Showing 237001 words to 240000 words out of 381117 words

Chapter 80 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2020

damuwa dukda baisan ma yanayi ba   are you okay?whats wrong with you 
Turo mashi bakinta tayi tace   babu komi, na dauka zan fadi ne kua ina tsoron kar bab&   saurin guntse maganar dataso yi tayi don saura kiris tace baby, shiko zuba mata idanu yayi yana sauraronta,.

Saurin zame jikinta tayi daga nashi ta mike da kyar   bari na kaarsa wankewa 
  no ki barshi  yayi saurin katseta
  ah ah bari nayi ay na kusa gamawa  .. sake katseta shima yayi bayan ya mike   I said noo, bana son gardama 
Yana kaiwa nan ya fuce daga bathroom din, yana fita itama ta futo ta dauki glass cup din data ajiye a gefe ta juya ta nufi hanyar futa ba tareda ta sake kallonshi ba.
Tana futa ya sauke wata nauyayya ajiyar zuciya, yana mamakin yanda heart dinshi ke racing sosai anan zaune don ba karamin tashin hankali ay shiga ba lokacin datakusa faduwa da yanda ta soma mashi kukan shagwaba don har cikin kwanyar kanshi yake jinta.

Tana futa ta wuce bedro??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????om dinta ta dauro alwala don an kira sallar magrib.
Tana idar da sallah salima ta shugo dakin nata, daga chan nesa ta tsaya   adda ki sauko muyi dinner inji ammah 
Dagowa amra tayi ta kalleta don tana shirin futa daga dakin   salima!! 
Ta kirata, juyowa salima tayi ta tsaya daga nesan don tun ranar da tace mata ta daina matsowa kusa bata son turarenta ta daina zuwa inda take.
  zo mana ya kika tsaya daga bakin kofa 
Zaro idanu salima ta danyi   inzo? Adda keda kikace na daina zuwa kusa dake bakyason kamshina dukda na daina saka turaren? 
Wani iri amra taji don bata ma san ta koreta ba harga allah duk sharrin tsirfan ciki ne,   sorry sweet sis, yi hakuri ki karaso, wallahi tsokanarki nake 
Tabe baki salima ta danyi ta kaarso har inda take zaune bakin gadon   uhm, ay ni adda lamarinki tsoro yake bani, kuma wallahi nasan akwa abunda kike boyemin bakyason na sani 
Hannunt amra ta rike ta marairaice   haba baby sis, yada fushi haka?,  
  eh mana dole nayi fushi ay, ni sometime inajin kamar bakyasona yanda kike sona ada 
Saurin toseh bakinta amra tayi   haba salima ki daina fadin haka, bani da waddda ta wuceki a matsayin yar uwa ta jinni 
  toh ki fada min meke damunki?, meysa kika sauya ba kamar da ba  salima ta tambayeta tana kureta da idanu
  zan fada maki amma ba yanxu ba kinji but wallahi I promise zan fada maki soon 
Rankwafar dakai salima tayi kafin ta danyi mata murmushi   toh shiknan muje muyi dinner kowa na zaune banda mu 
Mikewa amra tayi ta janyo dankwalin atamfar jikinta ta daura akanta kafin su fuce daga dakin, salima nag aba tana biye da ita don ahankali take tafiya don ammah na nanata mata lura da steps dinta musamman idan zata hau ko zata sauko daga stairs,

Da sallama suka shigo dining din, kowa na zazzaune, ammah amar aman da salim, dukkansu harsun fara cin abunci,   sannu daughter bismillah, salima zuba mata tuwo taci 
Zama gefen shi tayi inda ammah tayi mata nuni da idanu tayi kafin salima ta soma zuba mata tuwo,   adda wani miyan zan saka maki? Kuka ko egusi? 
  kuka  ta amsata kai tsaye don bata jin zataci wani egusi, amar dai bai dagoba tun da ta shigo dining din hankalinshi na kan abuncin da yakeci, hes trying so had to control and maintain himself.

Anatse kowa kecin abunci sai karar cokali, amra dai tunda ta fara da cokali taga kamar baya shiga tayi saurin ajiyewa ta wuce kitchen ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara loma, duk motsinta akan idanunshi harta wuce kitchen ta dago, saidai bai yarda sun hada idanu ba sabod idonta na affecting dinshi sosai yanxu, dan wani duk yanda ta lumshe su sai tsikar jikinshi ta tashi.
Suna gama cin dinner suka dawo parlor kowa ya baje ana hira banda amra da amanr da sukayi tsit sua zaune opposite din juna ita hankalinta nakan tv ma tana shan agwaluma idan anyi Magana takan dan jefa bakinta a cikin hira while shi kuma idanunshi nakan wayarsa saidai duk hirar da sukeyi yanaji and time to time yakan dan dago ya kalleta.

Salima ce ta maido dashi daga tunanin daya fada   ya muhammd gobe zamu gama exam fa kuma ranar Tuesday zamuyi graduation
Dan dagowa yayi ya kalleta   masha allah allah yasa asamu result mai kyau, and congratulation, wani gift kikeso 
Gyara zama tayi don a kasa take zaune ta tankwashe kafa   ya Muhammad digital drawing book nake so 
Da sauri amra ta dago ta kalleta tana mamaki kafin ta jefa mata harara,   shine baki fada min graduation din ba?
  toh ay adda kullum kina daki, idan nazo dakinki ma korata kikeyi shiyasa ni nama manta ban fada maki ba 
  ay shikenan saikije grad din naki ke kadai  amra ta fada ranta adan baci

Kallonsu ammah tayi tace   ayi hakuri yaya babba, mantawa tayi 
Sauke kai amra tayi tace   toh shikenan ammah, 
Kallon salima ta sakeyi ta gallo mata wata hararar   saboda ammah kawai na hakura 
Amar ne yadanyi gyaran murya, salima najin haka tace   sorry yaya, adda ta kaste mu, digital drawing board nake so 
  okay  ya amsa ta kai tsaye yana latsa wayarshi
Cikin murna salima tace   ammah ki tayani godiya thank you yaya 
  allah ya saka da alkairi  ammah ta fada tana kallon, kowa amsawa yayi da ameen,
  toh yarinyar kirki ni me kikeso na baki?  ammah ta tambayeta tana kallonta,
Hannu salima ta saka akan habarta tana nazari, amra dai bat ace komai ba tana sauraronsu aranta tana cewa   oh su salima an samu waje 

  ammah, basai kin bani komai ba, kawai inason ki kasance a wajen idan akazo bani certificate dina  salima ta fada tana murmushi
  toh shikenan dear sai kuma me kikeso?  ammah ta sake tambayarta yayin da take shafa kan salim daya kwantar da kanshi kan cinyarta   babu komi ammah na, wannan ma ya wadatar 
Dariya duk suka danyi, kafin a kalli aman,   toh su yaya aman me bazama a tambayi me za a bani ba 
Hararar ta ya danyi kafin yace   anqi tambaya din, 
Dariya duk sukayi gaba daya harda amra don inkaga yanda suke kamar wasu tom and jerry kwata kwata girmanshi faduwa yake idan har suna magana da salima.
Karfe goma daidai kowa ya fara waste wa, amar ne yafara mikewa,   ammah ina son coffee  ya fada baima tsaya sauraron response dint aba ya wuce bedroom dinshi, bayan tafiyarshi aman yayi masu sallama shima ya wuce kafin amra ta mike itama tana hamma,   ammah saida safe na fara jin barci 
Kallonta ammah tayi kafin tace    ki fara kai mashi coffee din saiki kwanta daughte 
  tohm ammah  ta fada kanta a kasa don kwata kwata bataso zuwa part dinshi ba don wani irin barci takeji sosai.
Sama ta fara wucewa ta watsa ruwa a gaggauce ta sauya kaya zuwa doguwar rigar bacci cotton wadda ta dan sauko mata har kasa don ta gifta gwaiwarta, sai yar hula data saka same color da rigar.
Tana gama shiryawa ta sauko kasa direct zuwa kitchen.

Kitchen ta wuce ta hada mashi lafiyayyan instant coffee sai kamshi ke tashi ta zuba mashi a cup ta futo daga cikin kitchen din, lokacin data futo duk sun wauce sama har ammah ta rage hasken parlor don haka kai tsaye ta wuce part dinshi, da sallama ta shige cikin bedroom dinshi kai tsaye bayan tayi knocking daya.
Tana shiga ta rufo kofar kafin ta juyo, a zaune yake kan gado ya rufe kafafunshi da duvet sai laptop kan cinyanshi yana typing cikin kwarewa sanye yake da pjs dinshi milk color, takowa tayi ta karaso inda yake zaune ta ajiye mashi gefen bedside   ga coffee din 
Bai kalleta bay ace   thanks  yana typing.
Juyawa tayi zata fita ya katseta   come back here  
Ya fada in a commanding way babu wasa, wanda yasa gabanta dan faduwa ta dawo ta tsaya dan nesa dashi   gani 
Banza yayi mata ya cigaba da aikinshi, saida ya dauka kusan minti goma yana aiki, ganin haka yasa ta zamu waje gefen gado ta zauna kusa da kafashi, saboda kafanta da baya juran tsayuwa.
Saida ya shafe awa guda yana aiki yana shan coffee harya gama kafin ya rufe laptop din, sai a lokacin ma yaji nauyi akan kafafunshi ashe hartayi barci abunta ba tare da snainta ba, ajiye laptop din yayi ya janye kafafunshi ya sauke su kasa ya mike tsaye, bathroom ya shige cikin mintuna kalilan saigashi ya futo, direct gaban switch ya wuce ya rage haske kafin ya kaarso bakin gado ya rankwafo ya gyara mata kwanciyanta gefe kafin shima ya kwanta dayan gefen ya lulluba masu duvet bayan ya masu addua& .
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited page
Kasa motsawa yayi daga tsaye da yake bayan ammah ta katse wayar, gaba daya baima gane kan zancen ammah ba kwata kwata, meysa ammah zatace yaje ya nemo waennnan abubuwan da baima sansu ba? Ya tambayi kanshi, dan shuru yayi tunawa da wadda tace tana son abubuwan, ranshi ne yayi mugun baci lokaci guda, may yarinyar nan ke nufi kenan? Saboda ya saukar mata yanxu shine take neman kawo mashi raini? Inba raini ba Har tana da guys din da zata hadashi da ammah? Wani abun ya sake tunawa kafin ya danyi yar tsuka ya wuce cikin motarshi azafafe, yana shiga motar ya kunna yayi reverse, already securities sun bude mashi gate don haka ya fusgi motar ya fuce da high speed.
Tunda ya hau kan titi ya rasa tunanin da zaiyi, babu abunda yake sai cije lebe yana tunanin kalaman ammah, Ina take cewa  Duk inda za kaje Ka nemo su na baka nan da 30mins
Haka ya dunga nanata kalaman ta a zuciyarshi yana tunanin meysa ammah ke bama yarinyar nan too much attention, yanxu abun Har yakaiga sai abunda take so za a sayo kuma ma babu wanda ta raina da zai sayo mata useless abubuwan nan sai shi saboda ta gama rainashi, and she s shamelessly asking for too much, shi kalaman ammah ne sukafi tayar mashi da hankali yanda take nanata mashi akan dole saiya nemo abubuwan da baima taba ganinsu ba baima sansu ba sai avocado kawai alya sani, haka nan dan dolenshi ya fara tunanin yanda zaiyi karshe sai gashi a wani babban grocery mall anan cikin guzape, yana karasowa yayi parking, saida ya danyi jim a cikin motar kafin ya fara kokarin tunanin abubuwan da ammah tace ya siyo, wayarshi ya fara janyowa ya fara kokarin browsing abubuwan,  what is agbalum ya fara searching, haka ya dunga browsing dinsu daya bayan daya yana duban sunayen su da turanci, yana gamawa ya fito daga motar ya saka dark shade dinshi don Ana kwala rana sosai, cikin mall din ya shige atsanake cikin kamewarshi,Duk wanda yazo wucewa cikin mall din saiya juyo ya kalleshi.

Kai Tsaye ya shige cikin mall din yabi direction din wajen groceries, yana zuwa ya dan tsaya yana duban wayanshi, haka ya zagaye wajen nan baiga ko daya daga ciki ba, yanda yake zagaye wajen shi kanshi mamakin kanshi yake, don saida yaga 30mins sun da ammah ta deba mashi ya kusa karewa hankalinshi ya Tashi sosai, wani attendee ne dake kula da harkokin kayan lambu a wajen ne ya karaso inda yake don yana daga zaune yana kallon yanda yake zagaye wajen,  good day sir mutun ya fada yana karasowa inda yake,kallonshi Amar yayi ganinshi da uniform din workers din wajen yayi saurin cewa  thanks
 Sir kana neman wani abu ne? Mutumin ya tambayeshi yana kallonsa,
Sauke glass din fuskanshi yayi ya kalli mutumin yace  yauwa, kunada uhm& agbalum, gunji and uhm&  ya dan tsaya yana nazari, Yalo
Dariya mutumin ya danyi kafin yace  yallabai Ay bazaka samu agwaluma anan ba da su data, saidai irin kan hanya haka,
Shuru Amar yayi yana tunanin wani kan hanya kenan,  inane kan hanya kuma? I mean wani direction kenan?
Gaskia oga bazan iya cewa ga inda zaka samu saboda yawanci masu baro ne zakaga suna yawo a hanya haka, abunda na sani shine bazaka samesu a presidential root ba saboda basa bin irin manyan hanyoyin nan
Kallon agogo Amar yayi ganin 30mins din ya cika, baima kaiga gama tunanin ba wayar ammah ta shugo wayarshi, cikin sauri ya dauka yakai kunnenshi,  Muhammad kana Ina ne? What s the meaning of this?
 Ammah please ina nema ne, nazo mall
Babu, Amar ya fada yana kokarin yi mata bayani
 Yanxu ina Ka taba ganin Ana saida irin waennan fruits din a mall? Kaje kasuwa fruits Ka nema, na baka nan da 1hr, Wallahi son karka bari na sake kiranka baka dawo gida da wannan fruits din ba, kuma duka zaka sayo mata karka bar ko daya
Ahankali ya soma magana  tohm
Bata ma amsa shi ba ta kashe wayar, sauke wayar shima yayi daga kunnenshi yana cije lower lips dinshi,  pack those avocados
Kallonshi mutumin tayi jin abunda yace  sir duka??
A harzuke Amar yace  yes all
Shuru mutumin yayi ya fara packing duka avocados sun wajen don yakai kusan katon kwado daya, saida ya fara weighing kafin ya daukar mashi suka wuce wajen cashier, tunda suka tsaya mutanen wajen suka bisu da idanu dashi da wanda ya dauko avocado din niki niki,,
Kallonshi cashier din yayi  sir 50k ne balance dinka
Ba tare da tunanin komai ba ya zaro wallet dinshi daga aljihun sa ya ciro black unlimited card dinshi ya miqa mashi, da mamaki cashier din ke kallon card din don bai taba ganinshi ba kafin yau I inserting cikin pos, yana gama payment ya fito wannan mutumin na biye dashi Har wajen motar shi, boot ya bude mutumin ya saka mashi uban tulun avocado din da sukayi mashi packaging a manya manyan kwalaye kafin ya rufe.
Cikin motar ya shige ya zaro kudi daga cikin dash board dinshi da baima san adadin su ba ya miqa mashi, cikin jin dadi mutumin ya karbi kudin yana godiya don kudin yakai kusan albashinsa koma yafi haka, yana bama mutumin kudin ya zuge glass din motarshi yayi baya da motar ya fuce daga mall din.

Haka ya dunga zagaye akan titi yana tunanin ko maybe zai ga masu sayarwa saboda mutumin yace mashi akan hanya ake samun su, haka ya kusa cinye Rabin awa, ganin yana Jan lokaci sosai gashi yana tsoron bacin ran ammah yasa yayi parking gefen titi ya soma dialing number asad don shi kadai ne abokinsa anan Nigeria.

Ringing biyo asad ya daga wayar tare da sallama, gaisawa suka farayi kamar yanda suka saba kafin amar ya danyi jim yace  Ina san zamu wasu fruit anan abuja?
 Wani irin fruit kenan oga? Asad ya tambayeshi
 Uhm Wai abaluma da data da guji da sauransu
Shuru asad yayi kafin yace  Toh fah, gaskia bansan inda ake samun su ba, saidai maybe fruit market Koh ya tsaya irin su hanyar waje wajen garin abuja zaka samu, yawanci dai nafi ganin irin Abubuwan nan a buari
 Ina ne buari? Amar ya tambayeshi
 Hanyar fita daga abuja, zaka dauka wajen awa daya kafin kaje wajen ,asad ya bashi amsa
 No it s urgent, Ina ne fruit market din? Amar ya sake tambayarshi
 Akwai a garki2, Ka duba map asad ya sake bashi amsa
 Okay thanks
 Zan zo gaisheda hajiya anjima da daddare  asad ya fada yana sauraron amsarshi
Kai tsaye yace  okay yana kaiwa nan ya kashe wayar ya bude map,

Yana saka wajen a map ya kunna motar ya hau titi a guje, haka ya dunga wuce motoci yana kutsawa Har yakai fruit market, koda yake da kyar ya samu Yalo da agwaluma nan ma saida ya saya kusan kwando kwando, kafin yayi payment ya koma motarshi hankali atashe, haka ya juya akalar motar ya bar wajen, haka ya dunga bin hanya yana fatan samun masu saidaga akan hanya, yana cikin driving kuwa ya hango wani mutumi yana tura baro, da sauri ya gangara motarshi gefen titi wajen da mutumin ke tsaye da baronshi a tsaye, sauke glass din motar yayi ya kalli mutumin  barka dai malam
 Barka yallabai
Kallon abubuwan da yake sayarwa yayi kafin yace  menene wannan kake sayarwa?
 Wannan gurji ne yallabai sai kwakwa
Hamdala Amar yayi ya kalli mutumin ba tare da bata lokaci ba yace  Nawa ne duka?
 Dubu goma ne yallabai ya bashi amsa
 Hada mun duka Amar ya fada yana kwaso sauran cash din dake cikin dash board din, baima taaya irgasu ba ya Mika ma mutumin, karba mutumin yayi kafin ya Mika mashi duka Gurjin da kwakwar  Nagode yallabai bismillah
Karba Amar yayi ya ajiyesu agefen seat din gaba, baima tsaya sauraron mutumin ba da yake cewa  kudin sun haura yallabai ya fuzgi motar yabar wajen.
Haka ya dunga zagaye, baiga wasu ba don haka ya wuce gida kawai jiki a mace, cikin minti biyar saiga shi a gida, yana shugo wa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login