Showing 333001 words to 336000 words out of 381117 words

Chapter 112 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2050

salima dake tsaye dan nesa dashi kadan tana daukan hotuna ita da kawayen ta, daya daga cikin kawayen nata ne ta dan tabota tace  kaii sal wannan yayan naki Akwai kyau Wallahi, dama& 
 Shut up Malama, shi Zan aura fah kike maganan banzan nan
Aman dake gefensu yana jinta ya soma dariya, yanda tayi maganan is so funny, ahanakli ya karasa inda take fuskanshi dauke da murmushi, tun kafin ya karaso inda yake ma Tayi saurin tunkararsa tana Galla mashi harara,  muje chan mu zauna, waennan Yan sa idon har sun fara kai maka hari
Tana kaiwa nan ta ja hannunshi suka wuce wajen chairs don garden sun school.
Suna zama ya zaro jakar da yake boyewa a bayanshi ya Mika mata, kallon hannunshi tayi kafin ta karba jakar tana murmushi,  yaya ashe zaka bani gift
 Yea love Nina isa naqi bada gift, yaufa is one of our special day, now open it
Ahankali ta soma bude jakar, tana budewa taga kwali anyi amshi wrapping, dagowa tayi ta dan kalleshi, kifta mata idanu yayi don haka ta maida idanunta kan kwalin, ahankali ta soma bude wrap din, tana budewa taga kwalin waya iPhone 14 pro max sabuwa dal, cikin sauri ta dago da idanunta ta kalleshi kafin Tayi saurin rungumeshi,  laaa iphone, iPhone 14 yaya thank you so so much love
Ba karamin dadi yaji ba yanda ta nuna farin cikinta sosai  thank you yaya Allah ya azurtaka ya saka da alkairi I love you so much ta karashe tana kai mashi peck a kumatu, tsabar murna batama san tayi ba.
Saida ta dago ta maida idanu ta kan kwali tana jujuyawa, shiko kasa motsawa yayi,fadin irin farin cikin da yake ciki bata lokaci ne, finally ta furta mashi abida he has been longing for tun last time data fada, baby say it again
Dagowa ta kifta mashi idanu alamu bata gane ba,  you mean I love you? Ta tambayeshi saurin runtse idanunshi yayi ya sumbaci hannunta  I love you too so so much, I can t wait to make you my wife, zaki haifa jin babies ko?
Saurin rufe idanunta tayi kafin ta mike ta shige hall, shiko da idanu ya bita yana godiya ga Allah don sai yanxu yasan rayuwarshi ta sauya ba kamar ta da ba.


Bangaren Amar tunda suka fito daga school dinsu salima yake kakin calls,Cikin Yan mintuna qalilan suka iso gidan,yana parking bai ma tsaya sun gama fitowa daga motar ba ya wuce cikin gidan yana receiving emergency call.

Atare ammah da amra da Salim suka fito daga cikin motar, ammah ce ma ta tsaya ta rufe mashi motar ta zare key din motar kafin su wuce cikin gidan, suna shiga amra ta wuce sama zuwa dakinta don agajiye take, ammah ma part dinta ta wuce ta sauya kaya.

Bayan ya shiga dakinsa, a gaggauce ya zaro traveling bag dinshi da laptop dinshi saida ya gama shirya Duk wani abu dayasan zai buqata kafin ya wuce bathroom ya sakarma kanshi ruwan dumi, ya dan dade tsaye a tsakiyan shower ruwa na sauka akanshi, yanda ya dafe gaban shower nitch da hannayenshi babu abunda yake tunani sai amra, haka kawai ya tsinci kanshi da tunanin ta wannan lokaci kafin ya fito daga bathroom din waist dinshi nade da towel, a gaggauce ya fara shirinsa,cikin Yan mintuna qalilan ya gama shirin nasa kafin ya janyo baggage dinshi da laptop bag dinshi ya fuce daga dakin.
Koda ya fito sitting room saida na kalleshi na sake kallonshi, fadin irin kyau da yayi ma bata lokaci ne, kakin sa ne a jikinsa da five stars dinshi maqale a gefen right shoulder dinshi, kafanshi kuwa sanye yake da boot dinshi same color da kakin sa, cikin kamewa yake tafiya harya karaso sitting room, ganin babu kowa yasa ya ajiye baggage da laptop bag dinshi anan sitting room din kafin ya wuce sama cikin natsuwa,
Da sallama ya bude dakin ammah, a zaune ya taddata tana latsa waya, idanunta sanye da farin glass na karfin idanu, karaso yayi inda take zaune bakin gado ya dan duka ya kamo hannunta cikin nashi, fuskanshi gwanin nan tausayi ya soma magana  ammah na, Har yanxu kina fushi dani ko? Ina rokon ki yafemin, I m so sorry bazan iya tafiya da fushinki akaina ba,
Da farko daya durkuso gabanta kauda kanta tayi don Har lokacin fushi take dashi kuka tana son ta nuna mashi kuskuren sa sosai,kallonshi ammah tayi nan take taji wani irin tausayin da kaunar sa a zuciyarta, Muhammad is her world shine komai nata, shine farin cikinta don shi kadai Allah ya bata, bazata so ya tafi da tunanin tana fushi dashi ba.
Hannunta daya ta sanya ta dago da fuskanshi kafin ta sauke mashi murmushi, shafa sajenshi ta danyi kafin ta soma magana  Allah ubangiji ya kiyaye ya tsareka ya dawo mana dakai lafiya, bakayi min komai ba, na yafe maka
Wani irin dadi ne yaji ya ziyarce shi, cikin sauri ya mike ya rungumeta tsam kamar za a kwace mashi ita,  thank you ammah na, I love so so much, please take care of your self, da yaran
Dan bubuga bayanshi ammah tayi har lokacin fuskanta dauke da murmushi  Insha Allah, take care of your self as well,
 Insha Allah ammah na ya fada yana sakinta fuskanshi dauke da murmushin jin dadi,  yaushe zaka dawo? Ammah ta sake tambayarshi
Nunfasawa yayi kafin ya dan dago ya kalleta,  Wallahi I don t know ammah, amma Muna gamawa Zan dawo
 Toh Allah ya kiyaye ya tsareka
 Ameen ya rabb bye ammah yana kaiwa nan yayi mata sallama, idanunshi Har sun danyi jaa sosai saboda kewarta daya farayi, yana futa daga dakin ammah ta zauna bakin gado gabanta na faduwa kamar this is the last time da zata ganshi, ahankali hawaye ya soma sauka akan fuskanta, wannan hawaye ya kasance kamar routine a wajen Duk sanda yazo niger idan zai koma saita zuba da hawaye, hankalinta yafi kwanciya idan tana tare da dashi koda yaushe saidai bazata hanashi yin abunda yake so ba, abu daya ne yanxu take tunawa saitaji sanyi aranta.

Amar na futowa daga dakin ammah ya dan tsaya a corridor tsakanin dakunan nan saman,kasa daga kafafunshi yayi idanunshi na kan kofar dakin ta, da kyar ya tattara kuzarinshi ya soma takowa zuwa dakin nata, dan tsayawa yayi jim kamar mai wani tunani kafin ya danyi knocking, amra dake zaune, tun bayan futowanta daga toilet bayan tayi wanka ta kasa motsawa saboda wani azababban ciwon kai daya kawo mata ziyara a tsakiyan kanta sai bayanta daya dan rike saboda tsayuwan da sukayi wajen daukar hoton graduation din Salima, tana nan zauna ta dafe kanta ko kaya bata saka ba tana zaune da pink towel dinta don Har lokacin bata son saka kaya saboda yana takura ta, knocking din da akayi ne yasa ta dan dago kanta don Duk a tunaninta ammah ne  yea come in ta fada ahankali muryanta chan kasa tana kokarin rike dafe bayanta da hannu daya tana  washh
Ahanakli ya bude kofar ya shugo anatse kafin ya rufe kofar ya tsaya yana binta da idanu.
Jin shuru yasa ta dan dago da kanta, nan idanunta ya sauka a nashi, sai kamshinsa daya bade dakin gaba daya lokaci guda,
Saurin kauda kanta tayi gefe ta mike tsaye ta nufi hanyar bathroom yana Ganin haka yayi saurin takowa zuwa inda take, cikin sauri ya kama hannunta  Aisha!!!
Chak ta tsaya ta kasa motsawa don gab take da shigewa bathroom din gashi ya rike hannunta, ahanakli ya Kara matsawa inda take ya tsaya a bayanta  Aisha please!!!
Gabanta ne ya dan fadi yanda yake mata magana da yanda ya kira suna ta calming kamar bashi ba sai taji kamar wani Amar dinne a tsaye a bayanta bashi general din data sani ba, kokarin kwace hannunta ta fara yi, yana Ganin haka ya rike hannun nata sosai kafin ya dan juyo da juyo da ita tana fuskantarshi, kasa dagowa tayi ta kalleshi kanta a kasa, fuskanta a hade babu annuri ko kadan,  Aisha please look up ya fada in a calming tone, Har voice dinshi na cracking
Samun kanta tayi da dagowa ta kafe shi da idanu Har lokacin bata sakin fuskanta ba,
Bakinsa ya soma budewa yana son ya fada mata abu ya kasa, haka ya dunga mimicking ya gaza Tara courage dinshi, ganin haka yasa Tayi saurin kauda idanunta akanshi  Zan shiga bathroom tana kaiwa nan ta zame hannunta daga nashi ta juya mashi baya ta nufi hanyar bathroom
Taku daya yayi ya cinmmata tare da rungumeta, ya hade bayanta da kirjinshi, Lumshe idanu yayi yana jin wani irin natsuwa na zuwan mashi, itako tunda ya rungumeta taji ranta ya baci sosai, kokarin kwacewa ta soma yi ya qi bata damar haka don kwakwaran rungume yayi mata, ahankali ya sauke kanshi daidai kafadarta, ahanakli yake sauke mata nunfashi anan wajen kafin ya matso da fuskanshi daidai wuyanta, yana sauke fuskanshi a wajen ta lankwasar da wuyanta,
Daidai bakinshi yayi wajen kunnenta kafin ya soma magana ahankali kamar mai rada  I m sorry ayeeeshhh& .I m sorry for what I did the other time
Yana kaiwa nan ya saketa tare da juyo da ita sautin fuskanshi ya saqalo hannunshi a kugunta kafin ya matso da fuskanshi saurin fuskanta nunafshinsu na gugan na juna,  I& I& .
Saurin katseshi tayi ta hanyar yin baya ta nunfashinta na fita sama sama, hawaye na gangarowa daga fuskanta, amaimakon kalamanshi su mata dadi sai suka bakanta mata zuciya, ya kaita maqura sosai inda take jin bata kaunar ganinshi ko kadan saboda abunda yaso yi kata shekaran jiyan, she begged him, but bai damu ba he s selfish kanshi kawai ya sani, bayan abunda ya mata sai Yanxu kuma yazo yace sorry? Me yake nufi kenan? Ta hakura daga just saying sorry,
Saurin girgiza kanta tayi tana tunanin tana hawaye  no no,
Ta dunga furtawa a zuciyarta, ya kaita bango sosai bazata iyaba, sorry dinshi is nothing to her compare to abunda ya mata all this while, Yan a Ganin haka ya soma matsawa inda take  stop please karka matso inda nake
Chak ya tsaya jiki shi ya mutu sosai, harga Allah so yake yayi reconciling da ita Kodan saboda ammah don yasan tabbas bata huce dashi ba, dazun ma ta kulashi ne saboda zai tafi badan haka ba bazai ga murmushi ta bama.
 Why? Ya tambayeta kai tsaye
Dan dago da jajayen idanunta tayi ta mashi kallo daya kafin ta sauke idanun nata ta kauda kanta gefe, yana Ganin haka yasa ya juya ba tare da yace mata komai ba,saida yazo daidai kofar futa daga dakin ya dan jinkirta  take care of your self and your siblings
Yan kaiwa nan ya fuce daga cikin dakin, yana futa ta shige bathroom sai hawaye,haka nan ta dunga kuka?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, ta dade sosai a cikin bathroom din tana hawaye kafin ta wanke fuskanta ta dawo cikin bedroom din.

Amar kuwa yana futa daga dakin amra ya sauko kasa, kai tsaye ya nufi Inda yabar jakanshi.
Saida ya karaso ma ya Lura da ammah dake zaune a sitting room din, sanye take da hijab tundaga sama Har kasa, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi kafin ta mike ta tako Har Ind a yake ta karba laptop bag dinshi, yana Ganin haka ya rike hannunta suka fuce zuwa inda driver yayi parking, suna karasowa shida ammah ya saki hannunta ya dan rungumeta yace  bye ammah take care of your self for me pls
 I will son, kaima Ka kula da kanka, don t forget to call us idan kaje chan
 I will Insha Allah ammah na yana kaiwa nan ya shige bayan motar driver yaja motar suka fuce daga gidan,
Jiki a mace ammah ta juya ta koma cikin gidan tana mai yi mashi addauar kariya da tsari.

Wunin ranar dai ammah da amra sunyi shi ne cikin rashin jin dadi,kowannen su na zaune a daki, karshe dai amra barci tayi wanda ya fusge ta batare da ta sani ba, while ammah kuwa tunda ta zauna kan sallaya bata mike ba tun bayan sallan dhuru datayi.

Amar kuwa suna fita da motar airport suka wuce direct, suna isa airport management suka shaida zuwanshi don haka takanas Aka saka mutun daya daga cikin officials yayi masu jagora zuwa wajen jets departures, bai fito daga cikin motarshi ba Har suka iso babban cikin da jet ke sauka, daga dan nesa jirgin driver yayi parking, ahankali amar ya futo anatse hannunshi cikin wandon kakin sa,kwarjinin sa ya gama cika wajen gaba daya, ahankali ya soma takowa cikin kamewa while wasu officials biyu na rike da baggage dinshi da laptop bag dinshi, direct gaban jirgin uae armed force ya tsaya, saida ya dan tsaya ya suke nauyayyiyar ajiyar zuciya kafin yayi addua yana gama wa fara hawa matattakalar jirgin, tundaga kan steps din jirgin yaranshi dake tsaye sunsha uniform dinsu kowannen hannunsa rike da manya manyan bindigu kamar zasuje yaqi, fuskokinsu a rufe da wani black helmet, sai inner bullet prove Riga da Kowannen su ya daura akan kakin, haka suka dunga Sara mashi Har ya shige cikin jirgin kafin su bi bayanshi, su kansu zasu kai akalla su talatin, wani special waje aka bashi nan ya zauna ya daura kafa daya kan daya, cikin sauri m5 y a karaso inda yake shi baima saka helmet dinba don Ana Ganin fuskanshi,  welcoming sir m5 ya fada yana kamewa, kallonshi Amar yyi kafin yace  drop the formalities, seat
Zama m5 yayi ind a yake mashi nuni nan opposite kujeran da yake zaune, nan ya buqaci da yayi mashi bayani akan operation din da komai daya kamata ya sani.

Cikin Yan mintuna qalilan jirgin su ya daga sararin samaniya& ..
Adawo lpy sir general=?-?

Yau kwana biyu kenan bayan tafiyar Amar, gidan yayi shuru kamar an dauke masu annurin gidan, ammah kullum tana daki, abu daya ke fiddata daga daki shine dubo amra don sanin yanda ta Tashi, aranar da Amar ya tafi wahee gari ya chanza masu securities na gidan gaba daya, Banda baba mai gadi, sannan ya sanya asad yayi mashi inspecting wani babban company da suke kawo helps daga wata kasar, nan yasa asad yayi mashi kwakwaran buncike akansu kafin a kawosu gidan, ya mata ne guda biyu akalla zasukai shekaru talatin talatin, dukkansu Yan phillipines ne, bai yarda ya kawo Yan Nigeria ba,
Salima ne tayi kokarin training dinsu akan ayyukan gidan don kusan a tare suke yin komai, daya danganci abunci don basu iya abuncin mu na nan Nigeria ba,yanxu ayyukan gidan Duk ya koma hannunsu.
Yau sati guda kenan da graduation din salima, don haka amra tayi deciding fada mata komai, don daman dalilin dayasa ta ki fada mata was saboda Karta fada ma Aman don idan ta fada mashi zai ita fada ma Amar shiyasa ta qi fada mata a wanchan lokacin, yanxu kuwa inka ga yanda suke ma junansu kamar zasu cinye juna.

Zaune take akan gado hankali kwance tana chan mango da salima ta yanka mata,ayanxu bata da wata damuwa kwata kwata, don daman Amar ne ke bata ciwon kai, tun bayan tafiyarshi kuwa hankalinta ya dan kwanta, bata wani damu ba da alamarinshi don harta ma manta dashi saboda basu da wani memories mai dadi da zaisa ta tuna dashi saidai sometimes yakan dan fado mata arai.
Sallama salima tayi hannunta rike da wani plate din ta sake yanko mata saboda ta buqaci hakan, tana zuwa gaban gadon ta ajiye mata akan gado tana turo baki don hira take da habibinta a sabuwar wayar daya bata don yaje office shine ammah ta tado akan tazo ta yanka ma amra mango.
 Gashi nan, dan Allah abarni na huta haka nan, Wallahi adda lamarinki gaba yakeyi kamar wata mai ciki tana kaiwa nan ta juya, amra kuwa mai zatayi Banda dariya din haka Tayi saurin katseta  ba laifina bane laifin danki ne ay
Da sauri salima ta juyo don bata gane inda ta Dosa ba, shafa belly bump dinta tayi kafin ta maida kallonta kan salima  kingani ba? Shike damunki bani ba
Da sauri salima ta tako inda take idanunta a waje Bakinta ya kasa rufuwa ta shafa cikin amra  adda baby ne anan?
Salima ta fada tana shafa cikin amra, girgiza mata kai amra tayi tace  yes& 
Fadin irin farin cikin da salima ta shiga a wannan rana bata lokaci ne don kowa saida ya shaida hakan a gidan, she s so happy Harda dan kukanta.


After one months& .
A kwana a Tashi babu wuya yau wata guda kenan da tafiyar Amar, ayanxu hankalin ammah ya gama Tashi, wata guda kenan tun bayan tafiyarshi da sukayi waya sau daya lokacin daya shaida mata sun isa wajen operation inda bai fada mata ba saboda basa fadin work related to anyone hatta family wannan dokar sojoji ce.
Fadin irin tashin hankalin da ammah ke ciki bata lokaci ne ta rame sosai saboda tunanin Amar, this is the first time hankalinta ya Tashi da tafiyar da yayi don this is not the first time yake tafiya operations, don Duk sanda zaije koda yana chan dubai saiya fada mata kuma haka zasuyi kusan wata biyu basuyi magana ba idan yana chan Duk bata damuwa saidai akasin na wannan Karan abun ya dameta sosai, Wai irin unnecessary tunani take yi aranta wanda ada bata yinsu kwata kwata,  what if wani abu ya sameshi? What if something is wrong? Kullum tambayar da take ma kanta kenan, abunda yafi damunta shine sai yanxu take dana samun fada mashi maganar cikin amra.
Tana nan zaune amra ta shugo dakin, kallonta nayi sama Har kasa sanye take da doguwar rigar atamfa bubu anyi nata free gown da ita, tayi wani irin bulbul skin dinta yayi haske sosai kamar jini zai fita, fuskanta tayi fayau, ga dan baby bump dinta daya futo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login