asad yake kallonta, haka kawai yaji bayason ana kallonta kwata kwata, haka ya dunga zarya a cikin dakinshi ya rasa abunda ke damunshi, zuciyarci cushe take da bacin rai mara dalili, babu abunda yake sai tsuka, he can t believe yanda yake behaving when it comes to her wanda ada kwata kwata baitaba tunanin zaiyi hakan ba akan wata mace ba.
Haka ya kwana cikin bacin rai, hade da tunaninta aranshi wanda ya kasa hana kanshi yin hakan.

Ita kuwa bayan ta hau sama hijab din jikinta kawai ta cire ta wuce bathroom jiki a mace tayi wanka ta sauyo wani towel din ta futo ta kwanta abunta.

After one week& .
Yau sati guda kenan rabon shi da ganinta, tun bayan zuwan da asad yayi ta sauko kasan bai sake ganinta ba dukda baya wuni a gidan, yana tashi yake fucewa sai kuma yamma zai dawo.

Bangaren amra, itama dai rabonta dashi tun lokacin, bayan wannan ma yanxu bata wani damu da al amarin shi ba, kamar yanda ammah ta fada mata akan tayi focusing akan lafiyarta da babyn dake cikinta kawai, har lokacin kuwa batayi gigin fada mashi komai
ba kwata kwata.

A cikin kwanakin ta samu kuzari sosai ba kamar da ba, don ba laifi yanxu ta rage yawan bacci sosai, sai ci, yanda take cin abunci sosai har mamaki ammah keyi sosai ita da salima dukda ita ammah tasan dalilin cin nata, salima dai mamakin addar nata takeyi sosai don ta chanza dukda bataa bata wani mahimmanci ba saboda karatu dayasha kanta sosai saboda sunyi nisa sosai suna gab da gama neco.
Friday morning&
Yau ne 3rd time dinta na zuwa asibiti da ammah, yanda sukaje last time haka sukaje this time around babu wanda ya sani, kulawa da tarairaya babu wadda ammah bata nuna mata, babu abunda zata buqata wanda ammah bata kokarin ganin ta bata, har alokacin babu wanda yasan cewa tana da ciki musamman amar.

Fitowa sukayi daga cikin asibitin, a,,ah na rike da magungunan ta da suka karba a pharmacy, ahankali amra ke tafiya saboda kumburin da kafafunta sukeyi saboda zama waje daya da takeyi wanda doctor yanxu yayi advicing akan ta dunga exercise sosai don tayi nisa a 6th month dinta.
Bude motar ammah tayi shuka shige kafin taja motar suka bar asibitin, ko akan hanya saida ammah ta tsaya tasaya mata agwaluma da take yawansha sosai, allah ya taimaka lokacinta ne ma, saida ta saya mata cikin leda kafin su bar wajen.

Driving ammah keyi a natse tana murmushi kafin ta dan waigo gefen amra tace   daughter kinji dai abunda doctor yace ko?, you have to be excercising saboda kumburin kafan nan, 
Dan murmusawa amra tayi kanta a kasa tace   inshs allah ammah.. 
  yauwa baki fada mashi ba dai ko?  ammah ta sake tambayarta
  ah ah ban fada mashi ba ammah, rabo na dashi ma harna manta  amra ta bata amsa.
Dan jim ammah tayi kafin tace   bana son ya sani yanxu, so nake muyi surprising nashi  

Hira suka danyi inda ammah ke buncikan cikinta akan yanda yake treating dinta ganin yanxu ta dan sake sosai da ita sosai ba kamar lokacin da taji tana da ciki ba tana kunyar ta.

Suna karasowa gida ammah tayi horn securities suka bude gate, suna budewa ta shige da motar har wajen parking space inda take ajiye motarta, tana kashe motar suka fito atare, cikin gidan suka shige ammah na rike da magungunan ta, da sallama suka shige gidan, salim ne kawai a zaune a parlor yana buga game da ps5 dinshi da amar ya saya mashi, yana ganin su yayi saurin ajiye game din ya miqe ya taho wajen ammah, rungumeshi tayi tsam a jikinta   mun barka kai kadai a gida ko?  girgiza mata kai yayi kafin ta sake tambayarshi   son ya futa ne?  nan ma girgiza mata kai kafin su karasa sitting room.
Kallon inda amra ke tsaye ammah tayi tace   daughter kije ki huta ko 
  tohm 
Tana kaiwa nan ta wuce sama anatse,.

Karfe biyar daidai ya shugo gida, yana futowa daga motarshi ya wuce main entrance kai tsaye, da sallama ya shugo cikin parlor cikin kamewa da izzarsa, sai buga kamshinsa yake, yayi wani fresh ya kara kyau kana ganin fuskanshi kasan yana cikin kwanciyar hankali sosai, sanye yake da kaftan sky blue da baqar hula, kayan sunyi masifar yi mashi kyau, kamar wani arab guy, kanshi a kasa ya shugo parlor har zai wuce part dinshi ya jiyo dariyarsu, juyowa ya danyi inda suke zaune a parlor, da amra ya fara cin karo, tana zaune kan kujerar zaman mutun uku ta mikar da kafarta daya akan kujerar daya kuma a kasa sai plate akan cinyarta da aka yayyanka agwaluma a ciki.

Sanye take da doguwar riga ta atamfa, kanta babu dankwali sai gashinta data nade tayi bun a tsakiyan kanta, rigar jikin nata ta zauna mata dam a jiki boobs dinta sun futo sosai don yana iya hango yanda suke sheki daga nesa kamar zasu farka mata rigar, tayi wani irin haske dake daukan idanu, gefenta kuwa ammah ce da salim dake maqale da ita duk suna zaune kan kujerar gefenta suma, gaba daya hankalinsu nakan tv suna kallo suna dariya.
Saida ya kaarso parlor yak are mata kallo sosai kafin ya dauke kanshi ya kalli inda ammah ke zaune yayi gyaran murya, gaba daya juyowa sukayi suka kalleshi, banda amra datayi mashi kallo daya ta maida idanunta kan tv, da fara a ammah ta kalleshi   son har an dawo?,sannu da dawowa 
  thank you ammah  ya amsa atakaice
Samun waje yayi ya zauna akan single chair dake facing tata, tunda ya zauna taje jin yanda idanunshi ke yawo a jikinta, agwalumar dake hannunta ma kasa kaiwa baki tayi, kamar wadda aka zare ma laka haka ta juya ta kalli inda yake, cikin muryanta mai sanyaya zuciya da kasha garkuwar jini tace   barka da dawowa 
Ahankali muryanta ta ratsa kwanyarshi don lokacin data juyo ta kalleshi ya kauda kanshi gefe, maido da idanunshi yayi kanta ya zuba mata wannan mayun idanun nashi,   thanks  ya amsa ahankali

Saurin sauke idanunta tayi daga kanshi ta cigaba da shan agwalumarta tana kalllon, zaman shi anan baisa tabar dariyarta da yazo tadda sunayi ba don wani funny movies suke kalla, datayi dariya haka zai dago ya kalli kyakyawar fuskanta da yanda sound din dariyar nata ke fita daga bakinta da yanda kumatunta ke lotsawa, zai iya cewa wannan ne first time daya ga tana dariya haka sosai, tayi masifar tayi da imanin shi, tayi mashi kyau sosai, yanda yake ganinta yanxu kamar ba it aba, ta cika mashi idanu.

Ammah ne ta juyo ta kalli inda yake zaune   son kayi lunch kuwa ko zakaci yanxu? 
Jin shuru babu response ya kafa ma waje daya kallo yasa ta waiga don ganin inda yake kallo haka daya dauke mashi hankali don kwata kwata baima ji abunda tace ba, tana ganin amra yake kallo ta sauke wani lausassan murmurshin jin dadi, ko ba a fada ba tasan y agama kamuwa saidai taurine kanshi bazaisa ya sauke kanshi ba yayi admitting hakan,   son?? Are you okay  ammah ta sake fada tana murmushi,
Da sauri ya kauda kanshi don sai yanxu yaji muryan ammah, baiyi tunanin ta ganshi ba don haka ya mike tsaye yace   im okay ammah, sai zuwa anjima  yana kaiwa nan ya wuce part dinshi, binshi da idanu ammah tayi tana murmushi kafin ta maida hankalinta tv.

After like 5 mins haka, ammah ta waigo inda take zaune tace   daughter, kije ki kai mashi ko dan juice ne 
Saurin dagowa amra tayi, hannunta rike da bawon agwaluma data gama sha, jin abunda ammah tace yasa tayis aurin sauke kanta kasa tana mai jin kunya,
Kauda kai ammah tayi ta maida idanunta kan tv tana murmushi ganin kamar ta zama uncomfortable lokaci guda, amra dai kamar ta nitse dan kunya, haka nan ta sauke kafarta ta mike tsaye ahankali ta wuce kitchen, bata ma tsaya daukan dankwalinta ba ta.
Tana shiga kitchen ta dauka wani babban glass cup mai tsayi sosai ta wankeshi tass kafin ta goge kafin ta bude fridge ta janyo wani exoctic apple and mint juice mai sanyi.
Zuba juice din tayi a cikin cup din kafin ta janyo inda suke ajiye veggies, nan ta dauko mint leaves da cocumber , suma saida ta wankesu kafin tayi slizing cucumber a cikin juice din sai dan mint din kuma ta jefa shi a ciki, tana gamawa ta dauka cup din ta saka shi wajen ice dispenser, bata saka mashi ice da yawa ba ta cire cup din ta futo daga kitchen din kanta a kasa, dan dagowa tayi ganin ammah bata parlor yasa a dan sake kadan ta wuce part dinshi.
Anatse take tafiya saboda kafarta daya dan kumbura kadan, da sallama ta bude sitting room dinshi, k ina lum lum babu wani haske sosai sai sanyin ac daya cika dakin.
Bata tsaya dube duben parlor nashi ba ta wuce bedroom dinshi kai tsaye,   assalam alaikum  ta fada da yar siririyar muryarta tana rufe kofar dakin bayan ta shugo.
A tsaye yake dagashi saidan shorts dinshi yana tsaye bakin windown dakinshi ya bama kofa baya yana receving call, batajin me yake cewa saidai dagjin yanda yake Magana kasan work related call ne, takowa ta dan soma yi har inda yake tsaye, bata yarda ta sakekallonshi ba bayan kallon da tayi ma jikinshi data shugo ba, saida tazo dan dab dashi tace   uhm&   kasa karasawa tayi don tayi niyar kirasnhi ne idan ya juyo saita miqa mashi saidai ganin kamar baima san ta shygo ba yasa ta dan yi jim kafin ya tako har inda yake tsaye ta zagayo gabanshi.
Unexpectedly ya ganta a tsaye agabanshi, tunda ta staya gabanshi maganar dake bakinshi ya maqale saboda kamshin ta daya buge shi lokaci guda, idanu ya kura mata yana kallonta, itama shi take kallo.
Saida suka dauka kusan minti biyu suna kallon juna, da kyar ta samu ta dauke nata idanun daga nashi ta dago hannunta muryanta chan kasa kamar mai rada saboda bata son interrupting call din nashi   bismillah  bin bakinta yayi da kallo don muryanta bai futo ba sai motsin bakinta,kafin ya sauke idanunshi zuwa hannun nata dake dauke da juice din, dagowa ya sakeyi for the second time ya daga mata gira daya alamun menene?, tana ganin haka ta sake motsa bakinta   juice 
Wayarshi ya cigaba da m5 don dashi yake wayan tun kafin ta shugo inda suke Magana akan ayyukan da suke kan desk dinshi idan ya koma sai kuma report din da yake bashi kullum akan abubwan dake gudana acahn.

Kallonta ya sakeyi har lokacin tana rike da juice din ta dago shi tana miqa mashi, gaba daya ta gama gajiya da tsayuwan dukda ko minti biyar batayi ba, kanta a kasa tana tunanin kodai ta ajiye mashi ne ta tafi, idan y agama wayan saiya dauka,
Da sauri ta dago idanunta jin hannunshi kan nata, ya dago hannun nata yakai cup din zuwa bakinshi, saida ya danyi sipping kafin ya ire cup din da hannun nata, zuba mashi idanunta tayi tana ganin sabon salo daga wajenshi, bata gama tunani ba ya sake daga hannun nata da cup din yakai bakinshi ya sake sha for the second time yana lumshe idanu at the same time yana amsa m5 cikin harshen turaenci, samun kanta tayi da kallonshi da bakinshi dan yanda yake Magana kamar wata mace a gayance babu hayani cikin kamewa, dan jefi jefi shima yake maido da idanunshi kanta har ya shanye juice din tass, dukda bayan y agama sha dinma bai saki hannunta ba ya rike gam har saida y agama wayar.

A wannan lokacin already ta gama galabaita da tsayuwar, kafarta tayi tsami sosai tadan kumburo, cute feet dinta yayi bul kamar ka bula jinni ya futo, sauke wayar yayi daga kunnenshi ya maido da kallonshi gareta, kamar bazaiyi Magana ba chan kuma yace   meysa kike yawo babu cover? 
Da mamaki ta dago tana kallonshi kafin ta shafa kanta da dayan hannunta don dayan har lokacin yana rike dashi hade da glass cup din.
Muryanta baya futa sosai ta soma Magana   na mantashi a parlor ne 
  dazu ban ganki dashi ba?  ya sake tambayrta
  na manta ne, kaina ke itching shiyasa   ta sake bashi amsa a natse kanta a kasa don kwata kwata bata son hayaniya yanxu.
  meysa yake itching  ya sake tambayarta yana matso da fuskanshi wajen gashinta don yana iya hango tsakiyan kanta, san sana gashin yayi, babu abunda gashin keyi sai kamshin haddadun oils dinta wanda yasashi saurin runtse idanunshi ya saki hannunta ya dora hannunshi kan gashin nata ya fara shafwa ahankali,   uhmmmmm? Meysa yake itching? 
Ya sake fada yana kokarin shige mata, da sauri ta danyi baya kadan har tana kaiwa dab da bangon dakin nashi   ya cika ne da yawa  tana kaiwa nan ta juya zata fuce daga dakin, cikin sauri ya riko hannunta   ay ban sallameki ba malama 
Juyowa ta danyi kamar zatayi kuka,   dan allah ka barni na tafi, kafana yana min ciwo kuma inajin jiri 
Duban kafar nata yayi ganin yanda ta dan kumburo kafin ya maida idanunshi kanta   meysa kafan naki ke ciwo? 
  ba komai, tsayuwan da nayi ne?  ta bashi amsa
  tsayuwa yana saka ciwon kafa ne harda kumburi?  ya sake jeho mata tambaya babu wasa a fuskanshi
Ganin tayi shuru ta daburce yasa ya saki hannunta ya koma baking ado ya ajiye wayanshi, ba tareda ya kalleta bay ace   wanke min bathroom dina 
Da sauri ta dan dago ta zuba mashi ido, kafin ta sauke, ta fara takowa zuwa bathroom din nashi, ta gabanshi ta wuce ciki ta rufo bathroom din, gaba daya bata da wani kuzarin wankin toilet ammah haka ta fara wanke mashi, tana yi tana zama tana hutawa, toilet dima baiyi komai ba babu datti ko digo amma don tsabar neman Magana ya sata wankewa, tana cikin wankewa bata dauraye ba ta zauna agefen bath tana hutawa.

Cikin daki kuwa bayan shiganta bathroom ya kasa sukuni, don baiso ya sata wani wanke toilet ba kawai bayason ta fita ne yanxu, he just feel like dama ya ta zauna yayi ta kallonta yaan teasing dinta, wani iri yake ji game da ita sosai wanda yana jin yanason kasancewa da ita koda yaushe, dukda tana ciikin dakin nashi kasa sukuni yayi yana mai jin haushin kansa yanda yake acting.

Cikin sauri ya mike ya daidaita natsuwarshi ya shige bathroom din, yana shiga ta dawo idanunta da suka danyi jaa sosai, tana ganinshi tsaye tayi saurin miqewa da kyar, kaffunta sun fi da kumbura,   sorry yanxu zan gama  ta fada tana janyo shower don ta dauraye bathroom din, taku daya biyu tayi kafarta tayi gaba dayar kuma tayi baya, saura kiris ta fadi don tama saddakar faduwa zatayi, da wani irin sauri yayi taku biyu ya cimmata gaba daya suka fadi ita ta fado jikinshi while shi kuma ya fadi a kasan,   washhh allah na ciki na 
Ta dan furta ahankali, damamaki ya dago ya kalli fuskata, shida ya fadi akan tiles din wajen baice wash ba sai ita data fadi akanshi, samun kanshi yayi da cewa   are you okay? Kin buge ne? 
Saida yayi Magana ta luar a ajikinshi ta fado don haka tayi saurin kokarin janye tana sauke ajiyar zuciya don gabanta faduwa ya dungayi sosai don inda ta fadi ba karamin muguwar faduwa zatayi ba, babu abunda ya fado mata aria lokacin sai cikinta, da sauri ta shafa cikin nata tana hamdala kan kace me sai hawaye sharr afuskanta, kallon mamaki yake mata, don duk a tunanin ko ta fadi taji ciwo ne kafin ya taro ta saida tunawa da a jikinsh ta fado ya tabbatar ma da kanshi cewa bata fadin ba,   heyy heyy whats wrong? Are you okay  ya fada adaburce, don lokaci guda yaji kukan nata ya sakar mashi da jiki tausayinta ya baibaye shi, ay tana jin haaka ta sake fashe mashi da kuka tana kankameshi donta tsorata sosai, saurin rungumeta yayi hankalinshi adan tashe har hannunshi na danyin karkarwa ya soma shafa bayanta, mai ciki dai da shagwaba haka nan taji kawai bari tayi ta yin kukan, don sun dauka kusan minti goma ana abu daya, dago da fuskanta yayi jin ta rage kukan ya sake tambayarta fuskanshi dauke da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login