Showing 66001 words to 69000 words out of 381117 words

Chapter 23 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1979

kota taqi maida hnaklinta wajen yin karatu yanda ya kamata, Ibrahim kuwa bayan wucewar haj labiba ya wuce cikin mota haladu ya danna horn driver ya wangale masu gate suka wuce da gudu, malam audu na rufe gate ya koma kan bencinsa da yake zama a bakin gate a waje yana shan iska, nan yan abokanan sa suke zuwa susha hira suna tsaida masu talle suna sayan gyada da rake, malam audu irin masu gadin nan ne da tsegumi baya wuce bakinsu, yana nan zaune abokinshi iliya ya karaso kamar kullum hannunshi rike da ledar shayi da burodi harda soyayyan kwai da yake sayo musu suna ci, ganin shi yasa mlm audu wangame baki yace   ah ah abokina iliya, yauma ganimar zamu kwasa, kaidai baka gajiya da hira, kullum saikazo hira,  dariya wanda aka kira da iliya yayi ya zauna gefen bencin suka gaisa kafin audu ya dakko masu kofi suka rama shayin suka kora da burodi da kwai saida sukaci sukayi nak kafin audu ya soma Magana   kai abokina wallahi mutanen gidan nan basu da Imani ko kadan  , da sauri iliya ya soma maganar irin ta mutanen da sukayi zaman legas don kwata kwata ba bahaushe bane amma zama da yan arewa yasa hausa ta zauna radau a bakinshi, kallonshi iliya yayi kamar wanda yake jiran zancen yace   mazaa ya akayi bani labara maisa kace haka don ni ina ganin masu gidan nan kamar sunada mutunci  ..tsaki kawai audu yayi yace   wallahi a fuska ne amma waennnan da kake gani mugaye ne na karshe wallahi, nan ya fara bashi labarin yanda suka shiga dakinsu saluma suka gansu kamar gwawawwaki da irin bakar wahalar rayuwa da suke ciki, kai karshe harda rayuwar da su amra sukayi tun farkon zuwan su har zuwa lokacin da ta tafi karatun har labarin fyade itama da wahab ya mata da yanda itama salima Ibrahim yaso yi mata amma allah ya kubutar dasu da yanda alhaji ke wulaqantar da rayuwar su kamar ba yayan qaninshi ba, sannan ya kora mashi da hakkin yaran bazai bar alhaji mustapha ba da iyalanshi don tun a gidan duniya shima iyalanshi sun fara shiga cikin babbar matsala gashi yanxu an kama danshi dake safarar miyagun kwayoyi zuwa manya manyan kasashe daban daban har kawo yanxu babu wanda yasan inda yaran yake yana kaiwa karshe iliya ya karbe da   kai amma mutanen nan anyi azzalumai, allah ya saka masu, dana dam babu tabbas, duk wannan abun ace yayan dan uwanka jininka don kasa ta rufe mashi ido shikenan sai jinisa da ya kamata a basu kyakyawar kulawa su ake walaqantarwa, yana kaiwa nan ya zaro wayarshi ya danyi yan latse latsen shi kafin ya miqe yace   to abokina sai gobe idan na dawo, Allah ya basu lpy akwai aikin da zanje nayi, kasan talaka bawan allah saida nema  ..yana kaiwa nan sukayi sallama ya wucewarshi.
Iliya na wuce hanyar gidan ya cire mustache din daya manna a gaban bakinshi ya cizge gashi daya manna cikin facing cap, wipes ya zaro ya goge yan pente pente da yayi ma fuskarshi saida y agama ya dago kanshi, wani mutumin ne daban ba iliyan da audu suka sha hira dashi ba, wannan kana ganinshi kaga tantiran yan legas, kanshi ma sol yake babu digon gashi, wayarshi ya daga yayi yan typings sannan ya tura komai da yayi recording lokacin da suke Magana da audu da duk wani information daya samu daga wajen shi,yana sending ya tari mai mashin ya wuce abinshi.
?
Kano private hospital& .
Muhammad na isa asibitin da kanshi yaje ya duba su, bakamar jiya ba har sun dan marmare don kuwa salima harta dan watsake saidai itama bata farfado ba amma an gyara ta, an wanke kanta dake da muguwar dauda har waka saida nurses suka mata a kwance, shima salim an gyara shi saidai shi yayi wani irin haske kamar gawa jikinshi yayi wani irin sandarewa don har lokacin bai yana coma, ammma ana fatan ya tashi anytime soon, anan asibitin ya wuce shida ya kamat ya fara aiki Monday sai gashi yayi reporting tun ranar friday, wunin ranar shine ke dubasu da assistant dinshi, every 2 hours saiya dubasu har aka cire drip din salima sai jiran farfadowarta ita,
Karfe tara daidai na dare ya koma gida agajiya, saida yayi wanka ya saka jellabiya ya rama sallar da bai samu yayi ba kafin a wuce dakin mama kareema, yana shiga tana zaune gaban gadonta ta rabka uban tagumi, gefen khady ce wadda take ta rafka uban bacci kamar wadda tayi maye, abugen take saidai karyar data zagba ma maman nata na cewa ciwon kai takeyi wanda ya jawo mata jin juwa akanta, tana nan zaune har barci ya kwashe don tayi high sosai, haj kareema wanda tunanin duniya ya mata yawa na rashin Ibrahim yasa batama gane cewa khady a buge take ba, saida tashi muryarshi kafin yta dawo nutsuwarta,   mama is everything okay?akwai wani abu dake damunki ne  & gyara zamanta tayi tace   daga ina kake tun safe muhammad  & atakaice yace   naje asibiti  na dauka sai Monday zaka koma duty m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aisa ka koma yau?,&   inada patients ne shiyasa na fara yau  .. nunfasa tayi kafin ya sake kallonshi   yayan badaru kakai asibiti ina yayan badarun suke, waima tukunna ina ruwanka Muhammad da rayuwar wasu,  , mamaki ne karara dauke a fuskar shi ?don baiyi tunanin ta haka zatayi tambayar ba ya dauka zata tambayi ya lafiyar dasuke ciki, jinjina kanshi yayi aranshi yace   lallai akwai matsala, what going on in this house meke faruwa ne  , bai amsata ba yace   mama abinci fa,  im hungry,  , ganin bai amsata ba yasa ta bar zancen kawai don batason karama kanta matsala kan wadda take ciki ta rashin jin labarin Ibrahim kamar an shafe babin rayuwar sag aba daya, abinda yafi damunta yanda dady ya nuna bai damuba kwata kwata. Anan yaci abinci sukayi sallama ya koma dakinshi ya kwanta abinshi. 90-91
Dubai uae& ..
Satinta biyu da dawowa daga asibiti ta koma office inda suka samu zama sosai ita haifa wanda sun kwana biyu sosai basu hadu ba, murna sukeyi sosai dan yanxu aiki ne sosai a gabansu ita da haifa, don yanxu har time din tashinsu ya chanza daga 4 zuwa 5:30 wanda general ne ya chanza haka, oga kwata kwata sir general amar Kenan, tun bayan sun koma aiki ganin juna ya zame masu abin wuya don ita dadin haka take ji don yanxu ta koyi kama kanta bata shiga sabgarshi sannan tana kokarin danne tsoranshi da take ji idan ta ganshi, babu abinda ke hada ta dashi sai gaisuwa bayan wannan kuwa ko kallo basu damu dayi ma juna ba, yanxu tayi settle da zaman apartment dinshi harta saba, wataran idan ya fita baya dawowa ma saiya kwana biyu uku har biyar bainshugo ba kuma bata damu da hakan ba don kowa rayuwarshi yake, duk lokacin office kuwa baya neman ya rage mata hanya itama kuwa bata buqatar haka kullum da safe tana shiryawa zatayi requesting ride azo a dauketa ta ta wuce lokacin tashi nayi ta dawo, yanxu kusan watansu daya da komawa office kuma duk wata saitaje ta diba blood sample dinshi kamar yanda ta saba a baya anan ne ma kawai take samu ganinshi a office, cikin headquarters kuwa few mutane sukasan oga general yayi aure don yawanci daga asibiti ne gossip din ya fara wanda haifa ce ta haddasa shi kuma tayi hakan ne da gayya don idan anzo investigation ko an biyo ta hanyar headquater za a samu shedu cewa akwai aure tsakanin sir general da intern amra, tun gossip din na damu amra har yazo ya daina damunta, yaxu haka ma wasu basa kiranta yanda suke kiranta ada wato intern mss badaru saidai ma, ko ina ma tun tana dauke ido harta saba ahankali ahankali gossip ke shigewa har cikin headquarters wanda yawanci daga ma aikata mata wanda suke kishi da ita don general ya zama kamar secret crush din kowa harda sojoji mata dake cikin headquater zuqa zuqan mata kyawawa sosai, ayanxu hankalinta yadan kwanta sosai don aiki takeyi sosai har allah allah take su gama haousemanship ta koma school ta karashe duk wani abunda zatayi daya rage mata don ta samu tabar kasar dukda har yanxu tana kwadaituwa da samun katin kasar don yanxu fargabarta day ace, kudin da daddy yace zata biyashi, don ayanxu ya daina tura mata upkeep daya saba dole saida savings dinta take amfani, yawan idan damuwar tayi mata yawa in haifa ta lura da ita tayi mata tambayar menene matsalarta saidai ta boye mata don haifa tayi mata abubuwa da dama wanda ahakan ma tana gode mata.
Yau watan auren su biyar cur, wanda kullum cikin lissafi take don tun bayan da suka cike form din citizenship da take nema tun farkon watan auren har yanxu shiru ba a nemesu ba, ganin haka yasa duk suka sakankance itada shi, itadai burintaa kawai ta samu katin kasar inhar kuwa bata samu ba harta karasa makaranta tofa zata tafi ne kawai don bazata zauna ba, zaman shekara uku da tayi duk tayi shi ne cikin kunci da zulumin halinda kannenta suke ciki. sati guda Kenan rabonshi da gidan wanda hakan yasa ta sake sosai tana tashi daga bacci ta wuce dakinsa kamar koda yaushe idan baya nan haka ta gyara mashi dakin fess fess saidai a kiyayi hannunta daga taba mashi duk wani abubuwan amfaninshi, har wani haushi take ji idan yana kafafa akan taba mashi abubuwan, da yanda yake magan   yen yen yen don t you dare touch my belongings amma ya iya barin abokinshi ya shugo dakinshi dukda baya nan, ta gama fadi tana tabe baki bayan ta kwaiwayi yanda yake Magana da gunguni irin yanda yake Magana, tunawa da yanda hammam ke zuwa gidan cikin yan kwanaki dukda yasan cewa baya gidan kuma ta fadi mashi amma haka zaizo ya wuce dakinsa ya dade kafin ya futo ya mata sallama ya wuce, akwai ranar da yazo ya kafeta da wani irin kallo wanda samm ta kasa gane ma anar kallon karshe ma dai miqewa tayi ta koma kuryar kitchen ta zauna tana dafa abincin da bata shirya ba nan ma bai kyaleta ba har ta gaji ta juyo tace mashi   uhm bana tunanin yanxu zai dawo amma zaka iya tafiya gobe saika dawo koka kirashi kaji idan zai dawo anjima saika dawo  , murmushi kawai yayi still yana kallonta yace   okay alllah ya aimu goben  yasa kai ya fuce, ..bata son kawo wani tunani aranta don tasan yanda haifa ke qaunar hammam sannan bata son yi mashi muguwar fassara shiyasa tabar maganar a cikin ranta, washe gari ma dai ya dawo kamar yanda ya saba kai tsaye ya shigo byan ya danna pin saijin budewar kofa tayi don ko knocking baya yi, azaune ya tadda ta saida suka gaisa kafin ya wuce dakin amar still yasan cewa baya nan, zama tayi tana tunani idan zata kirga yau kwana biyar Kenan yana zuwa ajere sannan da salo daban daban saidai ta hana kaanta da mashi mumunan fassara don tare ta gansu kuma taga yanda suke tsakanin su, dukda haka zuciyarta azalzaalarta take amma ta ?dage ta hana kanta yin abinda zuciyarta ke saka mata na ta shiga cikin dakin taga me yake gudun sharrin shedan gashi dagashi sai ita a gidan yasa taki zuwa duba me yake yi acikin dakin hakan yasa tayi zamanta harya futo bayan 30mins da shiganshi sannan yace   uhm zan tafi na jira bai dawoba, if ya dawo ki fada mashi nazo  ..cikin harshen larabci ya gama kafin sukayi sallama ya fuce, yana fuce ta shige dakin, da safe ta share dakin so zata iya tantance idan akwai abinda aka sauya mashi guri, ganin duk inda ta gyara daga gadonshi zuwa tsakar wajen yasa ta kawar da zancen kawai har zata fuce ta tsaya ta juyo ta zubama gefen bedside dinshi ido tachan dayan barin gefen gadon, takowa tayi har gaban wajen kafin ta tsaya, idanu ta kurama wajen wanda files ne nashi da laptop dinshi wanda yake yawan ajewa a gidan, hannu takai wajen daidai kan laptop din kafin kuma ta dauke hannunta kawai don tuna gargadinshi akan kayanshi amma tana mamaki don kamar da tayi gyaran gado ta danyi goge goge ba a juye ta hango laptop dinba ganin ta kasa gane komai yasa ta juya kawai ta fice.
Firgigif ta dawo daga dogon tunanin hammam da chanji da ta gani daga wajen shi dukda ta tsame kanta kuma babu ruwanta, hakan yasa ta wuce cikin toilet saida ta gyara fess kafin tayi wanka ta mulka mayukanta wanda ta kwaso su da sabulanta da skincare dinta duka, mulka scrup din tayi a jikinta sannan ta wanke kanta da shampoo masu shegen kamshi na l orel wanda ya sanya gashin nata santsi sosai, tana gamawa ta wanke duk wani lungu da sako na jikinta wanda a yan kwanakin nan take jin sanyin zuciya da kwanciyar hankali haka kawai, don tana jin kamar kannenta na cikin kwanciyar hankali, ta dauki hakan ne sbd yanda ta dukufa da addua akansu har allah ya sanyaya mata zuciyarta, tana gama wanka ta nado kanta cikin towel mai laushi peach color, babban kuma nade a kirjinta wanda yadan rufe mazaunanta, santala santalan cinyoyinta abayyane sai shek sukeyi don har wani walwali takeyi sosai, yau kusan wata biyar Kenan ta zaro sabulun da ummi maman haifa ta bata ta soma amfani dashi shima acikin kayanta ta gano shi, sabulun wani rirn secret ne kunshe a cikinsa, wanda ke sa jikinta sulbi da taushi kamar fatar jariri, ita kanta idan ta shafa jikinta wani ririn dadi take ji, ga hutu ya zauna sosai a jikinta da dan nutsuwa data samu, har wani irin cickowa kirjinta yayi wanda tudun kirjin nata ya bayyana ta sama dan yanda ta daura towel din sai yayi kamar ta buntsuro su gaba gwanin birgewa, tattara duk kayan wankanta tayi ta saka acikin bath bag dinta ta futo tana dan waqa tare da juyi saida ta zo tsakiyan dakin ta dan wani rankwafa in a stylish way ta juya mazaunan ta tana fadin   oh baby let me whine my waist  , wannan ce favourite waqanta sosai shiyasa koda yaushe takan dan taka idan tana y, takawa tayi gaban socket din dakin ta kashe burner din da ta kunna a dakin kafin ta fuce, tana zuwa tsakiyan parlor ta jizge towel din kanta curly gashinta suga zubo har kafdunta, ruwan gashin na diga a kafadarta zuwa kirjinta, bata tsaya shafa mai ba jin kaurin abinci data dora yasa a guje ta karasa gaban gass cooker ta kashe ta sauke tukuyar don abincin har ya fara kamawa, saida ta sauke ta dawo natsuwar ta don duk ta daburce har kauri ya fara mamaye parlor ta juya ta fara takowa zuwa parlor tsayawa chak tayi bata juyo ba jin kamshin sa wanda ya kama duka gidan sosai itama kanta ya kama jikinta,girgiza kai tayi azuciyarta tace   oh yaya badai kamshi ba  , buge bakinta tayi tace   wai yaya yaushe ya zama yayan naki, kalan dangi  tabe baki ta kuma yi tana gunguni tace   wannan mafadacin hmm Allah ya hadaka da daidai kai  & & anatse ta daga kafarta ta cigaba da wakanta ta juyi left and right, amar wanda bai dade da shugowaba jin kauri yasa yaja ya tsaya bai tako ba harta zo ta tsaya tsakiyan walk way din tsakanin kitchen da parlor, runtse idanunshi yayi wani irin bugawa kirjinshi nayi, gwalo idanu yayi jin furucinta na karshe   waye ne mafadacin  ,,,,ay da sauri ta tsaya kirjinta ya bada dammmm, da sauri ta juyo tana fuskantar, don harya tako yazo dab da bayanta, yana shaker kamshin bady wash dinta da tururin zafin hot bath din da tayi sai abin ya bada wani succulent serene a wajen, tsit kake ji nunfashin ma da kyar take fuddawa harta karasa juyowa ta fuskanceshi,   ya allah  ya furta chan kasan maqoshinsa, yanda gashin ta ke dripping zuwa wuyanta har kirjinta ya zubama idn=anun, lokaci guda idanunshi suka soma lunlumshewa runtse idanun yayi ya sake cewa   uhmm??  alamun ta bashi amsa, baki na karkarwa dukta daburce ta soma Magana, kafinma ta karasa don baya baya takeyi santsi ya kwashe saura kirish ta fadi, da sauri ya cire hannunshi daya dake cikin aljihu dayan kuma yana ciki bai cire bay a saqalo da hannusnhi around her tiny waist, da sauri ya fusgota ta bugi kirjinshi, har saida ta dago kanta yanda yafita tsayi sosai yasa ta saukewa, wani irin shock ne ya ziyarcesu daga shi har ita, matseta yayi sosai a kirjinshi yace   answer me now kafin ranki y abaci bana son yawan magana  , ya fada idanunshi na sauka akanta da yake daidai kafadarshi don har tsakiyan kanta yana hangowa ahankali inadunshi suka sauka kan curly gashinta zuwa wuyanta dake dripping ruwan gashi zuwa tsakiyan mulamulan kirjinta da tudunsu suka buntsuro gaba, yanda ruwan yabi tsakiyan tsakannin bobbies dinta ya sashi saurin rufe idanunshi, wani irin sanyi da tsikar jiki na taso mashi tun daga makoshi, da sauri ta soma janye jikinta ta kasa, riko ya mata bana wasaba kamar za akwace mashi ita, kallonshi tayi anatse tace   let& & ..gooo of & ..me pls lebbanta ya zuba ma idanu ya rankwafo da kanshi daidai saitin fuskarta wani irin bugawa kirjinta keyi, nunfashinsa da breath dinsa mai kamshi mint na dukan nata dukta daburce, kwata kwata shes not confortable, jin saukar labbanshi daidai kunnenta da saukar zazzafan numfashinsa ya sata kankame gaban towel dinta sosai don kanta ya fara kwancewa, ?natse ya furzar da nunfashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login