Showing 201001 words to 204000 words out of 381117 words

Chapter 68 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1997

sallama salima ta shigo dakin amra, sanye take da hijab har kasa, amra dake zaune baking ado ta rafka uban tagumi, sanye take da doguwar riga abaya baqa, fuskanta tayi fayau alamun damuwa kwance akan fuskan nata.
Anatse salima ta kaarso har inda take ta zauna gefen gadon ta dafa kafadarta   adda lafiya dai? Are you okay ko akwai abunda ke damunki, 
Firgigi amra ta farga da ita, jiki amace ta kalleta tace   yashe kika shugo 
Da mamaki salima ke kallonta,   adda something is wrong with you ko? Ki fada min dan allah, akwai abunda ke damunki da kike boyemin 
Murmushin yaqe amra tayi ta miqe tsaye tayi rolling mayafin abayarta akanta tace   babu abunda ke damuna, kece dai kike boye min abu, na lura kwana biyu bakya cikin wlwala 
Shuru salima tayi son tasan waske zancen take son yi don haka itama tace   ni babu abunda yake damuna, abu daya ne ke damuna 
Da idanu amra ta kalleta   meke damunki fda min my baby sis 
  kece adda na, wallahi damuwata damuwarki ce,ki daina boyemin komai don allah, we only have each others back 
Nunfasawa amra tayi ta dan kakalo murmushin d bai kai xuci bat ace   nidai babu abunda ke damuna, kinga taso muje mu daura breakfast yanxu naga karfe tara ta kusa 

Atare suka sauko kasan zuwa kitchen, anan suka tadda lantana tana ayyukanta, saida suka gaisa kafin su fara preparing breakfast, suna gab da gamawa amra tace   baby sis, kije ki fada ma ammah an gama breakfast, sannan ki taso salim 
  okay adda  salima ta fada tana kokarin fucewa, amra ce da kanta ta jera komai saboda salima ta wce sama, saida ta gama tsaf ta dawo kitchen ta kalli lanatan dake yankan avocado tace   oh anty lantana bakya gajiya da aiki, ayda kin ajiye idan kin gama cin abunci saiki hada juice din 
Da murmushi lantana ta kalleta tace   ah ah gwara n agama duka na huta 
Shuru amra tayi tace   toh shiknan bari na wuce sama 
Amra nakaiwa nan ta juya zuwa sama, bata kaiga karasawa ba ta tuna da wayanta data bari a kitchen don haka ta juya zuwa kitchen din, koda ta karaso kicin din batayi sallama ba ta kutsa kai,   kingaa na man&   kasa karaswa tayi ganin yanda lantana ta daburce kamar wata barauniyar da aka kama, da mamaki amra ke kallonta da yanda take kokarin kare abunda ke hannunta da zaninta, staff amra ta ngo qamshin rashin gaskia a tattare da ita, ance kayi ma mutun kyakyawan zato koda yaushe don haka ta basar kamar bata ga komai bat ace   ashe anan nabar wayar 
Cikin yaqe lanatana ta juya gefe tace   au laa ashe mantawa kikayi, kinga nida nayi zaman akuye daurin zani na neman gagarata  ta fada tana gyaran zani, murmushi kawai amra tayi ta fuce daga kitchen din tana mamakin abunda ta gani.

Karfe goma daidai kowa ya hallara banda amra, ammah na zaune salima tayi serving dinta, kafin tayi serving salim, tana shirin zubama aman yayi saurin janye plate dinshi ba tare da ya kalleta bay ace   no thanks 
Jiki a mace ta zubama kanta ta zauna chan gefe ta fara cin abunci, da sallama amar ya shugo shima ya zauna, saida ya fara gaisheda ammah kafin suma su gaishesa, duban dining din yayi zuwa kofa hoping ko zai ganta, ganin babu ita yasa ya fusge, salima ce tayi serving dinshi tana gamawa shima yayi bismillah ya fara ci.
Suna nan zaune saiga amra kamar wadda aka wullo, ta sauyo kaya zuwa wata abayar mai kyau lemon green color, tayi mata kyau sosai kmar ba ita, anaste cikin takunta mai daukar hankali ta karaso dining din fsukanta fayau, kusa da ammah ta fara zuwa ta gaisheta kafin ta ja kujera kusa da ita ta zauna, daya bayan daya ta bisu ta gaishesu, amar dai tunda ta fito ya kasa dauke idanunshi akanta, har saida ya kusa kwarewa kafin ya sauke idanun nashi, itako bata wani bi takanshi ba ta soma serving kanta.

Shuru kake ji a dining,babu wanda yace kala sai karar spoon dake tashi.
Da sallama lantana ta shugo dining din hannunta dauke da dogon cup data hadama ammah green juice aciki, saida ta gaishe da kowa kafin ta matso kusa da ammah ta aje mata kan table tace   hajiya ga girin juice din 
Dariya salima ta danyi data kubce mata tace   kai anty lantana, keda wannan girin din 
Murmusa duk sukayi ammah tace   nagode lantana sarki aiki, bakya mantuwa,ni wallahi mantawa ma nakeyi da green juice din 
Murmushi kawai lantana tayi ta juya da nufin shiga kitchen, amra data kafeta da idanu tana ganin juyawarta tace   ji mana 
Juyowa lanatana tayi ta tsaya tace   naam anty 
Miqewa amra tayi ta tako inda ammah take zaune tana kokarin kai juice din bakinta tace   ammah zansha 
Da mamaki ammah ta kallota, kafin ta dan murmusa tace  gashi doctor ay bana hanaki ba, 
Karba amra tayi ta juyo gaban lantana ta kalleta tace   anty lantana ko zaki fara sha kiji min idan da daci  adaburce lantana ta kalleta tana yaqe tace   ay na taba sha, akwai daci kam wallahi, anya zaki iya sha kuwa keda kike son zaqi 
Shuru amra tayi ta sake kallonta fuskanta babu wasa, tace   yaushe nace maki inason zaqi?, kedai ki dandana min kawai 
Atsorace lantana ta sake kallonta tace   kaii ni zawayi yake sani saidai ki bama ammah ta dandana maki 
Amar da kanshi ke kasa yana jiyo su sama sama ya dago ya kallesu, nan kowa ma ya maida kallonsu kansu, amra dai ta dage akan lantana saita dandana, ita kuwa lanata data gama tsurewa sai dojewa take karshe ma cewa tayi,   na doraruwan zafi akan gas bari na kshe 
Kamar daga sama taji muryar amar   stoppp there 
Ya fada a kausashe kafin ya tako har inda suke, hannu ya sanya ya janye amra gefe anatse kafin ya karbi juice din daga hannunta ya kalli lantana yace   shaaa 
Haba waa nan take lantana ta saki futsari, gaba daya alamunta sun nuna bata da gaskia kiri kiri,
Akaro na biyu ya daka mata tsawa yace   takeeee it and drink it up 
Jiki na bari ta karba ta fara kokarin kaiwa bakinta, bata kaiga sha ba ta saki cup din a kasa wanwas ya fashe juice din ya malale, saurin miqewa duk sukayi daga kan ammah zuwa ga aman da abun shima ya daure mashi kai,
Kallon cup din amar yayi zuwaga juice din dake Malala, ahankali idanunshi suka sauka kan wani yellow drug da bai gama melting ba a cikin juice din, tsugunnawa yayi ya dauka kwayar yak are mata kallo sosai, if hes not mistaken wannan molly ce wanda daddy yake safarar su ga manyan kasashe, wanda a shekara sau daya yake hadata kuma baifi mutun biyar yake sayarma ba duk duniya, kuma da ita yake amfani yake kashe mutanen da suka nemi susha gabanshi, hankali atashe amar ya dago idanunshi sun kada sunyi jaaaa, jikinshi harya soma bari barr barr, ya kalli lanta adata saki futsri, yau karyarta ta kare asirinta ya tonu, yanxu ko tace zata falfala ta gudu bazata tsira ba, ammah ce ta kaste silence din ganin amar ya furgice lokaci guda, anatse ta tako inda suke tsaye don nesa kadan suke da dining tace   muhammad whats wrong? In tace bata son sha ku kyaleta mana 
Hanakali aatshe ammah tayi baya ganin yanda amar ya karade ya sauya, idanunshi sunyi jaaa fuskanshi ma tayi jajawur, lantana na ganin haka tayi saurin zubewa a gwiwarta ta dora hannu aka   na shiga uku ni abida wayyo allah na, yau karshena yazo, don darajar allah ku yafe min wallahi wallahi bayin kaina bane, sharrin shaidan ne na rantse da allah 
Kallonta amma tayi don bata gane kan zancen ba   ke lantana meke faruwa anan? Me kikayi da kike neman gafara 
  wallahi hajiya ba laifin&   tassss taji saukan marinda saida ya toshe mata kunnenta nan take taji wani dummmm saida ta yi baya, bata gama jin zafin marin bay a sake kwasheta da wani marin, fuskanshi yayi jaa sosai jikinshi har rawa yake,wanda yasa ammah da amra yi baya son sun tsorata da yanda suka ganshi, lantana dai ta tafi hutun wucin gadi kafin ta dawo ya sake ball da ita, aman ne yayi saurin taro shi yana kokarin kamashi ya hambare hannunshi gefe ya sake bata wani blow daya sata gangarawa har wajen parlor, dukda haka bai barta ba saida ya bita ya dunga kwallo da ita gaba daya ya fuce daga hayyacinshi, ammah na ganin zai kashe yar mutane tayi saurin bin bayanshi tana   muhammd kaii muhammd menene haka, dukan mace kakeyi? Kome tayi maka bai chanchanci kayi mata haka ba 
Ay muhammd fa ba sauraron ta yake ba, haka su amra sukabi bayan su suma aman ma da y agama gano komai yayi saurin bin bayansu don tabbas amar zai iya kasheta anan take, don haka yayi gaggawar janyo wayarshi ya soma kiran hukuma,
Ammah dake bin amar har suka fito tsakar gida yana ball da lantana tayi saurin kallon amra tace   aisha meke faruwa ne?, 
Kasa cewa komai amra tai don itama Karin bayani take nema, saida amar yayi mata lugu lugu idanunshi sunyi jaa sosai ya janyo wayarshi daga aljihunsa baya gani ma sosai yayi dialing number asad,yana picking azafafe yace  idan ka wuce 5 minutes baka zo nan gida b azan kashe wannan wicked soul din  yana kaiwa nan ya kashe wayar ya fara neman abunda zai dauka ya karasata, ganin wani karfe daga chan gefe yayi saurin juyawa ya dauko yayo kanta dashi, ammah na ganin haka ta dafe kirjinta tana innalillahi, Muhammad zaiyi kisa akan idanunta, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, bat agama tunani ba taji kwal ya bugama lantana a kafa daya saida kafar ta balle, daga hannu yayi zai sake buga mata amra tayi saurin tahowa inda yake ta rungumeshi ta baya   yayaa don allah calm down, karkayi abunda zakazo kayi dana sani 
Baya ji baya gani yace   sakeni, 
  wallahi bazan sakeka ba yaya, bazan taba bari kayi abunda zai jefa rayuwar ka a halaka ba, 
  aishaaaaaaaaa  ya daka mataa tsawa, dukda ta tsorata hakan baisa ta sakeshi ba, wani irin juyi yayi ya zubar da ita a kasa, nan take ta kwala uwar kara dayasa ammah ta kalleta, kankace me cikin kankanin lokacin ammah ta zube a kasa wanwas, jini na fita daga bakinta da hancinta hankali atashe salima ta kwala kara   ammahhhhhhhh!!!!! Wayyo allah na shiga uku 
Amra da bat agama dawowa daidai tana ganin ammah a yashe a kasa tayi saurin rarrafowa ta karaso wajen, ganin ammah a kwance hankali aatshe ta taba ammah tace   ammah ammah  jin shuru ya sata taba wajen zuciyar ammah, dipp komai ya tsaya chak, hankali atashe amra ta dago agigice ta kalli salima da aman da suka zagaye ammah tace   am& .mahhh..ta mutu.uu..  hannunta da bakinta duk karkarwa suke, da sauri ta miqe tsaye kamar mahaukaciya har veil dinta na faduwa ta kaarso inda amar ke bugun lantana da duk jini ya gaba malalewa a jikinta ga uban raunuka daya ji mata, amra na karasowa ta daka mashi tsawa daya sashi tsayawa babu shiri   amarrrrrrrrrr!!!!! idanunta sunyi jaa sosai sai sauke nunfashi takeyi
Da sauri ya waigo ya kalleta ya zuba mata idanunshi, tana ganin haka ta juya ta nuna mashi ammah   ammahhhh & ammahhh  
Ay baisan lokacin daya saki rodin ba taku biyu uku ya iso inda ammah ke kwance kamar gawa, salima a furgece ta dago tana kuka   ya aman wai ta mutu, ammah ta mutu, na shiga uku na wayyo allah na 
Amar daya tsaya kikam ya kasa yin komi, jikinshi na bari ya durkuso ina ammah ke kwance rai a hannun allah& & & [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: UPDATE
Unedited page
Ba tareda ya saurare ta ba ya janyo table din da chef din ya ajiye abuncin kafin ya fuce yace   bana son gardama eat 
Kauda kanta gefe tayi jiki amace tace   toilet nake son shiga 
Mikewa yayi ya sungumeta gaba dayanta, arazane ta juyo ta kalleshi, gaba daya bata da wani kuzari ajikinta don hka ta lafe a jikinshi har ya shige da ita bathroom din, yana shiga ya sauketa akan wc ya fuce daga bathroom,
Bayan fitarshi ta soma tube kayan jikinta tayi wanka da ruwan zafi sosai kozaji dadin jikin nata, tana gamawa ta dauro alwala jiki amace dukda tana jin jiri sosai.
Tana gamawa ta maida kayan asibitin ta fito anaste,lokacin dta fito yana zaune kan kujeran dake gefen gadon asibiti, ya dafe kanshi dake sara mashi, baiji alamun fitowanta ba saida ta rufo kofar bathroom din, dago kanshi yayi ganinta tsaye tana shirin takowa harta karaso baking ado kanta akasa, tana zuwa bakin gadon ta janyo jallabiyanta datazo asibitin da ita ajikinta, kokarin komawa bathroom tayi ganin haka yasa yayi saurin   let me excuse you 
Yana kaiwa nan ya juya ya fuce, da mamaki ta bishi da idanu kamar bashi ba,gaba daya yayi laushi sosai, tausayinshi ta soma ji lokacin data maida idanunta kan abuncin day ace taci, yanxu haka shima baici ba ta fada aranta,jiki a mace ta sauya kayan jikinta zuwa abayar nata kafin ta zauna a kan carpet ta tada sallah.
Tan idarwa ta koma kan gado ta lafe jikin gadon ko kallon abuncin batayi ba don bakinta ma daci yake mata sosai.

Wajen karfe daya tana nan zaune kafin ta miqe ta gyara mayafin abayarta ta fuce daga dakin, direct emergency ward ta wuce zuwa inda aka kwantar da ammah, anatse take tafiya kamar zata fadi harta karaso wajen, batama lura dashi ba, yana zaune daga gefen kujerun reception din ya dafe kanshi dake sara mashi sosai,
Gaban dakin da ammah ke ciki ta tsaya, ta jikin glass din kofar dankin take hangota hancinta maqale da oxygen dake taimaka mata waje fidda nunfashi, ba karamin tausayinta taji ba, ta kasa gane dalilin da zaisa lantana ta cutar da wannan baiwar allah, dan zaman datayi da ammah ta karanci halayyanta, macece mai tausayi da kaunar kowa, bata da ha inci kwata kwata ga son mutane ga hakuri uwa uba ga kyauta, batada matsala kwatakwata kowa nata ne, idan kowa bai shaide ammah ba toh tabbas ita da kannenta zasuyi mata sheda mai kyau don tayi masu komai a duniya, ammah uwace ta gari a gurin kowa.
Fashewa amra tayi da matsanancin kuka sosai tana wannan tunanin aranta harya dago kanshi don kwata kwata baijin motsin ta ba data karaso wajen ba sai yanxu, samun kanshi yayi da kallonta ba tare da tasan yana yi bama, kuka sosai takeyi kamar ranta tana tausayin ammah sosai, ayau koda ance ta bata zuciyarta zata iya, ba karamin tashin hankali ta shiga ba lokacin data ga lantana tana saa mata abu acikin drink, don bashine frist time da hakan ya faru ba, dukda bata kawo komai aranta daga farko ba saidai dole yanda lanata tayi acting kamar mara gaskia lokacin data shiga kitchen dinnan ya tabbatar matar mata da something is fishy, tana nan tsaye wani irin karar na ura ta soma tashi daga dakin, ammah dake kwace ta soma jijiga, zaro idanu amra tayi kan kace me saiga nurses gaba daya sun taho hanyar dakin harda likitoci guda biyu, hankali atashe amar ya miqe yazo gaban dakin inda amra ke tsaye, nurses na ganinsu bakin kofar suka ce   sir ku bamu waje, 
Hankali atashe amar yace   waaa& waaas& whats going on? Meke faruwa, you guys should fucking explain whats going on 
Ba tareda sun bashi amsa ba suka wuce cikin dakin gaba dayansu harda doctors din, nurse day ace kawai ta tsaya bakin kofar tana kokarin yi masu explaining,  sir dan allah ku kwantar da hankalinku, zamuyi iya kokarinmu akanta please 
Tana kaiwa nan ta koma cikin dakin suka dukufa akan ammah da likitoci, amra dai kasa tsayuwa tayi saida ta dafe bango, amar kuwa tunda ya kafama kofar idanu yana hango yanda suke fidda wasu na urori agaban ammah hankalinshi ya tashi, yanda likitocin ke zarya akan ammah suna kokari cetota, babu abunda amar ke fadi sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sun dauka kusan minti ashirin a gaban ammah suna kokarin daidaita bugun ziciyarta saidai kasha bun yaci tura, kafa masu idanu amar yayi ganin sun tsaya gaba dayansu, nan take gabanshi ya fadi dammm, bude kofar doctor yayi jiki a mace kanshi a kasa ya karaso inda amar ke tsaye yace   im so sor& . 
Janyo rigarshi amar yayi yace   what do you mean by that?, why are you sorry 
  yallabai sai hakuri, zuciyanta ya tsaya chak bata nunfashi babu abunda zamu iyayi im sor& . Doctor bai gama fadaba amar ya katseshi ya soma cewa
  innalillahi wa inna ilaihi rajiun, innalillahi wa inna ilahi rajiun  , nan take yayi baya yuuu zai fadi, cikin sauri doctor ya taroshi, mikewa amra tayi aguje ta karaso inda amar ke yashe a kasa babu numfashi yayi passing out, saurin kamo hannunshi tayi   yaya yaya dan allah ka tashi na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login